← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 157

Sashe 100

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ata fannin zamanta da yasrah kuwa Duk dama basa wani kula junansu agidan amma izuwa yanzu sam bata jin wani haushinta kamar dacahn
Probably bcos nasihar hjy ya dan taɓata, har Ahmed din shima taga yau ya dawo kwana da ita acikin dakinta har in zatay fitsari da dare zai rakata har bakin door intagama ya dawo tare da ita.

Rayuwarce ta soma tafiya musu ahaka cikin wani irin yanayi mai sauki tare da bambamci.

Tsakaninsa da yasrah kuwa iya daure fuska ne da kuma saka ido akan lamuranta musammn ma na makarnta, he took it upon himself koyaushe shine zai na kaita schl da safen da yamman ma yanzu bakasafai yake son aika ta schl da driver gidansun ba sam ya kasa yadda da batun hadin kansu da Fahad he is bcoming insecured akanta batare da yasani ba duk gani yake kamar duk harsashen sa akan su gaskiya ne.

Kishi tare da saka ido dayake mata yasaka take daukar hakan a matsayin takuri da bakin hali...

He hates it musamn idan yaganta tay dressing tay kyau kowa yana zumudi akanta duk inda ta wulga ana masha Allah duk sai yaji kamr ransa ne ake tabawa..

Salon kishin dayake nunawa akanta yafara bawa Fahad wata daman kasncewa kusa da ita.

Agidan kuwa Dakadan kadan har yasrah tafara sabawa da dan taimakon da takey wa Adiaha msmn wajen tayata kananan abubuwan da baifi karfinta ba sumtime har Adiaha tafara jin tana son taga suna zaunawa tare a falo suna kallo ko hira amma dake bata sabar mata da hakan tun farko ba kullum sai kaga yasrah tana daki inhar ta fito saidan schl ko cin abinci ko in Adiahan ne ta kirawota waje domin tay dinner. Abincin dare dana sfiya kawai suke ci atare like one big family.

As usual da safe Adiaha zata wuce shago yasrah kuma zatabi Ahmed ya ajeta schl,assigment din da fahad yay mata wncn karon shiyasakata a front line a class dinsu dan duka ta cinye ita kadai, hakan ne yasa suka dan fara magana da fahad din ahankli ahankli har suka fara sabawa dashi cos he knws alot of things akan course din kuma ya lura kamar she is sooo passionate akan ambition dinta.

Da passion dinta na son taga tay karatun ta jajirce ya dinga samun damarsa ne neman shakuwa da ita acikin makrnta.

Most time inbata tare da maryam toh zaka gansa awajen yana koya mata abu ko sunayi tare...

Little attention datake basa means alot to him cos Each day feelings dinsa yana dada yin karfine akanta kuma gani yake kmr Ahmed ne kawai obstacle atsakanin su, dan haryau basa haduwa a ko ina sai a schl gata bamai son amsa calls din sa bane musmmn ma da dare, duk a tunaninsa tsoron Ahmed din yasrah takeyi datake cewa bazai barta tana fita agida ba.

Yayi yai akan koda tazo gidansu maryam suna haduwa suna xtra karatu harma suje sudan zaga gari dukan su in a grop of friends amma haka yasrah taki firrr sabida sosai ta fara fahimtar manufarsa na son da yake mata a boye, shikuwa duk tunaninsa yanayin takurin Ahmed ne yasaka take janyewa dasu.

Dk yadda bata son Ahmed yana ganinsu atare amma fahad yaki kmr ma tunda ya lura kamr Ahmd ne matsalar sai ya fara cusa kansa a duk inda Ahmed zai gansu ataren yawanci haka zaita hadasu faɗa suyi kwana da kwanaki basa kula juna wani hin Adiaha tay ta mamakin yanayinsu wasu lokutan kuma bata ma noticing sabida haryau bai fasa zuwa duba yasran sama da kowa akowani lokci ba.

Akan yawan tsabaninda suke samu dashi akan tarayyarta da fahad yasaka yake yawan fushi da abincin matarsa.

itakanta Adiaha bata gane masa wata rana indan taga wai har ya kasa bacci yana tunanin yasrah da saurayinta na makrnta.

Fahad kuwa is tryng his best to manipulate her dan ta bar zama agidan ta dawo hostel har Abin yafara shigar kanta kullum tana waya da yaya sdq dan ya tayata rokon su mummy amma haryau shidin ma bai bata cikakken amsa akan hakan ba dake auren sa ya riga da yazo kusa.

Kwana biyun nan bata da lokci sosai tana yawan test, ga karatu sabida exams din su daya fara gabatowa kusa saidai adaidai wann lokcin ne kuma Misconception din Ahmed akan tarayayyrta da fahad yake dada ginuwa kowani rana tareda salon saka idon dayake mata yabi ya saka mata kahon zuka akan zaman ta schl tana karatu bana wasa ba Wanda hakan yasa hanklinsa ya gushe yazo ma bai fiye saka hanklinsa akan Adiaha ba duk damuwar sa ya koma kaga kan yasrah da fahad baima san halin da kwana biyun take shiga ciki ba.

Gani kawai yay ta dena zuwa shagonta tana yawan zaman gida gidan ma a dakinta mafarke mafarken datakeyi yasaka adan dole ta fara yin azumi a boye wanda shine ya ja kwanan cikin ta har ya wuce kwanaki goma sha hudun da kafayat ta deba mata.

Tana yawan jin yadda kanann gulmace ke tashi a main house daga fannin su anty adizat da su anty nurat game da bacewar kafayat din agidan yau har ana neman wata guda kenan bata gidan kwata kwata.

Immidietly after 14 days din nan babu ranan da Adiaha bata zubar jini wanda hakan yasaka dan dole take gujewa Ahmed shibaima lura ba cos he is busy wajen bibiyar rayuwar yar uwansa yasrah daya dorawa zuciyarsa mummunan kishinta.

Yau asabar da sassafe cikin Adiaha yay clocking four month ta farka da murmushi akan fuskanta tanamai godewa Allah daya bar mata shi..

Tana fitowa ta samu Ahmed har ya kammala shiri da alaman zaiyi tafiya, yace mata garin babanshi zasuje wato garin ibadan, tare da babansan da brother hamzat zasuje ta'aziyar wani dan uwan babansu ta fannin uwa daya rasu.

It wll only take them 7 days to go and come back sabida zasu danyi ziyara wajaje da yawa.

Sosai tasha mamkin yadda ya sake mata fuska musmmn dayake mata bayanin yadda zata na kulawa masa dakanta in baya nan.

Dake tana tsananin son shi daga ya dan acting romantic da ita duk sai kaga ta dau abun har cikin zuciyarta..tana ta murna cos of sweets words daya furta mata na cewa he is going to miss her and the baby.

Yace mata inya dawo zasu sakawa babynsu suna tun yanzu cos at four month already bby ta zama rayayye aciki.

Zumudin nasa nayau din ma daban ba cos He just cant wait to hear his babys first kick, yau Bakin adiaha har wuya tsabar murmushi ganin yadda yake furta mata matukar alfahari da abunda ke cikinta dayakeyi ayau da cikin ya cika wata hudu.

Yay mata alkwaruwa da yawa aciki har da wanda yace sai in ya dawo zai cika matasu Kamar cewa da yaay zasu je shoping tare zasu fara siyan kayan baby idan sukayi scanning sukaga movement din babynsun for the first time snn yace mata zai kaita wani waje tay spending moment din tare dashi and he wll listen to all her complains she was soo happy a lkcin har tafara jij kamar bashi bane yake furta mata hakan da bakinsa.

Tarasa shinko zumudin cikin sa yakai 4 month ajikinta ne koko zancawa yay haka kawai overnight yake mata irin wann dadan kalaman.

kudi ya dauka ya bata yace mata ta aje incase she need anything snn ya bata amanan yasrah tare da gindaya mata iya lokutan da zasuna fita gidan yace daga yasrah ta dawo schl karta sake ta barta ta kara ficewa koda nan da bakin kofa ne.

Bayan nan dakin Yasrah suka nufa tare suka sameta zaune akan gadonta da earpice na iphone a kunnnemta tanakan waya da kawar ta maryama ganan computerta agabanta tana latsawa.

Yadda taga sun shigo mata su biyun yasata aje wayar batare da ta katse shi ba,gaishe su tay duka a ladabce kafin nan yay dabara ma Adiaha ta basu waje.

Tana fita yana harde ransa ya fara mata bayanin cewa zaiyi tafiya snn ya kara jadadda mata Abunda yagaya ma Adiaha na zancen zamanta agida

Bayan nan ya ciro kudi mai yawa a envolpe ya aje mata akan table yace zaina aikowa dakansaa ana zuwa daukarta so she dont have to bother akan hawa motar haya.

Takan sha mamkin yadda aakayi yake sanin komi datake ciki da studies dinta Indirectly yake mata warning akan kasancewrta da fahad acikin makarnta amma tay kamar bata fahimtar meyake cewa saidai ya gama surutunsu sa tace masa toh taji.

Hatta maryama datake jin maganan nasu sosai ta fahimci manufar shi...

Bayan ya fita yasrah taja wani uban tsaki snn ta cigaba da abunda yake gabanta batare da tay tunani akai ba, duk takurin maryama dataji bayani akan alakarsu da Ahmed yasrah bata son gaya mata komi a filla filla saidai sama sama.

Ata fannin Adiaha kuwa Haka suka rabu da mijinta yau cikin dadin rai da shaukin juna.

Duka family suka fito aka masu adu'a tare da musu sallama, daga ita sai yasrah a gidan rayuwar su was quite peaceful sabida babu wanda yake shiga tsabgar wani.

Tun da suka isa Ibadan Adiaha bata samun daman yin waya dashi sosai kamar yadda yasrah take samun wnn daman, dan kuwa duk safiya zai kirata da sunan tashinta tay sallah snn taje schl snn inta tafi duk sanda aka tashi zataga wai har ya aiko driver saiya kirata Snn ya matsa mata sai ta koma gida adede lkcin dayake so dan kawai baison ace dan bayanan shkenan sai fahad ya samu wani dama da ita.

She is feeling really suffocated da saka idon da Ahmed yake mata har Allah Allah take ayi exams din ta tattara taje hutu lagos kawai ta huta da fitinarshi while ata wani bangaren kuwa kkri fahad yake dan yaga yaja ra'ayinta ta dawo hostel d zama wanda shine zai basa cikakken daman samun lkci da ita.

Tun Bayan tafiyar su Ahmed din da kwana uku kwasam saiga kafayat ta dawo gidan itama saidai tun dawowarta batay magana ma kowa ba duk dai ta canja tayi baƙi ta dan zube wanda daga ganinta kasan ba lafiya kalau take ba.
Chapter 100 · 0% Book details