← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 157

Sashe 68

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigowar dare su hjy maimunatu sukayi amma hakan bai hanasu murnan ganin junansu ba. Kusan kwana akayi ana hira, banda yasra da zazzabi tare da change of environmt ya sakata bacci mai nauyi.

Washe gari da Asubahin fari dukansu suka shirya suka wuce katsina state babban mansion din hjy maimunatu dan acan ne za'ayi dukan wani shagalin da aka shirya na hidima.

Wajajen karfe 9:30 na safe mutane ne makil agidan dan Kan kace kobo gidan ya kacame da yan zuwa kawo gaishe gaishe itakanta yasrar ma tasha jagwalgwalen gaisuwa harna fitan hankl.

tun shigowarsu ake ta zancen hidiman auren ya sadik da wata babe mai suna Amal khashim،yar gidan politician business partner na hjya maimunatu dake uwar yarinyar ma tazo.

Saidai dayawa daga cikin matayen idanunsu nakan yasra ce, kowacce tana neman irin haɗa zuria da danta ganin ta nitsatsiya kuma kyakkwa, yasra sam bata son irin wann hirar hadin auren shiyasa ko kadan bata iya sake jikinta acikinsu ba musammn ma wajen big rich women din da suka zazzo wayanda suka kawo yaransu yan samaruka da suke ce mata taje sugaisa dasu a waje.

After some mints su Adda nafisa suka shigo suma, jirginsu ne karshe basu biyosa da asubahin ba, tuni falon ya kara cikewa da wani sabuwar surutun anata gaishe gaishe da gudu farida ta taho suka rungume junansu da Yasra da alaman Suna tsananin murnan ganin junansu.

murya na rawa farida tace "hey pretty how fa?Dan Ajiyar zuciya yasra ta sauke dan tamkar wacce take cikin rudanin hayaniyar mutanen daya cika mata kai.

cikin sassauto danata murmushin bayabo ba fallasa tace "i am fine, wai ina kuka tsaya nifa tun jiya dana zo banganki ba? Farida tay murmushi tace "its late, kuma ance baki da lpya shiyasa,da safe dana farka kuma sai mumy tace aitun da asubahi kuka taho katsina mune zamu zo daga baya, ure very much welcome back dear.
bayabo ba fallasa yasrah tace thanks sis,
daga nan suka rasa nacewa ma juna akahau kame kame dan sun jima basu ga juna ba sai ta waya ko video call wanda shima basu cika yi ba ,a hnkl yasrah ta zame jikinta ta wuce ta barta a tsaye wajen ta koma room dinta ta kwanta sabida yanayin jikinta da haryanzu bai wani warware ba,daga nan basu kuma kara hadewa ba saidai kallon nesa da suke yawan aikawa juna kowa tana admiring kowa axuciyarta a sirrance, Har yammaci gidan na acike da jama'a anata zumunci anata surutu ana jin dadin.

Harsai Bayan kwana biyu da dawowarsu nigeria snn jama'a suka fara rage zirga zirga aka fara shirye shiryen hidiman da za'ayi karshen satin wanda yau baifi saura kwana hudu ayishi ba.

Yasrah bata da wata abokiyar zama ayi hira inba farida ba saidai rashin zamansu waje guda yasaka suke samun hard time wajen adopting halayyar junansu dake kowacce tana irin nata salon wayewar.

Farida ce take bata labarin yanayin yadda tazo ta tarar da garin ciki harda labarin first encounterta da uncle dinta Ahmed,sadik kuma bai fiye zama ba dan absence din Ahmed din yasaka aka sakar masa komi yana mai kulawa da sauran abunda ya rage na batun hidima.

Dagata can Abuja kuwa kusan komi acikin sauki yake tafiya musu a kwana biyun musammn ma da kafayat bata dawo Abujan ba tukuna. Su anty adizat kuwa duk sun fara kame kansu daga shiga harkan Adiaha daan cikinsu kaf babu wacce ta karajin sha'awar shiga tsabgarta musammn ganin yadda aka fara lailayata agidan ana bata special attention hardaga wajen father inlw dinsun.

Life was pretty normal agidan jimada kwana biyun kowana nayin harkokin gabansa ata sashensa..

A fannin Adiaha kuwa yau a kwance ta wuni Ahmed bai barta tay aikin komi ba duk dama bai iya aikin gida ba amma ba laifi yakan saka ayi mata,ta farka abacci kenan lkcin ta tarda shi a falo yana zaune itama tabishi ta zauna tanakan cin abincinta a hankli tana taunawa kmr bazatayi ba, yayin da ya lafe jikin kujera kamar mai kallon wani abu saidai ita yake satar kallo time to time Yana wani tunani aransa.

Mikewa tsaye yay ya wuce ya bar dakin tabi bayanshi da kallo,jim kadan sai gashinan ya dawo dakin rike da wani envelope ahannun sa.

Kirjinta ta ne ya buga cos duk inda surprise yake sai kajishi daban ajikinka dama can da akwai kudin dayake shirin bata for her general upkeep wanda zatana kashewa intana so basai ta tambayeshi ba.

Mika mata envelope din yyi da kallonsa na its urs,.zumudi fall ranta ta saka hannu ta karba ta bude taga cheque ne na kudi wanda bai taba bata irinsu ba.

Da wani irin wawan runguma ta fado jikinshi tana tsala ihun murna tanajin kanta kamar a
mafalki ta hau yin dariya sosai whats this for?am so happy...a gefen kuncin shi ta sumbace shi..yy murmushi yana kafeta da kwayar idanunshi masu narkarwa da saka kasala hakanan tana jiyo hucin numfashinsa kusa da ita sosai..

tallafo fuskarta yay suka jingina da jikin kujerar ya manne ta ajikinsa tanajin kamar ta nitse cikin jikin shi danwani sanyi dataji yana ratsa mata kwakwala...

da wata irin kwantaccyr murya taji yace.."Babe kada kina manta ke wacece bana son yawan stress, kuma ya zama dolene yanzu kina kulawa dakanki sabida kinga halin da kike ciki na risk din hawan jini, Ki kiyayemin kanki da mutuntuncin igiyar aurena akanki, zai iya kasancewa na shiga rubibin hidima kinga ai anty na ta dawo ko,..My mum needs me der,gobe zan wuce nima zan tafi katsina so absence shudnt be bothering u kinji? Beside Idan an kammala komi kinsan my sister wll be here to keep u company ko?

Cikin ladabi da fahimta ta amsashi..

Washe gari Kafin nan ya
Tafi saida yay mata kashedi akan yadda zatana kare lpyarta since already akwai complication na hawan jini and all that stress.

Duk yaja mata kunne yace mata kartana stressing kanta da wani aiki ko yawace yawace ta zauna kawai tay relaxing kanta ko tunaninsa kartanayi har kafin nan cikin yay kwari.

All the money he gave her yana xpecting tana amfani dasu wajen siyen dukkan wani abunda takeso and he make special oder wajen sabbin masu aikinsu akan zasuna mata special duty na goge goge, aika da sauran errands din datake so har yamma zasuna serving inta, dan kartana wahalar da kanta for a while
Sosai Ahmed ya nema mata sauki ya kuma dorata a salon kulawa da gata.

Lafiya suka rabu ya taho katsina nan ma ko zama bai yi ba suka shiga zirga zirga na tarban manyan bakin hjiya maimunatu a hotels din da suka kama gabaki daya na saukan bakinsu already yau baifi kwana biyu ayi bikin hidiman ba but mutane daga wajaje dayawa har sun hallaro sabida dadewar datayi bata zama a kasa gata da farin jinin al'umma sabida irin taimkon su datakeyi musnmn ma maarasa karfi yan kauyuka kai zuciyar taimakon hjya maimunatu bai tsaya akan kowa ba. Duk wanda yake bukatar taimako takan yi iya baakin kokarinta shiyasa cikin yansiyasa mata na garin katsina babu wanda yakaita bada free scholarship na karatu wa yaran talakawa. Already sum of them are in the millitary, wasu engineers، lawyers wasu kuma suna lecturing. Duk wani hidima nata sai kaga taro iya taro sabida itakanta batasan iya mutanen data ke taimaka musu ba.

Aikin kulawa da masauki da kuma ma'aikatan event shine yasako su Ahmed din agaba tunda ya isa katsina baima samun daman ganawa da mahaifyarsa sosai inbawai Adiaha ce ta kira ba. Hjya khadijatu taso ace Adiaha din is part of the celebration sai kuma hajy maimunatu bata wani bada fuska akan hakanba dadin karawa ma da irin condition din Adiahar na stress da kuma shawarwarin da likita ya bayar wanda shine yasaka Ahmed yace mata a'a cos he just cant risk anything happening to his baby dan baisan wani irin rashin kirki zai ayyana mata idan cikin nan yazo ya xube adalilin wani rawan kai ko gangancinta ba.

Atmspher na Gidan was filled with noise da zirga zirgan Suma din acikin gidan bakine suke yawan shigowa musu dan Already hjy maimunatu sunje Abuja sharply ita da jikarta farida, yasrah ne a gida dake harynzu tana dan jin zazzabi.

Ana washe gari hidima hjy maimunatu da farida suka dawo garin katsina kowa nata shiri hanklinsu bai kwanta da laulayin da yasra take tayi ba irin dao intermittent fever din nan ne na rashin sabo da environment din datake irin zazzabi mai zuwa ya koma yana dawowa akai akai yana kashe mata karfin jikinta sosai.

Sassafe suna farkawa hjy khadijatu ta cewa Ahmed yajeshi ya duba jikin yasrah dan for security reasons ba ason ma a fitar da ita bare akaita asibiti acikin rubibin shirin hidiman nan.

Tun safe ya shirya kansa tsaf bayan sunyi waya da matarsa Adiaha yaji lapyar babynsa hnklinsa ya kwanta sosai.

Kafin kace wani abu Qamshin ralph lauren ke tashi ko ina ajikin sa,
hannun sa da ke sanye da verrizon wirelees watch ke gyara zaman necktie din sa ya fito rass Cikin dark grey suit sai brushing kansa yake dada yi agaban madubi

Bai taba kawo tunanin ya fuskar yarinyar ma take ba yanzu ne dai daya ke shirin zuwa duba ta dan zuwansa he had been busy basu taba haduwa da ita ba.

Cikin sauri sauri ya fito don baya so yaci karo da kowa cos its almost 8.30 morning kowa na dakin sa har yanzu.

Site din hjy maimunatu ya wuce straight bai ganta ba ya shiga dube duben ko zaiga mai kama da ita. He doesnt even knw how she looks likes dan rabonsa da ganinta tun tana yar karama da aka tafi da ita.

Dakin dake gefe dana hjiya yasa hannun yayi knocking Duk dama dai gidan ba bakonsa bane amma sam Shi bai cika zuwa tanan ba.
Chapter 68 · 0% Book details