← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 157

Sashe 90

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya yayi ya bar ta nan tsaye ta bisa da kallo snn ta ci gaba da tafiyarta ita ma, maimakon yaji haushinta ya cikashi sai yaji for the first ta burge sa sosai, he kinda love stubborn girls amma ba masu girman kai ba, Upon all, ya lura kmr she is kind at heart bata wani daukar dumi.

Harsanda ya shuga motarsa snn ya juyo ya sace kallonta yaga tana kan tafiya saura kiris ta karasa Dept dinsu tana dan sauri ganin few minutes ne kawai ya rage a fara musu lectures nayau.

Bayan an tashesu around 12am, card din ta ciro ta kira lambar jiki jim kadan driver dinsu na gidan ne yazo ya dauketa taje gidan ta samu sashensu duk a kulle Adiaha ta wucce shagonta gashi bata bar key dinta ma kowa ba. hakanan tay ta zaman jiransu awaje gashi nan batason ta kira layin Ahmed karshe alhaji bello ne daya fito sallahn zuhr yaganta tana zaune cikin takaici shine haryayi inviting dinta cikin main house ta zauna a babban falonsu tare dashi suka sha hira.

She enjoyed her stay with him duk da bombastic side eye din da kafayat ta fito tana bata. Ko ba a gaya mata ba ta lura da cewa kafayat din nan bata kaunarta kona minti daya. She cant even stand her, ko gaisuwarta bata amsa ba sai harara, snn Wucewarta goma sai ta tsaya ta masa wata magana in a harsh tone da yarensu.

Wani abin ma basarwa kawai yake yay ta yake amma sosai yasrah ta fahmce cewa kafayat bata ragar masa ko kadan gata da rashin kunya.

Bayan kwana biyu yau yasrah take kaiwa 3wks a Abuja tare da Ahmed da matarsa har ta fara sabawa da gidan jimada da kadan kadan, saidai rayuwar ta kasance mata ahakan wani iri tsakanin ta da matarsan babu wani dadin zama dake tana yawan bata silent treatment na baqin hali agidan kuma ita bata jin sha'awar ta gayawa Ahmed cewa Adiahan bata barin mata keys duk ranar da bata da lectures din yamma ba abun ya taru ya fara mata yawa dan shkansa driver din da aakace yana dauko ta idan an tashi yana bata wahala dan baisaba jigila irin wnn ba,sumtimes sai ya manta da ita, ko ta kirashi yay ta ringing baya dauka saidai tabi kawarta maryam kota sabule taje tabi motar kasuwa batare da fahad ya lura ba cos akowani rana binta yake yana neman duk wata hanyar da zasu kulla amintaka na kut da kut duk yadda take basar dashi baya jinta kamr wanda ake masa asiri akanta.

A fannin Adiaha kuwa har yau iya dai tsakanin su gaisuwa ce ta fatar baki.

A Wknds haka suke yawan haduwa da sauran mutanen gidan irinsu anty adizat da nurat da yaransu ayi hira tana jin yadda suke cakke cakken junansu da baqaqan magana acikin raha Ahaka ta fara sanin tarihin adiaha dan sosai su anty nurat suke tona mata asiri wani bin harsai taji kunyar idon yasrahn.

Ita kuwa sam taki sake musu dan duk basa gane kanta sabida sam ita batada surutu da kuma son shiga jikin mutane masu azaban gulma.

Adiahar ce dai kullum take cikin saka mata ido akan yadda Ahmed ke kulawa da ita abun har na damunta ganin yadda ta cusa mijinta aranta kuma take jin tsoronshi kamr wani Allahnta,duk ta tsani ta gansu tare, gashi ita kuma bata taba nuna mata tasan tanayi ba.

Yasra Bata tabuka musu aikin komi a gidan sabida weird bhvrs din Adiaha Daga taje lectures ta dawo shikenan sai taci abinci, Saidan indan ikon Ahmed din yafara mata yawa ne sai kaga ta kulle kanta a daki harsai washe gari snn zata fito, by now sosai tay suna da farin jini sosai a schl dinsun dan tsabar yadda kowa yake admiring din all these signature dressing dinta datakeyin shi with full concentration duk dama bata fiye saka atamfa ba.

Koyaushe zaka ganta da full accesories daya dace da kayanta, kmr agogo abun wuya,chains and bracelets, kayanta kuwa basa wuce Matured Abayas,kimonos,turkish sleeves,gowns kala kala highwaists,gata tana son rolling colourful veils da saka dogayen shoes ko booth masu daukar ido da kyau.

Week nagaba da zasu shiga Adiaha da Ahmed suka fara shirin zuwa awun ciki cos cikin ya fara shiga kwanakinsa na cika 3 months gashi suna son sufarayin Awun da wuri sabida tana da complication na hawan jini data fara samu a farko.

She was so happy dan tasan dolene aranakun awun suna kai yasra schl tare kafin su wuce asibiti.

Ranar da suka fara haka tayi ta masa kisisina tana masa hirar cikin a cikin amotan dan yasrah tanajinsu sai babbasar da ita yake yana sha mata qamshi amma bata fasa ba, gashi sai taga yasrahn batace musu uffan, ko da ihu zatay magana sai taga bata ko dago kai bare kuma kulawa, ko taga tana kallon window kotana danna wayarta wata rana har assigment zakaga tanayi acikin motar kafin su isa. Kullum haushin da kishin karuwa yake aranta dan ko kadan ta tsani yadda Ahmed yake treating in yasrah like a queen musmmn agabanta.

Kudi banata ba amma She is almst chocked up daya kasance duk sanda suka aje yasrah a schl sai ya barta a cikin motar yabita abaya sunje can gefe ya bata kudi duk da tasan bawai rasawa tayi ba...

Abun na damunta aranta duk sai tarasa tomesa ita baya mata abunta privately cikin tarairaya da darajawa, ta tuna itafa har agaban yasrahn ma yana iya bata kudi snn ya gaya mata mezatay dashi amma ko sau daya bai taba bawa yasra kudi agabanta ba bare ya mata fada ko wani tsawa kwana biyun har mmki yake bata cos bata san yana da soft side ba sai da yarinyar nan tazo.

Haka intaki cin abinci ko ta kulle kofa taki fitowa toh ranar Ahmed zaita bori harsai ta sauko, infact sosai ta lura da cewa izuwa yanzu baya jin qwiyuwa ko nauyin ya deba abincin dakansa ya kai mata har daki snn in taki ci yace zai bata abaki na dole. Yanzu Har ta saba da kowani dare haka yake share mood dinta musmmn idan zaije ya duba yasrahn sann ko wani safiya ma inya farka itadin yake fara dubawa kafin ya wuce masallaci ko in ya yadawo.

Komi na yarinyar na cusa mata damuwa da kishi cos her husband Ahmed is gradually bcoming a dfrent man agaban yarinyar, tana son taga ta shige rayuwarta da makirci ta rabasu amma Abu biyu ne suke karya mata zuciya musmmn yadda yasrahn take yawan girmamata, kullum saidai basu hadu ba itace zata fara budan baki ta gaisheta snn bata taba yin fushi ko ta rainata ba.

Na biyu kuma tanajan baya baya ne sabida yadda kowani wkdsn su anty adizat suke kunce mata zaninta a kasuwa

Duk sanda akazo main house duka during wknds toh sai sun tabbatar da sun kunyatar da Adiaha agaban yasrah asigar wasa da habaici.

They wll joke and joke about yadda Adiaha tazo gidan miji bata da komi infact komi da Ahmed ya mata a zaman auransu saida suka gayawa yasrahn stylishly acikin raha snn agaban Adiahan suke abunsu dan su cusa mata baqinciki.

Yasrahn kuwa bata wani iya nuna damuwarta akan zancen gulmansun duk dama tarihin Adiaha ya bata mamaki kwarai dagaske.

She find it very hard to believe a farko,koda ta tabbatar da labarin batace uffan ba, ita dai bata kushe qaddarar Adiahan ba, cos she knw is very foolish mace tanayin fahariya ko tana boasting akan cewa abu kaza bazai sameta ba ko ita bazata taba fadawa tarkon soyayyr wani namiji tay kaza ba, saidai labarin Adiaha yasaka tun ranar ta fara saka hakan acikin Adduarta cewa kada Allah ya saka mata son wani da namiji wanda har zata bar iyayenta da kabilarta da addininta akansa na har abada. Duk dama rayuwarsu is none of her business but story na Adiaha yaso ya mugun jan hanklinta, bata son ma kula tasharsu agidan amma sanin tarihin Adiaha abakin su anty nurat yasaka tay saurin gane cewa Adiahar ce take son Ahmed fiye da yadda shi yake sonta..

Ata daya fannin Wayann dalilain biyun sune suka mugun taka ma Adiaha burki wajen zagewa ta yaki Ahmed akan special treatment din dayake bawa yasrah agabanta.

Tun zuwanta gidan ta fara fahimtar cewa Halin Ahmed is not the same for evrywomen dat means bakowace mace bace yake iya cin musu fuska ko yana walakanta su ba.

Saidai a memakon ta nemi dalilin dayasaka bata cikin jerin wayann matayen ita neman shigewa take tsakaninsa da yar uwansa wanda tuni ya riga ya gano matsalarta shiyasa yake gaslihting dinta sosai.

Idan yay abun da yasan bai mata dadi aranta ba ko idan ya lura tanajin kishin wani abu toh bazai bari ba, saidai ya basar yay kamr baisani ba, ko karshe ya nuna mata kamr itace da laifi.

Satinsu guda da fara zuwa anternatal kafayat ta bace agidan batare da kowa yasan inata dosa ba, Ya rage alhaj bello ne kawai agidan duk sanda driver yazo daukar yasra akan lokaci inta dawo gidan babu kowa saitazo cikin mai mansion din ta tayashi hira,shikadai ne yasan cewa Adiaha bata barin mata keys din gida aransa yana ta son ya gaya na Ahmed amma baya samun dama, haka har suci abincin rana atare da ita wani bin suyi kallo ko suje waje suzauna susha iska a kujera, she doesnt even knw how it feels to have a father, ta taso ne batare da ta samu kulawar mahaifinta ko mahaifyarta ba,they both died when she was very young, shiyasa takejin mugun dadin kasancewa tare dashi.

He is quiet calm and comfortable a satin sabida kudin da matarsa khadijatu ta tura masa ta hannun dan aika daya boye a dakinsa yake dan zara yana kashewa.

Yasrah inta dawo haka wani bin zai aiki biodun yasiyo mata ice creams ko wani small chop zuwa yamma kafin Adiaha ta dawo gidan,duk izgilin Adiaha bata taba tsammnin aranta cewa father inlw dinta zai dawo da abin wani abun magana ba.
Chapter 90 · 0% Book details