Sashe 99
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin haka yasa naja bakina nayi gum har muka koma gida Daki da na sauke su suka shige bamu kara jin su ba sai washegari,Tare suka tafi ya Sauke su gidan Adda ya wuce Office Daganan kwana hudu suka yi suka wuce Lere harda Adda Sadiyan da taje saboda Gorin Iya na bata zuwa sai an yi wani abu,Kwanan su biyu a lere Mujaheed yazo ya Dauke su suka tafi Abuja Daganan suka kwana Daya suka Dawo Abunsu su kuma su Laala Ummi da kanta ta kaisu har Sulaja wajen Dangin ubansu zasu karishe Hutun su achan.
*****
Majeeda da taje Lere hutu cikin zence take fadama inna Talatu zencen Rashin Lafiyar Muhibba ita kuma taje har Dakin iya tana Fadin"Iya ashe matar Saifu Ciwo ta yi ta yi kamar dai Aljanu yadda Majeeda take fadamin har Zaliha ma taje ta ganota"
Iya na kishigide ne sai da ta mike zaune tana Fadin"Ke talatu yaushe duk akayi haka bani da Labari..?
Talatu ta kwalama Majeeda kira tazo ta tirketa gaban Iya tana Fadin"Ba ke kika Fadamin matar Saifu tayi rashin Lafiya kamar aljanu ba har ta ma koma gida kwanaki ba?
Majeeda ta daga kanta kafin tace"Eh ammh ai ta warke ai gidan hamman muka fara zuwa chan muka yi sati daya duk wannan siyayyar da nazo da shi su suka yi mana."
Iya ta jinjina kai ranta ya baci Talatu ta kallah kafin tace"Hashimu na gidan nan ne ko ya fita..?
Talatu tace"Ya fita.."
Iya tace"In ya shigo kice ina neman sa"
Talatu tace"Iya ba dai ri.."
Hannu Iya ta Dagamata Lokaci daya tana Fadin"Ki je kawai"
Dole ta fice domin Majeeda ta Dade ta fita abunta tasan Halin iya tsoronta Allah kada iya ta tada rigima ace majeeda tazo tayi gulma ai hakan ba dadi.
Aiko sai dai kada a kara,Domin Hashimu na shigowa iya ta Sakemin mganaar tana yi tana mita tana Fadin"Har ace Matar Saifu tayi ciwo bamu sani ba Hashimu..?
Kai tsaye yace"To daman mana Iya..Ai na fada miki zaliha bazata bar Saifudeen tare damu ba ballatana ta samu ya auro bangaranta sai abunda muka gani"
Iya ta muskuta tana Fadin"Shiyasa yama rage zuwa rabon sa da nan tun rasuwar Habi"
Nan dai ya cigaba da zugata ya na bata Ummi har Goggo Atika ta shigo taji mganar itama ta zauna ta kara Hura wuta har tana fadin"Iya shiyasa naso ya auri yar"uwansa Dole dai zai zo saboda ita ammh kika bari ya auri dangin Zaliha to ai ga abunda ya faru nan"
Baffa Hayatu ne da yazo yaji zencen ya fadi abu mai kyau cewa yayi"Kada mu yanke hukunci cikin Fushi bamu ji ta bakin su ba Iya"
Iya ta aminta dashi tace ya Lalubomata Zaliha tana wajen aiki taga kiran Hayatu Lere tasan iya ke son mgana da ita sai ta kashe sannan ta kira bayan sun gaisa da Hayatu ya mikama Iya suna mgana gaisawa Iya tace"Zaliha kin kyauta kenan..?
Ummi tace"me nayi kuma Iya..?
Iya tace"Ace matar Saifu tayi ciwo har da komawa gida ammah ban sani ba..?
Ko domin har yanzu baki Daukemu da Daraja da mutumci ba ne Zaliha..?
Ummi tayi salati acikin ranta Daman sai da tayi Tunanin haka bata zargi Majeeda da gulma ba kila mganace ta kawo mgana.
Cikin kwantar da Murya Ummi tace"Kiyi hakuri Iya wlh ba laifina bane..Naso na kiraku na fada muku Yaya sunusi ya hanani yace zan tayar muku da hankali kinsan Allah iya ko Gidan baffaninta na Gaya wlh tallahi ba wanda yaji iya kin ji ma na Rantse ammh kiyi hakuri don Allah mun yi kuskure."
Iya sai taji jikinta yayi sanyi cikin Sanyin murya tace"Naji ammh dai baku kyauta ba..Zaliha ban ji dadi ba sam ai sai yarinyar ta Dauka mun ji da gangan muka ki kira ayi mata sannu"
Ummi tace"Hakane ayi hakuri Iya"
Iya tace"Ya wuce yanzu dai ya jikin ita Muhirban..?
Majeeda tace abu kamar aljanu ko..?
Ummi tace"Da sauki an yi ta mgani tana ma koma gidanta sai dai saboda Firgitan datake yi an daukar mata yarinyar dake tayata zama"
Iya ta gyara zama tana fadin"Daga ina aka Fahimci matsalar Zaliha..?
Ummi tace"Iya ana Tunanin Daga gidan ne an sa anyi saukan Qur'ani kafin su koma"Taki fada ma Iya matsalan Muhibba saboda wani abu daya Danganci sirrin Rayuwar ita Muhibban ne.
Iya tace"Ni kuma sai nake ganin kamar matsalan Yaron nan ne ta shafeta kinsan fa Aljana ta auri biladama mallam Rilwanu ya fadamin basa rabuwa da mutum"
Ummi tace"To waya sani Iya..ana ta dai mganina Allah yasa adace"
Iya ta amsa da Ameen kafin tace"Tunda an samu waraka shi kenan bari zan saka Hayatu ya kiranin ita muhirban na gaisheta.
Da haka suka rabu da iya salin alim Duk aranar ta sa aka kira mata Saifu tayi mai Tas shi dai nashi ban Hakuri ne Daga baya tace ta Hakura.
Waahegari aka kira mata ni kamar yadda take kirana Muhirba mun gaisa tamin sannu tare da fadin"Bamu sani ba Domin zaliha da yaron nan basu gayamana ba da kin ga karan Dangin Uba"
Ni kuma nayi dariya nace"Bakomai Iya hakan ma nagode"
Muka rabu cikin aminci ni dai Tsohuwar na Burgeni bata da Hayaniya shikenan mganar ta mutu iya bata kara Tada ita ba duk da su Goggo Atika basu so haka ba.
Na kwashe tsawon wata Uku cikin Lafiya da kwanciyar hankali na fara maida kibata nayi bulbul hankalina ya kwanta har na gama amfani da mganina sai dai ban daina kwana da karatu da rike addu'a ba ashe kuma wani al"amari ke bibiyata ban sani ba.
A wani Weekend da Saifudden ya dawo cikin Tsananin kewata da Bukatuwata,bukatuwar da bai taba nuna min yana yi dani ba, wannan karon ya gwadamin a daran na Fara Kirga munanan kaddarorina.
*Janafty*
*SFD0036*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban
daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
A yadda naga ya zo gidan a Gaggauce cikin wani yanayi yasa jikina ya bani ba lafiya ba,Saboda har mun kwanta yamin waya nazo na bude mai kofar Falo abun da ya kara bani mamaki har da mangariba mun yi mgana bai cemin yana tafe ba tun daga naga Jumma'a ta wuce asabar ta shiga bai ce min yana tafe ba sai na dauka yana da uzurin da bazai kawo sa zaria wannan satin ba.
Na riga na yi shirin barcina Wasila ta Dade da yin barci abunta ni kuma Daman tun bayan Lalurar nan ko nace Kaddaran data fadamin sai na kai tsawon wani Lokacin ban samu barci ba,Shiyasa sai na Zumbula Hijabin sallah na saman riga da wandon da na saka masu taushi na barci,Ina bude mai kofar ya jawoni da karfi ya Rumgume ni karon farko da Rumgunarsa bata haifarmin da Natasuwa ba sai fargaba da wani Tsoro dake tasomin daga kasan raina.
Ya dauki Lokaci yana kamkame dani yana kuma shinshinar gefen wuyana sai da ya gaji sannan ya sake ni na bisa da kallo kamar yadda yake bi na da kallo cikin rawan baki da na jiki nace"Are u ok..?
Saboda naga yanayinsa duk ya Sauya ba Fara'a sosai a saman Fuskarsa Mirmishi yayi min ko nace yake kafin ya Raba ta gefe na ya shige yana Fadin"More Than ok Muhi..Rufo kofar Falon ki zo kiji"
Ban musa mai ba na maida kofar na Rufe mamakinsa bai kara kamani ba Sai da naga ya Daukeni cak har Zuwa Dakinsa bai Direni ko"ina ba sai kan gadonsa ganin yadda nake binsa da kallo ne yasa ya barsa yana Fadin"Bari nayi wanka ki zauna kada kije ko'ina kin ji ko..?
Kamar wata gaula haka na Daga mai kai sannan na kasa yi masa gaddama Duk daman ba Hali na bane.
Ina kallonsa ya cire Tie dinsa Ya Rage kayan jikinsa sannan ya shiga Tioler ni dai kaina na kasa ina Fama da Sake saken da bani da amsarsu.
Mintina goma suka Dauke sa kafin ya Fito yana Daure da Rigar wanka fara tas da ita a koda yaushe ina mamakin meyasa yake son abu fari da baki Saboda yanayin yadda Surar jikinsa ta bayyana yasa na kauda kai gaskiya bazan iya kallonsa haka ba ina da matukar jin kunya indai ta wannan bangaran ne.
Bansan har ya kariso gabana ba sai da naji hannunsa yana Dago Haba na sannan na Dago na kallesa har ya sanya Farar Jallabiya Kansa da akwai dashin Ruwa Ban san dalili ba sai naji Tsoro yana shiga jikina zan fara kyarma kamar wani abu zai faru ina ji ajikina adaran nan wani abu zai faru mara Dadi gabadaya yanayi na babu dadi,Shi kuma kwata kwata bai Dauke haske akan Lamarina ba in da ya san abunda zai faru kenan har abada sai dai ya cigaba da kallona bazai taba Tunanin ni da shi muzama Daya ba.