← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 157

Sashe 26

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adiaha ce kawai karamar dangansa idan ya kwaso fushi da takaicin yay masa yawa aransa sai kaga ya juye akanta ya kuntata mata haka za tay ta kuka batare da sanin laifin data aikata masa ba.

Da abun kafayat din ya fara musu yawa sosai sister zainab kawai tace makanta enough is enough kawai zata dawo gidan ubanta koma yaya ne dominta dakatar ma kafayat din nan koda sau daya dan tagane cewa ba tsoronta akeji ba.

matsalar data samu shine mijinta ya hanata zuwa gida amma haka tay masa taurin kai ta dauke yaronta ta taho abunta.

Da sassafen Allah tazo tun lokcin kowa bai tashi ba,sashen baban nasu taje direct aikuwa taci karo da kafayat lkcin ta farka a barci kenan ta sako wani tsinannen nite mai igiya igiya dayawa ajikinshi.

Kafayat Tana ganinta taji wani irin dadi aranta dan dama nematake wani abu ya shiga tsakaninsu ta rama zagi da watsa mata ruwan datay ranar awaje .

Sister zainab bata kulata ba kuwa ta kama hanya zata wuce bedrom din da baban nasu yake domin ta masa magana acikin ruwan sanyi dan tasan babanta yana sonta sosai duk dama tafi kowa yi masa rashin kunya acikin dukan yayansa daya haifa.

Zata wuce kafayat tay wani wuf tasha gabanta cikin gadara tace mata bazata shiga ciki ba sai ta tsuguna ta bata hkr snn ta gaishe ta as her step mother dake dama acike suke da juna hakanan suka kaure da dambe mai zafi.

Nan Sister zainab ta kanannade ta ta daure mata hannu da bakinta da dankwalinta, snn tay mata daukar rakumi ta fito da ita har waje acikin kokawa da firgici da komi haka ta fitar da ita acikin gidan tare da jonata da karnukan makwabta.

Haka nan kafayat taci gudu gashi ta daure mata hannu da baki babu halin yin ihu gashi lokcin kowa yana cikin gidansa saboda safiyane sosai.

Haka karnuka suka yayyaga mata nitynta ta koma gidnsu almost half naked babu takalmi tanata kuka tana zage zage.

Ran hjy fatihat ya baci sosai, wato zainab ita kullum tazo saita ci galaba akan yarta kenan?

Acan gidan kuwa alaji bello ya farka abacci wajen karfe 12 na rana dake yau baiji kafayat ta zo da rigimarta bare ta damesa ba, harya fito tsakar gidan yanata neman kafayat din duk wanda suka ga abunda ya faru da safen babu wanda yace masa uffan hanklinsa duk ya tashi dabai ganta ba.

Haka yayi zugum ga kuma can wayarta a daki babu halin kirarta.

Harsaida kafayat ta huce snn ta kirashi a wayar mamanta da yamma can snn ya fahimce asalin abunda yake faruwa da ita ransa a bace yaje har gidansun dakansa ya dauko amaryansa kafayat din suka taho tare har da mamnta hajy fatihat, bayan ishai akazo aka tara kowa aka fara case kusan dukkan yaransa suna nan babu yadda hajiya khdjatu ta iya hakanan tazo ta tsaya ma yaran nata duk dama batace komi awajen ba.

Yau kwanan kafayat shabiyu da dawowa amma kusan kowani rana sai anyi karami ko babban rikici acikin gidan

Yau din ma haka alhaj bello ya kwanta agaban yayansa yana ihu yanacewa _wa lati sa_ kuzo kubugeni..

Dukanku uku Kuzo ku bugeni ku huce takaicinku akaina

Wann rainin wayo ya isheni haka _imọran onilàkaye yii dara_

Duk saida ya daga musu hanklinsu sosai

Nan aka fara warware magana yafara tuhumar kowa akan ketare iyaka, duk yaransa suka taru sukace idan har kafayat din bazatana kama kanta ba suma bazasu hana kowa rainata agidan ba.

Hayaniya aka dingayi 1-1 dan kusan kowa yana da point dinsa mai karfi.

Kafayat ta tubure tace masa sam ai tun farko yaransa sune basu dauketa matar uba ba, su kuma yaran suna tuhumarta da rashin kame kanta acikin gidan nasu. Ahmed ko tari baiyi awajen ba, nashi ido dan baison ma yasaka musu baki ta rainashi, Dake duk tasan mijinta bayanta zai bi hakanan ta dinga kukan makarici tana kawo karairayi har dai tasaka aka mare sister zainab aka saka ta bata hakurin dole snn aka rufe case din mai gabaki daya.

They agreed that kowa zai tsaya adede limit dinsa amma kafayat cewa takeyi aranta yanzu ma zasu fara gani.

Wani irin tijarar bori da mahaifinsu yay musu ranar dukansu saida jikinsu yay sanyi sosai

Kowa acikinsu saida yay wa zagin tass tass yace musu duk wanda ya sake
Masa bori akan aurensaa da kafayat toh ranan zai tsine masa albarka.

Jikinsu yay sanyi sai basuce masa komi ba Musammn ma brother kazim da babu abunda yake memetuwa a idonsa face yadda ya dinga fadi akasa agabansa yana birgima yana cewa suzo su bugesa idan suna jin haushin aurensa da kafayat har akantane yake cewa zai rabu dasu zai tsinemusu albarka.

Sister zainab kuwa tunda akasata ta bawa kafayat hakuri ta dinga kuka tana tsinuwa mai zafi akan babansun tanacewa yaci amanansu ne danyaga mamansu na ainihi bata raye bayan itace silar dukkan wani arzikinsa dayay arayuwa da har dayake tinkaho da sunan sa ayanzu.

Agidan ta kwana wajen hjy khadijatu tanata aikin rarrashinta wai koda zuciyarta zaiyi sanyi.

Duk hanklinta sai ya tashi dataga yadda kafayat ta buga makircin ta saka mahaifinsu yaci musu mutunci sosai ya nuna kamar baisansu ba.

Yau Kusan kwana tay tana waya da yar uwarta dik tausayin yaran ya kamata sosai dan aranta tasan kafayat batada hankli taga bazata iya da ita acikin sauki bane shiyasa takeson ta bada karfinta akan yaransa.

Da asubahin fari bayan ta idar da sallah ta nemi ganinsu asashenta dukansu..

Babu bata lokaci suka hallaro sashenta iya suya yasu yaran jimada.

She make sure dat agidan Babu wani wanda yasan ta nemesu privately dan A dakin daga ita sai Brother kazim da brother hamzat
Da zainab tare da Ahmed daya shigo daga baya.

Dukkansu a dar dar suka gaisheta sabida yadda suka ga fuskarta babu alaman fara'a ko yanayin lallami duk fargaba ya gume musu zuciya,har sun dauka itama masifa zata musu kotace zata rabu dasu na har abada.

Bayan sun gaisheta ta amsa musu babu yabo babu fallasa Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin nan tafara musu magana dukansu cikin nitsuwa da sonta fahimtar dasu yadda ake cin ribar rayuwa.

Saida ta gama musu nasiha mai yawa snn tace musu su dinga danne zcyarsa Dan da akwai matattu dayawa da kalmomin su na raye snn da akwai rayayyu dayawa da ba'ajin kalmarsu dan haka susan irin kalmomin da yakamata suna furtawa.

Tace musu basuda zabi akan abunda zasu ji ko zasu gani yanzu,amma sunada zabi akan abinda zasu iya fada snn Batace musu su amshe kafayat a matsayin uwa ba.

amma tace musu shi
Kalman iyaye bayana nufin wayanda kawai suka haifi y'ay'a bane,
Shi kalmar iyaye itace ake bawa wanda yake kulawa da yaransa da kuma basu tarbiya mai kyau. tace Idan suna son susan matsayin tsoron Allah a zuciyarsu, su fara duba halinsu tukuna, snn ya kasance duk wani abunda zasuyi suyishi dan Allah badan kowa ba.

Game da auren baban nasu tace musu tasan yay musu zafi sosai harda itama,amma su sani cewa iya matsorata sune suke tsoron shiga duniyar soyayya, kamar yadda Masu hankli basu zama acikin duniyarta.

Tace su mance da zancen fushi da sukeyi da auren mahaifinsu dansu huta ma ransu daga walaknci da tozarci dan kuwa yawan hayaniya baida wata riba face kaskantarwa.

Barema ita kanta sai yanzu ta fahince cewa Ba'a tuhumar wanda yay aure da kalmar rashin adalci, tace dan haka Karku zauna kunata tuhumar mahaifinku da kalman yaudara dan yaje yay aure..

Da ace muku yana neman wancan karuwar yana neman wann gara yay auren koda auren baizama irin wanda sukeso din ba.

Tace Idan namiji ya aure mace toh wallh matarsa ce, idan har kuma ba matarsa bace toh kuna zamanku auren nan zai tarwatse basaima kun daga jijiyar wuyarku ba.

Tace ma sister zainab Shirunta shine zai rabata da kowa lafiya.

Tace ma su brother kazim mai hankli shine yasan inda dare yay masa ba. duk kun girma yanzu kun zama abun alfahari na, Bayan darajarku ta dan adam Lokacin ku shine mafi tsada agareku.

mahafinku ya riga da yaci zamaninshi da wata kafin nan ni,shin zaku bata kuriciyarku ne kuna fada dashi dan ya karo wata koko zaku ci naki zamanin cikin kwanciyar hankli?..

Sosai ta musu nasiha mai nitsuwar tare da igniting positive mindset a zuciyoyinsu.

Lokaci guda tasaka suka fara ganin cewa duk wani masifar da zasuyi da mahaifinsu akan kafayat is not even worth it.

Kamar yadda hajy khadijatu ta basu shawarar cewa yanxu lokacine da zasu tashi su cigaba da neman kudi suyi rayuwarsu mai dadi su moreshi dakyau tare da iyalansu hakan kowa yafara tunani.

Bayan sun kammala maganan kowa yay mata alkwarin zai gyara halinshi, snn suka babbata hakuri.

after a while bayan komi ya lafa nan tafara kiransu da daya bayan daya tana samun alone time tare da kowannensu batare da sunsan da hakan ba.

Brother kazim tafara yiwa nasiha akan cewa ya koma America bakin aikinsa dan izuwa yanzu yaci 1 month kenn anan nigeria bayan aikin kamfaninsa nacan yafi kawo masa kudi..

snn ta kara nitsar dashi a matsayinsa na babban yaya, tace masa komin rintsi karya dena kiran mahaifinsa ko ya dena tura masa kudi ko wani alheri, duk wani abunda zaiyi he shud do so with respect.

Brother hamzat kuma shine kamar jagoran gidan nasu anan nigeria musmamn idan brother kazim din baya nan.

Shima haka nan ta masa nasiha akan ya rinka kyautata muamalarsa da mahaifinsa batare da ya shiga harkan kafayat ba gudun karta ballo masa da rigima. Snn taja masa kunne akan yanayin zaman matayensu da yadda suke ware kansu wani lokaci tace masa aikinsa ne ya dinga saka musu ido sabida sudinga hada kansu dukansu uku domin cigaban family.

Sister zainab ma kusan irin wa'azin datay mata kenan na batun hada kan yan uwansu mata dake karkashinsu acikin gidan aciki har ta sako mata zancen Adiaha tace mata mace ce yar uwarta,taji tausayinta mana a matsayin wacce bata da kowa nata snn sudena blaming dinta akan laifin da babansu da kafayat suka aikata musu su riketa hannu bibbiyu.
Chapter 26 · 0% Book details