← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 157

Sashe 20

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banji Yaki sam ya gaya ma Ahmed hakan a fili saidai kaga yana cusa masa ra'ayin hakan cikin salo, amma the more yana fada masa the more Ahmed yana nuna masa cewa shi bazai kwanta da ita yanzu ba sabida baijin sha'awar komi gameda aurensu yanzu snn baison yay forcing din kanshi akanta cos bayason yay wasa da feelings dinta akaro na biyu.

Akaro Nafarkon ma nadamarsa yakeyi aransa bana wasa ba dan yayi danasanin aurenta aransa yafi sau a kirga.

Duk wa'azinsu haka suka gaji suka kyaleshi.

Adiaha kuma ta sako Banji agaba da complain akan hakan, daya rage kirarta awaya sai ita ta fara damun shi wani bin ma yana kwance da budurwansa cikin dare zata fara kirarshi kuma kulllum dai maganan kenan.

Da Banji yaga bazai iya danne zancen ba haka ya tsare Ahmed da maganan ya fito masa fili yagaya masa abunda Adiaha take ciki, nqn sukayi ma junansu kacaca suka bata har suka dena magana da junansu na yan kwanaki akanta.

Ranar da yafara sanin cewa tanakai maganan sa wajen abokinsa banji abun bai wani damesa sosai ba amma datacigaba da kai korafi akansa like evry bit of abunda yake faruwa atsakninsu bakaramin damunshi abun yazo yafarayi ba

Ranar Haka kawai Ya kwace wayarta snn yay mata warning akan yawan alaqarta da banji.

Bata daddara ba bayan kwana biyu bayan sun shirya kenan sukazo gidanta ranar juma'a da shi da Bankole da banji din sunzo gaisheta sama sama as per abokan mijinta sai suka kawo mata tsaraba na abubuwan tabawa masu yawa da tsada a manya manyan ledoji.

Taji dadi sosai dan tun zuwanta gidan Haryau Ahmed bai taba siya mata komi dan taji dadi kona kashe kwadayi ba.

Bayan Sun kammala hirarsu lpya lpya sun tashi zasu tafi kenan taje ta tsare banji agefe, just to thank him for the gifts and also ta gaya masa cewa Ahmed ne ya kwace mata yawa yace tadena yawan alaqa da shi.

Shikuwa banji bai wani nuna mata komi ba kawai ya bata hakuri yace zai saka Ahmed ya maida mata wayarta ko ma ya saya mata wani sabon wayan tana ta murna ta koma daki duk Ahmed yana lura da ita amma baice mata komi ba.

Saida suka bar gidan washe gari yana office sai ga banji ya shigo fuskarsa a daure.

Nan ya tsaresa da maganan yake tuhumarsa akan maganan kwace mata waya da hanata mu'amala dashi yay.

He mistook dat as mistrust sai ransa yay mummunan baci da Ahmed yay masa hakan

Ran Ahmed bai taba konuwa kamar na ranan ba musmn da Banji ya hau gaya masa baqar magana har yanace masa he is traumatising his wife kuma hakan zai iya sakawa tafara jin sha'awar kulla alaqar da bai dace ba da wasu majazen awaje.

Ya masa gori Yace masa matarsa bata iya rike sirrin kanta ba,snn shi babban abokinsa ne na kud da kud shiyasa yayita ignoring dinta amma idan wani namijine saidai yay amfani da wann daman su kulla wata alaka da ita na daban wanda bai dace ba.

Banji yay fushi yace tunda hakane shi yama cire hannunshi akansu suje can sukarata dashi da matarsa bazai kara zuwa ma gidansun ba.

Ahmed baice komi ba ya dinga bashi hakuri dan su rabu lpya amma aranshi sam baiji dadi ba sam musmmn da Adiaha tamaida maganansa na hanata magana da banji awayan ya dawo musu kamar wani abin rashin yarda da munarfuci a tsakaninsu ba.

Sai tun alokacin zuciyarsa tahau tafasa taki yin sanyi sam yanajin kamar inya kamata a hannunshi yau bazatayi numfashii ba.

Daurewa kawai yay yazauna a office dinshi yau, dan baison yaje gidan ya sameta a lokcin da zuciyarsa tadau zafi, bayason yay mata abunda zai zamo musu nadama dukansu anan gaba.

Sai can Da yamma ya dawo gidan fuskarsa a mugun daure yau kwata kwata bata gane yanayinsa ba. Ita harta manta da cewa jiya ta fadawa banji komi, a tunanin ta kawai banji zaice ma Ahmed ne ya siya mata sabon waya ko ya bata wayarta batasan abun yay ma banji ciwo aransa dayaji tace akansa Ahmed ya kwace mata waya ya kuma datse alakarsu ba.

A matsayin nuna rashin yadda banji ya aje hakan aransa, shikuma Ahmed yay hakan ne sabida baiyajin dadin yadda take yaɗa sirrinsa awaje. He despise it, shikansa bakomi ne yake fadawa abokansa ba amma alkci guda ita tagayawa banji komi da komi..

Yanayin yadda ya daure mata fuska a gidan ya saka ta fara shan jinin jikinta akansa ganin bai kulata ba kuma yau baije ko ina ba har bayan sallah ishai yana cikin dakinsa yana kwance.

Can cikin dare tana bacci taji an jawota kasa an yarfata akasa saida ta tashi a firgice batare da ta shirya ma hakan ba.

Tunda ta ga Ahmed acikin dakin cikin dare gabanta yahau faduwa dan tasan tabbas akwai mummunan matsala yau

Fuskarsa a daure Yafara tambayarta iya sirrikan shi da take gayawa banji tana bashi amsa ,nan ya zage ya mata zagin kare dangi zagin dayasan zai mata ciwo aranta..yace mata tana da son kanta dayawa, dat she is demanding too much from him bayan tasan ta wargaza masa iyayensa tana son kuma ta kara wargaza tsakaninsa da abokinsa banji.

Acikin wann daren saida Adiaha taga salon tijara da rashin mutuncin da bata taba gani arayuwarta ba, bayan tsawa daya dinga daka mata, ga zagi, ya shakure mata wuya kamar zai kasheta ya tsorata ta sosai, yace mata duk sanda ta kara kai maganansa wajen wani ko ba abokansa ba wallh saiya saketa saki uku saidai intaje ta kashe kanta awani waje. tay ta kuka kmr ranta zai fice tana rokonshi gafara amma kamar bayajinta,

Haka Yaje ya dauko wayarta ya wurga mata yace mata gashi ta kira duk wanda taga dama amma tasani ranar da wani ya kara masa magana akanta ranar zai mata dukan tsiya snn zai saketa saki uku snn ya koreta agidansa.

Cikin dare sukayi case din wajajen karfe 1 na dare, bayan yaci mata mutunci sosai haka ya korota waje ya turata akasa cikin fushi haka ta kwana awajen tana kuka abakin kofar shashensu acikin duhu da sanyi.

Washe gari bata tashi farkawa ba sai agdon asibiti an daura mata drip a hannunta ahankli ta bude lumsashun idanunta tana kallon wajen dayake mata dishi dishi.

Ajiyan Zazzabi mai zafi ne ya rufeta ta suma, Ahmed din ma baisan hakan ya faru ba dan da asubah ya shirya ya fito ko kallonta awajen data dukunkune baiyi ba haka yazo ya wuceta ya dauki motarsa ya wuce garin katsina wajen mahaifiyarsa.

Da safe Mai gadi ne yazo ya sameta awajen a sume shine ya kira anty nurat ita kuma ta kirawo sister zainab tazo suka kaita asibiti aka bata gado. Anty nurat duk ta dauka ko ciki ne, sister zainab kuwa tasan ba hakan bane, duk dai jira suke ta farfado ta gaya musu abunda ya sameta ta suma. Farkawan ta keda wuya tana bude idanuwanta hawaye masu sanyi suka soma saukowa daga cikin idanuwanta.

She was feeling very very remoserful dan tasan tay kuskure sosai data hada Ahmed fada da abokinsa Banji tun bai gama hucewa akan abunda aurensu ya jawo kafayat tay ma iyayensa ba.

Acikin zagin dayay mata jiyanne ta dada fahintar cewa koma meya faru atsakaninsu jiyan duk laifinta ne, dan bai dace tana matar aure ace tana daukar dukkan sirrikanta tana gayawa wani namijin awaje ba.

Abunda yasa ta karajin babu dadi aranta shine rashin gayawa Ahmed bukatarta datay tun farko,she was scared of mood dinsa na rashin nuna mata kulawa lately shiyasa bata tabajin zata iya gaya masa cewa tana bukatar ya bata hakkinta na aure ba,hakama batun kayan sawa bata taba gaya masa cewa tana bukatarsu baki da baki ba,dan duk a tunaninta tabari akan cewa shine zai kawo ya bata dukkn wayann abubuwan batare da sai tambayeshi ba.

Saida hakan yazo ya faru jiyan kuma saita fara tunowa da yadda banji yake yawan cemata tay hakuri tadan yiwa Ahmed din uzuri izuwa lokcin da family problems dinsa zai dan ragu, duk ita alkcin bata fahimce hakan dakyau ba, she was just soo desperate, ta kasa iya yin hakuri sabida damuwa da wahala yana yin ma zcyarta yawa tanason itama taga mijinta yana kulawa da ita kamar sauran mata.

Adacan Tay tunanin cewa alaqarta da banji zai taimaka mata wajen samun kan Ahmed cikin sauki batasan da cewa dada kwaba makanta lamarin tay ba.

Duk gulman Anty nurat haka tay ta gama Batare da Adiaha ta gaya musu asalin abunda ya faru da ita ba, itakanta tasha mamakinta ayau dataga wai zuciyarta ya denajin sha'awar yin maganan Ahmed da kowa.

Bayan dan wani lokci zazzabin nata ya sauka aka sallamesu suka koma gida, sister zainab ce ta kaita harsashenta ta zaunar da ita ta kawo mata abinci tadanci.

Sosai tafara fahimtar matsalar Adiaha tun bayan data kikkira wayar Ahmed din tun a asibiti taji wayar nasa kashe bata ji kuma Adiahan tay magana sosai akansa ba saidai tay ta zubda musu hawaye..tun a asibitin take tajin tausayinta dan tasan is not easy ace a farkon aurenka mijinka yay ignoring dinka haka.

Da can tay niyyar ta sauko tajawota ajiki ta rarrasheta taji asalin matsalarta daga bisani kuma saita fasa data tuna cewa adalilinta ne kafayat ta aure musu ubansu.

Bayan Adiaha taci abinci tadan samu karfin jiki sai tafara mata surutu acikin salon masifa tanamai bata shawara acikin salon hannunka mai sanda.

Acikin magangunta take cewa Adiaha bazata taba samun kan Ahmed ayanzu ba face harsai matsalolin dake gabansa sunkau cos Ahmed is still feeling guilty akan halin da mahafyarsa take ciki ayanzu...All she need to do is to stay patience bawai tana damunsa ba.

Adiaha ta lumshe ido tana hawaye duk dama tana fahimtar abunda take gaya mata acikin salo amma abunsun na damunta aranta itama.

Its like nobody care about her own feelings

Bayan ta gama mata nasihan cikin mita ta kama hanyarta ta tafi gidan mijinta ta kyaleta ita kadai asashenta tana zaune tana kuka..

Duk sai taji duniyar yay mata daci, zuciyarta na mata kuna dan kuwa tana bala'in son Ahmed dinta,fushinsa da bacin ransa tamkar garwashin wutane ajikinta dayake konata akowani lokci.
Chapter 20 · 0% Book details