← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 157

Sashe 103

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga ciki kuwa doc yay duban duniyar nan baiga ta inda yasrah tay karaya ba, harya daga waya zai kira Ahmed ta katse shi cikin langwame murya tare da shagwaba tace masa sam bata son agaya masa komi kawai ya bata wayan ta kira mumynta..

Kuka ta dinga mishi tana harhardo masa karya har saida yaji tausayinta ya bata wayar snn yace bazai gaya ma Ahmed komi ba tukuna..

Tana amsar wayar ta dannawa hajiya khadijatu kira ta gaggaya mata abunda yafaru jin tace mata wai har ta karye a hannu yasaka hanklinta yay mugun tashi..

Daga waje Ahmed yanata ziriya cikin damuwa Abun ya ishi Adiaha tafara kkrin tuhumarsa akan meyasa yake over reacting akan case din yasrah as usual lkci guda ya maida magana ya dawo kanta,memekon ta samu amsa abakinshi sai shine ma yake neman karin bayani abakinta na gaskiyan abunda ya faru.

Tsorata ta dayay da maganganun rabuwa da ita yasata tay confessing tace mishi itace ta tursasa fahad ya shiga dakin wai atunaninta ai saurayin yasrahn ne.

Ahmed yafara jin kamar ya shake mata wuyarta awajen. Har office dinsa yajata dan kawai yay mata isashen masifa domin ya huce gabaki daya.

Bayan ya masifetan kuwa haka ta fito tana kuka kamar ranta zai fita dan ya jima bai mata gori akan rayuwarta ba sai yau daya kirata tsohuwar karuwa..dayake cewa ta dena comparing kanta da sistersa, sabida ba irin rayuwar datayi da maza na watsewa kowacce ya mace zata yi arayuwarta ba.

Adiaha tabar Asibitin kenan saiga kiran mum dinshi yasha mamaki sai yaga ko saurararsa batay ba tace mishi acikin daren take son ya kawo mata yarta da tsananin bacin rai ayanayinta tafada.

Hakanan yasrah ta dinga labgwame wuya wa doc tana bashi tausayi tace mishi sam wajen yana mata zafi ya saka mata bandage har sai intaga mum dinta kafin nan ta fadi gaskiyan cewa bata karye ba.

Doc kuwa Duk ya dauka post traumatic stage na home sickness take ciki sai kuwa yay mata zak zak abinda take so snn ya mikata wa Ahmed daga nan taga ya wuce dasu airport yay booking musu flight zuwa lagos ya biya komi.

9:30pm suka samu flight din abuja to lagos acikin daren, yadda yasrah take narkewa tana pretending tana kafafa da hannun zaka rantse da gaske karayan ne.

Duk ya damu zuciyarsa na bugawa sosai haka suka wuce lagos batare da suncewa junansu uffan ba suka isa lokacin ana neman goma da rabi ya wuce da minti 15.

Isarsu gidan hajiya khadijatu ta saka aka kai yasrah room dinta tun anan ta rufesa da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba har kamar zata wanka masa mari akan fuskansa cikin daren.

Yau tsabar damuwa ma baiyi sallahn isha'i ba sai can wajajen karfe 1 na dare kafin nan ya samu ya runtsa bacci kadan..

Ata fannin Adiaha kuwa tunda ta isa gidan sai ta ji sam ta kasa zama taci kukan harta share hawayenta amma bataji sanyi aranta ba..

Wani zuciyar na gaya mata cewa tay kuskure amma wani ce mata yakeyi batay ba dat she is just protecting her husband.

Haka tay kwanan jiran ganin dawowarsu gidan har karfe biyu saura tana ziriya kishi da damuwa yasaka agaba batay bacci ba.

Harsai can wajajen asubahi snn baccin ya kwasheta na dole anan kujeran falo inda take jiransu ta kishingida tahau bacci mai wani irin nauyi...

Jiya tun da suka izo lagos Haka yasrah taki ta kula kowa acikin iyayen nata, kwanciya tayi ta kwashi baccinta mai ji da lafiya sai har washe gari da hajya maimunatun ta sake kiransu awaya daga katsina dake tunda ta dawo daga dubai tana can snn ta kulasu.

Idon yasrah murmur a bushe cikin sanyin shagwaba ta zauna tafara gaya musu duk abunda ya faru tare da ce musu ai likitan ma yace mata bata karye ba..

Hanklinsu ya kwanta da sukaji hakan amma Hjya khadijatu duk abun saiya bata haushi sosai yadda Adiaha taso shiga tsakanin su da irin wann salon makircin sai kuma mamakin Adiahan ya fara cika mata kirji.

Hjiy maimunatu kam ko ajikinta dan dama ita bata taba yarda da matayen kabilu ba.

Acikin ranta she was quiet happy musmmn data lura kamr hanklin Ahmed din sosai yake kan yar uwansa yasrah and dat means komi zai iya zamo mata daidai kenan anan gaba.

Hirarsu sukayi har suna dariya shikuma yanacan dakin daya kwana yanata waswasin yadda zai fara fuskantar mahafiyarsa da gaisuwar safe duba da yadda jiyan tay mummunan fushi.

Hakanan dai ya daure ya fito a shirye kayansa na jiyan ne still ajikinshi yay sallama ya shigo inda ya samesu su ukunsun sunata waya yasran ta dora kanta akan cinyar mum dinsa idonta a lumshe jin hjya khdjan tana shafa gefen fuskarta ahankli suna hira.

Kirjinshi na bugawa yay sallama ya karaso duk a tsarge ya tsuguna ya gaishesu, tare da tunowa da abunda Adiaha ta gaya masa ya gane cewa ba laifinsu bane duk sai gwiwansa ya sace yay sanyi.

Hjy khadija fushi takey dashi still amma hjya maimunata bata ɓata ranta ba bare harta masa fada,sai ma hakuri datake basa akan yana daurewa yana bincike kafin ya yanke hukunci..

Bayan nan ta bukaci zatay magana da hjy khadijatun in private hakanan ta tashi ta fice ta barsu awajen atare..

Kallon yasrahn ya dingayi
Da idanun tausayi ganin ta juya masa baya ko kallonsa yau batayi ba bare ta gaishesa wanda hakan ya dada sawa yaji hanklinsa ya mummunan tashi duk yanajin babu dadi aransa daya karya mata hannu...

Dada lumshe idonta tay jin ya matso kusa daf da ita,bugawa kirjinsu yake atare duk taki ta motsa tsam ya tsaya yanata kallon kyakkwan fuskarta wanda kamar wani abu zai dauka akai mayun idanunshi masu cike da wani yanayin nadaban yana gangarowa tun daga kan karamin bakin ta har izuwa saman kirjinta inda yaji gabaki daya zuciyarsa ta tsaya cak bata bugun numfashi Hmm Sunan wani Abu wai zuciya da kwanji dan iyakan kirjinta dayake kalla ganinsu soo tender and full saida yaji tsikar jikinshi na tashi...

Yafi minti goma ahakan Motsin da eye lashes dinta yakeyi yasashi sanin ba baccin takeyi ba. Ahankli ya mika hannunsa batare da ta hankara ba taji saukar hannun nashi akan forehead dinta a firgit ta bude idanunta inda taci karo da nashi shanyayun idanun da suke nan stiff akanta cikin sarkafewa yake kallonta tana kallon shi jin wani abu kamr sihiri na jansu alokci guda. Saurin dauke kanta tay ya saka hannu tate da tallabo fuskanta yace "ya jiki?..kin amsa shi tay yace "hey"..are u still in pains? bari na duba hannun mana dada hade ranta tay tana kkrin tashi ya fixgota ta fado jikinshi ya rikota tsam sabida firgita datayi..

Wani iri taji ajikinta dan ji tay kamar ta danna masa ihu cikin kiciniya tace yaa Ahmad bana so kadena Muryanta kamar na mai shirin fashewa da kuka tace i told u to stop holding me like this.
Baisake tan ba yace toh in ina miki magana kina amsamin..cike da bori tace ni me zance maka?
Just leave me alone i don't want to talk to u ever!! Ahankli ya saketa ganin fushin datakeyi cikin sauke ajiyan zuciya yana kallon cikin kwayar idanunta yace so kawai nake san yadda kikeji..c'mon tell me.

Tay masa shiru tare da bashi baya, har zai kara jawota jikinshin tay wuf ta miƙe tsaye cikin masifaffen bori har ta mance da hannu..

..jikinshi har na bari ya bita tsayen cike da kulawa yanamai cewa
"Are u insane, ya zaki tashi haka..ko sai kin fama ciwon zaka gane kina bori. Yana fadin hakan ta tuna atake ta langwame tare da riko wajen kamr dagaske.

"Is it paining u? Jiya muna sauri ban tambaye doc ba..wai meyasa bai daure miki ba? Meyace miki? Isit dat bad karyewa ne ko gurdewa.

Cikin yanayin harara Tace "both..yamata wani irin kallo "bazaki fadamin ba kenan"..bakinta ta turo masa a sanyaye snn tace toh ina ruwan ka just stop worryn abt me okay? jikinshi ne yay sanyi ganin harta fara sauke masa hawaye masu sanyi..

Baya ta bashi tanakan share hawayen suna dada sauka alkcin ji yake kamr tana zuba masa ruwan zafi akan kirjinshi cos ya tsani ganin wnn hawayen nata..

Muryansa atausashe cikin saukar dakai yace Yasrah pls listen to me

Da murya mai saka tausayi tace i dont want to, kata fashe da kukan tay tace Ba zargina kakeyi ba,tunani kake ni zan kawo namiji daki na wato ni yar iska ce knn ko yaya? I think u said ma bani da tarbiya bani da hankli to ina ruwanka dani aida sai kadena damuwa da Hukuncin daka yanke akaina koda yanke min hannun akayi da sai kayi murna..i don't need ur fake sympathy!!

Tunda tafara maganan idanunshi a lumshe har cikin ransa yanajin bai kyauta mata ba.. he just have to bury his pride ya lallabeta. Hakan kuwa atake ya sassauta kamr bashi ba yafara mata magana atausashe yana maida mata abunda yaji aransa adede wann lokacin daya ganta tare da fahad.

Yace "shima baisan meya shiga kansa ba kawai ganin yaron ne ya bata masa ransa but he don't mean what he said yasan tana da tarbiya da kamun kai.

He care about her alot duk dama yana kakkauce wa baisan ya fadeshi a lokaci guda kuma kai tsaye.. sai amfani yakey
Da alakarsu na yan uwantaka yana gaya mata yadda take da muhimmaci arayuwarsa

Muryansa Cike da lallashi Yace "If i'm over reacting with you is bcos
I dont trust dos guys amma ke na yarda dake i don't want anyone to take advantage of u..idan na bari wani abu ya sameki yasrah it will hurt me badly,it will hurt all of us sabida ke amanace agareni da agaremu duka I made a few mistakes jiya okay..pls let me help with this.

Shiru tay batare da ta jiyo ba dan Har mamakinshi take sha yadda taji ya dauketa da mugun muhimmanci acikin zuciyarsa, wani bin yadda yake mata magana daban ne, tay kyam a tsaye bata juyo bama bare ta kallesa amma sosai mamkinsa ya cika mata kirji.
Chapter 103 · 0% Book details