← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 157

Sashe 58

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yawan yabata da aka farayi kowa inyazo wajen zaice mata ta hadu tayi kyau awajen yasakata tafarajin kanta sosai

Mrs Ahmad ta dawo tamkar tozali haska idanun kowa su anty nurat suka dawo daga uhmmm sai uhmmm yau babu magana dan kuwa sunga alaman Adiahan nan da zafi zafinta take tana son tafi karfinsu sosai.

Tunda Ahmed ya kammala zagawa da ita yasaka ta gaishe da wayanda yake respecting
Acikin manyansu shikanen ya kyaleta ta nemi wajen zama itama ta zauna tare da kawayen amare.

Komi yadda ya gaya mata takeyi wanda yasaka kishi ya dinga cin zuciyar kafaya da su anty adizat.

Coments da girman da ake bawa Adiaha yasaka ta fandare da jiji da kai tafarajin kanta wani abu ne,nan ta zubawa coupls mannin sabbin kudi kmr bata sonsu, gata da son tiƙan rawa kowani waka aka saka zagewa take tayi rawa abunta batajin kunyar kowa wanda hakan ne yasaka sbbin mahassadan ta suke mugun jin haushi.

Ba a kare hidiman ba kafayat taji haushi ta bar wajen taje wani club domin shan giya dan ta jima batasha ba dama gashi yau ta kumsu baqiñ cikin ganin Ahmed da Adiaha ayanayin da bataso ba.

Kawai gàni take kamar an cuce rayuwarta har Ahmed ma wai ya mance da ita tulin shekarun nan da sukayi dashi suna tare. Babu abunda ke taba mata rai face sai taga irin kaya da kuma jeweries da Adiaha take sawa wanda tasan duk da kudin Ahmed dinta ne.

Can da yamma bayan an gama hidima aka rage yan rawa Ahmed tuni ya tsame kansä yabar filin Adiaha ta zauna taci rawa da familyn ango da amarya kamar bikinta akeyi...

sai can da yamma ya fara rufawa ta nemesa bata gansa ba ta kira layinsa ma dik kasshe

Tana ganin su anty nurat suka ja motarsu suka koma gida basu ko kulata ba sai can da basira yazo màta ta aika aka kawo mata nata motar kafin nan ta dawo gida duk ta kwaso gajiya ajikinta bana wasa ba.

Da kyar tay sallah tay wanka kafin nan taci abinci awajen bacci yay awon gaba da ita bata tashi farkawa ba sai can da asubahi.

Ganin yadda ta bar kofar abuda hakanan yake ta shaida cewa Ahmed bai dawo gidan ba, wayarta ta dauka ta kkirasa bai daga ba, ta tura masa tex dik baiyi mata reply ba.

Dagata bagarensa kuwa a hotel din da suka shirya ya kwana yana fama da tunanin yadda zaiyi kewar babban amininsa banji, dayan abokinsu bankole kuma sai tsokanansa yakeyi akan irin rawan haukar da Adiaha ta tika awajen biki.

Duk sai yaji ya kule ya shaƙa abun aransa, wato dai duk yadda akayi da jakar mace saitaci kara ko? Haka kawai ya yanke hukunci aransa cewa bazai kara nunata a matsayin matarsa awajen hidima bare taje tana rawan yan tasha irinna jiya acikin taro tana zubda masa mutuncinsa ba.

7.30 suka shirya suka fito sallamar amarya da ango dan jirginsu 8am zai tashi izuwa canada..

Haka Duk suka taru suka masa Addua da shi da matarsa, Ahmed ya dingajin kamar zai zubda hawaye dan shikadai yasan amfanin da Banji yake dashi arayuwarsa gashi yau zasuyi ban kwana zaikoma wata duniyar daban da zama.

Sallamarsun was so funny and emotional duk kinsu da suyi hawaye ma juna saida sukayi..

Har aiport suka rakasu shida matarsa hidayat basu bar wajen ba har saida sukaga tashin su ya rage baida wani na kusa dashi sosai ayanzu face banky..
[6/19, 10:04 PM] SURAYYAHMS: Tun dawowarsa bayan biki Adiaha ta kasa gane masa sabida daure mata fuska dayake yawan yi agidan..

Wann yanayin na rabuwa da abokinsa Banji shine ya dan taɓa walwalsan na kwana biyu wanda yasaka yakejin baison dawowa ma gidansan sai kawai ya dukufa kan aikinsa na asibiti da kuma hidimansa acan katsina da za'ayi nan da sati mai kamawa.

Adiaha duk tabi ta damu da recent behvrs dinsa, Abu dayane kawai yake sakata cikin nishdi data lura cewa su anty nurat sun fara jin shakkarta sosai snn kafayat ta shiga wani irin yanayin shiru shiru kwana biyun duk sai taji kamar taci galaba akansu ne shiyasa duk sanda ta hadu da dayansu bata ragarmasa musnm ma idan ya shige tsabgarta

Yanzu kam basu isa su gaya mata baqar magana ba sai ta amsa musu,anty nurat tay tay dan ta gaya mata sunan tailor dinta amma haka taki firrr yanzu haka ko yar gaisuwar fatar baki basa yi tsakanin su.

Adiaha kullum tana sashenta tana minding business dinta, Iya kaci da safe daga ta kira mother inlaw dinta ta gaisheta sai inta shigo gidan taje ta gaida alaji bello a nashi bangaren tanajin dadin yadda yake yawan son saka mata albarka arayuwarta kullum,dan inyana mata haka sai ta tuna da nata iyayen duk tausayin kanta danashi sai yana damunta aranta sanin cewa kafayat bata kulawa da shi sosai.

Haka kawai intanajin neman tsokana zata yi wanka tasaka hadadden leshi wanda yaci ubansa da dinkin zamani tazo har bangaren anty nurat gaishe da brother hamzat dan kawai ta gigita ma anty nurat din hankli dan duk sanda tazo sai sunyi cakke cakke maganan, ita kanta ta gane cewa Adiaha ta fara raina musu hankli sosai.

Badon islamiya schl din datake zuwa da safe ba da hala abun nasu wata rana zai iya jawo musu hayaniya mai yawa dan bakaramin kufuluwa suke da salon rashin kunyar data fara musu ba.

Samun Dama da sauyawar rayuwa da kuma privilages din data samu awjan mijinta duk sun saka mata izgili da girman kai inka ga tana cikin damuwa ko fushi toh akan Ahmed dinta ne amma yanzu bata jin shakkar uban kowa.

Bayan bikin Banji da kwana hudu Ahmed yay tafiya ya wuce katsina domin fara supervising din shirye shiryensu acan ganin lokacin dawowar su hajiya maimunatun nigeria kwata kwata baifi saurayan kwanaki shida ko bakwai Ba Snn daga dawowar sun baifi da sati za'a gudanar da hidiman ba.

Yana yin tafiyarsa garin katsina Adiaha ta Samu filin fandarewa tanamai baza iya nata tsiyar wa matayen gidan har sanda tafara tunzira kafayat ta cusa mata bacin rai aranta sosai..

Kwana biyu da suke dramar su na cakke cakke magana kafayat tana yawan gaya mata cewa sai taga karshenta agidan.. snn lokacin ya kusa da zata fara koya mata hankli, zata sakata ta shiga uku,.zatay dan dana sanin auren Ahmed, amma dik Adiaha bata daukar zancen serious aganinta duk dai a baki take maganan kamar yadda tay mata afarko batare da ta mata komi ba.

Hakanan suka zuba mata ido kowa na kallon gudun ruwarta agidan ta dawo bata harka da uban kowa daga taje islamiyya ta dawo shike nan bata kara lekowa waje sai washe gari da safe.

Kwana biyar masu kyau Ahmed yay a katsina yana mai kulawa da dukkanin abunda ya kamata ga albarkan iyayen nasa dayake samu akowani rana.

He is an upright classy person, akomi ma ilimin sa da nitsuwar sa yake zubawa shiyasa komi akayishi in double high standards duk wani abu da yake shiryawa na hidiman anayinsa ne a salo na kece raini dan shikansa yana da high taste of time and materials idan yazo baya sake aikin ma workers yana zama ya bata lokcin shi wajen supervising komi.

Hatta mansion din ta na katsinan da aka sake renewing dinsa ya dawo tamkar sabo duk shine ya saka kulawarsa akai sosai har komi ya kammalu akan lokci.

Dan kwana biyar din na dayay awajen kusan duk wokers din saida suka sanshi sabida shidan qa'ida ne, iya abunda yace yana so shine agabansa wanda ya kawo masa wasa kuma yanzun nan zai koreshi.

Hakan dayakeyi yasaka workers din jajircewa akan aikin nasu sosai ko sadik ma dayake can yana monitoring he was very much impressed.

Saida ya tabbata an kammala komi kafin nan ya tattara nitsuwar ya dawo Abuja a tsatsaye dan yana sone ya aiwatar da abunda yake da niyya tuntuni akan future din Adiaha..

Ganan ma hjya khadijatu data fara matsa masa akan ya amsa mata appoitment na gwamnati awajen antynsa amma yace sam shiba hakan yake so Adiaha business tace zatayi.

Dan tsabar baison ayi diverting intrest dinsa izuwa wani waje yasaka yay sauri wajen bada cikiyar available store na hire a babban plaza dake cikin anguwar gwarimpa hadadden storey building ne mai suna shagari shopping complex .

Dawowar sa da kwana biyu aka sama masa babban shago mai ruɓi biyu acikin wajen Babu wani bata lokaci ya biya kudin ya kama mata snn ya saka enough labour workers suka hau gyara shagon ba dare ba rana nan da nan shago yay fess yay masifar kyau har ana fadarsa awajen sabida show glasses daya saka aka mata aciki da waje.

A ranar kwanansa na hudu da dawowa yau baije wajen aikinsa ba bayan ta tashi daga islamiya ya dauketa yakaita wajen ya nuna mata yace mata nata ne anan ne zata fara business dinta and she can choose what eva she want to sells duk profit da income nata ne..

Fadin irin murnan da Adiaha tay bazai fasaltu ba, dan kuwa Ahmed ya sha luguden rawa,amasa wann amasa wancan ji take kamar tay postern sa a sama tafara masa sujada tsabar sonshi daya karu ninkin baninki acikin ranta.

Daga safiyar ranan har dare family da inlaws dinta duk sun mata murna, kukan murnan datay wa kakarta yau ma bazai iya fasaltuwa ba Dan Komi yana zuwa mata tamkar a mafarki yau Ahmed ya gama mata komi arayuwarta har bakin mahassadanta ya mutu akanta.

Tun da haka ya faru su anty nurat suka fara tunanin sauya taku dan yanzu kam sunsan bazasu iya samun daman raina mata hankli ba. Anty adizat tuni ta yarda makamin gulman ta fara kame kanta a bangarenta aka bar anty nurat da tunanin yadda zatay ta jawo Adiaha ajiki dan ta cutar da ita.

Kafayat kuwa tunda akayi haka agabanta bata kara dawowa gidan ba daga can gidansu ta wuce lapiya wajen kawar mamanta anty rakiya..

Bayan kwana biyu Ahmed ya bawa Adiaha isashen kudin da zata saro duk kayan datace tana so tare da jadadda mata cewa ya kammala bata capital kenan inta je ta salwantar da kudin ita ta juyo babu ruwansa.
Chapter 58 · 0% Book details