← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 157

Sashe 44

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma haka fir taki ta gaya mata duk wani wahalan data sha a farko
Farkon zuwanta gidansa Kakar nata tasha matukr mamaki snn taji dadi aranta duk dama ta riga ta dago kwane kwanen Adiaha sosai tasan dolene kawai tana boye mata other side of the story domin iya wajen dadin kawai ta fada mata bata gaya mata wajen wuyan ba.

aranta tasan dolene akwai wasu kalubale in ma badaga wajen miji ba dole a samu awajen iyaye da yan uwansa.

Duk dabarar ta hakanan Adiaha taki fir tace komi akan Ahmed bare kuma familynsa har kakarta ta gaji ta share zancen itama, hira sukayi sosai kakar nata ta dada yi mata nasiha akan ta rike mutuncin kanta ta nemi nakanta tay investing kartayi zaman banza tunda tace mijinta yana bata kudi gudun bacin rana.

Duk wa'azin zaman gidan miji da kakarta tay mata iyakar wann shawarar kawai ta iya daukawa a mind dinta, she have already make up her mind to worship and love Ahmed like her demi god,.

kudin nasa ma ba ason ranta take son kashewa ba, she just want Ahmed to be great and all that, wanda ba komi bane yasata ta dauka shwarar investment saidan gorin da su anty adizat suka mata yau nacewa a matsayin house wife zata kare bazata taba zamowa irinsu ba.

Bayan sun kare wayar ta shiga tunanin abunda zatayi na business itama domin ta zama cikakkiyar mace mai abun kanta ko su anty nurat zasu dena raina mata wayo.

A fannin su alaji bello kuwa sai wajajen hudu saura zagayen su yazo

Dan wani daki ne haka aka shigar dasu gaban wani tsoho daya saka fararen kaya daga sama har kasa babu takalmin akafafunsa. Tun daga yanayin gaisuwarsu ya fahimce cewa su anty mojushola tsoffin customers dinsa ne.

Nan ta hau baje masa damuwar dan uwanta tace masa a duba musu aga ni menene yake faruwa da shi..

Mutumin yay yan tsibabbace tsibbacen sa yana mai karkada kararrawa sai can ya fara zabgawa alhaji bello wani bulalan ganye ajiki

Nan Duk suka rashi tsaye acikin yanayin razana sosai Yace musu Ai yaga mugayen aljanu ne da aka hadashi da su da kuma evil spirit mai karfi.

Yace musu aljanun sune suke sakashi kunci da damuwa da bakin ciki kuma inbaiyi wasa ba sune zasukaishi har lahira. Snnn acikin daya daga cikin matayensa daya itace take da hannun akan dukkan wani damuwarsa.

Atake alaji bello ya rude yafara zufa ann yafara musu sumbatu yana son lallai malamin ya bayyana masa wanda wacace acikinsu ke masa wann abun acikin matansa Duk dama ya gama kullawa aransa cewa khadijatu ne.

gashi yana mutuwar son khadijatun acikin ransa tun ba a fada ba yafara jin tsananin bacin rai atake zuciyarsa ta karye gabaki daya jikinshi ya fara ragwabewa yanamai jin tsananin azaba irinna cin amana daga wajen wanda yake mutuwar kauna.

Ganin rudewar da yayi yasaka Anty moju tasaka aka kaishi waje dacewar itace zata ji musu komi

Nan malami ya zauna ya fede musu biri har wutsiya bai boye musu komi ba duk wani kalar tsafin da shedananci da hajy fatihat da kafayat su keyi da wanda ta shirya shi ayanzu snn ya gaya musu dukan motive dinta akan dan uwansu karara.

Bakaramin kaduwa sukayi da jin dukn wani sirrin kafayat ba, hakan suka biya malami suka fito waje jikinsu a mugun sanyaye duk sunzo ne da zimman fada ma dan uwansu gaskiya.

Kamaar ruwa ya kwaso su haka suka fito amma koda suka fito falon basu sameshi ba aka ce musu yaje bayin masallaci zaiyi fitsari.

Nan anty mojushola ta jawo anty ramoutu sukayi can gefe inda babu wanda zaiji maganan da zasuyo snn tace mata sam karsu gayawa dan uwansu gaskiya na cewa kafayat ne acewarta idan suka fada zaiyi blaming dinsu yace sune suka tursashi ya aurota snn zai gayawa yayansa suma zasuyi blaming dinsu,hala ma daganan kuma shikenan alakarsu ta yan uwan jini ya kare kenan har abada.

idan kuma hajy khadijat ta iya yafewa mijinta suka dawo daidai zata sake kwace ragamarsa a hannunta su dawo masa banza, gashi akan shi da yayansa kawai suka dogara a duniyan nan basu da wani hanyar samun kudi ko wani madogaran yin rayuwa mai dadi face ta hannun sa da yayansa.

Tace ma anty ramotu Muddin maganan nan ya fito waje ba zallan kafayat kawai za'a kama ba hardasu dan haka su yanke hukunci kawai su zaɓe kansu inyaso su zasu san yadda zasuyi da makircin kafayat da mahaifiyarta in their own way.

Da kyar tay convincing din anty ramoutou dan abun su kafayat din ya girgizata bana wasa ba danko acikin mafarki bata taba tsammanin cewa kafayat da uwarta matsafa bañe saiyau.

Bayan anty moju ta tursasata akan su boye mishi gaskiya ta tambayeta to akan waye kenan zasu laka sharrin

Tashi daya tace kawai su lakawa hajya khadijatu dan already dan uwansu yana suspecting hakan inhar suka gaya masa zai iya yadda, snn in ya kore hajy kahdijatu agidan sa duk burinsu ne ya cika tunda ta haifa musu jinin su Damilare aganinta basa bukatar ta kuma.

Duk jikin anty ramoutu na bari bari sabida tsananin tsoron yaudarar dan uwansu da zasuyi akaro na biyu amma hakanan suka zage suka fiske tare da gunduma ma dan uwansun karya akan cewa matarsa khadijatu ce take shirya masa komi bayan ya dawo.

Sosai yay bakin ciki aransa,hawayensa nata zuba har suka iso gida bai dena mamakin hakan aransa ba, duk bai lura ba sunata kallonsa da gefen ido basuce masa komi ba sai tausayi dayak bawa anty ramotou dna harga Allah bataso hakan aranta ba.

Jikinshi duk a sanyaye ya koma gidansa, sashen sa ya wuce direct ya kwanta akan gadonsa da bakincin tuna irin tsafin da malamin nan ya dinga bayyanawa yana cewa anayine akansa ashe wai kahdijatu ne take cutar dashi tuntuni bai sani ba.

Yaso yay ma malamin tambayoyi domin yasan waiko rabasa da yaransa khadija take sonyi dan ta hanashi cin kudinsu ko akan kishin kafayat tayi masa hakan amma haka su anty mojushola suka hanashi komawa wajen malamin firr sukace sune zasuna jiyo masa komi.

Da yamma lis ya rufa kafayat ta kammala shiri tsaf dan yau ita dayanta ta shirya zata dawo gidan da zimman shirin yaki da auren Adiaha da Ahmed dinta.

Bakin abaya ta saka duk wani maganin da goddes ta bata yana cikin hand bag dinta, iya wanda zata fetsawa alhaj bello ne kawai ta damko shi a hannu sabida tsaro dan batasan awani yanayi zataje gidan ta tarar dashi ba.

sallama tay da mamanta tareda mata alkwarin cewa bazata kara dawowa gidansu ba harsai ta kammala cimma burikansu duka ko da zata haihu da alaji bello ne bata damu ba muddin zata ga bayan auren Ahmed da duk wata macen dazatazo kusa da shi.

Tana bude kofa zata fice taci karo da isowarsu anty ramouto, a tsorace taja baya ganin yanayin su mai tattare da girmammen bala'i da kata'i, Guilty consience bai bari sun samu nitsuwa ba shiyasa suka zo domin suzo su sameta ayita ta kare tsakaninsu da kafayat dan tasan cewa sunsan duk wani sirrinta ita da mahaifyarta.

Da karfin balainsu suka iso anty ramoutu harda wanka ma kafayaat din mari mai zafi..

Rikici ne mai zafi ya kaure tsakaninsu aka fara tone tonen asiri saida suka bari su anty moju sun gama zazzage sirrikansu da suka sani kafin nan hajy fatihat ta laluma da wayo fito da bindiga a drawarta na falon ta harba sama tai tau duk suka rude snn ta fara tsoratasu dashi tace zata harbesu ta harbe banzaye.

Atake Duk cikinsu ya duri ruwa hanjin cikinsu yahau kadawa, hakan nan ta sakasu kneeling akasa da gwiwan su snn ta kara jadadda musu cewa duk abunda akace akansu sunyi eh gaskiyane sune sukeyi ma dan uwansu asiri harda matar Damilare har goddes tace bazata taɓa haihuwa dashi agidan ba.

Su anty moju sunci kukan tsoro suna dan dana sanin hada kai da sukayi da su kafayat, duk awautarsu sun dauka an hada kai dinne duk dansu taimake dan uwansu bello ya auro mace yar kabilansu wanda shine yasakasu sukayi wann harkan da kafayat ashe basu san dacewa kafayat da mamanta suna da motive dinsu na daban ba.

Babu imani Kafayat ta dauko wani garin magani na mantuwa ta watsa musu a fuskansu suka fara tari suna shakewa atake komi ya shafe musu a brain dinsu suka dawo basa iya tuna komi Snn suka sakasu agaba akan su kaita har cikin jimada mansion in a bridal escort style.

Lokcin alaji bello yahaura sama kenan neman hajy khadijatu bai sameta ba yanata zagawa a sashen ta cikin fushi da son ya tona mata asiri...

Bai sani ba aka dawo da kafayat, suna kaita bangarenta ta koresu tare da musu gargadin cewa zata kashesu idan har suka karayin wani bincike akansu tun ficewarsu agidan anty ramoutou tafara wani irin zazzabi mai zafi.

A fannin Adiaha kuwa as usual tay wankanta snn tayi ma mijin nata lafiyayyen abinci na tarbansa duk da kasancewar yadawo agajiye amma bata barshi ya daga ko tsinke ba domin kuwa wani irin sakaltashi takeyi hatta takalmi itake cire masa tay masa wanka ta shafeshi har ruwa in zai sha bata kyaleshi yay komi dakansa itace nan kamar robot zata masa komi bata gajiya, sai yadawo kmr nashi aikin gidan kawai shine ya make sure yay satisfying dinta wajen kwanciya.

Yau dinma da wuri tajashi suka kwanta shiyasa basu san duk wata dramar dake wakana acikin gidan ba.

Hjy khadijatu tana can waje suna zaune suna shan iska tare da brother kazim suna dan tattauna batun tafiyar zainab gobe da kuma komawar shi brother kazim din bakin aikinsa acikin karshen sati..

Hakan ne yasaka alaji bello jimada yagama hargaginsa har yagaji yabar sasshenta bai samu daman tattaunawa da ita acikin daren ba dake wann karon itace taje ta same brother kazim a garden bashine yazo sashenta ba..

Hirarsu sukeyi kamr babu gobe, dake shine babba agidan washi tafara gayawa zancen new office appointment dinta A lagos state data samu, tace masa tanason inta kammala komi nata zata koma can amma zatana dawowa Abuja wkends idan sun amince akan hakan da mahaifinsa.
Chapter 44 · 0% Book details