← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 144

Sashe 134

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin girma ya kara gaida kawu kafin Baba mallam ya dubesu cikin kauna mai Tarin yawa kafin ya kalli su kawu yana Fadin"Dukkan su nan ya"ya nq ne..Wannan shine Babba shi ke zaune a madina da iyalansa wadanan yan Biyu daga bangaran sa ne..ga Nazir mai binsa ne da yana Lagos da zama ne ammh yanzu ya Dawo Dutse,Sai sauran kannen su ga su nan duk ma"aikata a ma'aikatu Dabam Dabam duk sun zo sallah ne da iyalansu"
Su kawu suka jinjina kai suka Hada Baki shi da Baffa Hashimu suna ta saka albarka.

Alhaji Sa"idu ne yace ya navnuna su kawu"Suma duk yan gida ne..Dalilin nemam mgani suka zo daman..kuma Shi Alhaji sunusi akwai sanayya Tsakanimu muna cinikayar Dabobbi dashi sama shekaru talatin.

Ya nuna su Majaheed yana fadin"Ga ya"yan nasu sauran mata da iyayen su suna cikin gida sun zo godiya ne da zumunci"
Nan fa aka sake sabon gaisuwa da su Dan mallam da su Saifudden,Kafin kace kwabo su Jawaad sun cika gaban Su kawu da abinci kala kala Baba Mallam ya kalli su shamsu yana Fadin"ku kwashe komai ku kai musu Cikin Dakina su ci su huta zuwa anjuma mu fara hirar mu ta yan"uwa nan bazasu sake ba sosai"
Kafin me duk sun kwashe komai zuwa Dakin mallan na musamman da sai manyan baki na kusa yake Saukewa..

Ba kalan abinci da babu har da Nama Dawisu Sani na yaga yana Fadin"Ni dai naga wuri don Allh ko akwai wata yar shilla na shiga sahun manema?

Aka saka Dariya gabadaya Kawu yace"Sai dai cikin jikoki ammh ya'ya sun Dade da karewa"
Sani na Sosa keya yace"In dai tana cikin zuru'a no wahala ko Bro.?

Ya fada yana kallon Isma"il dake faman da Cinyar kaza ya gyada kai yana Fadin"am comming aftar u Bro"
Gabadaya suka saka Dariya har da Saifudeen..sani ya kallesa yana Fadin"Ga Big bro din mu nan zai shige mana gaba"
Saifudden na kurban Lemun kankanan dake hannunsa ya jinjina kai yana fadin"in sha Allahu"
*****
Muma acikin gida afalon Hajiya haka muka ga wannan karramawar Ko da muka karisa falon nan cike yake da ya"ya da Jikoki,duk girman falon Hajiya sai da suka cika shi muna shigowa Hajiya na Daki ta fito da murnanta Ta rumgume su Ummi tana mana Maraba Nima ta rumgumeni Tana Fadin"Muhibba..Kai masha Allah"
Sannun ku da hanya"
Hanne,Amina ku basu waje"
Bazn iya tantance su waye aka kira ba suna da yawa afalon sannan atare suka mike suna mana Maraba kafin su fara Ficewa Daya bayan daya naji Dai wata na fadin"Hajiya bakin ne suka iso..?.

Hajiya tace"Eh Abida a kawo musu abinci da abun sha"
Kafin ma wani yayi mgana sai ga Anty Hadiza tana shigowa bakinta har kunne ta karisa gaban su Ummi suka gaisa da su Adda cikin Fara'arta tace"Hayaniya ce tayi yawa afalon Hajiya sai na shiga wajen Hajiya nasara na kwanta to hayaniyar su naji sun shigo sukace bakin da Hajiya take zencen su tun jiya ne suka iso nace Inga kune barka da zuwan ku"
Muka amsa cike sakewa ta kalleni Tana Fadin"Masha Allah muhibban ce ko..?

Ummi na Mirmishi tace"Itace"
Ta kara kallona kafin ta rike baki har hakorin makkanta na bayyana tace"Masha Allah Tubarkallah"
Sai dariya su Adda Sadiya ke min ni kuma kaina na kasa.

Wata matashiyar matace ta fito,fara ba sosai ba Doguwa ta leko Daga kitchen tana fadin"Hajiya falon nan za"a kawo ko falon sama..?

Hajiya ta juyo tana Fadin"Hamida inaga ku kai musu falon sama zasu fi natsawa"
Anty Hadiza tace"Eh sai su yi wanka ma su huta Hajiya"
Hajiya tace"Hakane ku taso mu isa Falon sama kun sha hanya ya wajen su Surajon.?

Ummi ta rika amawa da Lafiya har Falom sama in da aka sauki su Ummi wanchan zuwa akwai falo da Dakuna babu abunda babu aciki.

Mun zazzauna Ummi na mata bayanin su Inna da Mama zuwaira da Umma Babba.

Hajiya babba ciknn Fara"a tace"Maraban ku..ai ni na kwace Muhibba zan hadata cikin ya"yana na rike"
Inna na Dariya tace"daman waya ce va yarki bace..?

Na baki auta Halak malak"
Hajiya ta kalli Anty Hadiza tana Fadin"Tayani godiya Ta hannun damana"
Anty Hadiza na Dariya take godiya su Ummi na tayata ni dai ina gefe bana mgana sai bin ko"ina nake yi da kallon Sha'awa barin ma su Laala da suka Takure gefe Hajiya ta kalle su tana fadin"Ku sakin jikin ku nan duk gida ne"
Ummi na Dariya tace"Haka suke Zaibabu da Suhaima da Majeeda dukkansu ya"ya na ne,Sai Nihad diyar Sadiya ce gata nan"
Hajiya ta karbi Nihat tana fadin"Kema na kwace ki cikin jikokina zan hadaki"
Adda Sadiya tace"Mun baki Hajiya"
Kafin Hajiya tayi mgana sai ga matashiyar ta dazu bayan tacma wasu mata ne su Biyu suka yi ta shigowa da abinci suna saukewa sai da suka gama sannan Hajiya tace"Ina Mamah ne ban ji Duriyarta ba..?

Hamida ta Dago tana fadin"Ta shiga ta kwanta Hajiya wai kanta na sara mata"
Anty Hadiza tace"Hayaniyar yara ce kawai da gajiya.

Hajiya tace"Ku tashe ta ba kyau barcin La"asar"
Suka amsa mata kafin su fice Hajiya ta kira su ta yi mana bayanin su tace"Ga Hamida ga Hanne..Ga Abida duka ya"ya ne"
Kara gaisawa muka yi nima na gaishe su suka min mirmishi har suka fita ina bin su da kallo sun bani Sha'awa ko wacce shar da ita fatar su ta goge kayan jikinsu cikin burgewa da iya Dressing kallo daya zakayi musu kasan ilimi hutu da jin Dadi ya zauna musu.

Hajiya da Anty Hadiza suka fice suka barmu muci abinci Hajiya ta kara da Fadin"ku huta fa anjuna akwai hira sannan gida cike yake da baki sai kun gaji da amsa gaisuwa."
Daga haka suka fice suka barmu,Ni dai ban ci komai ba sai nayi wanka na natsa Tunda duk an shigo mana da kayanmu kwana daya zamu yi gobe zamu juya..ban sa komai acikina ba Tunda bakomai nake iya ci ba..

Na kira Saif naji ko yaci abinci yace min shi he is ok.

Ya tambayeni naci Saboda na kwantar mai da Hankali nace eh sai yace na kwanta na Huta nagaji da yawa da toh muka rabu.

Falo na fito in da su Adda da Anty Habiba ke ta hira na lafe kusa da Inna ta kalleni tana Fadin"Auta kada ki yi barci yanzu"
Da kai na amsa mata ina jin Duk hirar da suke yi suna cin abinci nagaji barci ke cina ammh bazan yi ba Saboda nasan Haramun ne barci bayan sallaar la'sar.
*Janafty*
*SFD0048*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Duk yadda naso kada barci ya kwasheni sai da ya fizgeni sai da naji mganar Ummi a saman kaina tana tashi na na bude idanuwana da suka fara sauya launi saboda barci na ganta tsaye a kaina cikin Taushin murya tace"Muhibba ta shi ki yi sallah mangriba ta gabato"
Da toh na amsa mata na yunkura dakyar na mike har tana taimakamin ina mikewa sai naji kunya ta kamani na sunkuyar dakai na wuce cikin bedroom din da aka sauke mu na Dauro alwala ina alwalan naji an Tada Sallah Radau kamar acikin Falon nan ne masallacin yake mamaki da Al'ajabi ya kamani domin muryan mai bada sallar kamar ta Sudes na Saudiya sai dai bambamci kadan ko da na Idar da alwalan na fito falo su Ummi sun kabbarta sallah kuma dukkansu jam"i suke bi nima sai nabi ayarin su gaskiya na samu natsuwa Saboda muryan mai bada sallar karatu yake cikin natsuwa da salama wanda ke saukar ma da masu binsa Sallah natsuwa da salama.

Bayan an idar da sallar ina zaune Anty Habiba da Adda suna ta labarin gidan da muka zo suna yaba Tsarin Tarbiyan gidan da komai da komai nasu abun burgewa ne gaskiya ko ni na ji ina sha'awar zamowa Daya daga cikin wannam kyakyawan zuru'an.

Muna nan zaune har aka kira sallah Isha"i Ummi da Inna sai Umma Babba suke mganar su sama sama ni kuma ina ta azkar,bayan na gama na fara karanta suratul Rahma tana kai na Haddaceta,Ana tada sallah muka mike wannan karon wani ne ya ba da Sallar ba na farkon ba sai dai shima Muryansa akwai taushi Sosai mun idar da badewa sai ga Hajiya ta shigo Sanye da Hijabi da Cashaba a Hannunta tana ta Dingisa kafa sai wata mata itama Dattijuwa da ita sai dai bata kai Hajiya shekaru ba duk jin Dadi da Hutu ya Boye shekarun su.

Hajiya har turgudewa tayi zata Fadi ni ke farkon Shigowa falo nayi maza na tashi na tareta ni da matar dake bayanta Cikin mganarta tace"Hajiya ki yi fa ahankali kinsan baki da Lfiyar kafa"?
Chapter 134 · 0% Book details