← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 157

Sashe 21

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakaramin shiga cikin damuwa yau tayi ba har yamma yay bata tabuka komi ba, su anty adizat ne ma suka zo suka dan dubata sama sama da yaranta suka tafi daga nan babu wanda ya sake dawowa sashenta ya dubata.

Yayunsa mazan dama bakasafai ake ganinsu ba,brother kazim already ya tafi lagos yin wani business meeting tun bayan tafiyar hjya khadijatu katsina hutu lastweek.

Brother hamzat kuma bai fiye samun zama sosai ba saida daddare inya dawo.

Cikin dare Adiaha ta kasa bacci sai kuka tanason koda sau dayane Ahmed ya bude wayarshi koda zata bashi hakuri taji sanyi...

Tay nadamar kulla alakar datay da Banji har washe tanakwance akan gadon ta tana zubda hawayen danasani musammn ma dataga Ahmed bai kwana agidan yau ba.

Gashi tana farkawa sassafe anty adizat ta aiko sulu yazo ya gaya mata cewa wai idan ta samu sauki tafito tay musu abincin safe.

Hakanan ta daddafe tay wanka ta fito ta yi aikin gidan kamr yadda ta saba dik bata jin dadi ajikinta sosai.

Fanninsu su kafayat kuwa acikin satin nan daya wuce banda yawan zuwa gidan goddess babu abunda sukeyi da mahaifyarta, hardai tazo ta kulasu ta gaya musu abinda zasuyi domin kominsu ya dawo daidai.

Duk matsinsu anty mojushola akan zancen bikon kafayat haka hjy fatihat taki sam ta amince musu akan kafayat ta dawo, ja musu aji ta dingayi harsai da ta kammala shiryata tsaf da maganin da suka karbo. Ranar lahadi ranar ne Ahmed ya je katsina wajen mahaifyarsa, at same time aranar aka dawo da kafayat gidan alaji bello aka sasantasu.

Hjy fatihat kafin ta tafi saida ta jadaddawa kafayat dokokin da zatabi dan su cimma burinsu akansu.

Tana son ace kafayat ta samu cikin alaji bello akan lokaci sabida ta samu daman da zata walakanta kowa da kowa acikin salo,sosai ta gyara kafayat ta mata guzurin maganin mata sann ta zage ta koya mata yadda zatana gamsar dashi.

Kafayat duk batason hakan aranta amma tunda goddes ta gaya mata cewa zata iya raba auren AHMED intana gidan shikenan taji aranta zata iyayin komi kodan su taru suyi asarar rayuwarsun atare.

Yau tunda ta shafa wani kwalli a idanunta ta kalle alaji bello dashi shikenan kuma ta samu daman yin masa duk abunda taga dama, intace masa tashi sai taga ya tashi, zauna saitaga ya zauna, da daddare haka ta bashi abinci mai barbaden garin magani sukayi sex ta gamsar dashi sosai yaji dadi yay mata irin tarairayar datake so din abaya duk dama ba nashi takeso...

Daga nan shikenan ta fara samun gangararsa tafara gaya masa cewa lallai saidai ya roke yaransa amaidata sabuwar gidan inhar yanason sucigaba da zama a amtsayin miji da mata cikin kwanciyar hankli.

Ahmed kuwa tunda ya isa katsina duk wata damuwarsa da fushinsa sanda yakau sabida yadda yaje yaga mahaifiyarsa ta canja ta warware tay bulbul tana fara'a kamar ba ita ba.

Hutun sati daya datay anan din babu kowa agefenta sai masu aiki, hakan yasaka mind dinta ya samu cikakken hutu da nitsuwa tareda kwanciyar hankli shikuma sai ya boye mata damuwarsa.

Kwana biyu yay mata suna dan waya da sauran yan uwansa har suka fara maganan zancen dawowarta Abuja sai Brother kazim yace zai taho ta katsinan zaizo ya samesu saisu taho tare.

Ahmed was busy having a good time tareda mahaifayrsa dan yana samun nitsuwa in yaganta acikin kwancyar hankli, abudayane mamansan tay noticing daga yanayinshi dataga kamar baya kirar matarsa bare kuma yamata magananta.

Kusan tunda yazo gidan kullum saita tambayesa lpyar Adiaha saidai yace mata lpyarta kalau tana tare da su anty nurat agida daga nan bazai kara ce mata komi ba.

Jikintane yafara bata wani abu game da zaman auren dantan.

bayan kwana uku ana washe gari zasu baro katsina su dawo Abuja

Da safe haka tana zauna abakin gadonta tana waya suna yar doguwar hirarsu da suka saba da yar uwarta hjy maimunatu awaya nan take gaya mata abunda take lura da Ahmed a kwanan nan. Tausayi Adiaha take bata tun datasan dacewa ta rabu da komi nata ne akan danta Ahmed.

Hjy maimunatu kuwa abun bai wani dameta ba sabida bata kaunar duk wasu tarukucen kabila aganinta ko Adiahn ma inta samu waje zatazo ta fandare.

Acikin yanayin damuwa da halin dan nata Tace Adda karki wanisha bakin Ahmed dayawa, wani bin shima halayyar ubansa yananan ajikinshi suna da son kansu idan mace ta nuna tana sonsu sosai sukan nuna cewa basusn darajarta ba..yarinyar nan ta rabu da komi nata ne dan tana sonshi amma tunda yazo wajena yau kwanansa uku kenan amma bantaba ganin ya kirata awaya sunyi magana ko sau daya ba.

Hjy maimunatu tace kedai karki tsawwala masa tunda dai matarsa ce. Kibari inkin koma gidan saiki bincike meyene matsalar.
Sann kuma karki manta sa abubuwan da muka shirya nidake.

Tace toh Adda in sha Allahu bazan mance ba zan kuma shiryawa tarbanku dake yasrah.

Ahaka suka kare wayar.

Washe gari around 10 am brother kazim yazo katsinan ya samesu suka shirya a nitse suka sissiyo tsaraban da zasukawo ma kowa
Sai can da yamma suka biyo jirgi su ukunsu suka dawo Abuja.

Acikin kwanaki ukun nan lokcin Adiaha duk ta galabaice ta shiga damuwa sosai tun ba'a ganewa har aka fara ganewa sosai.

Saiyau da safe ta samu karfin gwiwar turawa banji tex message ta bashi hakuri tareda fayyace masa cewa laifintane bana Ahmed ba. Duk ta gwada masa cewa tay nadamar daurawa Ahmed wani sabuwar pressure akansa bayan ga yanayin yadda iyayensa suke ciki, ga zafin betrayl din da kafayat tay masa snn at same time yana tare da kunci da damuwar cewa mahaifyarsa batajin dadin jikinta sabida abinda aurensa ya jawo ma nata auren.

Koda banji ya karanta text din nata shikansa aransa baiji dadi ba, musmmn ma datace masa sai yanzu ta fahimce duk abubuwan dayake gaya mata nacewa akan ta kara hakuri da Ahmed izuwa lokcin da komi zai dan lafa masa.

Baice mata komi ba snn baiyi mata reply ba, tun ranar da suka bata da Ahmed bai kirashi ba saiyau, normally suka gaisa yanemi su hadu saiyake ce masa yaje katsina amma zuwa ajima zai dawo zasu iya haduwa agidansa da daddare.

Adiaha batama san yaune Ahmed zai dawo ba kawai ganinsa tay dataje cikin main house gaisheda hajiya khadijatu data dawo.

Kallon da hajy khadijatu ta dinga mata haryasa taji tana tsarguwa dan ita kanta batasan da cewa ta zabge sosai ba. Duk kowa saida aka bashi tsarabarsa.

Bayan dan wani lokci suka watse a sashen hajiya khadijatu kowa ya tafi bangarensa da mijinsa da yaransa.

Itakam Ko kulata AHMED baiyi ba dan ko gaisuwarta bai amsa ba, suna komawa sashensu ya shige dakinsa ya kulle kofar ya fada wanka ya sauya kaya, kafinn ta hankara harya sace jiki ya fita batare da sanninta ba.

Duk dama bata shirya ba
Amma taci alwashin yau komin dare saita bashi hakuri..

Bayan sallan ishai acan waje suka hadu da abokinshi banji suka yi magana ta fahinta snn suka shirya kansu cikin dan kankanin lokci.

Banji yace masa yy hkra bawai yana shiga hidimar iyalinsa bane, kawai tausayin Adiaha ne yake rufe masa ido musmmn idan ya tuna yadda ta rabu da komi nata tazo tana zaman aure dominshi.

Ahmed baice komi ba kawai ya nuna masa ya fahimce komi kuma bason ranshi yake ignoring dinta ba kawai damuwane yake masa yawa akansa.

Ahaka suka bar maganan ya wuce tsakaninsu suka cigaba da wani hirar na daban wanda bai shafe rayuwar familynsu ba.

Kafin nan a fannin Kafayat duniya sosai take kaimata dataga cewa tunda ta dawo gidan alaji bello yay sanyi ya dawo sai yadda tayi dashi. Gashi yanzu tasha gyara dn irin maganin mata mai asirin nan suka siya take amfani dashi.

Acikin kwana ukun nan saida ta dedeta masa hankli tace masa sam saidai kawai yasan yadda zaiyi su koma sabuwar gida..

Yau alaji bello baima iya kwana acikin gidansa ba, tsabar masifa da takuri irinna kafayat haka ya koma wajensu anty mojushola ya zauna musu zaman diris yace saidai suje su roka masa yayansa amaidashi da kafayat sabon gida.

Anty moju tay tunanin duniyan nan bata samu mafita ba sabida suna mutuwar jin tsoron taba hjy khadjitu kar yar uwanta hjya maimunatu
Tazo ta kullesu.

Tana cikin wann damuwar ne saiga wata kawarta ta buga mata waya, nan suka tattauna tace mata tasha kuruminta ita tana da hanyar da zata saka alaji bello ya koma gidan yayansa da matarsa kafayat basai ma anroke kowa ba saida suka tsara faruwar hakan sann hanklin Alaji bello ya dawo jikinshi ya saamu ya koma gidansa acikin kwnciyar hankli

Anan kuma Adiaha tay ta jiran shigowar Ahmed waidan ta bashi hakuri babu irin kalmomin da bata nemo masu dadi dan ta bashi hakuri dasu ba amma haka taji shiru bai dawo gidan ba har dare yay nisa.

Gashi tanajin mugun tsoron kiran lambar banji

Haka tay ta jeka ka dawo a dakinta ko bacci bata samu damanyi ba bata sani ba shi yana can a kwance acikin motarshi acikin gidan yanata bacci hanklinshi akwance.
[6/8, 6:57 PM] SURAYYAHMS: Washe gari da sassafe harsai bayan da aka idar da sallahn safiya a masjid kafin nan Ahmed ya dawo cikin bangaren sa, wayarsa ne ahannun shi yana tafiya yana latsawa acikin nitsuwa.

lokcin Adiaha ta fito kenan daga dakinta sanye da bakin hijabinta dan daidai idanuwanta duk a kumbure sabida rashin baccin da bata samu kwana biyu, sauri take zataje kitchen tayi musu breakfast taci karo da inuwarsa abakin kofar.

Tsayuwar cak tay jin gabanta yayi mummunn fadi da suka hade ido waje guda dashi cikin sauri ta sauke kanta kasa muryanta na rawa rawa tace gu..gud..good morning hubby.."Ka tashi lpya? Da har kamar bazai amsata ba, ya hade ransa, muryansa ciki ciki yace lpya snn ya wuceta ya wuce dakinsa direct ya kulle kofarsa ta ciki.
Chapter 21 · 0% Book details