← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 157

Sashe 112

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan yasaka yay making few contacts da wasu wanda suka taba aikin reserch dasu aka samu wani mai shago sananne wanda shine ya fara bashi information akan iyayenta da Adress nasu da halin da suke ciki ayanzu batare da yasan shine mijin nata ba.

Anan ne Mutumin yake ce masa aiyanzu ma mahaifinta baya iya zuwa ko ina sabida shanyewar rabin jiki na paralysis dayake fama dashi a sanadiyar tafiyar yarsa Adiaha,he mentioned how deeply ashamed he was, har baya iya zuwa taro ko wani community gathering sabida gulman familynsu da akeyi ana cewa mahaifyarsu ta gudu tabi musulumi ga yarsa ta farko ma ta aikata the same sabida tsabar son abun duniya.

Mahaifyar tan ma kusan irin abunda take fuskanta kenan daga wajen mutane musmmn ma wajen elders dinsu na community da wajajen biki..izuwa yanzu bata isa ta saka baki acikin wani magana ba dan kuwa baza a rasa mai binta da habaici akan cewa bata bawa yarta Adiaha tarbiya ba shiyasa tagudu tabarsu tabi musulmi.

Everything about deir life is affected by her actions hatta wajajen kasuwancinsu saida suka rasa customers kusan da abunda Adiaha tay ake kwatance da su saida suka sha wuya sosai kafin nan abun yadanyi musu sauki.

Mutumun yace tun bayan shanyewar jiki da baban ta ya samu mamanta ne kadai take fita taje kasuwa ta nemo musu abin rufin asiri saidan abunda kannen Adiahan suke turowa daga Inda suke dan dukkansu suna da aure yanzu mace da namiji, na mecen ce urua dake zama a Abuja mijinta yana aikin delivery services, sai kuma dansu na miji Dayake aure da matarsa anan cikin cross river yana saida kayan abinci.

Jikin Ahmed yay sanyi sosai ya kuma ji tsoron tunkarar familyn Adiaha aransa duba da irin halin da suke ciki.

Abokiinsa banji ya kira dan yasan shikadaine zai bashi shawara mai kyau.

Yana kirarsan kuwa ya dauka suka fara gaisawa snn ya gaya masa halin da ake ciki da zancen iyayen Adiaha..

Banji bai bashi shawarar yaje kai tsaye ba, amma ya bashi shawarar akan ya kyautata musu, snn in yaga zai iya sai yaje har gidan tare da ita koda ma miyene za'a masu atleast dai taga iyayenta..

Hakan kuwa ya dauka ya harhada abubuwa na abinci da kudi dubu dari snn ya bawa mai shagon yace yakai musu gidan a matsayin irin kyautar stipends din nan da ake bayarwa a asibiti karma a fadi sunansa.

Mai shago kuwa baiyi wata wata ba yakai musu hilimi guda na Abinci doya da sauran tarkacen abincin da suke ci din da su buhun shinkafa dana manja da gishiri.

Koda yakai bakaramin godiya sukayi ba har da hawaye sabida rabonsu da sukaga irin hakan ma har sun mance sosai tay convincing dinsu cewa tallafi ne kawai suka samu abunka da mai nema basu bata lokci wajen zafafa tambaya akai ba.

Haka har ya dawo Ahmed ya bashi kyautar dubu goma na yi masa aikinsa da kyau.

Bai gayawa Adiaha kome game da hakan ba har ana washe gari da zasu bar garin da ssafe yace mata ta shirya suje gidan su ta gaishe da iyayenta.

Her body immidietly become weak tafara jin tsananin tsoro da fargaba nan da nan tafara kawo masa kwana kwana sabida batajin karfin gwiwar zuwa ko kadan bai biye mata ba a hakan yay convincing dinta.

Wa Driver da sukayi haya tayiwa kwatance ya kaisu har gaban gidan mr bassey da safe..

Abaya ta saka baki ta lullube kanta hannunta rike da babban bags biyu na shoping ta harhado expensive wine daga hotel din da suke ,da kudin da Ahmed ya kara bata a envelop, snn ta siya ma mum dinta kayan sawa.

Koda taga kofar gidansu saida kirjinta yay dukan tara tara da kyar da sanyin jiki ta shiga Ahmed na binta abaya abaya shikam bai damu ba sabida ya gayawa yayunsa inda yake snn brother hamzat na monitoring movemnt nashi nayau a tracker.

Kallon gidan Adiaha takeyi jin hawaye ya cikaa a idanunta ganin Gidan yay shiru duk ya balangwaje kamr ba mutane ne aciki ba.

Bata iyayin sallama ba da sanyin jiki ta tura kifar ta shiga babu kowa anan sai tabarma datagani a shimfide a tsakr falonsu.

Kkri take zata shiga ciki ta duba iyayen nata tana daga labule sukayi ido hudu da mahaifinta dake kan wheel chair dinsa yana kkrin turowa....
[7/16, 8:17 PM] SURAYYAHMS: Suna haɗe ido da mahaifinta atake ta tsandare cikin kallon kwayar idanunsa da suka cike da wata iriyar shock da kuma tsantsar kaduwar ganinta agabansa adede wann lokcin da baiyi zato ba.

Hannunshi dake wani irin bari ya daga zai nunata dashi sai ji yay zuciyrsa ta riƙeshi ya dafe wajen atake yafara groaning yana wani irin kakarin kara kamar wanda zai sheƙa lahira. Aguje cikin rudewa Adiaha ta karaso tare da zubewa agaban sa dan batasan ma ya akayi tafara kuka ba..

Motsinsu ya saka mahaifyartan ta fito a guje dan ta dubashi.

Lkcin Ahmed yana tsaye daga bakin kofar yanata kallonsu, maman Adiaha na shigowa ciki shita fara hade ido dashi amma dake batasan shi ba sai bata wani kulasa ba tayo kansu a gurguje

Jikinta na rawa ta tsuguna cikin rudani ganin yadda jikin mijinta yake vibrating yana tuttura Adiaha dake kuka mai dauke da karayar zuciya ajikinshi da wani irin tsana da kyamata.

A Lokcin babu abunda yake tunawa kamar tulin baqin ciki da tozarcin da ta sakashi a ciki..

Maman nata Koda ta shaƙo muryanta sai da tay tsayuwar minti biyu a daskare kafin nan ta dawo hayyacinta cikin Wani irin ihun barawo da ta saka mata.

Wani irin fixgota tay a rikice tanamai kkrin jijjigata cikin tsananin fushi da tashin hankali Ahmed ne yay saurin jawota bayansa ta koma bayansan ta boye fuskanta tana kuka sosai

Ihu maman nata take arikice tana cewa you... You,.you...evil woman,.. "have u come back to finish him?..Adiaha meya kawo ki? Why did u come back here oo, haiiii, Who call u here ? U evil woman ,apostate of hell fire, haiii ooo..it shall neva be well with u for the countlesss time Ahh Ahhhh Adiaha Adiahaa ashe har baki da kunyar nuna kanki agaban mu,havent u cover us in shame and ran away?havent u end our lives along with our dignity. menene kike si damu kuma? If my husband die bcos of U shall neva have peace in ur life oo, "god will not let u sleep well" uve tortured us enough..just go away..
tana fadin hakan ta rushe da kuka sosai tanamai jimantawa.

Itama Adiahan kukn take kmr wanda zata cire ranta ..

batay tsammanin hakan datay da rayuwarta zai zamo mata babban matsala ba.

Ahmed duk ya rasa me zaice musu.

Ita din ma Kuka takeyi cikin rasa na cewa ganin iyayenta duk sun hatsala da ita babu wani abunda ya ragu agame da fushin su akanta saidai ma wanda ya karu.

Cikin kuka da magiya mai ban tausayi ta fito daga bayansa jikinta a sanyaye tay kneeeling da gwiwowinta akasa tana cewa "papa, Mammy pls now, pls forgive me, i am still ur doter, its hard for me to do this, am sorry
..And...and i just come to check on u nd papa.

Idonta nakansa ganin shanyewar da jikinshi yay yasaka ta kara fashewa da kuka mamy pls what happen to him..meyasa yake kan wheel chair What is going on mammy?

Tari baban nata yake kanyi sabida tsabar maganan dayake son futarwa daa ya shake masa wuya. Sai can da abun ya dan sakeshi snn ya rarumo wani sanda ya wurgesu dashi yafara ihu da yarensu na calabar yana cewa ta fice masa agida bayason yaganta har Abada...

Ahmed baijin me suke fada dake yarensu sukeyi
But She was begging and begging with tears amma duka suka ki sauranta Ahmed ne ya dinga rirriketa gwanin ban tausayi.

Haushi ma suka fara bashi ya hade ransa sosai cos why wundt they listen to her for once suke mata korar kare.

Mamanta data fara sauke mata buhun bala'i da masifa da harshen yarensu tana gaya mata duk bala'in da suka shiga ciki adalilinta saida zuciyar Adiaha tayi kusan tsinkewa tsabar tausayin su dataji. Worst da suka dinga cewa itace silar da rayuwarsu ya dawo haka kuma har Abada bazasu yafe mata ba. Da kyar baban yake fidda magana sabida condition dinsa na ciwon, Koda ya fara jefansu da mummunan baki yana cursing dinsu yasaka Ahmed ya fara ce mata tashi kawai su tafi dan shi kam aransa yanajin tsoron bakin iyaye.

Adiaha da already ta ragwabe taki sam ta motsa awajen, cikin kuka mai radadi ta kafe tanamai cewa baban nata yay hakuri,tace masa ganan mijinta Yagansa da idonsa she is in safe hands, snn yazone domin ya gaishesa and she is also pregnant for him ko da sau dayane suyi hkuri su sakama aurensu albarka koda ma hanklinta zai dan kwanta.

Iyayen nata suka dada hatsala data nuna musu shi, basuce ma Ahmed din komi ba but the way da suke kallonshi wani iri iri shikansa yasan sun tsaneshi da tsana mafi muni,nan mamanta ta ruga guje ta koma daki ta dauko ruwan zafi ta kore su har waje cikin compound din dashi.

Saida suka kai har waje ta bakin gate snn tafara zagin Ahmed din shima tanamai tsine masa tace shine yazo ya yaudare yarta ya lalata mata rayuwa and for that she wll neva forgive him or accept him...At dis point Ahmed ya fara ji aransa babu amfanin aurensa da Adiaha saidai baisan ya zaiyi ba tana dauke da cikinshi and he wants his baby.

Atakaice dai tun zuwansu har suka bar cikin gidan basu samu wata kykkwyan kalma ko tarba ba...adiaha kuwa tun da tagani kuma taji yadda rayuwar iyayenta ya dawo sai tafarajin ina ma da yadda zata iya tamaida hannun agogo baya tabisu ahankli.

Banda kuka da cursing dinta da suke babu wata kalma mai kyau dake fita abakinsu duk abunda ta kawo musu duk suka kwashe suka watsa musu shi ajiki..

Ahmed dayaga bazai iya ba ya fincikota na karfi yafara janta izuwa gaban mota dan su kama gabansu tun kafin nan mamanta dake musu ihu ta tara musu mutanen anguwar akansu.
Chapter 112 · 0% Book details