← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 157

Sashe 78

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin kofa yasra ta kusa cin karo da hjy khadijatu tayi zuru zuru tace "meyasameki ?Auta kinga abinda nake gaya maki ko.,bata karashe maganan ba tayi shiru ta riko hannun yasran a dame tana tambayar ta lafiya yanaga kamar kinyi kuka? Mey ya sameki kuma idonki ya canja kala, kamin ta bata answer ta sukaji muryan shi ya sake kwada ma mai aiki din kira, bata jira cewan yasra ba ta sauka kasa tanacewa hmm ke da Ahmed ne ashe...bari naje na same sa.

Isarta ke dawuya tay gyaran muryan akansa " a nutse ya juyo ya kalleta yace mummy yawwa tun tunii nake ta jiranki .tana isowa daf ya dan rusuna ya gaisheta,ta amsa.

Tafara tambayarsa meya hadashi da yasra, a farko ma yay kamr bai tuna sunan ba, daga bisani kuma ya dubi mum din nasa da sigar masifa yana cewa bataji ne,inna mata magana bata amsa wa wai ita kurma ce?doesnt she talk,ko kuma gaisuwa ne bata iya ba?

A zuciyanta murmushi take jn komai saiyay ƙorafi,nima ynzu in nayi magana yace na cika bin bayanta, Tana cikin tunanin taji yace anyways mum next week zasu fara lectures na new student so koma yay ne dai ya kamata ta dawo ta fara attending itama.

Tace its okay, munakan shirin tafiyarta abujan ma..Adda maimuna nake jira kasan jiya sadik ya tafi London attending mata wani summit shiyasa duk abubuwan suka dan tsaya but tace min jibi zata iso lagos din .. amma kaima zaka dan jira mu mukoma tare ko?ko tafiya zakayi muzo musameka .

Yace "gobe zan wuce.
Ina da aiki dayawa kawai dai sun kun iso.

Daga nan tafara tambyarsa jikin Adiaha duk ta lura yadda kwana biyun nan ya dan xube yay fayau kamr wani abu na damunsa, daga bisani suka shiga hirar yan uwansa dan bakaramin kewarsu takeyi ba.

Sai can ta barsa yana kallon ball ta haura sama cikin Ɗakin ta nufa,tana shiga ta tarar da yasrah tsaye tana riqe da foams dintan a hannu ta gama karanta komi dake jiki, idanunta sun fiffito waje, suna hade ido da hjy khadjatu cikin sakaltaccen salo ta makale wuya tare da shagabe murya snn tace "mumy nifa bazan je schll din nan ba saida ke, idan ba haka ba kawai na fasa karatun,..

kallonta hjy tayi ahnkli tana murmushi snn tace "hey, kidena cewa haka, waiko yayi miki wani abu ne kiketa fushi? dan nasanshi da son yiwa mutane masifa.

Da wuri tace A'a Ni baiyi min komai ba kawai bana son na bishi ne..

Nan hjya ta zauna gefenta tare da riko hannunta cikin nuna mata kulawa sosai, tace Auta na babu yadda zamuyi mubarki kije schl ke kadai karki damu duk tare zamu kaiki abujan kinji?

Boyayyar ajiyar zuciyane ya kufce mata cikin gyada kai tace okay mumy.

Tace Yanzu ki shirya kije ki gaishe shi, u shud get along, kinga yanzu baki da wanda zakina looking upto acan ABUJA in bashi ba, he is alwys ur quardian, ur protector, ur guide, duk wani matsalar ki washi zaki fada, since sadik is not der, Adda kuma ina zakina ganinta bare ni?

Shiru tay da yanayin sanyin jiki da alaman duk
Dai bata son wnn hadin

Cikin karantar yanayin ta hjya tace "Ahmed is a nice person, inhar kika kwantar da hanklinki u wll enjoy his company very well, and his wife is very kind too, ai na fada maki ko?..

Ajiyar zuciya ta sauke tace okay naji mumy kawai dai bana son masifa ne. Mumy kice masa karyana min masifa kuma fa ni karatuna kawai zanyi acan babu ruwana da shi.

Tace dont worry we wll talk about it more, amma dai ki sake jikinki dashi..
learn how to adopt with him kinji? Shima fa babban yayan ki ne dolene ki basa hadin kai, kinga Jibi mumynki zatazo mufara shirin tashi i hope kinakan tattara kayanki?

A ladabce ta gyada mata kai ta kyaleta tafara shiri ta saka riga da skirt ta fito har falon tazo ta gaishesa kmr yadda akace mata cikin girmamawa shidai yanata kallonta da mamaki daganan tay shiru itama ta zubawa tvn ido bata masan metake kalla ba.

Fannin Adiaha jiya da safe bata gansa ba washe gari ba batagansa kuma bata nemesa ba.

Abun na damunta sosai amma memakon ta barshi acewa yana asibitin kamr yadda tay harsashe tun farko saita fara kawo tunanin ko ya sabule yakoma wajen mummynsa ganin waccan kyakkwan yarinyar ne.

She was feeling very very insecure lokci guda ta dama cikin zuciyarta da mummunan zargi, zato, da kuma kishi mai tsanani bata tunowa da komi sai irin maganganun da su anty nurat suka cika mata akan kirjinta akan event din ranan.

Shiyasa When ever bata gansa kwana biyu ba sai ta fara tunanin ko tafiyan kawai yay.

Yau ko shagonta bataje ba tana cikin gidan tana kokonton ta kirasa ne koko ta bari harsai ya dawo.

Daga can lagos kuwa Sai can da yamma Ahmed snn ya dawo with the little changes of bvhr dayagani awajen yasrah yasaka hanklinsa ya dan kwanta yafara tunanin dedetawa da lamarinta kadan.

Cos tunda hjiya tay mata magana jiya saita rage masa baqin halin nan nata tafara gaishesa normal batare da funny attitudes ba. He thinks she is actually cool saidai shagwabanta har caga masa brain dinsa yakeyi musmmn ma intana shiru shiru.

Har ya dawo Abuja tunanin yadda zamanta a hannunsa zai kasance yakeyi domin kuwa yasan he need to make no mistakes waajen kulawa da iya baison yay abunda zaije ya batawa iyayensu rai akanta.

Kullum iyayen nasa sai sun ja masa kunne akan zaman yarsu a hannunsa

They urge him to take care of her like his own child,basa son suji wani story nacewa yarsu ta rasa ko tana cikin takura

Hjya maimunatu hartay offering akan tana tura musu kudi amma yaki sam yace zai iya mata komi da kudinsa basai tay hakan ba.

Ga mahaifyarsa ta riga ta damka masa rikon nata a matsayin amana data bar masa a hannunsa.

Yasan dai Baida matsala da matarsa Adiaha cos all she have to do is to obey him as alwys, behvr din yasrahn ne baida tabbas akai But he just hope dat one day itama he wll be able to have full control over her...

Bayan dawowarsa Abuja yazo tarar da strange bvrs na Adiaha data fara nuna masa alaman ranta ya baci da yaje lagos din batare da ya gaya mata ba tunda ya lura da hakan saiya dauke kai yay kamar baisan metake nufi dashi.

Yanata son a gyara dayan empty dakin dake tsakiyar nasa wa yasra so that in tazo ta zauna aciki Sai yaga duk wani abunda yakece mata ta tayashi yi gameda lamarin dawowar yasrahn batason yi saidai tay faking wani complain na ciwo ko tace tana jin kasala zatay bacci.

Har Ana washe gari su yasrah zasu taho bata tabuka komi ba kawai saiya shareta baice mata uffan ba,da safe yau da suka farka yana kallo tay wanka ta wuce shagonta

chatting yau ta wuni yi tana kallon reels a ig yaran shagunta suna handling mata customers

Around 2pm na rana ta dawo gidan agurguje Dan already abiodun yakai mata gulman cewa home experts na kamfanin magicfingers sunzo suna aiki a sashenta,Kafin ta dawo gidan tazo ta samu har an gama komi suna kan kammala dan Abunda ya rage ne.

Dama medium size gado ne kawai da wardrob da mirror a dakin nan Ahmed ya saka akayi rebranding din room aka maida shi irin yadda yasrahn zata so a princess theme bedrom with all the fancy things na yan gata bai bar komi ba curtains, bargo, sallaya, beddings,kai lokci guda kawai dakin ya zamo tamkar wani ready made .

An shirya mata wajen karatu na musammn customise reading table ne da chair da headlight da wajen placing din system dinta gefen gadonta aka jona mata lamps guda biyu.

Sai aka saka mata sofa dan daidai da duk wani toiletries, kama da kan bathrobe, sleepers, towels,hair dryers da sauran tarkacen da zatayi amfani dasu.

Masu gyara suna aikinsu Adiaha sai shige da fice takeyi a room din duk ta musu magana basu wani kulata ba tinda wata ma'aikaciyar tace mata mai gidan ne yasaka su.

She called him many times tsabar tay fushi har jikinta na rawa amma bai daga kirar ba dan baisan me zaice mata ba since ita taki tay dolene yasaka wasu sumasa tunda dai baison suyi wata magana akan hakan ne bare yaje ya gaya mata maganan banza.

Tanaji tana kallo akayi ma room din yasrah more than necessry aka narka nera wajen tsara matashi ya dawo kmr sarauniya ce zata zauna aciki.

Tay fushinta harta gaji Ahmed ya dawo can da yamma tana gani yaje ya dudduba room din ya fito amma bata iya confronting dinsa ba sabida bai bata fuskan ba shima ransa a hargitse yau ya dawo yanata sha mata qamshi.

Lokaci guda kawai sai taji kuma ta damu sosai dataga ya dauke mata wuta kuma ko abincinta baici ba. chan dare dakanta ta sauko tazo ta sameshi da maganan, ta nuna masa kamr bataji dadin daya bawa wasu aikin bayan itace ya kamata tayi ba.

Sosai ya gano salon makircin datake so tay playing akansa aikuwa cikin ruwan sanyi ya gaggasa mata baqar magana dan tasan da cewa itace ta jawo harya bawa wasu suka masa aiki.. snn yace mata in the slightest way ta yarda ta walakanta sister sa agidan wallh saiya koreta a gidansa.

Haka yay baccinsa yau baiko kulata ba, duk sanda ta wulga taga yadda aka shirya dakin yasra shigen dakin yar gata, sai tay ta nadamar haukar da tay aranta nakin kulasa da ya mata tayin aikin,dan tasan da itace incharge da duk wann kudin gyaran da ba akasheshi ba.

Maganan da ya gaya matan haka ya dinga damunta aranta ta kasa bacci ma yau gaba daya, har sai washe gari data kira nurse din nan awaya suka danyi magana snn ta fara calming kanta ta gane cewa abunda takeyi ne bai kyautu ba sam.
Chapter 78 · 0% Book details