← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 157

Sashe 114

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya bakin kkrinsa yay domin ahmed ya nitsu amma ina bai gane komi ba..he is teribly disturbed
Hawaye sun cika idanun shi kawai lallabashi banji ya dingayi dan ya kwantar masa da hanklinsa yace masa kar yay tunanin komi yabari harsai hanklinsa ya dan kwanta.

Suna katse wayar Banji ya kira brother hamzat ya gaya masa komi da ake ciki, sosai suka tattauna akai har suka dan samu wata mafita, daga nan baiyi kasa a giwa ba yaje ya samu babansu agida ya zayyana masa halin da Ahmed yake ciki da iyayen matarsa Adiaha.

After like 5 hrs bayan komi ya lafa Adiaha ta farka tay shiru taki yi magana da kowa banda hawaye babu abunda takeyi dan gani take kmr aurenta da Ahmed zai kare kenan na har Abada.

Abokinsa doc banky ne yake kulawa da ita, duk dama Ahmed bai bude masa komi ba but he later try to pacify her yace mata karta sake tunanin aikata abunda ta aikata dazu tana sanin cewa ba ita kadai bace ynxu duk abunda ya shafeta zai taaba harda abunda yake cikinta.

Har suka dawo gidan jimada Ahmed baice mata komi ba itama batace mishi uffan ba ta koma room dinta taje ta kwanta..

Shima koda yay sallah baije ko ina ba for the first time yay makansa Alluran barci dan kar yana tuna abubuwan da suka faru dashi yau da safe.

Haka ya farka da safe ya gagga miscals din baban sa dana brother hamzat dana banji.

Wanka yay mai gabaki daya ya shirya kansa cikin neat white jallabiya snn ya wuce masjid bayan idar da sallah ya biyo bayan babanshi suka dawo cikin gidan atare.

A falonsa suka xauna shiyana kasa baban nasa nakan doguwar kujera anan ne yake sanin cewa banji har ya fadawa babansa komi dayake faruwa.

Kai tsaye Ahmed ya fara ma baban nasa complain shidai gaskiya yanata sone ya samu wani hanyar da zai yaface auren nan ajikinshi ya huta maransa kawai.

Yana cikin masa bayanin yanayin yadda abun ya kasance saiga nan brother hamzat shima ya iso haka duk suka tsaya suka saurarashi har ya gama fadar ra'ayinshi akan auren.

Nasiha alhaj ya fara masa, akarshe yace masa babu wata mafita face ya cigaba da rike aurensa msmmn ma da Adiaha take dauke da juna biyu,yace masa sam bai amince masa akan daya rabu da Adiaha ba sabida tsoron yadda rayuwarta zai kasnce nan gaba.

Yace kawai ya hakura ya zauna da matarsan da zuciya daya dan baisan meyasa Allah ya hadasu a matsayin ma'aurata ba.

Brother hamzat ma yabi bayan Alhj bello suka cemai dolenshi ne kawai ya hakura ya danne komi ya zauna da ita snn maganan rabuwarsu kam bazai taba yuwa aynxu ba.

Haka suka zauna suka dinga surfashi da nasiha har saida zuciyarsa ta karaya ya aminta zai zauna da aurensan zuciyarsa a raunatace amma babu yadda zaiyi beside shine yaje har garin su ya lalumota he must just face tue consequences kamr yadda babanshi ya gama fada.

Ahaka aka kashe maganan sosai Adiaha taji dadi matuka da ta fahimce cewa su Alhaj bello sun judging case din ne on her favour.

Saidai ta lura kamr wana biyun nan Ahmed bai fiye samun nitsuwa ba dan da kyar abun ya wuce mishi aranshi ya kawar yafara concentrating akan aikinsa.

With the help of kiran da Banji yake masa akai akai yasaka shi yafara dawowa normal saidai yanxu bai fiye son shigar harkanta ba.

Kusan sati guda yasrah ta kara akan hutunta a lagos sabida ziyara da sukakaiwa yaya sadik dinta a gidan aurensa na can dubai..

Yasrah Suna dawowa nigeria washe gari ta kira Adiaha Suka gaisa suka danyi hira, Adiaha taji dadi sosai daya kasance gobene yasra zata dawo gidan cos ahmed is becoming boring yanxu baison sakewa da ita sosai.

Bayan sun kammala wayar ne ta fita ta duba shi sai batagansa ba da alaman ya fice.

Kyabe baki tay ta dawo cikin room dinta tana murmushi cos gobe ne cikinta zai kara watanni..

Tana shiga room din tafara jin fitsari kafin ta isa toilet taga wai har tafarayi ajikinta.

Hakan tay fitsarin ga yawa ga zafi tana kammalawa ta wanke kanta ta sauya pants snn ta fito da tunanin zata kintsa wajen daknta tunda gobene yasrah zata dawo.

Kananan aiyukan datayi na share share da goge gogen shine ya dan ja mata lokaci saidai kafin ta kammala tafara jin kananan cramps acikinta kamar yadda yake alama idan period din mutum zaizo amma dake bamai yawa bane kawai sai ta basar batasaka komi aranta ba.

Washe gari Ahmed ya shirya tsaf ya tarar da ita
Ta fito daga wanka kenan,suka gaisa ya tambayeta lafiyar jikinta tace mishi komi normal.

Anan yake sanar da ita cewa zaije lagos ya taho da yasrah amma idan bataga dawowarsu yau ba sai gobe da safe.

Nan Tay murmushi ta masa Allah ya kiyaye hanya..

After like 2 hrs bayan isarsa ya kirata awaya kusan sau uku bata daga ba sai can datazo ta nemeshi yake tambayar ta metakeyi tace masa tana dada kimtsa gidan ne sabida yadda yake shako numfashinta acikin wayar yace mata ta bari kawai zaice masu aiki suzo suyi ita kuwa gani take kamar aikin daya ragen babu yawa kawai saita karasa abunta.

Da wasa da wasa taji duk jikinta ya mutu tay mugun gajiya bana kadan ba sai ta dan kwanta.

Bacci ne mai nauyi ya kwasheta bata tashi farkawa ba sai kusan asr
Ahakan ma wani fitsari ne dataji ya matseta irin na jiya da gudu tabisa toilet dan karyau ma tay

Tana tsugunawa fitsarin ya fara zubo mata shaaa yana daukewa sai taga gudan jini ya fado.

Wani irin bugawa kirjinta yay ko inanta yafara bari
Babu shiri ta wanke jikinta ta nufi asibiti wajen nurse dincan domin ta dubata..

Hanklinta a makurar tashe ta isa wajen nurse din As usual anan ma aka gwagwada ba'a ga komi ba, Nurse tace mata ta kwantar da hanklinta inta kara ganin jinin gobe ta dawo xa susan nayi.

Acikin zullumi Adiaha ta koma gidan nasu cikin ranta tana son ta gayawa Ahmed abunda yake faruwa na bleeding saidai idan ta tuno da yadda zai dauki abun sai taji duk ta rasa karfin gwiwarta cos nurse tace it involves her abortion history.

Haka tay xaman dar dar tana ta monitoring din kanta har yamma yy sai ta dan fito waje shan iska.

ta dade tare da yaran su anty nurat da anty adizat kafin nan can taga kafayat ta fito tana waya tana kwashewa da wata iriyar muguwar dariya.

Tsit da yawu tafarayi tsit tsirr tana hura hanci dan wai tabata haushi.

kafayat tabita da wani irin kallo tana kada kanta tanamai zagayeta cikin watsa mata kallon kallo

duk ta dauka salon rainin wayo ne yasaka kafayat din ta zagayeta har sau uku snn ta ja tsaki ta kama gabanta itama tsakin taja mata

Kafayat ta wuce bata kula ta ba, Da yare kafayat din take magana awaya Har takai bakin motarta ta shiga ta bar gidan abunta ta wuce wajen mum dinta...

Haushin kafayat din taji ya gunnitseta haka kawai taja tsakin itama ta koma cikin gida..

Tunda ta shiga gidan sai takeji zuciyarta na tashi tarasa haushin kafayat ne data kwaso ko wani abu nadaban,gashi har yamma yafarayi Ahmed bai nemeta ba tasan hala sai gobe da safe ne zasu dawo...

Jin yadda jikinta yake sarewa yasakata tay bacci har saida aka kira ishai snn ta farka agurguje.

Tana shiga bathrum taga dison jinin akan pant dinta sai bai dameta ba

Haka ta cire tay sallahn magrib da ishai din snn ta neme abinci taci ta kara kwanciya.

Tun bayan isha'i Ahmed bai kulata ba kwana biyun taga yanason chating da abokansa bai nemeta ba har wajajen karfe 12 na dare lokacin tay bacci.

Wajajen 1:30 ta farka jin cikinta na kugi da wani irin sauri ta nufi toilet dan da alaman tana jin kashi kashi.

Tana cire pant dinta ta tsuguna tafara nishi nan da nan taji wani abu zuutt kamr an tsinka mata mara kan kace wani abu sai shaaa jini ya fara sauka daga kasarta.

Agigice ta mike tay kusan minti sha biyar cikin kaduwa take taji hanklinta ya tashi is like bleeding din wancan karon ne yake son ya dawo mata.

Ko bacci batayi ba haka ta zauna acikin zullumi asubahin fari ta bude watsap ta turawa nurse din hoton jinin data zubar yau.

Nurse na ganin jinin ta tsorata ta dora hannunta akanta da alaman Emoji na shock.

Adiaha is already devastated tafara kuka sosai typing take aiko mata babu kakkautawa tanata tambayarta ya zatayi a magance jinin nan tunkan Ahmed ya gano.

She kept lamenting akan cewa bata son ya sake mata irin na wancan karon cos she is still feeling guilty gani take kamar sakacinta ne ya jawo suka rasa first baby dinsu.

Nurse tace mata kawai ta shirya tazo ta sameta a asibiti su duba lamarin da kyau.

Safiya na gama yi Adiaha
Tay wanka ganin har yanzu jinin na xuba ta dadajin hanklinta na tashi sosai,sanitary pad kusan double ta saka, banda tea data sha ko Abincin kirki bataci ba tana ta sauri tasan duk tsiya yaune Ahmed xai dawo.

koda ta fito bataga kowa ba sai motocin matayen gidan dake parke motar kafayat ne kawai babu a tsakar agidan batama lura da hakan ba tsabar yadda takejin babu dadi

Hijabi ta saka ajikinta 8 na cikawa ta isa asibitin ta same nurse din aka fara dubata,yau din ma babu wani check up din da basuyi ba amma basuga komi ba.

Karshe nurse din ta yanke draw aranta tace kawai zata kaita wajen tsohuwar nan ai ranan tace mata zata iya taimaka ma Adiaha intaga dama.

Batadai gayama Adiaha abunda sukayi ranar da tsohuwar ba Amma ta umarceta akan in sunje ta zage tayita rokonta har inta kama tayi kuka duk tayi..

Ayadda Adiaha takejin nan kuma she cud do anything..

Da motar nurse suka fice tsabar sauri Adiaha ta mance da phone dinta anata motar wajajen karfe 9 Ahmed yayi ta nemanta amma bata daga ba .
Chapter 114 · 0% Book details