← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 157

Sashe 50

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta kammala kominta nan ta shirya kanta tsaf kamaar ba abunda yake damunta ta fito sanye da abayarta baki mai tsada ta nufi gidan wata babban kawarta hjy aisha mahmud dake can cikin anguwar maitama dan ta samu hutawa kadan.

Wajajen four Anty adizat
Ta shawo kwanan gidan a motarta ta kama string tana tuki ahankli kamr bazata kawo gidan ba.

Tun 10 am jirginsu brother kazim ya tashi yabar nigeria a airpot din ma duk kannensa sun mamayesa bata wani samu daman yimasa complain akan kudin datakeso ya kara mata ba barinma da taji hanklinta ya mugun tashi da motar da Ahmed ua bawa Adiaha agabansu.

Brother kazim bai kulata sosai ba harsuka rabu.

Batayi niyyar zuwa aiki yau kwata kwata ba amma dan tsabar ta samu wani daman yin munafurci da makrici yasaka ta nace akan cewa zatabi motar da su Ahmed suke ciki shida brother hamzat nan tace musu itama office zataje.

Sun fara tafiya kenan ko nisa basuyi ba ta fara tsoma musu baki a hirar sabuwar motan Ahmed da akeyi dake shi babban lexus mai wani irin kyau ya siya makansa, he had dis strong passion for big flashy cars wanda are extensively fancy and classy irin wanda duk inda aka gani sai anjuya an kalleshi dashi.

Brother hamzat yafi kowa yin murnan bawa Adiaha babban motarsa dayayi sabida shi yana sane da irin gulma da habaicin da matarsa nurat takeyi akan Adiaha.

Da biyu ya dinga gwada motar yana zancen agaban anty adizat yana cewa duk cikin matayensu Adiaha ce dama tay zubin shiga babban motar irin wanda aka bata sabida yarinya ce mai jini ajika.. he jokes very funnly about how Adiaha will behave as a slay queen harya fara tsokanar anty Adizat yana cewa ta tsufa kuma ai dama Adiaha itace yar autansu a mata.

Anty adizat tafara jin kamar zata hadiye ranta ta mutu a tsakaninsu.

Brother hamzat na caccaka mata baqar magana acikin wasa.

Ahmed kuwa sai cewa yake Matarsa bazata yi amfani da anything less ba na yayan baba ba, yace shine zai tsara mata komi nata yadda yakeso sabida yafison yaganta daidai da ajinsa..

Suna hirarsu cikin raha anty adizat data shaka saita fara dawo musu da amsa acikn sigar fushi ta fara musu borin da basu san kanshi ba..

Duk sunki kulata suka nuna basu gane metake nufi ,kushe adiaha takey sosai babu kunya a lamarinta..tabi tana kushe dalilin da AHMED ya bayar na bata babban mota.

Acewarta indai qa'idar girma za'abi itace za'a bata wann babban motar
Tana tukawa amma Ba Adiaha datake karama acikinsu ba, sai cewa take, acikin salon wayo akan Ahmed ya karba motarsa kawai ya siya ma Adiaha karamar honda ko mota mai one door irin solara din na.

Brother hamzat ya dinga babbaka dariya yana kara kumtsa mata takaici yana kushe tunaninta itama.

Ahmed kam bai saka abun aransa amma furucin dayake bata amsa dasu bakaramin ciwo yake mata aranta ba, daga ta kushe Adiaha sai ya karyata ya gaya mata cewa he trust his wife, yasan abun duniya bazai saka ta raina kowa ba, tay musu dashi hartazo tay shoru data gane cewa haukata kawai zasuyi inta cigaba da zancen da su. Haka suka rabo kowa ya nufi wajen aikinsa taje ma bata iya aikata komi ba tsabar takaici da haushi daya cikke mata kirji.

4ocl ta kama hanyar dawowa duk tay fayau kamr wacce tayi ciwon kwana biyu ga damuwar tafiyar mijinta ga kuma baqin kishin sabuwar motar adiaha da aka bata dazu ta kuma dawowa dashi.

Tsaki take yi ayayinda Take tuka Nata motar dake karamar CRV ce gaba daya taji ma ta tsani motar, ganin shi din ba komi bane agaban na Adiaha, wani irin tsinannen haushi takeji aranta gabaki daya ta rasa meyasa Ahmed bazai siyawa Adiaha sabon mota karama ba ba zai dauki babban motarsa mai kyau yar yayi mai class ya sakar ma matarsa Adiaha dan har gani take kamar ma da biyu yake musu wn abun ko kuma adiahar ce babban makira algunguma taje ta gaya masa suna mata gorin mota.

Tunda tay parking anty nurat ta leka suka hade ido da window, jiki na rawa ta fito ta tareta kamar wanda dama lokcin haduwarsun kawai suke jira yay

Dake izuwa lkcin gidan babu kowa nan danan suka bude chapter zancen sabuwar motar Adiaha a harabar gida agaban motar anty Adizat..

Da yare suke maganan amma kamr wanda suke cacan baki kowa na Allah Allah ya fidda baqar aniyarsa dake cinsa a zuciyarsa sosaai.

Anty adizat tace sam munafurtansu Adiaha takeyi kasaa kasa tana musu zagon kas awajen Ahmed tana sone ta kuresu da wayo.

Anty nurat kuwa tace sam maganin mata ne kawai amma bazata iya amincewa da cewa kuchakar Adiaha din nan zata fisu wayo agidan ba.

Lokcin Adiaha na can bangarenta tun bayan wayar da sukayi da sister zainab taji wani sabuwar karfin gwiwa aranta na zagewa akan aurenta da Ahmed.

Dan data kira Sister zainab sam bata yi wani doguwar tunani ba ta fahimce lugganta ba.

Normally kabila haka yake da nuna tsantsar son kai akan dan uwansa wanda a jininshi abun yake ammaa adiaha bata gane ba.

Hakan ne yasaka duk wani shirmen hirar da Adiaha tazo ma sister zainab yau da shi akan cewa zatay ababen burgewa dontana pleasing Ahmed a gidan, da mai kyau din, da marar kyau wanda bai kamata tay ba dan kar darajata ya zuba, duk sister zainab tace mata tayi, ta zuzzuga ta, dan gani take ai dan uwanta yay dersving mace ta bauta masa haka tunda kudinshi yake kashewa akanta. aranta cewa take Adiaha bazata ci kudin dan uwanta abanza ba so if she wish to worship him so be it..

Adiaha kuwa daman abunda take so taji kenan cos dats what is in her mind to spoil the spoilers out of him,yau tayi tunanin dik wani kkrin da zatayi wajen maidashi dan lele, mijin ta mijin gwall, sarkin zuciyarta mai takalmin karfe.

Yau ta zage ne tayi masa hadaddun girki kala kala na zamani ta jerasu akan dinning komi yay tsaf.

Bayan nan wani irin wanka taci, tayi kwalliya ta saka dammamen blue jean da crop top fari kal ta gyara suman kanta da da gel da coils looking like a queen ta shafa jan jambaki yay madau.

She was quiet feeling her self as big madam har yanzu lamarin motar nan na sakata cikin nishadi marar misaltuwa.

Ta kammala komi kenan ta taho cikin falonta ta dauki remote zata kunna Tv ta kalli nigerian music tama zama kenan taji ana bugata mata kofarta..

Tsaki taja kasar wuyarta ta bata rai bata wani kula ba dan tasan ba Ahmed dinta bane ya dawo a dede wann lkcin snn koma waye ne tasan is an unvited quest..

Jin an ki a dena bugun kofar yasa ta miƙe a mugun kasale, fiskarta ba a sake ba ta aje remote din agaban center table ta mike tanamai mai gyara zaman rigarta da suman kanta da yay mata kyau tafara takawa anhkli tana tafiya tana juya manyan duwaiwakanta acikin damammen jeans din daya hasko shape dinta ga wani irin shegen heels din data saka akafarta wanda yakesata take tafiyar yanga sosai.

Da can Harta mika hannu zata bude kofar kai tsaye sai wani basira yazo mata ta dan leka ta bakin window, zuciyarta ne yay tsalle dataga su anty nurat ne awaje kowacce ta hade rai suna magana kasa kasa da yarensu

Kara murtuke fiskarta tayi snn ta lumshe idanunta dan ta kore tsoronsu dayake yawan mamayeta. Ji take kamr ta fara tafasa ata ciki, babu dai wani abunda ta rasa ynzu da za'ayi mata gori is better ta fara nuna musu true colours dinta.

Ajiyar zuciya ta sauke cikin tattaro makanta karfin gwiwa snn ta bude kofar ta zuba musu idanunta akansu dukansu biyu.

Uffan bata ce musu ba ganin suma itadin suke kallo, wani irin kallon kurilla suke bin jikinta dashi ganin yanayin shigarta mai kyau anty adizat ta juya ta kalle anty nurat suka wani irin kyabe bakinsu atare.

Haryau mamakin inda Adiaha taje ta samo hadaddun kayan datake sawa sukeyi.

Fuska ba yabo ba fallasa Adiaha tana dada gyara tsayuwarta dakyau cikin sigar shashantarwa tace "Anty nurat, anty adizat
Gud evening ashe kune kuke buga kofa na dauka ma yara ne.

Anty adizat tace haaaa karki wani mana kerya, wani yara kuma? Jikin Adiahan take kalla tace Just admit dat mijinki Damilare kike tsammani shiyasa kika fito ahaka.

"looking like a prostitute"
Anty nurat ta katsesu da muryan gatse ta yaɓa mata maganan a fuska.

Adiaha ta kyabe baki tay kyam tana kallon idanunsu sunata dariya ko ajikinta bata nuna taji haushi yau kamar dacan ba.

Hakan yasaka suka tsagaita dariyar tasu

Anty nurat tace No offence, im just saying just look at you ...

Adiaha tay mata wani irin kallon rainin daya sakata yin shiru sai bata kara magana awajen ba.

Sigar bugan ciki Anty adizat tahau murmushi tana kkron jawota wajen gaban sabuwar motar tanacewa nurat kigani fa karuwancin irin wann is good oo,bakiga reeema har ta saka damilare a hammatan ta ba, no wonder he gave her his big car. Congratulasion once again iyawo dami.

Adiaha ta dago ido ta kalleta tana shafa kan motarta sigar dada basu haushi, a dan dakile tace thank you,...So, How can i hepl u ppl? Cos As u can see Mijina ya kusa dawowa bana son yazo ya ganni awaje, ta dada gyara zaman rigarta a kisinance kasa kasa tana cewa kwalliyata mashi kawai nayi yau bana son na batashi anan.

Anty nurat tabita da harara so all this yangan kwarkwata dakike mana sabida ansaya maki mota ne komene?

Adiaha tace yes anty waye bazai murnan motar ba..ta yi dariyar kashe aure irin wanda bata tabayi agabansu ba.

Anty nurat bakarya Im feeling myself today.
Check my car out latest
Dbx jeep tafada tana shafa motar agabansu

baki bude anty adizat tace Oshey mumu girl..tsofuwar mota ma kina mana yanga akai?memakon kice ma dami ya siya maka sabo dal,
Chapter 50 · 0% Book details