← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 157

Sashe 14

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun kammala maganan ko sai anjima baice mata ya fice agidan sister zainab tabita da wani irin kallo tanamao kyabe baki daga can tace harkin yi sallahn? "Tace i am about to. Oya lets go let me see if u know how to pray dan naga alaman baki iya komi arayuwarki ba. Adiaha batace mata uffan ba ta shige dakinta itama sai ta biyota abaya suka shiga ciki kusan atare.

Ranta na baci sosai dan batason yanayin yadda sister zainab take raina mata wayo tareda treating dinta harshly amma daga baya sai ta fara fahimtar wani abu game da ita sosai.

Acikin masifar tata take dada koyar mata abubuwa wanda babu wanda yataba koya mata hakan arayuwarta.

She will insult her finish oo,sai bayan ta kammala zaginta kafin nan sai ta gaya mata asalin abunda ya dace tayi ta inda bazata taba mantawa ba. Dagaske wani lokacin baka tashi koyan abu dakyau cikin gaggawa face harsai anmaka gori ko fada sosai akai.

Tun da sister zainab tay mata gori akan yin Alwala daidai Adiaha tay zuciya ta saka zuciyarta akai tafarayinshi a dede.

Haka ma wajen gabatar da sallah ta saka mata ido sosai takanyi kmr zata hadiyeta inta ga ta yi kuskure,grandma dinta takan koya mata komi ne ahankli cikin lallami da nuna kulawa amma bata taba nitsuwa ta koyeshi dakyau kamr nayau ba.
alokcin daya kamatq ta iya din tunanin aurenta da Ahmed datasaka agaba bai sa ta fahimce komi sosai ba, Ayau kuwa abugu daya ta iya komi na ibadanta harda kari snn sister zainab ta bata shawara mai kyau acikin masifar tata tanacewa ta saka mijinta Ahmed yasata a islamic school dan ta koya komi na Addininta da kanta.

Bayan sun kammala ta kalli Adiaha sama da kasa lkcin zataje wanka kenan ta tsareta snn tace iyawo reema you cannot cook abi? Adiaha Tace i can, tace oya oya now, kishirya kawai ki fita yanxun nan dan daga yau kece zaki dinga mana breakfast har zuwa dinner agidan nan bcos ure the youngest wife, ko are u expecting adizat or nurat or hjy mumy dakan ta sumiki girki while kina zaune dan tsabar baki da tarbiya agidanku ko? Uhmmmm...

Shiru adiaha tay sai can tace To shikn bari na yi wanka zanzo na yi girkin

Sister zainab tay mata wani irin kallo tace harse kinyi wanka, reema ashe baki da hankli"..look ki kalli lokci yanzu kinsan akwai yara agidan nan kike wasa da breakfast dinsu, zaki kashe mu da yunwa ne? Zatay magana cikin katseta tace..cmn lets go jare. Muje kawai na nuna maki kitchen din yanzu ki fara aikinki and pls dont cook nonsense food dan bamacin hauka agidan nan. U have to cook good food for us.

Adiaha ta maida kayan jikinta tun na jiya ta daura wani mayafi akanta snn suka fito

Cikin main mansion din suka koma sister zainab takaita har backyard indq aka gina musu wani babban outdoor family kitchen domin yin wata hidima daya shafi gida.

Duk dama Kitchen din babba ne amma yana da kyau komi na cikinshi ma sabone kal.

Adiaha tanata kallon wajen, sister zainab ta tsaya daga can nesa snn tace.."get to wok oo we are hungry abeg.

Cikin sanyin murya Tace okay. Kafin ta juya ta tambaye ta inda abincin suke taga harta juya tabarta awajen.

Lumshe idonta tay jin kirjinta na bugawa da sauri sai can dataji ta samu nitsuwa kafin nan tafara duba wajen ahankli da kyar take gane inda abubun girkin suke anan saida taci minti talatin kafin ta same location din komi da komi.

Bayan nan ta kara shiga rudanin abunda zata girka musun,sam batajin karfin gwiwa ajikinta ko kadan dan abubuwa sun mata yawa acikin zcyarta and the last thing she want to do now is fara nadamar auren Ahmed tun ba'aje ko ina ba.

Kaucar da rudanin datakeji tay azuciyarta tafara tunanin abincin daya dace ta girka musu yau da ya kasance shine ranar girkinta na farko agidan mijinta, bata son ta kwafsa so she have to cook to impress, hala daga hakane zata iya samun sassauci daga wajen wasu.

Nan ta hau aiki, cikin dan kankanin lokci ta tafasa doya kafin ya nuna ta hada jajjagen kayan da zata hada yam balls dinta dashi, bayan ya nuna tayi marshing dinshi into balls tay kominta acikin sauri sauri snn ta saka ruwan zafi tay musu tea tasaka a flask, ta dafa indomie noodles da egg ta hada sai batasan inda zata kai ba.

Anan ma saida ta bata lokcinta wajen tunani daga baya ta yanke shawarar zuwa wajen sister zainab dominta tambayeta.

A main falo ta sameta ita daya tana shan green smoothie ita da danta shafiu, Adiaha tanayin sallama awajen yaron sister zainab tunda ya kalli adiaha yafara kuka kmr wanda yaga dodo.

Tsabar firgita dayay Haryana batan steps wajen dukunkunewa ajikin mamanshi.

sister zainab ta dago tay mata wani irin kallon zargi da tuhuma kafin nan tafara wani irin bambami da masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba. "Reema Kilode, What now? Ya zaki zo kisa yaro na ya firgice yana kuka are u a witch,are u sure ure okay?Adiaha ta lumshe ido ta bude tace sister zainab nazo ne na tambayeki inane zan kai breakfast din cos am done cooking it.

Ta kalleta rai abace snn ta dube lokci ana neman tara da rabi saura tace "Kizo ki daura akaina, nace kizo kidaura akaina idiot girl. Dama tun tuni baki gama ba sai yanzu bayan kinsan laifinki ne da kikayi latti memakon kiyi sauri ki kaima kowa nashi kinzo nan kinamin jamb question ure a mumu _ode, oya jade_
Kifita mana, ur bad energy is already scaring my son.

Adiaha tay sauri ta fice batare da cewa komi ba ta bar wajen tana tafiya da sauri da sauri har kafafunta na harhadewa tsaban fushi.

Koda ta isa kitchen din Tagumi tay ta tsaya tanata kallon abincin dan bata san ya za'ayi tafara rabashi har ya ishe kowa da kowa ba.

Ganin Lokci na tafiya kawai ta fara nemo serving plate da trays luckly enoug akwai dinner set maasu yawa da kyau acikin kitchen din.

Hakanan ta raba abincin into 4, gashi ba wani yawa yake da dashi ba karshenta haka ta diddisa ma kowa ita ta hakura batasaka makanta komi ba.

Plate din yayun ahmed mazan ta saka musu yamballs guda hudu da egg,matan ta saka musu uku da egg. Yaran kuma ta saka musu indomie da egg sai kowa ta sa masa tea dinsa a mug tafara kaiwa kowa sashe shashe.

Sashen anty adizat ta isa tayi kusan minti goma kafin nan aka bude mata kofar,yaronta na tsakiyar sulu shine ya fito ya tsura mata ido baiko gaisheta ba" tace hello is ur mum in?kare mata kallo yay snn ya juya baya ya shiga kwala kirawa mamansa yanace wa "mummy?mummy? Mmummm
Come ooo kizo mumy The new housegirl is looking for u..

Adiaha tace what? Sulu..Waya gaya maka ni housegirl ne?

Bai amsata ba ya bar wajen saiga anty adizat ta fito jikinta sanye da wani irin hadadden english wear dat is soo sexy ta baza suman kanta mai tsayi dayake nan acike gashi baki gefe ya zubo akafadunta da alaman tana busharwa ne da handrier..

Irin kallon admiration da Adiaha ta sake baki tanayi mata yasaka tayin wani irin sassnyar murmushi tanamai dada ji dakanta..

Gud ..gud morning anty Aadizat

Bata amsata ba saida ta danyi mata wani irin dariya dat is embrassing abit, adiaha tay saurin sadda kanta kasa tafara tunanin kodan yanayin ta ne na wanda batay wanka ba yasaka anty adizat tay mata wnn dariyar.

Au Dama kece sulu yake cewa housegirl? Lallai yaron nan,mmm is such a pity da baisan ke matar babansa bane. Ta karayin dariya anyways,ppl Dress the way thy want to be Adress right? Dont mind the kid jare.

Me kika kawo mana?

Adiaha ta hadiye takaicin dake son fito mata da kyar cikin sanyin murya tace "its ur breakfast'

Anty adizat tay wani juyi da hadadden gashinta tanamai yarfashi baya, cike da jiji da kanta ta bude abincin ta duba tagani tana kyabe baki"

tace yay kyau. Kece kikayi?

Tace eh nice anty
Wann nakine keda uncle sai wann na yara..

Tace ohh kinyi tunani mai kyau...bata karbi tray din ba ta juya tana kwalawa danta kira "sulu? Sulu oo?Zoka karbi abincin ku from ur new househelp, sanda ta fadi hakan snn ta juyo ta kalli adiaha ta fara mata dariya dont tek me personal dear its just really funny yara sun iya fadin abun dariya. Adiaha batace mata uffan ba saiga sulun ya fito yana zuwa ya karbe abincin ahannunta ya juya dashi ciki ba sannu babu madallah suka rufe kofar sashensu

Juyawa tay ranta a dagule snn ta dauki dayan tray na gaba takai sashen anty nurat.

Tana danna bell bada jimawa ba saigata ta fito
Sanye da wata arniyan leshi na lagos ja da fari tay kwalliya ma mijinta sosai kamr wacce zata je gidan biki.

Suna hade ido adiaha ta dauke kanta sabida wani irin kyamataccen looks din data bata up and down tabi ta hada rai kmr batasanta ba.

"Gud morning anty nurat"

Tace whasup meya kawo ki nan, has the water in your bathrom finished?

Cikin ignoring maganan Adiaha tace nakawo miki
Breakfast dinku ne.

Tace breakfast ke?naji kina ku ku ku me and who?

Tace da yara da kuma brother hamz...

Cikin tsareta tace Ehennn stop der karki kira sunan mijina abkinki ooo,are u insane? Ki dube kanki manou, u look..oh my god..ynzu idan nayi magana sai ace na zageki tun kina amarya.

karfe goma shine kin kawo mana breakfast
Who send u first? Yara na zasuje schl tun 7 and now is 10 kina kawo abinci hahaha u must be joking..

Baki na rawa adiaha tafara mata bayani saidai duk bajinta takeyi ba danvtana kare maganan taja mata tsaki tare da cewa kanki akeji.

'Ki aje anan ki tafi..ta nuna mata bakin kofa.

Adiaha tana ajewa abakin kofar Tafara mita tana cewa Thnk god My husband and kids sun fita tunituni i wll not have allow them to eat this dirty food sef.
Chapter 14 · 0% Book details