← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 157

Sashe 125

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kanta Adiaha batasan wani irin kuka mai tattare da azaban tsoro da rudewa datakeyi awajen ba.

Kafayat ce mai saka musu mugayen kalmomi abakinsu. Sai tana kawo zancen bambamcin kabila tana hadawa aciki, sai tana cewa ai asali yan calabar mayu ne dama,snn ma ai ance kakarta igbo woman ce.

Meaning Adiaha is both a suspected witch and a Wicked greedy person.

Tafara cewa matan association wai ai sabida kudin damilare ta aureshi acewarta ai itace tafi kowa dadewa da damilare tafi kowa sanin yadda rayuwarsa yake kuma tun dacan ma bata san shi da Adiaha ba kwasam kawai taga yaje har ya auro ta halama magani suka masa acan.

Har kasa suka saka Adiaha ta zauna kowa ya dumbulu toka a hannun sa zasu shafa mata ajiki su mata kwalalan maita komi acikin sauri sukeyin shi..babu wanda yasan cewa kafayat ta zaga tabi kulle kofofin cikin gidan dan tsabar mugun ta brother hamzat was stuck inside yanata jin hayaniyar su tawaje.

Karshe ta kofar kitchen dinsu na baya ya balle ya fita snn ya shiga main house domin ya fito da babansu domin shine zai iya zuwa ya tsaida su anty mojushola.

Su Ahmed suna kammala parking sukayo wajen daidai lokcin da brother hamzat suka fito a guje shida alhaj bello dake sanye da white jallabiya da hula

Anan awaje suka hadu da su hjay khadjitu suma
Ko gaisawa basu tsayayi ba suka dunguma izuwa can bangaren Damilare inda asalin hayaniyar ke tashi.

Mataye kusan biyar ne akan Adiaha suna kkrin zasu fara walakanta ta

Sauran kattin matayen kuma duk sunyi babakere sun tare hanya dan karsu alhaj bello da su hjya su zo su karbe Adiaha awajensu.

Hanklin su hjy sosai ya tashi ganin abunda suke shirin yi wa Adiaha? She was like What sort of inhumane treatment is dis for god sake akanta aka fara yin kuskuren zubar da aciki ne?

Alhaj bello yafara ihu yana daka musu tsawa akan subar masa gidan sa koyasaka hamsat ya kira musu police cos dis is strickly his family issures bana public ba hjy maimuna tafara taya shi sunata exchanging blows na masifa da sauran matayen tribal assocition din.

Anty mojushola ne ta dada birkita wajen tana cewa su Ahmed idan suka sake suka karaso wajen Adiaha waidan su ceceta sai ta tube kayan ta tsirara awajen tsinewa alakarta da ubansu na har Abada.

She started insulting jer brother bello in return.

Tafara ce masa baida kishin zuriarsa, zubar da cikin da Adiaha tay ai tamkar jinin iyayensu ta kwabar tunda damilare dansu ne..damilare's children are important part of they generational offspring they cant ignore that ,tace sam bazasu yarda ba, suda suke neman haihuwa ido a rufe sai wata wawiyar yarinyace zasu kyaleta tazo tana zubar musu yayansu abanza?

Hajiy khadija dake da tausauyi har hawayen tausayin Adiaha saida suka zubo mata.

Hayaniya ne ya kaure awajen kokowar tsare su alhaj bello da su hajiya da su Ahmed.

Yasrah dake tahowa acikin sauri tana kallon abunda ke faruwa gabanta ne yake tsananta faduwa kanta na kuma juyawa sosai.

Daf matan sun daga Adiaha tsaye kenan tanata kuka bata cikin hayyacinta tana layi zasu mata wanka da toka da fenti,wasu har sun debq suna shafa mata akan fuska basu hankara ba Da gudu yasrah tazo ta fincike hannunta daga wajensu acikin sauri tajanye ta turata cikin bangarensun agaggauce.

Ko Adiahan ma bata san yasrah bace ta kwaceta harsaida taji ta fado akasa acikin falonta ita kadai kuka takeyi marar kakkautawa.

Wani irin baqin ciki kafayat taji ya kamata bana wasa ba su anty nurat kuwa mamakin yasraan sukaji sosai

Yasrah ta tsaya abakin kofar cikin dirin masifa she instisted on telling that dat Adiaha bata da lafiya da karfin jiki inma kasheta zasuyi subari ta samu sauki tukuna.

Matayen suka dawo kan yasrahn su kayi chaaa suna mata surutu akan ta basu hanya nan ne su hajiya suka harxuko cikin zafi su ma.

Rashin kasancewar Adiaha awaje shine ya lafar da hayaniyar..

Brother hamzat da Ahmed suka kore matan association har waje inda brother hamzat yay musu rantsuwar cewa duk sanda suka kara shigowa harabar gidansu for whateva reason babu tantama saiya saka ankamasu an kullesu.

Anata hayaniyan man amm Ahmed baice uffan ba duk abunda akeyin nan na tashin hankli.

Tsakanin Alhaj bello da yan uwansu rikicine ya dawo sabuwa atsakar gida.

Anty moju ta dinga tsine tsine tana kwashe kwashen albarka gashi dama ta tsane tagansa da matarsa khadijatu

Duk gani take itace take juyashi shiyasa baya ganin daidai.

Ran alhaj bello yay matukar baci sai zage xage yake yana bori shiyana magana ne akan tona ma gidansa asiri da kayan xubda mutuncin da suke jawo masa adalilin gayyatar mata cikin gidan sa da suke yawanyi into his personal matters.

Su kuma kishi da hassadar matarsa khadijatune kadai ya rufe musu ido tare da toshe musu kwakwala.

Wato dan Damilare dan cikin khadijat ne shiyasa baza ma basai koyq musu baya ataru aga laifin matarsa Adiaha ba bare a hukunta ta.

Anty ramotou tace masa sam warayyya yake nuna musu. Yamaida su basu san abunda sukeyi ba.

Sukata zaginsa agaban yayansa da su hajiya khadija shima yau yaki sam yay shiru haka sukayi kaca kaca ma juna suka ce masa tunda bazaiyi adalci a tsakanin yayansa ba bazasu kara taka kafafunsu su xo gidansa ba snn duk wata matsala data ballo masa henceforth karma ya nemesu.

Kowa baiji dadin yadda suka rabu ba. Anty moju tanata kuka tana zagin hjy khadijatu da yarensu tana cewa basasu yafe mata ba har abada, dan itace ta shanye musu dan uwansu snn ta rabasu dashi.

Shima alhaj bellon a mugun zuciye ya wuce sashensa saying dat he dont care bazadai ya amince suna masa duk abunda sukaga dama agidansa ba.

Tuni kafayat ta bar wajen ta koma cikin gidan jikinta na bari da bacin rai, a hargitse ta fada sashenta cikin ziriya da tsananin jin takaicin xuwansu hjy khadijatu cikin bacin rai da hucin tsana mai tsanani.

Cikin main house na gidan kaf hajya khadijatu ta turasu kowa ya wuce nan suka zauna a falo ita kuma ta wuce daki direct domin ta samo alhaj bello.

Tana sallama a dakin shi ta Sameshi yana waya da babban dansa kazeem hawaye masu sanyi na sauka a idanunshi tsabar yadda ransa ya mugun lalacewa da irin abunda su anty mojushola suka gaggaya masa agaban kowa da kowa yanzu.

Ata fannin Adiaha kuwa kuka kawai takeyi jikinta duk a sake ta mugun raunutuwa, she was looking soo dejected iya kan yasrah da Hajya maimuna ne kawai suke tare da ita.

Dake Hjy maimunatun ce ta shigo ta dagota sama babu abunda takeyi sai rarrashinta tanamai bata hakuri basu kyaleta ba har saida ta dawo cikin hanklinta snn hajiya maimunan ta umarceta akan dataje ta watsa ruwa ajikinta dan ta dawo hayyacinta sosai.

Har yanzu Jikin ta rawa yakeyi, da kyar take daga kafafunta ga ciwon ciki cos She was soo scared and devasted. yasrah ne ta riketa suka karasa cikin dakin ta haɗa mata ruwa ta dawo ta fara tayata neman kayan sawa, riga da skirt da hijabi marasa nauyi ta neman mata mai kyau acikin kayanta na wardrobe.

After some minutes Adiaha tay wankan snn ta fito jikinta a mugun sanyaye tana jan shessheka hatta kallon yasrah bata iyayi sabida nauyi da takeji aranta.

Yasrah kuwa bata kulata ba ta taimaka mata tay kominta a nitse suna fitowa suka samu hjya maimunatu har ta dama mata kakkauran shayi tay toasting mata bread datagani akan dinning table.

Kanta akasa ta zauna jikin sanyin jiki, hajua ta miƙa mata tea din tace mata maza tasha shi yanzu..babu yadda ta iua ta amshi tea din tanamai godewa,wasu hawaye ne sabbi masu kuma tsananin zafi suka fara sauko mata sanda ta kurba tea din wanda badon Hajiya maimunatu ta kafe ta ido ba bazata iya cigaba da shansa ba tsabar damuwar daya cika mata kirjinta ayanxu.

Shiru wajen ya dauka har ixuwa lokacin da ta kammala shan tea din wani xufa ne na musammn ya fetso mata akai tanata jan ajiyan zuciya ahankli kafin nan akazo aka nemi ganinsu acikin gida.

Hajiya maimuna ce ya sako su agaba tana rike da hannun Adiahan sabida matukar tsoron dake tattare da ita..

Da kyar hjya kadijatu ta lallashi zuciyar mijinta data samu yana hawaye.

Normally shida dansa Ahmed suna da wani hali they love blaming sumone in ransu ya baci ko wata matsala ya samesu.

He kept saying dat yay danasanin fara biyewa Adiaha dan aganinshi duk itace ta jawo wnan hargitsi da bataje ta zubar da cikin nan acikn ganganci ba da duk haka
Bai faru dasu yau ba.

Da kyar ta lallabesa yay hakuri snn suka tattauna akan maganan su ukun tare da brother kazeem.

Kowa acikinsu yana fushi da Adiaha amma a matsayinsu na manya kuma adalai They equally agree to give her a last chance. Cewar Alhj bello idan har Adiaha ta kara memeta irin wann gangancin zai saka danshi damilare da ya maidata garinsu gaban iyayenta kawai. Hjy dai abu dayane Adiaha tayi da bataji dadi ba wanda shine boyewa Ahmed komi datayi game da cikin farkon dana biyun ma.

Ahaka suka tsaya da maganan dai kowa yay hakuri snn ta fito tare dashi.

Daga can sama kafayat ke satar Kallonsu dan ann tay niyyar tsayawa domin tanajin me zasu tattauna ataciki sabida mum dinta tace mata lallai itama taje ayi da ita amma harga ALLAH tana danjin shakkarsu hajiya khadijatun aranta gani take bazata iya suna fadan magana itama tana fada agaban kowa ba gara ma da a private ne.

Jim kadan falon hidan alhaj bello jimada ya cika da Ahalinsa.

Hajiy maimunatu ne matsayinta na babba sosai ta fara musu nasiha dangane da muhimmncin rufawa junansu a asiri anan inda tabawa kowa laifinsa dede gwargwado.

Bayan ita sai Alhaj bello ya amsa,yay masifar son ya dawo yay nasihar
Adiaha sai kuka takeyi kanta akasa jin inda ransa ya baci sosai da ita. Duk wani abunda ke ransa saida ya fitar.
Chapter 125 · 0% Book details