← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 157

Sashe 79

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

For the main time yau sai ta sauko sosai ta fara masa ladabi dan in akwai abunda take mutuwar tsoron ji arayuwarta toh kalman Ahmed zai koreta ko zai rabu da ita ne.

Ta yarda ta rasa ranta sau dubu akan data rasashi, tun safen ta fara shirin tarban yasra,cos she knew she just have to make peace da zancen zuwan sistersan nan kawai intana son kanta da lfiya.

Ata fannin su yasran kuwa yau tun bayan sallahr asubahi da suka farka babu wanda ya kara komawa bacci,kowa agidan shirin tafiyarta nayau din yakeyi,dan hjy maimunta ta iso hardasu din duka zasu rakota har Abuja saidai su aranan zasu kaita su dawo.

Knocking taji anyi Abakin kofa tana juyawa taga mai aikinsu ne ta shigo dauke da wasu kayanta data shiryamata zasu tafi dasu acikin jakka, ta tarar da ita tana kan saka kayanta ajikinta tace mata har yanzu baki gama ba karfe 8 fa ya wuce jirginku is taken off by 10.30 dot.

Ba yabo ba fallasa tace karki damu yanzu zan gama shiryawa, aje mata jakar kawa tayi ta fice,jim kadan sai gata ta sauko cikin wata kankararriyar atamfa babban super wax red colour da pattern in milk ajiki dinkin ya mata kyau sosai,riga da skirt ne peplum blouse mai donut three gtr hands sai Dan kunne da abun wuyarta masu kyau na karamar gwal hannunta sakale da agogon kamfanin zara duk dama tana da tsayi amma tasaka heel sandals akafarta marar kara, a hnkli ta jawo sauran luggages din kayanta zuwa bakin kofa tare da dan mayafinta dake famar lilo agefen kafadarta, saukowa tayi falo taga iyayen nata kowa ya shirya cikin shigarsu ta alfarmq sunata cin breakfast dinsu hankli kwance.

dan guntun murmushi ta saki da suka hade ido da dasu duka ganin yadda tay kyau sosai data saka atmfa.

karasowa tay tazauna cikinsu tana mai kara gaishe su cikin ladabi atare duka suka amsata tayi bismilla tafaracin abincinta ta nitse har suka kammala sunata mata nasiha mai shiga ciki.

9.30 suka firfirto driver ya jibga tulin kayan yar gata da suka tarkato dashi a booth sann suka kama hanyar airpot din atare

tun ana saura minti goma jirginsu ya tashi yasrah tafara taro ruwan hawaye a idonta addua ta dingayi har sanda taji fargaban datakeji aranta ya ragu mata sosai.

Karfe 11.30 dot suka iso garin Abuja Already driver daga gidan jimada yazo har airpot din yana parke yana jiran su,sai motar Ahmed shima..

Tun saukarsu jikin yasra yay sanyi sabida wani irin bugun zuciya datake fama dashi aranta wanda batasan daga ina ya fito ba.

gidansun direct aka wuce dasu aka saukesu suka firfito already Adiaha har ta riga ta shirya tarban su anyi girke girke da sauran tsare tsare duk dama ba awajenta suka soma sauka ba.

Ta window ta tsaya tana lekensu ayayin da suke shigewa main building da alaman wajen alhaj bello zasu fara isa.

kirjinta ya buga daga nesan yafi sau tamanin dik sai taji ta kasa zama tun kafin nan ta hango yasrahn dakyau ta daburce, sai can ta hangeta tana tafiya kussa da hjya kahdijatu shikuma Ahmed din nata na tare da anty dinsa abaya suna tahowa,.

koda ta tsaya cak tanamai kare mata kallo daganan taganta sai dataji jiri jiri na neman kwasarta izuwa kasa, neman waje tay ta zauna tare da shan ruwan sanyi cos she just wonder how dis beautiful lady beyond words is going to live with her, cos she is struggling hard to accept acikin zuciyarta cewa tsakaninsu da Ahmed zai kasance alakar yaya da kanwa ne na har abada..
#Sai bayan sallah..ayi ibada lapiya yan uwa.
[7/1, 8:00 PM] SURAYYAHMS: Kusan Kowa ya hallara cikin babban falon gidan jimada Adiaha ce kawai bata samu daman bayyana a wajen ba sabida ziriya na anxiety daya tutseta a sashenta tana ta jeka ka dawo cikin tsananin tashin hankli ita daya batare da tasan nameye ba...

Tana cikin wann yanayi wani Nannauyar ajiiyar zuciya ya kufce mata tabi ta lumshe idanunwanta tay tsamm tuna tunda can bata da wani matsala da zaman yasrah a gidanta amma batasan meyasa yanzu takejin gabaki daya batason faruwar hakan aranta ba.

Neman waje tay ta zauna ahankli cikin sanyin jiki tana kkrin dawo da kanta cikin hayyacinta na karfi da yaji,she was like how and why is she feelng this so much insecured bacin tasan idan har ta fadi wnn ra'ayin nata ta zai iya jawo hatsaniya wanda shi zai kaiga karshen zamanta a gidan Ahmed din gabaki daya
Sam ta kasa fahimtar kanta..like who is doing this to her Wayene yake sakata yin irin wayann tunanin dan dai tasan ba haka take ba,kai dolene ma da da akwai abunda yake son yay amfani da hakan wajen ruguza mata zaman aurenta nan ta shiga tunowa da magananan tsohuwar can na cewa iyayenta ne suke son rabasu, cikin sauke ajiyar zuciya tabi ta lumshe idonta ahankli tana huci mai nauyi jin kamar ma sihiri aka mata dayasaka take misbehaving kwana biyun amma bawai dan tsananin kishin mijinta datakeji aranta.

Da kyar dai ta danne zuciyarta ta kwakwalo makanta wata sabuwar nitsuwar kafin nan ta tashi ta nufi gaban madubi tadan kimtsa kanta sosai tadan gyara fuskarta da powder ta fito domin zuwa can cikin main mansion din inda suke tare. Tafiya take ahankli kirjinta na bugawa da sauri sauri.

Dagata cikin mansion din kuwa suna shiga Ahmed ya wuce dakin babansa domin fito da shi waje duk da baiyi niyyar fitowa aransa ba amma jin ance harda matarsa khadijtu a falon yasakashi jin wani irin zumudi da rashin iya dauriya dan yay matukar kewarta aransa bana wasa agidan ba, wata farar jallabiya ne da hula ajikinshi duk ya rame yana tafiya yana tuna cewa tun bayan tafiyarta banda yayansa dake kiransa akai akai sun dan dubashi bai sake samun wani kulawa daga wajen kafayat din ba dan yanzu tamkar zaman kanta takeyi agidansa bata ma kulashi.

Hakanan ya fito waje cikin falon da dan rawan jiki a kwayar idanunsa, Anan ya tardasu lokcin hjy maimunatu tare da hjy Khadjatun duk sun samu mazauni,idanu suka zuba masa har ya nemi waje ya zauna duk dama baiwani sake musu fuskansa sosai ba Ahmed ne ya zauna a kasa kusa da inda yake snn Brother hamzat yay zaune a dayan bangaren shima, Yasrah na zaune acan gefe kusa da hjy khadijatu kanta na kallon can can kasa bata iya dagowa kai sama ta kalle kowa ba dan dake yau asabar ne kusan kowa yana nan, hatta su anty adizat da anty nurat duk an hallara duk dama kusan idanunsu naga kan kowa ne ba zallan ita kadai ba.

As usual acikin girmamawa da ladabi duk matayen gidan suka rusunna suka gaishe su snn suma suka gaisa da alhaj bello jimada bbu yabo babu fallasa ya amsa su cikin salon mutuntuwa daga nan hjy khadijatu batace mishi komi ba duk ta lura ota kadai yake satar kallo, ji yake kamr baya cikin hayyacinshi ganin yadda ta karayin kyau ta murje tay wani irin haske duk alaman bata cikin wani damuwar rashinsa ya bayyana masa ayanyinta bayan shikadai kawai yasan wahalar zaman dayakei agidansa yanzu.

Shirune ya cigaba da ratsawa a tsakaninsu cos each time sai yay nitsu acikin nazari da tunanin abunda bokarsu anty moju ya gaya masa akan matarsa khadijatu yau akaro na farko daya samu jin kokonto.

hjy maimunatu ce tay gyaran murya cikin katse masa tunanin zucinsa, da can har zata tafara masa magana kenan sai ganan kafayat ta fito tana wani taunar cingam kas kas, sanye take da wata matsattsen riga da wando tabisu da wani irin kallo snn ta ja ta tsaya acan gefe daga nesa tanamai kare musu kallon jin tsananin takaicin ganinsu a gidan nasu duk kirjinta yahau bugawa yana mata zafi zuciyarta yanamai hura mata wuta a tunaninta ko dawowa da hjy khadijatu dakinta akayi ganin irin kwalliyar datayi ta zuba kyau kam kamr wata amarya farin leshi mai ruwan gold ta saka tabi ta yafa wata arniyar swvroski sequence veil mai azabar tsada batama kallon ta inda take bare abun ya dameta.

Haka ta zuba musu ido daga can ko uffan ba batace musu ba, Karkada kafafunta kawai take da alaman jira kawai take taji ance dawowa hjy khadijatu zatayi gidan ta tada wani irin rikicin da bazai iya kama hanklin kowa acikin falon ba.

Atake aranta tay alkwrin cewa babu mai zame mata cikas akan plans din ta na nan gaba domin kuwa saura kiris ya rage komi ya fashe game da abunda ta kulla akaan auren Ahmed da Adiaha jira take itama domin ta fara cin moriyar dukkanin abubuwan da ta shirya.

Yanayin kafayat awajen sosai ya sosawa hjy khadijatu ranta dan haka kawai jikinta ya soma bata cewa yarinyar tana azbtar da mijinta alhaj bello duk dama she care less abt that right now saidai tunda suka hada ido dashi taji kamr ma tausayi kawai yake bata dan ya rame yay fayau kamr bayacin abincin snn bataga alaman nitsuwa ko kadan ayanayinsa ba hakan yasaka taji sam batajin dadi aranta ko kadan.

Nan hjy maimunatu tafara ma alhaj bello magana gameda da abunda ya kawosu duk dama yasan ba neman izininsa sukeyi ba dan yasan sunada iko akan Ahmed din suma amma yaji dadi aransa sosai da suka darajasa wajen sanardashi yuwar komi personally and formally.

Hakan yasaka bai biye ma karamin fushi da takaicin rashin matarsa a gidansa dake damunsa ba kawai yay hkra ya dan sake musu fuska akan zaman yasrah a hannun Ahmed atake ya amshe abun hannu bibbiyu shima.

Nan hjiya maimunatu tay using styles tafara gayawa masa kalar gatan da suka bawa rayuwar yarinyar da wansa suke shirin bata nan gaba wanda ya saka su anty adizat kallon junansu ita da anty nurat suna masu kyabe baki jin abunda yafi karfinsu.

Alhaj bello Ya dubi yasrahn yanamai sam barka da ita dan duk sai yaga tana mugun kama da matarsa hjy khadijatu dan hatta farin fatarsun irin dayane tareda pencil nose dinsu da dan karamin hrt shape lips dinsu snn ba sai an gaya maka tana da suma ba kallo daya zaka mata kasan fulanin usula ce mai sulbabben fatar jiki.
Chapter 79 · 0% Book details