← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 157

Sashe 69

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

And he's very sure farida bata zama anan site din to wanne ne dakin da aka ajiyeta, Tsuru tsuru yayi gaban door din thinking weda to enter or not, Har yayi furzan iska zai juya yabar wajen kenan sai ga adda nafisa ta bude wani kofarta fito, Bai fiye sakin fuska ba dan haka ya tsaya gurum fairly enough yace mata ina kwana adda nafi Sai da tayi gyaran murya snn tce lpya suka gaisa sai kuma Ya rasa me zaice can yace"mumy fa?

Tasan ba tanbayar dayake so yayi bakenan amma sai tace"ta fita babban falo, bai amsa ba...itama bata damu ba, Cike da nitsuwa ta zo ta bude masa door din daya kasa budewar tace bismillh Anan ya sake slight smiles yace thanks. Ita kam Kamar walkiya ta bace a site din

Nan ya kutso kan sa ciki aransa yace Hmmm su disney princesss ya furta kasan makoshinsa ganin inda ta wani irin kawata room dinta da girly stuff kamar wata sarauniya...

ya kalle ko ina ataikace ya kafin nan ya dauke idanun sa.

Har yanzu yasrah tana bacci sakamakon tsanantawar da zazzabin ta tayi bata samu tayi baccin dare jiya ba sai yanzu..

Tun daga juyowar kallon sa akan gado ya sauke lumsashun idanunsa akan attractive model like figure inta Don haka bai tsaya ba ya cigaba da tahowa kusa da ita yanamai kare mata kallo..

She's both milk and honey but more of a flawless fairy kalarta kalar light skin columbians wanda suka ji hutu sosai..

Fatar jikin bana baqar mace bane amma bazaka ce da ita fara mayya ba. Duk dama karamin jikine da ita kuma ta saka sakakken riga amma bai hana shi ganin streamlined hour glass shape din jikintan ba,tana da dan tsayida da long tender nails both hand and feet,jikin ta irin shape din jikin nan ne da hausawa ke ce masa karuwan jiki wata rana suyi manya wata rana kagan su moderate kuma duk suturar da zasu saka zai dauke su sosai kamar dan su akayi..

Ga Shatin breast dinta full blown pear shape dake ke tafe da flat tummy wanda ya shiga dai dai da wings din budadden hips din ta dake nuna alaman tasowar girmansa sosai.

Baisan ya akayi ya zauna yanamai hana kansa shagala da kallon angel face din ta ba, aduk dama tafishi dogon hanci sosai amma size dinsa is more than perfect for her baby looking face shi bai cika dayawa ba shi ba siriri sosai ba. tana bacci ne amma sosai alaman sakalci da shagwaba ya bayyana akan kyakkwan fuskartan tata,.

musamman ma karamin bakin ta dayayi pitchy pink irin nasa sai dai ta cikin nata da shatin kwalliyarsa daya bada dark brown colour line zageye da shi she have this beautiful face and body. Sai dai a Duk wannan yanayin da yake ciki baisaka ya sake fuskan sa ko yayi murmushi ba

Da yayi tunanin ya duba ta anan dakinta kawai amma sanin halin mum dinsa ya shafa makansa ruwa Hannu ya mika Yana shirin aiywatar da abunda ya kawosa ..

A take ta motsa tana shirin juyawa ayayin da loose cotton nite dress din nata ya dan kwaye sama kadan ya bayyana kafafun ta ...haka kawai ya ji wani irin shocking ajikinsa,zuciyan sa na neman bugawa atake sai ya mike tsaye cikin dauriya ya kamo hannun ta duka biyu cikin bacci zai mata dauka daya su fice aje dayan bangaren dat is quiet kamr yadda hajya tace masa.

Qamshin turaren sa da suffocating warthm din jikin sa yasa ta Lokaci guda ta firgita ta bude idonta amugun kasale, "ko da tayi masa kallo daya out of tension sai data lumshe idonta sosai tana budewa sau ba adadi a tunaninta ma mafarki takeyi dan tsabar tanajin tsoron ayi mata auren nan.

Butttt ta kifta ido sau daya taga basu dena kallon juna ba lkcin zuciyarta yana buff buff kamr zai faso waje.

Hannunsa daya zageyata ta shikansa baisan wani irin piercing looks yake binta da shi batare da ya hankara,kusan atare kirjinsu yake wani irin tsananin bugawa kmr zai faso waje,a mugun hargitse ta hau tureshi cikin masifa tace leave me alone, who are you?
Data dada kallon kanta cikin nity saida taji ta kara rikecewa.

Nan ya hankara da sauri ya sake ta da sauri Ya dada daure fuskan sa yace "to me zaice mata? Yace mata shi yayanta ne ko me? Mtsss, cikin jan aji yace i am ur doc zamuje dake can in dubaki.

Wani dammm kirjin ta ya buga A shakure kuma rude tace "Can? ko shaidan baisan chan ba, Kai din kuma waye ?Muryan ta yayi cracking tana shirin watsa masa rashin kunyar data saba.

Confidence din datay masa maganan dashi ne yafara taɓa masa brain ya kalleta, tare dada shakure voice dinsa sigar rashin kulawa da yanayinta a dakile yace" koma waye ni, kisani ni ba sa'arki bane,"dont u ever talk to me like dat u hear me? Ya karashe a izzance kafin ta hankara ta budi baki yace ok now just get up lets go.

Ya kawo hannu zai sake taba Wani irin gulluton mamaki da fargaba da haushi ya sa ta wuntsulo zaune cikin masa tsawa tanacewa"dont u fucking touch me...

yayi shuru ya tsame fusknsa da mamakinta
"Irin what?..

A fusaceta dan ture hannunsa ganin bai motsaba, daidai tayi wani kyakkyawan yunkuri kenan zata sauko kakarin amai ya turnuke ta nn ta fetso masa amai ajikinsa ta karashe da tari mai shake da takaici..

a gagguce ya ja da baya Wani irin turirin haushi ne ya kama sa one time yafarajin kamar ya rufeta da duka.

Cikin ransa ya furta oh god..kamar zaiyi kuka ya juyo a mugun fusace "yace are you insane? katuwa dake zaki min amai ajikina msww ya ya tsaya daga gefe yana shirin barin wajen amma sai ya kasa Ita kuwa ta dade da zulmawa cikin tunanin takaicin dayafara bata tayi idonta a lumshe tana jin jiri jiri mai tsanani.

A gefe kuma haushin ta bata masa kayansa ya sa ya shiga bathrum din wajen kawai ya cire rigar jacket din suit dinsa ya bar kansa da shirt na ciki revealing the curves of his very strong self.

Anan ya taho ya dake yana ganinta ta miƙe hartana share ko ina da tabata da mopper tsaban zazzabi har jikin ta na rawa rawa. Agefe ya tsaya yana mamakinta

So she is even strong enough to clean up the room shine don sakarci shine har zata masa amai ajiki? Tsaki yaja abayyane yasra tafarajin kamar ta masa ihu tace masa ya fita ya bata waje dan ta tsani anaja mata tsaki.Tana sane da cewa ya fito daga bathtum din ya tsaya ata bayanta amma ko kallonsa bata sake yi ba ita dai ta bata rai tana jin haushi.

Bai damu ba ya zo gaban ta yace i ques ure alright now dama nazo nadauke ki ne ure going with me to the oda side Zanje na duba jikin ki.

Bata ko kulasa ba ta yarda mopper a kasa cikin fushi kamar zagin ta yayi,waje ta nema ta zauna ta hade ranta cikin zuciyarta tanamai cewa bazataje koina dashi ba.

Abun sai ya dada bashi takaici sai ya ja karamar tsuka ya kauda kansa Tare da sauke boyayyen ajiyan zuciya Haka suka yi zaman shiru mintina 10 .

Shikuwa ya dake ya sake hannun sa a aljhu yana tsaye yana bin ta da ido babu alaman komai a face dinsa kamar dutse durus baiya murmushi

Sai da taga ji ta shige bathrum din ta kimtsa kafin ta fito har yayi waje
Sai ta tattara slum book dinta da hijabin ta snn ta sauko kasa.

Bakowa nan sai masu aiki bata damu ba Tana isowa tsakar palour suka sake hade ido dashi cikin sauri ta dauke kanta sai ta ja ta tsaya..

This time tsakinsa ne ya bayyana sosai sai ya daure dai daf da ita ya matso yace im up here in kin gama ki same ni
Nan ya wuce ya barta

Cikin quiet room din gidan ya wuce tuni ya riga ya soma kulewa da haushi dafe kansa yayi cikin bambami yace shegen rashin tarbiya kawai, i just cant blive i have to deal with this silly girl Yayi karamin tsaki.

Cikin wannan yanayin ta bude kofar ahankli snn ta shiga batace uffan ba ta kime a tsaye tare da daure masa fuska.

Yayi shiru Bai dago ya kalle ta ba gashi gaba daya shaking take yi tunda aka fara rubibin shirin hidiman nan saiyaune ta fito sarari.

Baiko kalleta ba yace

"ke,Meke damun ki?...ya fada sounding normal..
As usual ransa a harde..

Shuru tayi masa saima sadda kanta kasa data dada yi.

Sosai zazzabin ke damun ta yanzu kam bata san ko ganinsa nema ya kara mata ba all she knows is bata jin dadi sosai yanzu..

Har ya taso ya iso gaban ta bata sani ba rai abace yace,"meke damun ki are u deaf .ya dan daga mata murya ko ajikin sa aganinsa ko zai ta kuka ne kamr yadda yasaka farida..

So take ta boye Razanan datayi amma ina tana hade ido da shi tayii luuiiiii zata fada kasa sumammiya da sauri ya taro ta ya fada jikin sa tare da kankamesa.

Arikice Ya rikota ta sace jikinta gaba daya ajikin sa dan kuwa Ta gama jigata koda ta fadon ma she was weak bata ma iya motsa ko ina acikin ta ba haka ma idanun ta suke lumshewa da kansu.

Yace..."ya salam...ke!!!
Emmmmm yay kmr ya mance da sunan ta, amma zahiri baison ma ya kirane dan karta fara rainasa..ita kam sai nishi take kan kace kobo ta dena motsi gaba daya..

"Ohh Shirt ...yaja adan fusace ya tallafo ta a hannun sa suka sauko kasa a maimakon ya kaita sama daga nan saiya kamo hanya zai komar da ita dakin da ta fito, but unfutonatly for him hjy maimuntu ne da adda nafisa falo suna zaune..

Ganin su haka ya sa suka mike,hjiya tace innilallih Ahmed tsaya tsaya ina zaka kaita meya same ta haka?

Ba yabo ba fallasa Yace 'haba mummy inaga fa suma kawai tayi zan ajiye ta ne a dakinta sai nasan nayi...
Chapter 69 · 0% Book details