Sashe 125
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Majeeda sai kuka ta kasa mgana Inna Talatu ta mike tana fadin"Tunda kin ce ba komai ki tashi ki Dauko kaynki ki wanke gobe tun Safe zaki kama Hanya"
Majeeda ta Runtde ido sai Hawaye ta kasa mgana Har Inna Talatu ta Fice ta barta ita fa bazata koma ba aure zatayi kuma Hamma take so a aura mata Tana so tama Iya mganar ammh kuma ta kasa ta rasa ta ina zata fara.
Ganin Inna Talatu ta Dau zafi yasa ta Fara Hada kayanta mganar wanki cewa tayi sai ta koma akwai mai yi musu wanki haka ta matsa kaya masu Datti acikin jaka tana yi tana kuka.
Chan da Rana Majeeda na Daki taji wayar Inna Talatubna kara,Kafin ta fito ma Inna tazo ta Dauki wayar ta yanayin yadda take mgana yasa gabanta ya fadi ta Fahimci da Ummi suke mgana kuma yanayin mganar kamar Ummi taji abunda Majeedan tace ashe Iya ne ta saka a kira mata Baffa Hayatu tace a kira mata Ummi tana kuka tana komai ta gayama Ummi abunda Majerda tace har da karawa da Fadin"Zaliha ki yi mana aikin gafara ba Laifin mu ba ne ya"yan zamani ne..Ki kyaleta ga Sailuban Atika nan sai ki tafi da ita Tunda kina da Zuciyar rike ya"yan dangin mijinki Zaliha"
Ummi bata yi mamaki ba sai dai bata Dauka ba"a Uwa Majeeda ke kallonta ba Daman ta zura mata ido ne tasan Daman haka zata faru.
Ummi ta nuna ma Inna Talatu ba komai in Majeeda batasan komawa ta kyaleta ammh ita zata zo gata ga Majeedan sai ta fada mata abunda akayi mata datace bazata koma ba.
Inna Talatu taji kunya ya kamata cikin wani yanayi tace"Ummin su ki yi hakuri,Na yi mata fada gata ma tana shirya kayanta zata taho gobe yarinyata ne kawai da shirme bakomai wlh"
Ummi tayi yake kafin tace"Ki dai matsa mata ta fada miki abunda aka yi mata talatu kin san zama kila wani abu ne muke mata ni da yara da bata jin Dadin sa in taki Fada miki ni zan zo da kaina In sha Allahu"
Da Sauri Inna talatu tace"Zan kara Bincikar ta don Allah ka da wannan mganar tataso ki."
Ummi tace"To shikenan sai na jiki..ammh kada ki matsa mata"
Da haka suka yi sallama duk kunya ta kama Inna Talatu tana Dagowa suka Hada ido da Majeeda Harara ta Wurga mata tana Fadin"Wlh ki Tanadi gaskiyan da zaki Fadamin in na kara tambayan ki baki Fadamin Dalilin ki ba,sai na yi miki bugun Tsiya acikin Gida nan"
Daga haka tayi Tsaki ta fice da Wuri Inna Talatu ta gama Tuwon Daranta Majeeda kuma kunya yasa ta fito ta share Tsakar gidam.
Sai da aka yi mangariba Yaran sun fita makarantar Dare Inna Talatu ta Sake Ritsa Majeeda kafin Baffa ya Dawo ta sake tambayanta sai kuka ta kasa mgana sai kuma alokacin take jin nauyin abunda ke cikim ranta.
Dundu taji a bayanta ba shiri ta bankare ta matsa gefe tana kuka Inna Talatu ta nuna ta da Hannu tana Fadin"Wlh in baki Fadamin gaskiya ba zan miki dukan tsiya,kin san Halina Sarai majeeda"
Tabbas tasan Halinta Shiyasa bakin ta na rawa tace"Ni..ni Aure zan yi"
Sai Inna Talatu ta kasa wani motsi ta koma ta zauna tana fadin"aure Majeeda?
Kanta na kasa tana kuka Inna Talatu ta Sauke Numfashi tana Fadin"Kin samu mijin ne achan habujan..?
Majeeda ta kasa mgana Tsawa ta Daka mata tana fadin"Nace kin samu mijin me achan Habujan da kika yanke shawaran aure zaki yi..?
Jikin Majeeda na rawa tace"Eh a"a...Ha...Hamma na ke so"
Inna Talatu na yi mata wani irin kallo tace"Hamma wani Hamman..?
Majeeda ta Dago ta kalleta tana Fadin"Hamma Saifuddeen..'"
Inna talatu ta saki Salati tana Tafa Hannu lokaci daya tana Fadin"Lalle baki da kunya Majeeda baki da kunya wlh"
Ta fada ranta na kara baci Lokaci daya da mamakin Majeeda wato Saboda haka ne yasa tace bazata koma ba ban da sakarci ba ke kika ce Daga baya baki so ba karatu zaki yi kuma ya biya miki muradinki kin Fara murmurewa shine zaki fito da iskanci bazata bari wannan abun kunyar ya fita waje har wani yaji ba Fada ba nata ba ne Nasiha ne da jan ta ajiki Ta Fahimci Kuruciya ce da Shekarun balaga ke Dawainiya da Majeedar ammh a shekarunta baza ma ta iya zaban ma kanta abunda take so ko akasa sin ba.
Cikin Taushin murya tace"Taso ki matso kusa da ni majeeda"
Majeeda ta kalleta cikin mamaki kai ta gyada mata tana fadin"Eh taso ki zo ku sa dani ki zauna"
Jiki a sanyaye majeeda ta taso tazo ta zauna agaban Inna Talatu tsoro bai fita Daga kasan ranta ba.
Inna Talatu ta sauke numfashi Tana fadin"Majeeda"
Majeeda kanta na kasa tace"Na"am"
*Janafty*
*SFD0045*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan
gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Inna Talatu tace"Dago kanki ki Dubeni Majeeda"
Jikin majeeda a matukar sanyaye ta Dago tana kallon Inna talatu gabanta na tsananta faduwa tsoro kai Tsaye ya bayyana acikin kwayar idonta.
Cikin Sanyin murya Inna Talatu tace"Tambayar ki zan yi kuma ina so ki bani amsa ta.
Ba a matsayin uwa da yarta ba Majeeda amsa zaki bani a matsayina ta wacce tafi kowa kusanaci dake anan duniya"
Shuru tayi na wani Lokaci Tana nazarin natsuwar majeeda kafin tace"Meyasa a baya san da Su iya da Baffaninki suka so su maida auran ku ke da Saifu kika Tubure Kika ce baki so..?
Meyasa kuma sai yanzu da abubuwa suka fara Daidaita zaki Dawo da Hannun agogo baya Majeeda..?
Majeeda sai ta kasa mgana kan ta na kasa tana ta cizon bakinta da Hakoranta Inna Talatu ta kara Sausauta Murya tana fadin"Ina jinki Majeeda ke nake saurare"
A hankali Majeeda tace"Innar mu to ba shi ba ne yace min gwara nayi karatu na zama yar birni a kan in yi aure in haihu na kamu da yoyon Fitsari ko na yi saurin Tsufa ba"
Inna Talatu mamaki ya cikata cikin mamakin tace"Shi wa..?
Majeeda tace"Hamma mana"
Inna Talatu sai ta gyara zama tana Fadin"duk yaushe a kayi haka ban sani ba?
Nan majeeda ta warware mata yadda Saifudden ya jata cikin motar a ranar da su iya suka yi mganar maida auran su da duka mganganun daya tsara mata ta karishe da Fadin"Innarmu shi yace in na zabi karatu zai maidani Abuja nayi karatu na iya Turanci kamar su Laala shiyasa alokacin na Tubure nace bana so"
Inna Talatu tayi shuru tana kallonta Lokaci daya tana kara ganin wauta da kuruciyar Majeeda ta gama aminta da Har yanzu bata san kanta ba Juya Tunaninta kawai ake yi bata yi girman da zata rabe abu mai kyau da akasasin ba.
Cikin Kwantar da kai Inna Talatu ta kalli Majeeda tana fadin"Naji to ba ya cika miki alkwarin sa ba ya maida ke Abuja ya sakaki makaranta ya inganta Rayuwarki ba,meyasa kuma yanzu kika Dawo da wannan mganar..?
Wani abu ya faru ne..?
Majeeda da ta ga Inna Talatu ta Sauko Sai ta saki jiki da Sauri tace"Innarmu ni kawai naji ina son auran sa ne yanzu"
Inna Talatu ta katseta da fadin"A"a kina da dalilin ki Majeeda na kuma san ba son shi kike yi ba ko kina son shi ne Har yanzu..?
Majeeda tayi shuru ta kasa mgana ta Fara Tunanin ko ta na son Hamma ko bata son shi ita daai ta san yana Burgeta dan gayu ne mai kyau ne mai Ilimi ne komai nashi mai kyau bayanan ita bazata iya dora komai kan Haka ba ganin yadda tayin ne ya Tabbtar da Inna Talatu zarginta Cikin Dubaran su na manya tace"Ko yana Burge ki dai Majeeda..?
Saboda Saifu abun so da Burgewr kowacce y'a mace ce acikin garin nan da Ko"ina ma bama ke ba"
Da Sauri Majeeda tace"Eh Inna yana Burgeni komai nashi mai kyau ne..Sannan..Sannan"
Sai ta kasa karisawa ta koma ta sunne kanta Inna talatu tace"Uhm ina jinki sannan me..?
Majeeda tace"Inna yana kula da matarsa kinsan Aljanu sun taba kwakwalwarta bata da lafiya sosai Allah inna komai shi ya ke mata sai naji Dama nice ita sannan ranar fa Har Laala sai da tamin gori wai nayi Rashi"
Sai kuka wiwi Inna talatu tayi Tsam kafin tayi mirmishi ta gode ma Allah daya sa ta gano bakin zaran Tunda wuri ba sai da komai ya kwabe ba..
Kasa ta sauko kusa da Majeeda ta zauna ta Dago Fuskarta ta sa ka Hannunta tana Share mata Hawaye cikin wani yanayi tana fadin"Shiii.Ya is bar kukan nan hakan kin ji ko"
Da kai Majeeda ta amsa tana Hadiye kukanta Inna Talatu tace"Natsu ki saurareni Majeeda"
Sai da ta tabbatar da ta natsun sannan tace"Ina fatan baki fada ma kowa wannan mganar ba sai ni kadai?
Majeeda tace"Innarmu ban fada ma kowa ba wlh sai ke"
Inna Talatu ta gyara zama tana Fadin"To Alhamdulillh naji dadin da nafara taran wannan matsalan da kaina..Majeeda ki Saurareni da kunnen basira da duka Hankalin ki da Tunaninki Shekararki nawa yanzu..?
Majeeda tace"Innarmu sai fa watan jibi kikace zan cika shekara sha shidda"
Inna Talatu tace"Dakyau kin san cewa ke yarinya ce karama har yanzu baki mallaki Hankalin kanki ba..?