← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 157

Sashe 24

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sassanyar muryanta ne ya firgita tanamaicewa
"REEMA lapiya kuwa?
Saurin dawowa hayyacinta tay snn ta karaso kusa cikin ladabi ta aje abincin akan table tafara gaishe ta.
"Gud morning momy...kin tashi lapya?

Murmushi mai sanyi tay mata ganin yadda kayan jikinta yay mata kyau tace lapiya kalau ya kuke? Ahmed ya tashi kuwa..i hope he is fine.

Adan rude tace A'a, sai kuma tace ehh. dan tanajin mugun tsoron yin wani magana kar Ahmed yazo yaji yay fushi yace tanason ta hadashi fada da mahaifyarsa yabi ya koreta agidansa ta shiga uku.

Nan tay saurin waskewa tace Mumy he is fine ainasan bada jimawa bama zai zo ya gaisheki he might be sleeping.

Tace its okay.
Hannu takai ta bude abincin ta kalla snn ta rufe ta juyo kanta tana kallonta Kamr wance take karantar zuciyarta babu yabo babu fallasa tace kinyi kokari sosai Harkingama rabawa kowa nashi abincin kenan?

Boyayyar ajiya Adiaha ta sauke cikin sann ta fara sum sum da fuskarta cikin i ina tace a'a mumy bankai ko ina ba..sai tay shiru..kanta ta sauke kasa snn tace mumy i wanted to ask u Nace since daddy is back tayaya ne zan kai musu abincin acan.. ko zan aje ne harsai kafayat ta fito

Hjy khadijatu tay karamin murmushi tace kafayat kuma reema? Why wud u call her by her name ?A'a, Karki kara furta haka kinji babu kyau raini.
Kidanga tuna cewa Matsayina da nata duk dayane agidan nan, she is also ur mother inlaw kisan abunda zaki dinga kiranta dashi kinji?

Politely tay mata maganan wanda yasaka taji takara respecting dinta aranta sosai.

"Am sorry mumy, in sha Allah zan gyara.

Tace its okay.
Amma gameda tambayarki gaskiya bansani ba saidai karki je musu sashensu gatsau haka kinga ai amarya ce shikuma surkunki ne akwai kunya ai ko? To tunda yana tare da amaryansa i will advice you ki aje musu abincin akan dinning table na falon baban naku saiki fita kibasu waje. If ure comfortable with that sai kullum kina aje musu awajen.

Adiaha taji dadin shawarar aranta ta dago kai tana murmushi tace nagode momy.

Tace toh ki tashi kije kar lokaci ya kure maki

Cikin girmamawa ta mike Tanamai cewa toh snn ta fita acikin sauri.

Ganin lokci yaja yasaka tay Sharp sharp ta raba abincin takai sashen su
Anty nurat da anty adizat as usual saida suka tsoneta da sukaga ta sako kayanta mai kyau sosai yau.

Hakan bai dameta ba taje ta hada nasu kafayat din takai musu kan dinning na sashen alaji bello, ajiyar zuciya ta sauke da bata ga kowa awajen ba, ta kammala jera musu abincin zata juya kenan taji an kamo hannunta ta baya.

Abazata ta juyo cikin tsinkewar gaba suka hade ido da kafayat ta sako kwallin sihirinta yay madau acikin kwayar idanunta.

Wani irin kisinnniyar kallo ta dinga yiwa Adiahar ganin babu wani abun aibu ajikinta ayayin da Adiahar ta fauce hannunta da karfi anatan batare da tace mata uffan ba, Ta juya kenan zata wuce tajiyo muryan ta abayanta tana cewa kin dauka na tafi na bar miki gida ko? Toh I am back for you..u better be ready.

Adiaha batace mata uffan ba ta kada kanta ta tafi tabarta awajen tanamai bin bayanta da kallo jin tsananin kishin adiahar na ratsata kamar tabita ta shakure mata wuya haka ta dingaji aranta.

Bayan dan wasu lokuta lokacin duk yayan alaji bello sunzo sungaida hjy khadijatu daga nan suka kama gabansu batare da zuwa sashen uban nasu ba, nan gidan ya dauka da wani irin shiru kamar babu kowa aciki.

Daga bangaren Alaji bello kuwa jiya baima samu bacci sosai ba sabida yawan tunani gashi kwana biyu frustration yana masa yawa bayashan maganin hawan jininsa akan lokaci, sai wajejen karfe 10am saura na safiya kafin nan ya farka ya fito falonsa ya same Kafayat dake sanye da wata tsinannen jan nity shararra wanda ko ina ajikinta yana nunawa tana kwance duk lissafinta shine yaran mijinta zasu shigo gaishar da ubansu sai tay iskancin data ga dama agaban idonsu da ubansu danta cusa musu baqinciki.

Tana kallonshi tay masa wani irin karuwar signal da kwallin dake idonta tare da wani kisinanniyar juyi tanamai kwaye masa malamalan cinyoyinta.

Tunda ya kalli kwayar idonta yay tozali da kwallin data shafa duk sai yaji ya susuce jikinshi na rawa ya fado jikinta rigijib yafara sumulmukata yana lasheta kamar kare.

Ahaka har suka rikito kasa tanamai juya harshen ta acikin nashi cikin kwarewa duk ya zauce ya kwaye mata nityn babu marabanta da tsirara Sanda sukayi mai isarsu snn ta tureshi tare da umartansa akan suje suci abincin safe.

Awajen cin abincin tafara kawo masa salon zugi na cewa yayansa basuzo sun gaishesa ba sun rainashi sosai tace masa kawai ya dauke mataki akansu sabida zugasu akeyi akansa dan anajin haushinta.

Tsabar tasirin sihirin dake idanuntan datake kallonshi dashi yasaka Baima karasa cin abincin ba haka ya tashi zumbur jikinshi harna rawa ya fita nemansu har waje yaje aka ce masa ai duk sun tafi wajen aikinsu tuntuni..

Yana dawowa ciki yazo ya samu kafayat tana tsaye a tsakar cikin falon gidan itama harta fito daga bangarensa sanye da tsinannen nityn nata bata daura komi akaiba.

Tun bai karaso ba tabishi da Da wani irin salon karairaya da fitinannen shagwaba tanamai cewa my darling baby daddy meyafaru kuma kake bata fuskanka? Ya turo bakinsa gaba kamr soko
Yanamai cewa can u imagine wai yaran nan duk sun tafi office basuzo nan sun gaisheni ba?

Cike da tsaurin ido Ta bata rai snn tace baby kai kadaine zasu gaisher nifa?nida nake uwarsu na dawo gidan nan ma basuzo sun gaisheni ba..hmm ai Banga laifinsu ba oo, ai kaima munafukine kasan wacece muguwar da ta hanasu suzo su gaishenin ai..ur wife is the one creating all this troubles kamata shiru kamar kanajin tsoronta.

tun bata karashe maganan ba cikin tsareta yace ahhhhh ure right let me go and deal with her..

Aharzuke ya juya cikin sauri ya nufi bangaren hajya khadijatu kafayat tafara binshi abaya tana baɓɓaka masa dariyar mugunta kasa kasa ayayin datake binsa abaya....[6/8, 10:33 PM] SURAYYAHMS: kusan atare suka isa kofar sashen hajiya khadijatun sunakaiwa bakin kofa kafayat ta tsime taja ta tsaya agefe tare da daure fuskanta nan ta umarce shi akan shiya fara shiga daga ciki.

Kai tsaye ya tura kofar sashen nata babu wani sallama fuskarsa a mugun daure ya shigo.

tsayuwar cak yay mata a tsakar falon yanata kallonta kmr wani wanda bai taɓa kallon ta ba,she look utterly beautiful as alwys dan farar sol din bafulatanace datake da wani sulbabben yellowish smooth skin mai shegen sheqi, gata da baki kuma doguwar suma marar cika sosai ta gyarashi tsaf ya wani kwanta abayan kunnenta izuwa kafadarta yololo dashi.

wani hadadden shadda lace ne a jikinta royal blue ta shafa light lip gloss akan lips dinta dayaketa ta glowing yana kyalyali,duk da tasirin sihirin dake dawainiya dashi koda ya kalleta sai da yaji dukkan tsikar jikinshi sun tattashi ya rasa gane ina hanklinsh yake, atake ya nemi zuciyar masifar dayazo mata da shi din ya rasa sabida wani irin kwarjini dayaga tay masa bana wasa ba.

Kallonta ya tsayayi lokcin hanklinta yay nisa akan abunda takeyi bata wani hankara da shigowarsa wajen ba har saida yay gyaran murya maidan karfi.

A Firgit ta dan dago kai sabida razanar datay suna haɗe ido dashi tay saurin dauke nata anashi
Shikuwa sai kallonta yake yi kmr zai hadiyeta

Kafayat dake dan lekosu har mamakinsa ta dingaji aranta.

gaban hajiya khadijatu ne yay mummunan faduwa taredajin wani irin takaici da tsinannen bakin ciki da kuma haushinsa na mamayeta..

ahankli ta lumshe idanunta snn ta bude cikin kwaro ma kanta karfin gwiwar fuskantar sa.

Yadda ya zuba mata ido yay shiru itama hakanan ta ɓata ranta tay masa shiru tanamai cigaba da karanta email din datay receiving akan screen na computerta. Dayaga fuskar matarsa sai Duk ya susuce ya daburce.

Basu san daga ina kafayat ta fito ba kawai ganinta sukayi wai harta shigo cikinsu tanawani cika tana batsewa. Ita ko lokcin kallonta ma batayi ba.

Takaici ya gama gume kafayat ta dubi alaji bello jin kamar ta kasheshi tana Allah Allah ya kalleta dan son ta bashi zazzafar ido da charm din sihirinta, da yare tay masa magana sabida nauyin hjy khadijatun datakeji aranta.

Tace masa alaji bello lallai ka cika babban munafuki, wato Abinda nace maka kazo kayi anan kenan ko ka saya kamar soko kana kallon tsohuwar matarka? Tsohuwa ma wai dame tafini ne?

Ya juya ya kalleta kamr soko din dagske yace kafayat wai me kike ce nayi ne ni namanta fa..

Ranta a mugun bace ta maimaita masa Abunda tace masa yay, nan da nan ya tuna ya juyo kamar wanda ake juya brain dinshi da remote control kusan a rude yace "khadijatu", khadijat, ki kalleni mana iya dami, i am talking u,wai meyasa bazaki amsani ba?

Kanta na kan computerta cikin shan qamshi sosai tace "me kace?.

Ganin yadda ta basar da shi yasaka Yafara mata masifa irinta borin kunya, yafara cewa yaranki sun dena gaisheni yanzu i demand sum explanation from u, ta inda yake shiga batanan yake fita ba,cikin mitarsa yafara gaya mata zafin dayaji aranshi da yaransa suka koreshi agidan, snn basu taba kiranshi a waya ko sau daya ba kuma jiya suna kallonshi sukayi ignoring dinshi basu gaishe sa ba. Sai babatu yake mata yana hargagi yanamai cewa itace ta lalata masa tarbiyan yaransa.

Da ikon Allah kuwa tana cikinsun amma kuma duk batajin wani shirmen dayake fada matan dan all she can see is a lost creature blabbering Abun tausayi dan shikansa kawai magana yake amma bai san meyake fada mata ba.

Yara nawa ne, gidan nan ba naki bane ure not the boss here ..Ki gaya musu oo, they have to respect me and my kafayat. Kinji ko? Khadija am talking to u ooo,pls dont ignore me.
Chapter 24 · 0% Book details