← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 157

Sashe 3

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji yay kanshi na sarawa gabansa na masa duhu duhu dan har rufewa idanunsa sukeyi tsabar bacin rai,lokcn da zuciya ya debesa ya juya yabar cikin gidan baisani ba.

Yana bude motarsa yaji duk jikinsa ya kwabe sai hawaye daya farayi na tsantsar bacin rai da takaici, wayarsa ya ciro hannunshi na rawa ya kira yayansa brother kazim, bugu daya ya dauka sabida shima ahnklinsa a mugun tashe yake yanzu, Da brother ya fara maida masa labarin Abunda ya shiga ya tarar agidan nasu har rawa rawa sanda muryansa yay sabida abun yaci masa rai sosai msnn yadda yaji cewa tun anan filin hidiman biki kenan mata suka fara baza kasuwar sirrikan auren mahaifinsu acikin tray suna wasa dashi.

Brother hamzat Yace im sorry brother kazim nifa Bazan iya hakri ba, i cant take dis, zubda mutuncin yay yawa, biki bidiri sukeyi acikin gidan kmr wasu mahaukata kuma wai acikin filin bikin ne ake gaya ma amarya yadda zata na kwana da babanmu, nide zan tarwatsa taron auren nan saidai in baba zaizo ya kasheni, cos how are you sure that yarinyar nan bazata je tana baza sirrinshi a waje ba inya kwana da ita gobe?

Yanzu haka rayuwar mu zai dawo kenan agidan nan? Mutuncin mu ya zuba duk da matsayin da muke dashi acikin al'umma sabida selfish interst din su anty moju? This is not fair to us.. sai yanzu nake dada fahimtar Ahmed daya ki sam ya aure kafayat din nan sabida dan yasan mutuncin shi zai iya kwabewa ne sabida bata da kunya kuma batada sirri ko kadan, to gashi mai kankat mahaifinmu ne yaje ya jajibo mana,.u shud see the way they are jubilating ,tsakar gidan mu yadda kasan kasuwa haka ya dawo and they are openly discussing how she will sex him tonite i just cant believe this life.

Brother kazim da kyar ya hadiye maganan aranshi
Yace "bazan iya magana yanzu sosai ba, sabida raina abace yake, amma duk wani abunda kaga ya dace kayi amma karka yadda kasaka musu hannunka aciki.

Bayan sun kammala wayar Direct yay hanyar police station bai tsaya dogon bayani ba kawai ya biya kudi yay bribing ogansu dayake on duty aka hadosa da mota guda na polisawa ana tsaka da hidima saigasu nan sun ta taho musu abaza..

Shikam Asibiti ya wuce baima tsaya ganin rashin mutunxin da za'a musu ba dan ya bada oder ne mai tsauri akansu.

Polisawa suna shiga gidan suka watsa tear gas, dake dare ne kowa saida ya rude babu wata bayani suka hau zabga ma yan rawan biki dorina suna tarwatsasu duk wanda yazo musu magana basa saurarar shi saidai yaji dorina zaff zzaffff, hatta har uwar amarya saida aka mata ciki da bai da su anty moju da sukazo masifa, sukam polisawa oder kawai suke bi,basu tsaya sauraran kowa ba, sai zana da suka dinga watsawa a iska duk wanda hannunsu ta sauka akai, nan da nan wajen ya dauƙe da wani irin hayaniyar nemn ceton rai mata sai gudu suke _kiti kiti kata kata_ kowa nata kanshi ana rabza ihu wasu sun yarda gogoronsu akasa,wasu sun fita babu takalmi, duk gwalagwalan mata ya bace a rububi, in a short while taro ya watse wajen yay shiru aka watse a tsakar gidan..

Masu gadi aka saka suka watsar da kayan kide kiden har waje izuwa bakin gate aka tarkata musu shi.

Polisawa ne suka ja gate din suka rufe bayan sun kore kowa awajen aka bar zallan maigadi

Jiki duk yaji tsamii haka su anty moju suka dauki amaryansu kafayat da aka zazzanawa jiki da dorina garin gudu acikin rubibi suka kaita can family house Acan Kowa yaje ya karashe jinyar jikinsa

Acikin tashin hankli da bakin ciki suka zauna sun kira lambar alhaji bello amma saiji suke wayarsa akashe da alaman baima san meke faruwa ba.

Hjy fatihat sai hargagi take tana zage zage akan cewa saita kaisu kotu akan cin mutuncinta da akayi mata aka tarwatsa ma yarta ranan farincikinta.

Ta kkira police station bata samu gamsashen bayanai akan operation din ba dan bakaramin kudi brother hamza ya biya dan amasa aikin ba.

Haka daren ya dawo musu tamkar wani sabuwar daren bakin ciki dan kuwa dukkansu sun zanu sosai, an musu korar kare, aka tarwasa bakinsu na kunya da sigar tozarci, duk shedanancin su da masifar su saida abun ya taba musu zuciyarsu sosai dan basuyi tsammani ba, duk sun dauka zasuci karensu ne yau ba babbaka, anty mojushola ma saida aka kwantar da ita ana mata fifita kafin nan aka saka mata engine din taya numfashi sabida tear gas din data shaƙa sosai.

Banda kuka da bakin ciki babu abunda kafayat takeyi, Su canko sunan wann, anjima su canko sunan wann, duk kansu ya kulle sun rasa wayene isashen da ya aiko musu polisawa aka musu wann kalar tozarcin acikin jama'arsu mafi akasari dai acikinsu suna zargin cewa Ahmed ne,A DAURE A DINGA COMENTING ZA'A FI SAMUN POSTING AKAI AKAI HARDA KARI..

*NA KUDINE, PAY 500* *NAIRA VIA 0152983148*
*MOHD SURAYYA SULE GTB*

SEND UR EVIDENCE
*TO 08060712446*
CHAT ONLY

KAR A TURA MIN KATI TRU TRANSFER PLS CHAT ME UP FIRST.

AIRTEL 500 CF FOR NIGER..

®SURAYYAHMS..
#KISHIYAR KABILA2023
[6/2, 9:29 PM] SURAYYAHMS: Tunda polisawa suka tarwatsa bidirin bikin komi ya kammala acikin sauki Brother hamzat yay maza ya koma asibiti batare da ya nunawa kowa alaman komi ayanayinsa ba. Normally ya shigo ciki fusknsa babu yabo babu fallasa batare da yasako wani expression na fushi a fuskarsa ko wani hargagin tashin hankli ayanayinsa ba.

Daga shigarsa direct ya wuce cikin dakin da hjya khadijatu take kwance ya tsaya daga kofa shima yanata kallonta da fuskan damuwa ganin haryanzu bata farfado ba wanda hakan yasaka yaji babu dadi aransa sosai.

shiru shima yay baice ma Ahmed komi ba dan tausayin dan uwan nashi ya kamashi bana wasa ba, musammn ma dayaga yadda ya dawo abun tausayi agaban mahaifyarsa dataki yin motsi bare farfadowa har yanzu yana rikeda yatsun hannunta cikin nashi ya rungumeta sosai yana sauke mata hawayeshi da suke fitowa ahankli.

Duk damuwar Ahmed bawai akan auren kafayat da mahaifinsa ba ne akan mahafiyarsa ce dan itace tafi masa muhimmanci sama da kowa acikin duniyarsa.

Nadama da fushi ne ya gama nakasa masa zuciya dan yay ta bawa kansa laifi mafi yawan har zuciyarsa saida ta raunutu da halin dayake kallon kansa a matsayin wanda ya jawo silar halin da mahaifiyarsa take ciki aynzu

Yanayinsa na fushi yasa babu wanda ya iya shiga dakin ya samesa bare ma su kusance shi da wata magana na ban hakuri dukansu matayen nasu a reception suka zauna, Adiaha ta rasa meke mata dadi sai juyi take a zaune kmr wata kurma,dan da yarensu suke magana idan zasu yi gulma ko hirar abun basa ma sakota aciki.

Zaman shiru tay har saida brother hamzat ya fito daga dubashi.

Nan kowaccensu tayo kansa da fuskar damuwa Anty adizat tace yay jikin mumy? Ahmed din fa? Adiaha ma ta tambaya sounding soo concern..

Yace musu bata farfado ba. Amma jikin da sauki.

Anan cikin hall din reception din suka zauna dukansu su hudun nan yafara jawo Adiahan kadan kadan acikin conversation dinsu dan ta fahimce Ahmed sosai.

Acikin salo ya gwada mata cewa tadan masa uzuri sabida yana cikin tashin hankli yanzu

Bayan ya gamsu da Cewa ta fahimce shi sosai snn yace musu suje gida tare da anty adizat su kwana acan washe gari saisu dawo dan bazai kyautu ace sun tattaru duka sun kwana a asibitin ba.

Babu musu sukayi masa sallama, snn suka shiga dakin da Ahmed yake zaune suka sameshi duk idanunshi yay ja rike da hannun mahaifyarshi yana mata tausa ahankli duk dama haryanzu bata farka ba.

Anty adizat ce ta dafa kafadunshi a hankli snn tace "Take it easy on ursefl damilare. _eṣu wa ni ibi iṣẹ_ kayi hakuri dan Allah komi zai wuce

Anty nurat tunda ta kalle yanayin hjya khadijatun sai idanunta yabi ya ciko da ruwan hawayen tausayi, jikinta yay wni lagwas cike da muryan jimami tace"Allah ya kawo mana saukin wann abun, Allah ya bawa mummy lpya, is not worth it Dami.. _e pele oo, crying will not ease the pain of betrayal, Allah ya isa mana; Ọlọrun yoo ri ọ nipasẹ_

Baice musu komi ba yay nodding kansa alaman ya gode musu bisaga kalamansu na taya jaje, nan suka dan tsaya akanshi kadan kafun nan suka masa sallama suka fita waje.

Adiaha tana ta kallonshi da mutaccen jiki aranta tanason ace ta kasance tare da shi ayanzu saidai tasan hala anties dinsa zasu iyayi mata magana idan tace zatayi hakan msmm ma da ta kasance ita Amaryace tanata tsoron kar azo a fassarata da rashin hakuri akan lamarin spending darensu na farkon aure.

Bayan ficewarsu anty nuratu jiki a sanyaye ta matso kusa dashi tana tabashi kadan ya daga kai tare da mata kallo daya snn ya dauke kansa ya kawar gefe bai ce mata uffan ba dan sam baya cikin mood din yin wani dogo magana, atakaice ma komi gameda rayuwarsa nayau takaici yake basa sosai.

Tay gyaran murya "Tace, hubby if u need any help, i can...bata ma karasa maganan ba cikin sauke ajiyan zucya yace "no thanks. I want to be alone..

Da muryan damuwa akansa sosai Tace but are u sure?Saida yadanja snn yace ."Yes..kije mana ba jiranki sukeyi awaje ba? Go'on karki bata musu lokci.

Ta gyada kai ahnkli har zata fice kenan taji shi yanamai ambatar sunan ta. adan hanazarce tare da sauke ajiyar zuciya ta juyo, Suna hade ido taga ya haɗa ransa sosai yace karki ce zakizo nan gobe. Ya isa haka just stay at home kijira harse mun dawo.

Da mamaki a muryanta Tace "ah'a,meya faru kuma hubby toh Meyasa? me zanyi a gida idan duka family babu lpya kowa yana nan tare da mumy.

Rai a harde sosai ya kalleta yanamai watsa mata harara mai sanyi snn yace"my family is alwys fine..xuwanki ne komi ya lalace, inkinason kanki da lpya just go home now and stay kmr yadda nace miki, kidena shiga cikin family for now dan kowa yasan akanki ne kafayat ta yanke wann wawan hukunci akan iyayena..
Chapter 3 · 0% Book details