← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 157

Sashe 120

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka zagaye falon daga bisani ta shige daki dashi ya bita ya kwaco wayar tureshi tay akan gado tana kufcewa a hannunsa ta fice a dakin
Da mugun gudu kafin ya taso ta kulleshi aciki ta waje batare da ta dauki kowani waya ba.

Jikinta na rawa tazo ta zube agaban ADIAHA wanda ayanzu kiris ya rage ta dena numfashi sabida amount of jininta dayake ta zuba.

Hakanan tay kkri wajen dagota, azaba yasaka Adiaha ta daddafa kafadun lokacin ana naman tara saura na dare kusan kowa yana cikin sashensa, ita kadanta ta fitar da ita waje cikin gaggawa wai dan kar Ahmed yazo ya same su anan.

Suna fitowa Biodun ya leko waje.

A razane yake kallonsu ganin da kyar da wahala yasrah take jawo adiaha sabida nauyinsu ba daya ba,biodun yace madam lafiya ina zakuje?shud i call the family

Cikin katseshi yasrah Tace nooo noo ..yaa Ahmed ne yace muje musameshi a hospital

Yace a"a haaa amma ai naga dazu ya dawo.

Ta bata rai tace ya kara fita.

Pls Help me and call the uber using ur phone its emergency and i can't drive.

A gaggauce ya dauko wayarsa "Yace why cant u let me take u, ai nasan asibitin da oga dami yake aiki.

Yasrah Tace no thanks can u just do what i ask u to do, okay?

Ganin ta bata rai kamr batason taimakonsa yasaka ya kira mata uber mai uber yana isowa gaban su yatayata tasaka Adiaha aciki suka tafi agaggauce

Daga nan kuma sai yaji Ta rasa ta ina zata fara

Gabaki daya kanta ya kulle gashi kuka kawai takeyi tanajin kanta daban dan bata taba zagin wani babba har haka ba.

Tunanin zuwa asibiti tay amma toh ko kudin biyan abun hawar da suka shiga ayanzun ma bata dashi.

Directing dinsa tay akan daya kaita gidansu maryam after a while suka isa asalin babban mansion su maryam dake cikin anguwar gwarimpa.

Sauka tay tace ma uber tana zuwa.

A gate ta tsaya bata shiga ciki ba sabida yanayinta na tashin hankli ga idanunta duk sun kumbura sunyi ja

Dake mai gadin ya san ta sai bai bata ciwon kai ba yaje ya kirawo mata maryam din ta fito.

Da wuri maryam ta taho tsabar mamakin jin wai yasrah tazo gidansu a wann lokcin haka kawai jikinta ya bata ba lafiya ba.

Tana fitowa Ganin yanayin yasrahn yasaka ta fahimce ba lafiya.

Ko amsa tambayoyin maryama batay ba tace mata she needs her help tabar kominta agida tana son takai antynta asibiti its an emergency.

Ganin yanayinta yasaka maryam takoma ta dauko kudi ta ara mata
Ta bata karamin wayarta aro tace mata suje tare amma yasrah taki sam tace mata dare yay kawai zata kirata dan batason asirin familynta yaje yana tonuwa.

Bayan barinsu wajen wani private hospital takai adiaha ta biya kudi tay komi aka fara attending dinta akay stabilising zuban jinin wani bacci ne ya dauketa atake.

Ta kasa zama sai jeka ka dawo take ta kira lambar iyayenta yafi sau ashirin saiji take bata shiga kwata kwata.

Haka kawai jikinta ya bata cewa Ahmed zai riga ya kirasu..but what will he say? Ko reporting kansa xaije yi? Mtswww.

ji take ta tsaneshi duk dama a Kasar ranta tana jin kamar bazai iya aikata abunda yakeyi din nan ba. Kirar Maryam ya shigo ta dauka maryan duk ta damu tanata tambayarta meya faru, she have no choice face ta gaya mata cewa rigima ne kawai ya shiga tsakanin antynta da yayanta akan barin da tayi..sama sama ta gaya ma maryam duk abunda ya faru duk dama maryam din ma cewa take laifin Adiaha ne datay komi abayan idonsa.

Har wajajen 11 Ahmed yanakan waya da iyayen nasu dan har aransa baison yasrah ta riga shi kiransu ya shiga uku dan yasan bazai tsira ba.

kamar yadda akace maganar farko shine ya fi daukar tunanin mai sauraro haka nan shima Ahmed ya lullube laifinsa
Ya bayyana na matarsa a fili baigaya musu ya bugeta bama.

Su hajiya khdija suka dinga shan mamakin Adiaha, lamarinta da nurse duk shi yafi sosa musu rai bana wasa ba.

Hajiya khdijatu da hajiya maimuna duk saida sukayi ta bambami akan hakan da Adiaha tayi suka bashi hakuri.

Saida suka gama snn ya gaya musu cewa ai ya mata fada amma yasrah ma bayanta take bi ta kulleshi a daki wai dan karyayi ma Adiaha fada

Duk dai basu dau abun serious ba suka ce masa yay hakuri kawai yasrah ai yarinyace suma kuma zasuzo Abujan nan da kwana biyu.

Harsaida ya gama dasu snn hanklinsa ya kwanta
Yafara tunanin inda zasu shiga sabida baiji motsin kodayansu ata waje ba

Anan dakin yasran ya kwanta babu halin fita gashi baison ya kira kowa yazo abude shi bare har asan halin da suke ciki.

Kwanciya yay atakure yana lumshe idonsa babu abunda ke dawo masa sai maganganun yasrah.

Tsaki yake jerawa cos He felt too big to accept the truth, Adiaha doesnt deserve this from him"
He knws saidai haushi take bashi, Kamr yadda yasrah tace aiko ma yayane yakamata ya sota yakuma ji tausayinta tunda rayuwarta gabaki daya ta dauka ta bashi yakanji hakan aransa amma bazai iya ba

he feel too egoistic gani yake ai bashine ya sakata tay secrificing kanta mashi ba.

Baida wani dalilin da zai tursasa kansa dan ya sota he cant, he cant musmm ma yanzu dayaji ta kara bata masa ransa akan batun cikin shi daya xuxxuba abanza.

Duk yawan guilt din dake cin zuciyarsa haka ya danne da zafin zuciya yanajin cewa yasrah bata kai wacce zata sakashi ya fara son abunda baiya so acikin ranshi ba.
[7/19, 9:11 PM] SURAYYAHMS: Ata fannin su yasrah kuwa wajajen 10;30 na dare lokcin tana tsaye taji an dafata daga baya a tsorace ta juyo suka haɗa ido da Fahad.

Da Mamaki take kallonsa sanye yake da bakin jean da rigar sanyinsa mai hoodie ya rufe kanshi da shi nan suka gaisa ta tambayeshi meyake yi anan bai boye mata yace mata wajenta yazo dan awajen maryam yaji labarin cewa suna asibiti suka dai ita da antynta.

Aranta Sam bata so hakan da maryam tay mata ba, dan kuwa batason tana involving dinsa acikin family issures dinta sanin cewa yana sonta ita kuma bason shi takeyi ba sai dai as a friend.

Tayi tay dashi akan ya tafi gida dare yayi amma yaki mata sam, duk wani karya da kwane kwane ta masa amma haka yaki ya turje yace saidai ya taimaka mata shima as a friend.

Duk matsinta haka ta hakura suka zauna a reception suna kallon tv daga bisani suka dawo suka zauna ata bakin kofar dakin suna dan hira
Duk dama taki sam tasake jikinta dashi .

Yayi yasha cikinta yaji asalin matsalar amma firr haka taki ta bude mishi asalin labarin.

They just discussed few things about it..

Kamr part din da Adiaha tay taking action abayan idanun mijinta wanda ya jawo duk wnn fushin dayayi.

Yasrah ita kadai tasan meyasa take kushe halin Ahmed, fahad ma kamar yadda maryam tace haka shima yake fada cewa laifin Adiaha ce, cos such a sensitive matter ba'a boye ma miji sabida akanshi auren ma zai iya karewa mai gabaki daya.

Yace ma yasrah shikansa yasan bazai iya tolerating yaudara ko karya a aure ba. Adiaha shud ave told her husband dat akwai matsalar datake fuskanta she did not once but twice ai dolene ransa ya baci kam.

Yasrah har tagaji da defending din Adiaha tay shiru cos she cant start telling all her friend cewa ga irin secrifices da Adiaha tay ma yayanta shiyasa aranta take tunanin bazasu taba ganr dalilin dayasaka take ganin laifinsa ba.

Bisa ga dalilin da Fahad ya dinga bata yasa ta amince yes Adiaha batay daidai ba..but still gani take dat does not warrant him to treat her like dat. Ga zagi na cin mutunci ga duka haba. Sai kace wanda baisan darajar uwarsa ba.

She feels like that was an immature way of dealing with the problem.

Aganinta ko acikin nitsuwa zai iya daukar fansa bada cin mutunci ba.

Gani take kawai kamar baisan darajar Matarsan bane asali bcos he got her so easily and cheaply kuma yasan bata da mai tsaya mata a yan uwanta ko iyayenta sai shi.

Haka sukayi musu akan issure din da fahad har asubahi yay snn ya kyaleta ta shiga room din shima ya tafi masallaci.

Har yanxu Adiaha tana kan bacci, Sallah yasrah tay dan dama hijabin datay sallahn ishai na jiya me ajikinta.

Tana idarwa nurse ta zo dakin domin ta dudduba jikin Adiaha, har ta gama ta tafi adiaha bata farka snn ta umarceta akan data farka tay wanka zasu zo su sallemsu cos she is stable now.

Ruwan zafi yasrah taje ta nemo awani room snn ta haɗa a bathrum dinsu ta taho ta zauna daf da Adiaha dake kkrin farkawa.

Kallonta takeyi da sanyin jiki dan saida hawayenta suka zuzzobo kafin nan idanun nata suka budu ahankli ta shiga lumshe idanunwantan thinking she will see Ahmed with her at that moment da taga babushi awajen sai yasrah dake binta da kallon tausayawa sosai atake taji wani karayar zuciya yakamata.

Runtse idonta tay cikin rashin jin dadin ganinsa da batayi ba, all she want is for him to forgive her and be by her side once again. Har ji take kamar taki bude idon har abada harsai anje ankawo mata shi.

Ganin yanayinta na runtse ido yasaka yasrah ta kira sunanta ahankli cikin snyin murya.

Daurewa kawai tay ta bude idonta ta kalleta wai dan kar yasrahn taji kamr tay mata butulci da rashin kirki.

Yasrah ta mata murmushi mai sanyi Tace good morning anty Reemah how r u feeling now?

Kikriran murmushi tay tace am fine my sister karki damu Ai Jikina yay sauki..

Ahankli Yasrah tace Alhamdullahi.
Chapter 120 · 0% Book details