← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 157

Sashe 64

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adiaha was feeling lonely ita kadai a asibitin duk ta rasa wanda zata kira awaya abun duniya duk yabi ya isheta bai ishi Allah ba. She cant even call grand ma now saboda kunya datakeji dan saida ta gaya mata cewa irin haka zaizo ya faru atsakaninta da Ahmed, but she neva believed her..

Zaman kadaici tay har izuwa karfe 12 biyu na dare, ba mai tayata hira bamai jin damuwarta, she tot of calling hajiya khadijatu many times sai kuma tafara tunanin kartaje tay subutar baki ta fadi wani abun da zai jawo mata wani sabuwar fitinnan da zai rabata da mijinta na har abada.

sai can kafin nan nurse din nan tazo duba ruwan da aka saka mata koya kare ta canja mata ta samu Adiaha ta kife kanta cikin nisan tunani rike da waya hannunta alaman jiran kiransa takeyi haryanzu

Harsanda nurse din nan ta dafata kafin nan ta firgita ta dago kai suka hade ido,murmushi nurse din ta sakar mata fuska ba yabo ba fallasa tace "sister are u okay?

Cikin sauke ajiyan zuciya Adiaha tace "yes"..

Batace mata komi ba ta kammala gyara mata abubuwanta, snn ta gwada mata jininta again bayanta gama..ta dubeta tana murmushi snn tace

If u dont mind can i seat with u for a bit.

Adiaha Tace yes sure.

Nurse ta nata kallon tsaf snn tace "I can see ure lonely babu wanda zaina kwana kusa dake ko, I bet wayancan matan ma amma ba yan uwanki bane am i right..?

Formally Adiaha tace yes, ba yan uwana bane ,matayen older brothers din mijina ne dukansu.

Nurse din tace ohhhhh No wonder..i dont want to interfer in ur personal life amma yakamata kina kwantar da hanklinki kidena yawan tunani kar jininki ya dinga hawa cos ure going to become a mother now..

Furta mata hakan da nurse din tay yasaka Adiaha yin blushing sosai...

Tace yawwa ko kefa, Ur baby dont derserv all this distubed face ure putting..kulawa dakanki yakamata kiyi ynzu...
...kowa yana da family issure but dont let it affect ur child pls.

Adiaha ta gyada kanta ahnkli snn tace yes ure right, thnk u nurse.

Tay murmushi har kamar zata tafi sai ta dawo tace "zan iya miki wata tambaya ? Adiaha ta kalleta tare da mata alaman eh..

Nurse tace "what about ur husband, i mean is ur husband not around?naga har yanzu bai zo ba
Kinga likiya ma yace yana son yaganshi..is important for him to come..

Adiaha bata iya amsa wa ba kawai ta gyada mata kai..dan shiru tay snn ahankli cikin sanyin murya tace "am not sure he is aware am sick ko ina nan asibiti, wayarshi akashe yake tuntuni im just worried about him bansan ina yaje ba last time i saw him was yestadey night..

Muryanta ya fara rawa kamr zatay kuka tace he dint call me, gashi har wani dare yayi..ina fatan yana lafiya wereva he is.

Acikin yanayin tausaya sosao nurse di tace "ayyya", it is we with u, No wonder naga kin saka kanki a damuwa..dont worry erhhh, he wll be here soon. Besides Who wundt be here for his first baby? Naga yadda father inlw nake yake rawa dazu, he sound very happy with ur prgncy, lam sure famlyn ki suna sonki, ur husband too must have love u very much..gobe hala shikuma zaizo mana da owambe dancers...i love happy couples..wow, ure soo lucky my dear..

Hawayen bazata daya saukoma Adiahar yuuuu yana zubowa kmr an kunnasa shi yasaka nurse din dagowa cikin mamaki tana kallonta....
[6/22, 6:36 PM] SURAYYAHMS: Bakinta ta toshe adan tsarge Tanamai cewa "opps, did i say sumting wrong? Adiaha tana share hawayenta tace "no..its okay, jiki a mugun sanyaye nurse din tace pls am sorry i don't mean to make u upset.."Adiaha ta share hawayenta cikin girgiza kai tace trust me bakimin komi ba.."a dan dame nurse tace but why are u cryn now nifa na zauna anan ne dan naga ure lonely kuma jininki yana yawan hawa inkina zama ke kadai cikin tunani..but if my staying here zai zama kuskure gara na tafi ..

No haba, nurse pls dont say dat..wallh ba dan ke bane nake hawaye

nurse Tace to akan menene dear remember i am woman just like u, and also from ur tribe zaki iya gaya mini damuwarki..if ure okay with that.

Shiru Adiaha tay sai can sann ta dago ta kalle nurse din snn tace mata
"When u talk about happy couples,happy marriage its just make me sooo emotional,.tafada muryanta a mugun sanyaye.

Nurse ta dubeta a mamaknce tace why? is ur husband no more?

Adiaha tace GOD forbid..

Nurse tace Okay i am sorry..but menene matsalar?

Cikin sauke ajiyan zuciya tace its just funny how ppl usually think dat my marriage is perfect, kema atunaninki mijina zaizo nan yana rawa akaina ko?wani Hmm taja snn tace"i am soo scared bansan ma ko zaizo ba.

A mamakance nurse din tace "why, meyasa bazaizo ba bayan kina da cikinsa,What do u mean by ure scared, ko ba cikinshi bane ajikinki?

Hawayene yafara saukowa daga idanunta sosai cikin girgiza mata kai tace "nashi ne,.
"i just dont knw what is happening to us Amma nasan yana fushi sosai dani,we had a fight,a big fight..data fadi hakan saita rushe da kukan sosai tuna dikkan abunda ya faru jiyan dataji tanayi aynzu.

Rarrashinta nurse din ta shigayi tana mai sassaita da kalamai masu sanyi har kukan ya dan tsagaita cikin sheshka, muryanta a tausashe nurse din takece mata is normal for couples to fight, ai wann ba wani abu bane, meyasa kike damun kanki dayawa haka ehh, bayan kinsn ko atsakanin harshe da hakuri ma ana samun saɓani bare kuma mutum maicike da kuskure?...

Adiaha tace matsalar shine bansan ko nine da kuskure ko shine yay min kuskure ba.U said ure a woman u can also feel my pain abunda ya faru shine...yar uwata ce tazo ta zage shi, but then he overeacted and insulted her back, ya hada harda iyayena fa yana zagi..and when i talk to him about it ,...bata karasa ba ta fashe da kuka sosai tuna irin gorin dayay mata harda ce mata she have nothing to pack in zata bar masa gidansa.

Jikin nurse din yay sanyi sosai tace "Did he hit u?

Adiaha ta dago jajayen idanunta ta kalleta bata iya cewa komi ba saima Kara sautin kukan datay wanda hakan ne yasaka nurse din ta fahimceta sosai"Hakuri ta fara bata tana rarrashinta,and she felt much relieve,dataji anrungumeta haka ana mata magana da yaren su,she felt much more at home and secured..

Take zuciyarta yay sanyi tafara gayama nurse din complains dinta suka dawo hirar da yare sabid adare yay wajen yay shiru basason ji mesuke cewa.
cewa take batasan metayi da zafi da mijinta yake yawan jin fushi da tsananin haushinta ba

Tace baya fahimtar ta,bayan duk wani Abu na hakkin aure da kulawa tana masa harda ƙari.

Tace "ina cikin rudani mai yawa, sabida bansan matsalarsa bane ko daga wajena ne, cos my parents have cursed me severally tunda na barsu na aureshi,babana yace i wll neva be happy in my marriage, sunce sai an yaudareni nima..alots of oda bad things sun gaya min, snn kwanan nan sai inata mafarki akan anason arabani dashi, just recntly sai gashi na hadu da sister na and now my husband is upset with me, and he is nowher to be found, am tired ni bansan mezanyi ba.

Rarrashinta nurse din ta dingayi tana lallabta har tay shiru snn suka fara magana ta fahimta..

Nan har take bata labarin yanayin zamansu da su anty Adizat wanda aganinta shiyasa bazasu kulada ita ba. She gave her a brief history of her sitiuation din gidansu Ahmed sabida nurse din tace mata zata taimaka mata akan matsalarta..

Sai wajajen karfe 1.30 saura na daren kafin nan nurse din ta tursasa akan tayi bacci cewarta zuwa gobe da safe zatazo ta dauketa suje wani wajen da za'a iya warware mata matsalar ta.

Karfin gwiwar data bawa Adiaha akan cewa matsalar ta yazo karshe kenan daga goben shiyasaka har ta iya runtsawa...

_Turkey:Birnin istanbul_

K'aran Alarm ne ya cika dakin gaba daya, kwance take tana baccinta peacefully har sai da ƙaran ya kusa katsewa tukunna taja tsaki,ta Janyo wayar da kafarta, ko kallon fuskar wayar bata yi ba ta saka hannunta takatse karan tukunna ta maida wayan, duk abin nan da tayi bata bude ido ba, sai da ta mike ta zauna daga bakin gadon tukunna ta bude idonta a hankali wayar ta sake dauka taga alarm din 7:01, tafi minti biyar a zaune daga bisani ta mike tana fadin "mutum da kanshi zai saka abinda zai dameshi da ihu, gashinta ta tattare ta hade su waje daya, snn ta isa inda hadaddun bathrobe dinta ke rataye ta cire kayan baccin dake jikinta ta saka bathrobe din ta shige toilet, sai da tayi brush tukunna tayi wanka snn ta fito jikin ta ya dauka da wani irin qamshin sabulan wanka

gaban mirror ta zauna bayan ta fito daga wanka ta shafe duk jikinta da mai,ta fesa body spray tukunna ta je saka kaya, closet dinta ta bude ta ciro wata maroon abaya mai Babban hannu da adon gold daga jiki, sai da ta saka kayanta tukunna tayi inda jakunkunanta ke rataye ta jawo daya daga ciki ta zuba tarkacenta a ciki sannan ta yafa gyalen abayar a kanta sannan taje ta saka flat shoe din amina muaddi shima gold. har ta fita ta tuna da key in mota da wayarta nan ta koma cikin hanzari ta dauko lokacin 8:00am daidai.

kasa ta sauƙo lkcin babu kowa a gidan ko ina yay shiru,tasan yay sadik dai ya wuce nigeria tun jiya Aunty nafisa da farida ma hala tun jiya suka isa.

mummy kuma maybe tanakan bacci,nn ta nufi dinning area,sai da ta bubbude duk kwanun dake dinning din tukunna ta dauki dauki sandwich a cikin wani transparent bowl da cup ta tsiyayi fresh mango juice a juice dispenser, har ta zauna zata fara ci taga time zai kure mata maza ta mike ta yi hanyan waje dashi a hannu.
Chapter 64 · 0% Book details