← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 157

Sashe 13

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hjy khadijatu tace Hmm toh Allah dai yasaka, dan banajin Ahmed zaiyi ra'ayin auren mata biyu arayuwarsa da dayan ma dayaya aka kare dashi.

Ahaka suka dinga hira har karfe bakwai ma safiya yay. Shawarwari masu kyau game da yadda zata handling din matsalar zamn aurenta ta kara nanata mata, bayan nan ta shiga wanka da niyyar wucewa turkey dan jirgin karfe 10 daidai na safe aka mata booking private plane ne na haya so she donst need to rush herself..

Ata fannin Adiaha kuwa sanyin A.Cn falon ne ya bugata ta dinga bacci awajen har safiya yay bata sani ba..

Bata tashi farkawa ba sai wajajen karfe bakwai saura, a firgit ta bude ido jin muryan sister zainab akanta wanda hakan yasata ta dingajin kamar ta saki ihun takaici

Suna hade ido tace gud morning sister zainab

Sister zainab dake dauke da jakarta na kaya da alaman shigowarta kenan tamata wani irin kallon tara saura snn tace haaaaa, reema or whaeva ur name is,so u mean u left ur husband alone in the room and slept here alone?

Adan rude Adiaha tace no sister, ba haka bane

Comn dont lie to me jare
Ta tsareta da tsawa

Adiaha batace komi ba tay shiru kanta na kallon kasa dan batasan ma wai anan ta kwana ba itakanta mamaki takesha

Tsaki sister zainab taja tace banga laifinka ba.
Dama me kuwa zamuyi tsammani awajenki,as long as akwai jinin igbo ajikinki dats d moment i knew dat baki dace da damilare ba..

How are we even sure u did not go to ur fathers shrine in calabar befor coming onto our family
Ni bantaba ganin irin worst combinatiion din yare irin naki ba..ur father is calabar and ur grand mother is igbo? Haaaa 2 evil and wicked kingdoms. Asanadiyarki ne kafayat ta haukace taje ta aure baban mu and yet kin bat dami acikin damuwa kinzo kina ta bacci anan ohhh reema ure a heartless girl

Baki cancanci akiraki da matar aure ba,cos a good wife shud alwys stay by her husband side
Saboda tana kwantar masa da hankli ba irinki ba.

Adiaha datakeji kamr zata fashe mata da kuka ta dago tana kallonta muryanta harna rawa rawa tace sister zainab
I tried my best, wllh bansan nayi barci anan ba i swear to u jiranshi nakeyi, yafita da abokansa har karfe 1 na dare ina nan bai dawo ba maybe dats why i slept offf..

Tsaki sister zainab taja tace kanki akeji..idan ma kince haka then what happen yestade..naji ance baki zauna tare da shi a asibiti ba. Kina nan kin boye kanki agidan anty adizat bcos u too u know ure a bad luck na

Hawayen daya sauko mata tay saurin sharewa
Jin sautin taku ata bayansu wanda shine ya katse su.

Gyaran Muryan hajy khdijatu sukaji akansu dukansu suka dago kai suna kallonta sanye da hijabinta da alaman ta fito hadawa yar uwanta shayine dan kar ta wuce turkeyn batasaka komi acikinta ba.

Tun bata karaso ba sister zainab tayi saurin tsugunawa har kasa cikin ladabi da biyayya sosai tace mumy good morning fatan kin tashi lpya? Tay murmushi tace morning zainb alhamdullh am fine please get up Ina kuma jikana shafiu ya naganki ke kadai?.

Tace yana can cikin mota da babanshi Nazo droping kayana ne

Nan ne Adiaha itama tace gud morning mumy

Ba yabo ba fallasa Hjya khadijatu tace gud morning dear how are u

Da sanyin murya sosai Tace am fine maaa how is ur..cikin katseta Sister
Zainab tace ah ahhhhh ya isa mana, Kije kiyi alwala kiyi salla ko kin dauka addinin musulunchi addinin wasa ne?..mumy see dis girl oooo.

Da mamaki hjy khadijatu tace Au, Reema wai bakiy sallahn safiya ba kinsan lokci ya tafi kuwa? Aiko yakamata kije kiyi yanzun nan

Adiaha taji kmr ta nitse a kasa awajen dan bataso da akace batay sallahn safiya agaban surkuwanta ba, tsoro ta dingaji kar sister zainb ta fadawa kowa cewa anan falo ta kwana, jikinta na rawa ta bar wajen acikin sauri batare da tace musu komi ba

Karasowa sister zainab tay kusa da hjy khadijatu cikin nuna mata kulawa sosai snn tace Mumy i hope ure fine, please be fine oo,ure all we have.. kece kadai a duniya mai share mana hawaye, adalilinki na girma batare da naji kewar mahaifya arayuwata ba, how can i stand to see u in sadness? shiyasa ma im going to stay with u for a week, bazan barki kina tunanin komi anan ke kadai ba...both of them dont deserve to be rmbd i will make sure i make u happy.

Ahankl hajya kahdijatu ta rungumeta sosai snn ta dago tana kallonta fuskanta dauke da murmushi tace nagode zainab..but i am fine.
Keda kike da miji da yaronki meyasa zaki barsu kizo kizauna dani anan nifa bana son naga matsalana yana shafar rayuwarku kamar yadda kukejin inada muhimci arayuwaku haka nima nakejin cewa rayuwarku tafi min komi daraja so Bazan so ace wani abu ya sameki a sanadiyata ba.

Zainab tace mum just leave that talk sati dayane kawai zanyi..mijina ma is in suppourt ko bakison shafiu yana damunki ne

Murmushi tay tace toh shikenan for shafiu's sake..kije ki aje kayanki
A daki one week and ure off

sister zainab tana washe baki sosai Tace toh mummy naji bari naje na dawo na miki delicious breakfast..duk abunda kike so nine zanmiki

Murmushi tay Batace mata komi ba har zata wuce sai ta kara kiranta ta dawo baya.

Tace Mumy what is the problem

Hjy khadjitu tace zainab
Ko zakije ne kifara duba su Ahmed, inaganin kamar matarsan nan tana bukatar kulawarmu sosai..why dont u go der and check if she is praying corectly kinga kar abarta hakanan Addinin bazaizo ya shige jikinta sosai ba.

Sister zainab tace okay badamuwa bari na aje kayan sai naje

Ahaka suka rabu..

Daga fannin Adiaha kuwa tana isa sashen nasu ta samu ko ina abude da alaman Akwai mutum aciki..

Bedrom din da aka kaita tafara wucewa taga babu kowa aciki, sai ta wuce dayan dakin tana budewa kuwa ta kalli Ahmed yana zaune abakin gadonsa harya kammala shirinsa tsaf yay fitinannen kyau acikin grey suit nashi zaije aiki.
[6/6, 6:55 PM] SURAYYAHMS: Da mamaki Adiaha ta tsaya kallonshi ganin kan gadonsan abarbaje da alaman anan din yay baccinshi shikadai,shiru tay ranta nabaci ganin baiko kulata ba,jimm tay da tunanin menene tay arayuwanta daya saka Ahmed yake treating dinta haka. Taga itama fa mutum ce,tana da zuciyar yin fushi snn tana fahimtar komai dake faruwa..ahankli ta lumshe idanuwanta Maganan yar uwarta Ekaete ne ya fara bijiro mata a mind dinta aranta tafara cewa Is it really her fault da bata dauke kanta da daraja ba?

Aurensu yau yake cika sati daya da kwana biyu amma tsakaninta da Ahmed inbanda matsala da rigingimun family Nayau da gobe babu abunda yake wakana a tsakaninsu.

Lumshe ido tay sosai da tunanin yadda zata fara amshar yancinta na aure awajenshi ko ba komi he need to start respecting her ya dena gaya mata maganan banza a duk yadda yaga dama.

tafara ayyana hkan aranta kenan Sai kuma maganan sister zainab ya fara toshe mata kwakwalwanta,tafara tuna cewa yanzun nan fa ta gama mata ihu akai tanamaicewa bata cancanci akirata matar aure ba laifinta ne data kasance bata kulawa da Ahmed a wnn lkcin.

Maybe is true she is not truly being understanding with him,Tasan yanayin da Ahmed yake ciki aynzu bamai sauki bane agareshi, tunda dai ance yarinyar nan kafayat daddadiyar budurwarsa ce toh hala dolene ya dingajin kishi,da zafin abun aransa fiyeda kowa, saidai nata bukatun dake wajenshi fa,shin zata danne nata damuwar ne domin ta bawa damuwar Ahmed kulawa dan ta zamo cikakkiyar gudwife agaresa da idon famlynsa?

..a tunanin ta in ba hakan tay bama hala bazata samu sassauci daga wajen yan uwansan nan ba musmmn ma sister zainab. Tana jin wani iri aranta daya kasance babu mutum daya acikin matan gidan data nuna mata tana sonta, all of them are just behaving formal with her bamai kkrin janta ajiki tana nan dai haryau kamr wata bare acikinsu.

Tasan duk suna jin haushinta ne sabida abinda yake faruwa dasu, suna ganin kmr itace silar da ta jawo musu wann bala'in na auren kafayat da mahaifinsu, and in oda to win them back dolene ta saukar dakanta kasa tare da nuna musu cewa zata iya kulawa sosai da Damilare.

Gyaran murya tay snn ya dago kai suka hade ido ya mata kallo daya snn ya kauda kansa, cikin sanyin murya sosai tace "Gud morning hubby.

Babu yabo babu fallasa yace "gud morning".

Tace ashe harka dawo jiya shine nata jiranka acan falo harnayi bacci bangan ka ba.

Batare da kulawa ba Yace yea, Bacci nakeji shiyasa. Shiru tayi kafin nan tace ai na dauka u will look for me inka dawo acan fa na kwana a falo ina jiranka. U shud have waken me up koda baka son mu kwanta tare.

Batare da kulawa sosai ba Yace dacan nine nakaiki wajen ne da zanje can na tasheki?

Tace a'a, but..

Cikin katseta yanamai duban agogonsa yace
Let it be inadai kingama yin baccin kuma kin tashe kanki? I am going to work, inada meeting dazanyi attending yanzu saina dawo.

Dacan har Zai wuce sai tadan tasha gabansa zatai masa maganan dake damunta acikin ranta game da irin zamansun.

Kafin nan ta bude baki saiga sallaman sister zainab a shashen wanda atake ya janye hanklinshi akanta.

Ficewa kawai yay ya barta wajen ya same yar uwansan a falo suka fara magana da yarensu.

Banda sunan ta da na kafayat babu abunda take ganewa aciki.

Agefe ta tsaya tanata kallonsu dan sosai maganan yay kama da wanda ake zance akansu musammn ma ita datakejin sunanta acikin zancen sosai

Duk ta rasa menene sister zainab take gayawa Ahmed akanta da yasa fuskarsa ya sauya atake .
Chapter 13 · 0% Book details