← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 157

Sashe 122

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tuna jiya da ace itace tay masa borin nan ta kuma cijeshi ko ta kwada masa wani abu akai kmr yadda yasrah tayi da halama gawanta kawai za'a fitar tsabar yadda baya sake mata fuska idan tay masa laifi.

Hakanan sukaje har kofar gidansu fahad Adiaha nata kallon mansion din ganin lallai iyayen fahad suna da kudi sosai,tay tunanin yasrah zata bishi sai taga bata motsa awaje n ba, suna wajen ya shiga ciki ya fito Ya bata keys na wani quest house din baban shi mai kyau acikin gwarimpa 4 bedroom flat ne mai kyau wanda is fully furnished babu abunda babu aciki.

Anan suka yada zango ita da Adiaha. Yasrah ta jona wayar da maryam ta bata a cagi.

Su ukun duka suka dan taya Adiahan hira dan ta sake jikinta kodan tay murmushi.

They forced her to gist them, haka sukata sakata magana, harsaida suka saka ta dan sake jikin nata sosai snn yasrah ta rakosu waje tana mai gode musu da taimakon da suka mata.

Tace zuwa gobe haka zasu koma gida she just want to give her aunty a breathing space, kowa dai ya nuna ta fahimce ta.

Adiaha na kwance cikin kamshi turare ga A.C mai ratsa kwakwala, ga abinci kala kala amma duk wann basune agabanta ba.

Babban damuwarta shine Ahmed and Ahmed Alone dan yadda kasan tay kwana hamsin bata gansa ba haka takeji aranta.

Tafi awa guda tana kwance cikin tunani musmmn ma da bataga yasrah ta dawo ba.

Yasrahn na can ta bisu a motan fahad suka kaita taje har cikin bank tayi withdrawing kudi a counter snn ta maida ma maryam 30k dinta duk dama taki karba.

Snn sukayi drpping nata agida, daga nan mall taje ta siya abaya nata da na Adiaha da dan abunda zasu bukata nayau.

Ta riga tay warning dinsu akan karsu sake su fadawa kowa cewa sunsan inda suke.

Hakan kuwa akayi da yamma fahad ya tafi niger state dan karma ayi suspecting dinshi.

Maryam sun tafi kaduna

Ahmed yay neman duniyan nan masu yasrah acikin garin Abuja ammai bai samesu ako ina ba tun baison hanklin sa ya tashi har saida yaji baiya ma iya zama.

Wasa da wasa saida hanklin kowa ya tashi agidan jimada at same time ana cikin tashin hanklin kafayat ma ta fito da kalar nata makircin tafara cewa Adiaha tasan metake kullawa da take yawan zubar da cikin Ahmed ita da nurse din can halama mayu ne dukansu tunda ance garinsu daya.

Haka Da yamma kowa ya firfito tsakar gidan ana tattaunawa kowa da kalar ba'asin dayake bayarwa akan Adiaha.

Anty ramotou ce tay tattaki tun daga gidansu tazo itama tanayi tanakai rahoto awaya ma aunty mojushola.

Take matayen gidan suka juya maganan sukace Adiaha ta yi kidnapping din yasrah ne sabida ta dau fansa..

Abu dan kadan suka maida shi babba, ga kafayat ta nace wajen kkrin cusawa alhaj bello jin cewa tsafi da maita Adiaha takeyi da jinin jikokinsa.

Anan kuma su anty nurat sukace ai she kidnapped yasrah ne for ransome money, tagama lashe yayan AHMED acikinta ta dauke sistersa kuma ta boyeta dan abiyata kudi.

Haka suka maida maganan ya zamo tamkar wani gaskiya sunatayi dan kowa da kalar tsanan da yay ma Adiaha.

Alhaj bello duk ya rude abu kadan sai ya nemi layin su hajiya kahdijatu dana hjy maimunatu saidai dukansu biyun basa shiga.

Bincike akeyi Ahmed yaki ya zauna waje guda yayansa ma nakan tayashi nemansu, basuda wani clue, yaje schl nace yasrah bata zo ba, fahad da maryam duk ance masa sunyi tafiya.

Dama Already Biodun ya gaya masa cewa shine ya kirawo musu uber nan ma akayi asarar kudi wajen tracking din uber din tun wajajen 12 na rana har saida yamma yay sosai kafin aka ci nasarar samo shi ta tracker.

Nan aka tattaroshi lokcin ana neman karfe 8 na dare. Iya abunda yasani ya fada musu yakaisu har bakin asibitin.

Koda Ahmed ya bincika ya gano eh lallai anan jiyan suka kwana yadan ji hanklinsa ya kwanta..

Tambayar duniyar nan yay ma nurse ko tasan inda suka dosa amma bai samu kwararren amsa ba sakamakon lokacin da sukabar asibitin basuyi ma kowa sallama ba kuma a motar mai tinted suka fita.

Ata fannin su Adiaha kuwa dawowar yasra ne kawai yasaka ta katse tunanin Ahmed din datake cusawa a zuciyarta duk dama yasrah ta lura da cewa har yanzu hanklinta bai wani kwanta ba gidan kawai take tunani.

Kowani lokaci taganta zaune saidai taga ta lumshe ido hawaye.

Inta fara mata magana akan tadena cusa damuwa aranta sai ta boye mata tace ai akan babynta data rasa take shiga damuwa ba akan Ahmed ba while the answers are writting in her eyes itadai mijinta kawai take so.

Abun nata damun yasra aranta can da wayar ya kammala cargi tafara neman layukan iyayen nasu bata samesu ba itama.

Haka sukayi zaman su biyun anan wani lokci atare wani bin kowa shikadai cikin tunani..

Time to time haka yasrah takan jata cikin magana sabida mamakinta take sha haryau ganin yadda ta cusa Ahmed aranta haka nan kawai.

Sumtimes she wll tell her some stupid reason takance ai zama dashi yafi mata zama agaban iyayenta datana living sinful life wanda babu kwaɓa aciki gara tay zama agidan mijinta.

Tace ma yasrah son Ahmed datakeyi aranta itama kawai Tsintarsa tay arana tsaka acikin zuciyrta..she feel he is her true love and her messiah, her life changer.. tafara gaya mata Abubuwan da ya mata na alheri arayuwa kamr sutura, ci da sha, ya bata mota ya bata kudi ya bata sana'a,. tana jin dadin fadin alherinsa amma inta kama na sharri ne sai tsamesu ta zubar ko tana boyewa wasu kuma tana lullubewa da uzuririka marasa kama hankli.

Itadai tanason shi..cos she thinks he is perfect bazata taba samun wani kamarsa ba, kuma aganinta duk abunda ke faruwa tsakaninsu laifinta ne yafi yawa aciki.

Tace ma yasrah kawai dai Ahmed bai iya fushi bane wani lokacin, amma
Ai duk abunda yay mata jiyan ma bason ranshi ba ne,He is a gentle man, He doesnt even meant it kawai dai tana kuka ne dan batason tanaganin bacin ransa.

Yasrah bata san yaushe tafara sauke mata hawayen takaici ba.

Tabi tarasa me zatace mata...gaskiya Adiaha tay nisa batajin kira.

For u to deny the truth in front of you and beautify ur worst realities ai tamkar ciwon tabun hankline dayake needing serious attention daga wajen likitocin mahaukata.

Saiyau yasra ta fahimce how easy is it for adiaha ta zaɓe Ahmed sama da Addininta da iyayenta da kuma zuriar'arta.

Tunda ta fahimceta ahakan sai tay shiru tafasa bata shawarar kai kararsa gaban iyayen sa datake da niyya kawai Kasa ce mata komi tayi ta zuba mata ido tanajinta tanata yabashi.

Sai Can da sukay wanka suka sauya kaya cikin samun wata nitsuwa suka ci abinci snn suka dawo suna dan Hira.

Adiaha was asking her about fahad tace mata bbu abunda ke tsaninsu they are just friends.

Hirar da ya jawo yasrah ta fara wayar mata dakanta kadan kadan kenan.

Tasan Adiaha ta girmeta a shekaru by far but as a sister in islam tana jin kanta free da ita so she feels she can tell her the truth acikin hikima.

Adiaha na tunanin inhar namiji ya fara crushing akanki kuma kagansa kyakkwa mai kudi just love him back wirh all u have sabida bazaka samu wani kamarsa ba

Yasrah tace mata ba ta haka abun yake ba..

Bakowani namiji bane yake derseving aso shi alkcin dayake so.

Snn tace mata ai Mace ansan ta da jan aji ne bada sake ajinta kowa yana daukarta easy and cheap ba. She gave her good examples of yadda ake neman soyayya acikin mutunci Yadda koma ace Mace ce taga wani namiji take so ba shawara mai kyaun bane taje tafara aproaching dinsa anyhow.

Tasha mamakin yadda yasrah take gaya mata cewa akowani hali taja ajinta kawai,namiji ba shine yake determining destiny ko fate dinka ba, idan ma yace yana son ka time to time yakama ta kana nuna ma namiji kaidin ma mai tsada ce snn zaka iya tsayawa da kafafunka ko babu shi.

Maganan har yadan fara shiga ran Adiaha sabida babbn burinta ne taga Ahmed yana daraja ta kamr yadda yasrah take fada acikin hira.

But later later bayan sunje bacci sai kuma tafara tunanin ai yasrah karamar yarinyace mai tasani akan maza da har zata faffadi hakan?
Juyi take da tunanin mijinta she tot maybe is just her own childish sentiment ai namiji yafi son submissive woman irinta bamai jan aji ba.

Dakyar akayi bacci yau agidan jimada Ahmed kam baiko iya runtsawa ba.

Asubahin fari layin su hjiya ya fara shiga, kirar alhaj bello ne ya soma tadasu abacci nan ya gaya ma matarsa hjy khdija cewa Adiaha ta tafi da yasrah wani waje anakan nemansu ba agansu ba.

Hanklinsu ya tashi sosai sabida yadda aka jujjuya maganan ya dawo kamr na kidnapping, tace masa ai suma sunxo abujan jiya cikin dare zasu shirya su taho.

Nan suka kira Ahmed bai daga ba..

Layin yasrah shima a kunne yake amma ba adagawa hakama layin adiaha dake duk wayoyinsu na gida.

Hjy maryam ce tace akira mata fahad da maryam duk dama an gaya musu
Cewa ai basa gari da abun ya faru.

Layin maryam bai shiga ba saina fahad ya shiga

Suka gaisa lafiya lafiya bai boye musu ba yagaya musu inda yasrah suke haka suka dinga masa godiya jin shine ma ya taimaka musu and they are safe.

Bayan sun kammala wayar Lambar da za'a same tan ya tura ma hjy khadija ta tex kai tsaye ta kirata lokcin tana sallah

Bayan ta idar ta dau wayar tana mamakin yadda akayi tafara maido mata kira sabida duk kiran data musu bai shiga ba kuma tasan bazasu bibiya unknwn caller ba.

Tana daukawa tay sallama hjiya kahdijatu ta sauke ajiyan zuciya tana cewa hajy maimuna Alhamdullhi na sameta Adda.

A handsfree suka saka call din ko gaisawa basuyi suka fara tuhumar ta meyasa tabi Adiaha suka bar gida.
Chapter 122 · 0% Book details