← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 157

Sashe 47

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitar Adiaha daga sashen su kafayat duk bai isheta ba ta dinga zugashi, hatta abunda ya faru tace duk sharrin hajy khadijatu ce itace tace su dinga rainata inba haka ba haryaushe natar dansa zatace mata karuwa agidan inba raini ba.

Bayan ta gama pumfa shi da fushi ya nufo sashen hjya khadijatu lokcin Ta kammala saka nitynta kenan zata kwanta bbau sallama taji dirar mutum akanta ya shigo yana huci

Tace Alhaj bello lfiya

A harzuke ya nuna ta dan dan yatsa yafara mata masifan da batasan kanshi ba.

Munafuka azzaluma matsafiya kin cuceni kin asiricemin yarana na

Duk wani abunda ya faru saida ya alakanta dashi yana zaginta dashi cikin fusata da tsananin jin takaicinta da kuma haushi, duk ta rasa menene guda daya tay masa, sai kada mata warning yake yana daga jijiyar wuya yana hargagin akan yayansa da matansa kafayat yanamai ce mata bata isa ta rabashi da kowa nasa ba

Duk ta kasa fahimtar inda ya dosa har ranta ya matukar baci tafara maida masa martani cikin bacin ran itama.

Zaginshi tay tasss ta dada kufular dashi suka tayi kafayat na bakin kofar dakin tana babbaka dariyar mugunta a kasa kasa hartana hawaye

jikinshi bari yake yanayi kamr xai rufeta da duka
Itama jikinta bari yake tana nadaman zaman datakeyi agidansa dan aganinta wann rainin wayon da batay hakuri ta zauna masa da yaransa ba da bazai samun fuskan yimata shi ba.

Allah ne kawai ya takaita cikin darene sukayi tashin hanklin kusan kowa na sashinsa amma badan haka ba da tuni kowa yaji tashin sautukan muryoyinsu sabida kowa anan saida ransa yay mumunan baci..[6/15, 10:46 PM] SURAYYAHMS: Hajiya khadijatu sai ta fishi azalzala da masifa ta fara bude mishi wuta duk bakinshi ya mutu sai bari yake yana memeta magana yakasa yin gaba musammn dayaji tafara cewa inba tsoro bane ya saketa mana, Meyake jira, ya saketa ya cinye yayansa da matarsa. Ita ba dan shi take zama ba sabida yaranta ne,kuma in har yanajin ya isa ya saketa yanzun nan yaga ko bazata bar masa gidansa har Abada ba.

Duk gorin arziki saida tay masa tace masa tafi karfin abunda yake dashi dashi da yayansa ma ita ba matsiyaciya bace irinsa.

Tunda tafara fadin hakan kirjinsa ya fara ciwo jinin shi yafara hawa sama sama masifar ma jijjijewa yakeyi abakinsa yana ta cewa bazan sakeki ba saina ga dama.

Kafayat najin yafara sanyi ta wantsalo ciki dan bata taɓa tsoma baki idan yanayiwa matarsa magana ba yau kuma datakeji da rashin kunyarta itama tazo tana huci tafara harbi iska a kasuwa tana cewa hajiya khdijatu tana kishinta ne shiyasa take sakawa yaranta suke rainata.

Rainin wayon yabi ya ishe hajy khadijatu
Dama can bahaushe yace duk yadda akayi da jaki sai yaci kara..

Bakowane yake gane karatun kurma ba amma ai kowana na fahimtar zafin dorinarsa.

Kafayat Batay tsammanin jin bugu ba saida hajya khadijatu ta capko ta taji ta kasa iya motsi ahannunta gabaki daya,da sauri yazo zai raba suka tureshi akasa,

wayan wuta ta zare ta zaneta a dakin ciki da bai yadda uwa take zagewa ta buge yarta ba fadar raba raini ba, kafayat ta dinga rusa ihun ceton rai

awuya da hannu da kafa da gadon baya ta zaneta tasss inda zai shigeta sosai har fitsari ya fara tsilala ajikinta kadan kadan.

Da kyar ya iya tashi a kasan sabida mugun buge kunkuminsa dayayi snn kwaceta ta fice a guje tana sose sose tana kuka.

Acikin masifa hjy tace shegiya yar iskan yarinya toh ni ba sa'ar uwarki bane bare ke. Shima ta juyo ta tsigile sa tass.

Fadar nasu bai kare ba saida ya tsinka mata mari mai karfi daya sakata faduwa akasa tare da dawowa cikin hayyacinta. Duk masifar nan batay mishi kuka ba saiyanzu.

Cikin hawaye tace
Zakayi dan danasanin sanina arayuwarka bello

A fusace ya fice dakin yabi bayan kafayat yabarta anan tana kuka sosai.

Da kyar hajiya khadijatu ta rarrasheta kanta ta dena kuka duk dama yau din nan sosai suka kaita makura, neman layin addanta ta dingayi har safe bata daga ba dan dama kayanta kawai take son ta kwashe anemeta arasa agidan dan ta tsani abunda zai jawo mata cin mutunci da rainin wayo. duk dama ta zane kafayat jiya amma hakan baimata wani dadi ba dan aranta bataso kwata kwata wani abu akan miji ya shiga tsakaninsu ba.

A fannin kafayat kuwa saida aka mata jinyar jikinta sann ta samu bacci tunda yace mata ya rama mata ya mare hajya khadijatu shikenan hanklinta ya kwanta ta yafe masa sukasha baccinsu.

Duk yadda hajiya khadijatu takejin bakinciki da damuwa hakanan ta cije ta daure dan bata son hakan ya jawo wani babban lamarin da zai shafe rayuwar yayansu musammn ma Ahmed.

Bata kuma son Abunda zai kawo mata koma baya akan qudirinta na komawa zama a lagos datayi,ata wani fannin ma faruwar hakan yay mata daidai sai a rabu kwata kwata inda bazata na zuwa yi ko wknds a gidan acikin sauki ba.

Badon ranta ya so ba haka ta danne maganan aranta bata nunawa kowa yanayin datake ciki ba sai Addanta,Allah Allah take gobe ma yay brother kazim ya tafi Can kasan waje ya zamo babu wani sauran mai danneta da kalaman hakuri. They mean alot to her tasan irin ciwonvda sukeji akanta musmmn ma idan tace zata bar rayuwarsu wanda aynzu bata da wani babban buri face taga tabar Abujana mai gabaki daya.

Yau kwata kwata bata fito ba tana sashenta kafayat ce taci duniyar ta da yar tsinke ta saka kidi da sassafe ta dinga rawa tana habaice habaice duk dama babu wanda ya kulata.

Yau din da sassafe tun Ahmed bai fita aiki ba ta kime ajikin alaji bello snn ta aika aka kira mata Adiaha cike da gatse da rainin wayo take fmr tuhumarta akan girkin datadenayi agidan gaba daya...wani irin tsula tsiyarta takeyi tanamai cin duniyarta da yar tsinke. Alhj bello ya bawa Adiaha oder akan dataje tayiwa kafayat breakfst.

Ta dawo zata shirya taje kenan Ahmed ya bata ransa ya hanata fita ko ina, Kafayat tay ta jiran breakfast daga wajen Adiaha har tagaji ta fito da kanta ta samu lokcin duk sun taho gaisuwar safiya acikin gida.

Ganinsu duka yasaka kafayat ta kara kaimi wajen taro kisisina da karairaya da kaudi tafara dagowa da maganan girkin tanamai cewa Dolene Adiaha ta dawo musu abinci akan lokci

Babu wanda ya kulata acikinsu saida brother kazim ya dauko cheque din kudi mai dan yawa ya mikawa baban nasa tare da gaya masa officially cewa gobe zai koma America bakin aikinsa.

Lokaci guda kafayat taga an shashantar da ita Alhaj bello yaga kudi shaf ya mance da abunda take cewa....sai addua yake ma dansa dan ya jima bai basa kyautan kudi irin haka ba.

Sukuwa Dansu kara cusawa kafayat baqinciki yasaka a lokci daya suka janye hanklinsa izuwa garesu gabaki daya suka maida ta kamar bata cikin falon dan kuwa maganansu kawai akeji su kadai.

Duk sun dago abubuwan dayake dada tunzira baban nasun, rashin kudi, rashin nuna kulawarsu akansa da yan uwansa da kuma sihirin kafayat wanda basu sani ba tukuna.

Brother hamzat yace masa zaije ya duba su anty mojushola magann kai musu kudin magani.

Ahmed yace matarsa bazatana girki agidan ba sabida zata fara zuwa islmic school kuma higher islam ne mai hade da boko da arabi, yace amma zai dauki nauyin biyan musu cook, dan haka anemo kwarraiyar wanda ta iya girki akawo yay alkwari shine zaina biyanta.

Wann mganan duk shine yaje ya cakke tsakiyar kirjin kafayat ta zabura kmr tababbiya tafara kawo dalilai na hana Adiaha na zuwa makarnta

Alhaj bello har zai biye mata, brother kazim ya bata rai yace inhar bata son mai aiki sai kowa ya dinga fitowa yana girkin dakansa agidan.. duk haushin su ya cikata ta tashi a zuciye ta bar wajen ta koma daki tanajiran sa ya gama ya shigo ta balbalesa. Kawai daga ganin kudi wai harya canja mata. Tsaki akan tsaki takeja.

Gabaki daya ranar bai mata sugar ba gashi hjy khadijatu taki fitowa tsakar gidan bare ta jawo mata wani masifar ayau.

Ata fannin Adiaha kuwa yau zaman kadaici tay domin kuwa Ahmed bai dawo gidan da wuri ba snn bai dauki kiranta ko sau daya ba. Babu dama ta dan leka waje sai ranta ya baci sabida irin habaici da gulmanta da su anty nurat sukeyi kwana biyun nan.

Tunda Ahmed yace zaina daukar nauyin mai girki shikenan suka dawo dashi abun magana suka fara cewa ta shanye shi da maganin mata. Har yau basu dena mata gori akan abubuwan da suke dashi wanda bata da shi ba kamr aikin gwamnti, business da kuma mota.

Yauko wani runtsawa bata samu damanyi da wuri ba sabida rashin dawowar Ahmed gidan gabaki daya,.

sai can cikin dare ya tura mata tex yace mata aiki yakeyi bazai dawo ba sai gobe, kwanciya tay da tunaninshi aransa tanajin daren daban sabida kewarshi datakeyi aranta sosai.

A sashen hjya khadijatu kuma babu abunda takeyi face tattara kayan ta masu amfani wanda tasan dolene zata bukace su a can dan sotake in ta tafi karta samu wani dalilin dawowa gidan nan kusa.

Iya abunda ta wuni tanayi kenan a room dinta tare da shirya abubuwan da sukayi saura na rayuwar Yasrah, dan izuwa yanzu komo na yasra zai dawo hannunta ne gabaki daya
To keep her safe and away daga political chaos din sabuwar mukamin da aka bawa hajy maimunatu da zata zo ta hau kai inta dawo kasar nan.

Bayanin da zatay wa Ahmed dik ta kammala shiryawa..yasran ne ma yau tayita tayata hira ta dan kwantar mata da hankli har dare yay bataji damuwa aranta sosai ba.

Awajenta da Adiaha jisuke kamar safiya bazatay akan lokci ba.

A fanni anty adizat kuwa dik damuwar rabuwa da mijintane ya saka ta dawo wani iri aranar ko runtswa bata samu damanyi ba dan bakaramin sonshi takeyi ba shiyasa take karajin ta tsani Adiaha data saka yay fushi da ita na kwana biyu.
Chapter 47 · 0% Book details