← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 157

Sashe 77

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun idarne yake gaya mata cewa ya duba yaga hawan jininta is now stable dan haka zata iya fita tana zuwa shagonta wai duk yana hakan ne sabida ta kwantar da hanklinta sosai kar wani abu yaje ya samu cikin.

Har yaran shago wanda ya aminta da su ya samo mata wanda zasuna mata errands basai tana stressing kanta wajen handling din wasu abubuwan ba.

She was happy yau atleast zata dan leka waje itama, ko wani baccin safiyar yau din batayi ba tana Allah Allah safiya yagama yi ta shirya tace taga shagon dayace yagama kammala mata komi aciki.

Tun 7.30 ya fice aiki ita kuwa bata fito ba sai can
wajajen 10 am yau ta daure taci kwalliyar big madam ta sako doguwar riga na atamfa an mata dinkin bubu ta yafa karamin mayafi.

Acikin tattali take bin kanta harta isa gaban motarta zata bude kenan aka bude kofar gidan tana daga kai taji gabanta ma faduwa sosai

Motar kafayat ta gani har ta karasa parking bara dena kallonta ba ganin yadda take kallonta kallon kurel tare da mata wani irin shuumin murmushin mugunta..

Tsaki taja batare da ta kulata ba tay sauri ta shiga motarta tabar gidan ta wuce shagari complex ta kama aikinta

Within few days sashenta a shagari luxury complex ya zamo wani abun kallo tsabar haduwar shi dan an kashe masa nera bana wasa ba,nan danan Adiaha tafara taji Rayuwar na bala'in kaimata ga manyan mata awajen na zuwa suna mata cinikin jewries dan ta iya kasuwnaci sosai.

changes of character sosai ya fara nunawa atattare da ita ta dawo tanajin kanta itama kmar sauran mata, duk wyan rashin manners wajen magana na matan masu kudi itama ta koya duk ta dauka shine yasa ake bibiyar shagonta yadda komi yahau tafiya mata akan sa'a kominta na wucewa daidai abun sai yay balain shaking dinta.

Jitake kmar She is at peace now bbu wani abunda yake sha mata gaba, musmmn ma da yanzu Ahmed ya kasance busy at his work sai dare yake yawan dawowa duk dama he is doing his best wajen kulawa da ita sosai tamkar bashidin data sani dan walakanci ba.

Abu dayane haryan yake kulle mata kai wanda shine yanayin kafayat agidan dan tun dawowarta wata kalma bai shiga tsakaninsu ba dan kwainanen cikin datakeyi atsakar gidan sumtimes danta bawa kafayat haushi sai taga ko gizau baya taba kafayat saidai ma ta dinga mata murmushin da haryau bata isa tace tasan fassarar wann wicked murmushin ma kafayat ba...
[6/27, 1:29 AM] SURAYYAHMS: Wann sudden weird gestures na kafayat din sosai yake jefata cikin tunani,tun tana tunani akai hartazo ta fara sharewa gabaki daya dan gani take kamr kafayat bazata taɓa iya mata komi ba dan ayanzu kam itama babu wani abinda take nema wanda bata dashi. Duk wani abunda matayen gidan suke baza taƙama da shi itama yanzu tana dashi.

Kullum in suka hade ido da kafayat taga tana mata wani irin kallo ko murmushi sai dai taja mata tsaki ta kara da gaba duk dai kafayat din bata kulata.

Bayan wasu kwanaki babu abunda ya sauya yau ne cikinta yake cika wata biyu da rabi,all of a sudden kawai saitaga kamr tana canzawa duk yanayin girman jikinta na dada canzawa tana dada dawowa katuwa tana buduwa ga nonowarta ya ciciiko har sun fara zuba suna damunta.

Ga wani irin kazamin hormonal imblance pimples dake fetso mata akan fuska for no reason duba da yanzu bata ma da lkcin kulawa dakanta sosai. Bullowarsu yasata tafara yin make up din dole dan koda bata so sai kaga tayi dan ta boyesu.

Wasu kayantan ma har sun fara kasa mata musmmn wanda aka mata skirt ko fitted gown Lokaci guda physical changes din ya fara depressing dinta tafara over reacting tana yawan saurin daukar zafi.

Abu kadan sai gaka ta bata rai tanata masifa tana mita duk tabi ta addabe yaran shagonta da yawan kwainane a gidan ma harsu anty adizat bata kyalesu ba.

Ata fannin Ahmed kuwa dake tanajin mugun shakka da kuma tsoron sa bata fiye masa irin wann haukar ba sabida tasan baida kirki inransa ya baci, amma duk da haka sosai take saka masa ido akan calls din dayakeyi, bai isa ya aje wayarsa ba sai ta leka ta gagga suwaye ya kira, yanzu duk wani wayar da zaiyi takan saka kunnenta tana jinshi musmmn ma wayar daya keyi da mahaifyarsa dan tana son ta fahimce ko dagske ne shine yake nanike ma yarinyar can.

Nan da nan rashin yarda da tsananin kishi ya fara controllling tunaninta musmn inyace zaije katsina duba mahaifyarsa koda na kwana daya ne sai ta dinga masa tambayoyi da suke kular dashi gashi bayason ya kara marinta ko ya gaya mata wata baqar maganan da zai jawo yay asarar gudan jininsa dake cikinsa.

For the sake of his bby He has becm realy calm amma duk bata fahimce hakan ba ta dauka kawai iyawarta ne.

Her insecurities started building up stronger day by day ga taurin kai da raini daya fara samun mafaka acikin zuciyarta sosai itama.

Yau sai wajen 9:45 Adiahan ta farka a bacci kusan a rikice ganin tay lattin fita shago "oh shit" ta furta snn tamike ta zauna tana dafe kai ganin ko sallahn safiya ma yau batayi ba...

da uban sauri ta diro kasa tana ta mamakin yadda yau Ahmed ya kyaleta tayi bacci har haka,da kallo daya tabi wajen kwanciyar sa ba taga alamar ya kwana anan ba,ta tuna ashe ma tajishi yana waya acan dakinsa da dayan Abokinsa Dr bankole, hala acan asibitin yay baccin sa ya barta, tsaki taja ta mike tsaye tana daura igigyyun nitynta tana wondering why havent he shwd up yet har karfe 10 saura?..

agogon ta kara kallla sann ta jawo jacket tana mai zura kafafunta a sleepers cikin gaggawa tayi waje ta nufi kofar dakinsa"..murdawa tayi taji a kulle,ta harde hannunta tana daga tsaye tana balla ma door din harara"..haka kawai ranta ya baci dataga hakan dan kwana biyu daya dan saba mata da kulawa sai Abun ya fara canja ta gabaki daya..

juyawa tayi tana shafa cikinta feeling really proud of it,cikin ranta tanacewa how dare he yauko lekata baizo yi ba dakinta kawai ta koma a kufule tana jan tsuka guguwar iskancin na bala'in wajijjigata tanajin kanta yau a sama daidai da uban kowa..

kayanta ta tube ta zari towel ta wuce bathrum tayi wanka harta fito sanna ta tuno batayi sallah ba ta koma tayi alwala tazo tayishi a girgije,awajen ta aje hijabin ta hau kujerar gaban madubi wani irin kwalliya ta tsantsalawa fuskarta dan ya boye canjin daya zo mata dashi,evrything with dark blue idonta yaci shadows wata tsaddiyar arabian gown ta dauko ta saka.

Tana ta kallon kanta a mirror thinking dat she needs sumone to fix her necklace and kiss her cheeks kamar wata princess, tsaki taja da har yanzu da bataji duriyarsa ba, haka ta hakura ta saka abun wuyarta dakanta..

itama tanaso tay rayuwarta ne irin na matan da mijinsu yake mugun jidasu tunda ayanzu takai, she lacks nothing, Ahmed ne kawai ya rage mata ta rikeshi gam gam, and she thinks dis pregrncy is already givong her a bonus chance da ya sanyaya mata shi yake mata duk abunda take so. She want to try her best to see of she can start securing and controlling him kamr yadda taga kowacce macce takeyi da mijinta.

Sabon Wayar daya sayamata ta lalumo kamar zata dialling numbersa saikuma ta fasa,agogo ta kalla ganin goma na shirin kufcewa tayi tsuka ta wuce waje abunta ta nufi cikin gidan tana takunta ahankli kamar yar sarki,a falo ta tarar da alhaj bello tare da kafayat tana phone call,irin kallon databi kayanta yasa tay rolling ido a sace, nan tsuguna har kasa ta gaishe da alhaj bello snn ta gaida kafayat a dakile bata amsa ba sai wani irin kallon da bata gane ba take mata tanakan mata wani irin murmushin mugunta.

Bayan nan shagonta na shagari ta wuce direct acikin motarta.

Izuwa yanzun Ahmed har ya kammala dukkan hidiman registration na Yasra,jiya daga office aka kawo masa komi dan dama ya gaji saiya wuce lagos din kawai daga nan batare da ya gayawa kowa ba.

Yasrah ta fito daga wanka kenan ta cire cap dinta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki favrite drink inta bata samu ba, nan ta sauka fridge din kasa domin ta dauko wani drink ko cocunut nd pineappl ta sauka ƙasa ta isa can ta dinning area ta bude wani babban standing fridge din zata dauki exotic drink harta mika hannu sai taji wata kasaitacciyar Murya mai tsananin sanyi yana cewa waye ne wann kawomin bottle water awajen.

Bugun zuciyanta ne ya kara tsananta, Bata juyo ba kuma batayi magana ba har sai da ya ƙara maimaita maganar amma yaji shiru.

a hnkli ya dago dara daran idanunsa ganinta awajen yasaka ya taso dan yaga abinda takeyi da har ya hanata amsa shi,yana zuwa baijira ba ya fizgota da ƙarfi da har saida ta dan fado akan kirjinshi kamin yayi sauri ya janyeta baya tareda da rike mata hannunta cikin nashi sosai.

Tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta na can kasa tanaji kamar ta sullebe kasa ta dawo ruwa ta narke awajen, ba a Jin komai sai motsin bugun zuciyanta da ya kara tsanantuwa dan batasan ma yazo ba.

juyowa da ita yay tare da kuma rike mata hannun dayay ne yasa bugun nunfashinta rikirkicewa hakan yasa hawayenta suka hau taruwa acikin idanun ta.

kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa sai kallon fuskartta kawai ganin yadda kullum take dada yin masa kyau wani Dumi yaji a hannunshi ruwa na sauƙa yajuya yabi hannun nashi da wani irin kallon hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya a dan rude, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga wai har bata wajen, tsaki yaja aransa, baikoma kan dinning din ba Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta bi da wani irin kallo snn yabi ya lumshe idanuwansa sosai.

lokaci daya ya shiga kwada ma mai aikin gidan ƙira.
Chapter 77 · 0% Book details