← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 157

Sashe 52

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dada rufe kan kirjin tayi
Tace"meyey hakan ? ta karashe maganan a shagwabance tana turo baki "karki sake kice min nono na yakara girma nifa bana son manyan nonon nan....

Rufe baki jasmine tayi don dariyar data ci karfin ta amma ena sam ta kasa daurewa Sosai ta gurfana kasa ta cigaba da zuba dariya abun ta...
Sai da tayi mai isar ta sannan ta juya ta kalle yasra data riga ta kule
tasako fuskan kuka Tace "...Ke haba da Allah yasrah,wai yaushe zaki dena wannan tsinannan kunyar naki ne iye? Big boobs are cute..ke Baki son a miki tickles, baki son aga girman nononki, ga shegen son yin tunanin aure "Kinsan tun yaushe na shigo dakin nan?

Yasra Ta harɗe fuska tace Yo' don kin shigo shine zaki wani razanar da ni jasmine? What an insult karki sake cemin ina tunanin aure.

Tahowa tayi tanamai ajiye bag din ta kan stool ta dawo gefenta ta zauna tana dariya sosai,ok im sorry"..shikenan?.
Ni ba wannan ba ne na tambayeki Tunanin me kike ko ince tunanin wa kikeyi yanzu? Ko har kin fara tunanin komawa nigeria ne da mumy in fara shirin zuwa bikinki da new catch din da mumy ta aje miki acan.

Yasra ta haɗe rai sosai tace sai kuma na tsaya yin tunani akan hakan?Allah ya kiyaye in tsaya tunanin kowa kinsan wuce nan Mumyn ma wasa take nidai bazan yi aure nan kusa ba, all her match makers can go to hell, see babe, i want to be a lawyer das all ba wani zancen auren hadi kicire wann maganan aranki kinaji na ko tafada tana zare mata ido tare da kau da kai..

Dan tabe baki jasmine tayi tace" amsa ta ai ta fito, Ashe kuwa tunanin Auren kike tunda tambaya biyu na miki kika amsa min daya'

Dan juyi yasra tayi alamn bata son cigaba da zancen Sannan tace

Ni wallhy jasmine kin ishe ni da maganan wanin nan na gaya maki cewa bazan yi auren nan kusa ba mumy ne fa take fadar cewa tamin miji acan nigeria dan jin dadin bakinta, Ni kenan ba dama na Zauna ina feeling kaina a daki na sai kice ina tunanin aure

Jasmine tace "Ah' ah ,ni bance ba, kiyi abun ki ..ai is part of relaxation '

sai kuma ta sake cewa "ummmm yasrah

Yes ' tafada a kasale

Naga kamar Wani abun kike karantawa ko ?tajau lekawa wai ko kawai imagination na keyi..is dat a slum book?I tot you hate ur all class mates hajiya rigimammiya kawai.

'Dan duka takai mata suka kwashe da dariya duka biyu ' tana cewa wallhy na dauka wani abun kirki zaki ce min iskanci kawai, ta dauki slum din cikin sauke ajiyan zuciya tanamai sakin murmushi mai sanyi tace idan har Allah ya qaddara nigeria zan koma da zama har abada ko? this slum will be my little memory of instanbul.
I wll miss the cold air, the tea..the drama..the games of thrones a schl with my tons of secret admirers..

Kawartan ta rungumeta suna dan murmushinsu atare wanda basai an fada ba zakasan cewa sunshaku matukar shakuwa.

Dan hira sukayi sosai irin na kawaye da suka gama secondry schl .

Chan da yamma sosai suka fito daga site dinta suka wuce sashen hjy maimunatu.

Anan suka rusuna duka suka gaishe ta tare da mata sallama Sosai taji dadi dan haka dukkan su ta bisu da albarka .

Wannan karon fitted gown na material golden brown yasrah ta saka ajikinta tayi rolling kanta da golden brown mayafi akan beige jacket dogo a hanyar su ta rakiya Suna tafiya suna ta surutu.

Nan jasmine tace" Kawata ashe badaga nan ba Kice yayan mu zai dawo yau mana shiyasa yau kaf na kasa gane miki...

Dan murmushi tayi
Ta kalli jasmine din
Murya a sanyaye tace
"wani murna?im alwys happy ni bana fushi. Kewai Daga mummy tace yaya na zai dawo sai kuma kice ena murna Wallhy kin raina ni jasmine.

Jasmine tace hm tsakanin ko dashi ai sai Allah naga duk bawanda kike so arayuwa sai shi.

Tace yes, he is my mentor, kuma Atleast yayana shine kadaine yasan abunda nake so da wanda bana so arayuwata all mumy thinks about is marriage marriage kuma ta rasa ma inda zata min auren wai sai munje nigeria...i just hate dat country..

Jasmine tace dont be ridiculous yasrah,nifa naji anacewa nigeria is a nice country with a diverse cultural adversities and mutanen dake wajen sunada liberated minds, they speak their minds out basa jin tsoron kowa bakamar sauran african countries ba. Koni nan Ina son nigeria, mutane daban daban, yare kala kala amma suna zaman su awaje guda as one isit not fucking amazing? Ko nan turkey ma we r almost same here shiyasa babu wani vibes.

Cikin katseta yasra tace Hakan baifi ba?Nigerians are godam rude not liberated, they are also Dogmatic..gani suke sunfi uban kowa bakin magana,ni bana son iyeyinsu, to me the country is just boring full of brats..

Jasmime tace "no not boring"..and i think nigeria zaima fi dacewa da mace irinki,kema kinada liberated mind, ure outrageous,confident, self obsessed, shiyasa a babu kamarki wajen aji a duk set dinmu..

rauu rauu yasrah tay da idanunta tace zagina zakiyi ko? okaay just forget it, abr wann hirar nan muje musha tea acan joint din..ta nuna mata wani hadadden tea tea cafe mai kyau na yaran masu kudi.

Jasmine ta bude baki tana kallon haduwar wajen itakuwa ko ajikinta dan yasrah macece
Mai daukar kanta da muhimmanci bana wasa ba,.

she have high standard, ta yarda dacewa mace bata cika asalin mace sai ta san yancin kanta a matsayinta na ya mace, she neva settle for less bare least,dressing dinta very porchy and classy kullum kamar celebritys dan cewa take itama celebrityn kanta ne.

shiyasa ma tay suna sosai na fitar hankli a makaranta musmmn yadda take daukar kanta da daraja da kima komi zatay arayuwarta sai ta tantanceshi inbaida kyau ko baihadu ba toh bazata kai kanta wajen ba..

Kai tsaye taja jasmine suka shiga wajen shan shayin suka zauna acikin kowa na satar kallonsu cos all the classy and rich women na turkey wasu sunzo suna shan tea, suma oder sukayi suna hirar kasar nigeria dan shikadai ne hirar da jasmine take jan yasra aciki inatana son su dade suna musu sosai.

After a while lokcn har dare ya fara rufawa suka bar wajen kowa ta kama hanyar gidansu....
[6/17, 10:20 PM] SURAYYAHMS: A fannin Ahmed Yana shiga cikin gidan nasu ya tarar yau babu motsin kowa aciki.

Kafayat na can bangarenta ta sako vest da gajeren wando tana kan gadin shigowar alhaj bello jimada dan tun ficewarsa da safe bai kara dawowa gidan ba.

Yay yawo har saida ya fice ahayyacinshi gashi dik inda yace yana neman bashi sai ata mamkinsa dan ansan yaransa maza kaf suna da arziki kuma basa barinsa hakanan kowa ya shaida cewa hargidan dayake ciki ma dansa ne ya gina musu. .

Sai kwata kwata Bai ci sa'an samun bashin kudin siyawa kafayat jeep din G wagon ko landcruiser ba gashi yanata tsoron ma ya fadi dalilin karban bashin a wani awajen kafin gulma ya yaɗu yaje har kunnen manyan yayansa suji.

Haka ya gama yawo akafa ya dawo yazo ya zauna agidan su anty mojushola anan ma duk hanklinsa baya jikinshi sabida ciwon da anty ramaotu take yi na zazzabi all of a sudden wanda harynzu dai babu wani sauki.

A nitse sosai Ahmed ya shigo bangaren mum dinsa cikin daren da sassanyar sallama abakinsa, nan ya sameta tana zaune akan doguwar kujera tanata rubuce rubuce, gaisheta ya farayi a ladabce kafin nan ya dawo gefenta ya zauna nan ya fara yaɓa mata shagwabarsa har yasata tafara mancewa da damuwarta tsabar dariyarsa datakeyi

Janshi tafarayi cikin hirar rayuwa, cikin hikima harta fara fahimtar dashi damuwarta na son zama nesa da mahaifinsa da matarsa kafayat, tasan kawo maganan raini tsakaninta da kafayat shine kadai abunda zai saka danta ya bata dukan goyan bayansa da zuciya daya dan haka ta bullo masa ahaka dan ya fahinceta dakyau

Duk da haka sai yaji wani daban datace masa gobe gobe zata koma lagos din sabida tana interview agabanta mai muhimmanci.

Duk yadda yake jin yana matukar son yaga mahaifyarsa a kusa dashi kowani lokaci tunda yagane cewa zaman ta anan din zaina taba musu mutuncinta sai baiyi mata musu yau ba.

Bayan nan sukayi hirar abubuwan dake gabansu kadan snn ta fara kawo masa maganan Zaman yasra awajensa

Bayan ta kammala masa bayani, Cikin sauke ajiyar zuciya tace."Ahmed kay hkri wallh banso in
takura ma lamarin aurenka ba, so, i hope ur wife wund mind the idea of yar uwanka tana zuwa tana zama tare da ku idan ta dawo nan Abuja da schl dinta? ..nadai san yar uwanka yasra bata da wani matsala ...,tay murmushi tare da tunota acikin kwayar idanunta tanamai cewa "bata da banzan hali, iya kan shegen shagwaba ne kawai da ita da rigima amma bayan nan bata da raina babba.

Babu yabo babu fallasa ya kyabe bakinsa snn Yace haba mamy na kidena cewa haka mana kema kinsan ko bamu ita kyauta kikayi zamu rike miki ita bare ma nasan zata na zuwa wajenki hutu ba zama sosai zatanayi da mu din ba, i am sure they wll they get along ai, ita ma kwanan nan zata fara zuwa islamiya...ita wancan din fa? ko kina ganin bokon kawai is okay ..tace "yeah" ai ta karantu, sndry schl datayi a turkey mai hade da islamic schl ne tun nursery ake gina musu foundation amma in kaga zaka nema mata extra class suna zuwa taren ma ai is good ilimi baya yawa saidai yay kadn...

cikin kyabe bakinsa yace uhm uhm um im just saying..she can do wat ever she wants. Tay murmushi Allah yasa dai zaka saka ido akanta kasan dai yarinya ce i hope zaka kuma bita ahankli acan dai bamu saba mata fada ba kaga dai marainiyace.

Murmushi yay a sshance mum wai yar taki yar gwal ce ne kam,kawai ki bari in lkcn zuwanta yay zamuyi maganan akanta
Chapter 52 · 0% Book details