← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 144

Sashe 133

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed ya kira kawu yace mun taso kawu yace suma suna Hanya shi da Mama zuwaira da Umma babba da Isma"il dake jansu a mota nima mun yi waya da Anty Habiba tace min yanzu zasu fito Sani zai tuko su Domin Sani yanzu fa ya kware a tukin mota.

Mun isa bazanga sha biyu da wani abu na Rana Ummi ita ta gane gidan mallam Surajo Daga Saifudden har Mujaheed sun ce
sun manta muna zuwa muka iske su Inna sun jima da isowa Tunda su daga zaria ne,har sun natsa,Su kawu ne karshen isowa Saboda sun fimu Nisa Mallan Surajo da iyalansa suka rasa ina zasu sakamu da Farinciki an yi mana girke girke an soya kaji da Zabbi da Naman rago,an siya mana lemuka sai wanda ka Zaba tsakani ga Allah ahalin Baba mallam suna da karamci da Sanin Darajan baki.

Duk yawanmu haka suka rika Hidima damu,Mazan duk suna Falon waje tare da Mallam Surajo mu kuma matan muna cikin gida,Sai da muka yi ci abinci muka natsa muka yi sallar azahar sannan muka yi shirin Tafiya Ummi da Inna suna ta yi ma Matan mallam Surajo godiyar babbar Cikin su mai Sunar Babar Karima haka suke kiranta tayi mirmishi tana fadin"Haba ba komai an zama Daya..An samu abunda ake so Tunda an samu waraka..Sannu Muhibba kamar bake bace akazo dake ba yarda kike"
Mama zuwaira tace"Wlh kuwa ga shi yanzu har da Rabo ma"
Babar karime ta Daga Hanci ta Rangada Guda Adda Sadiya na gefe ta tayata su Ummi nata Dariya sai jin Muryan Mallan surajo muka yi Daga tsakar gida ya Leko yana Fadin"Sannu da aikin Bidi"a Halima baki su fito zasu kama Hanya"
Dariya ta saka tana fafdin"Abun farinciki ne mallan barni na Taba Bidi"ar nan kadan"
Ni dai kaina na kasa na kasa Dagowa Saboda kunya Babar karime ta kalli Adda Sadiya tana fadin"Kema Allah dai ya sa wannan rabom sai ya fito Dunuya nan kuka bar garin nan baki lafiya"
Ummi tace"Wlh ai har asibiti sai da ta kwanta aka bata bedrest tsoro da Zirga zirga ya kusa fitar dashi"
Mama zuwaira tace"To ko ni da Labari naji ba karamin tsorata nayi ba"
Babar karime tace"ai mu duk mun Saba..Nan ma ai mallam ya Daina Tunda Mallam babba yamai Fada ammh chan Gembu da muka zauna ba abunda bama gani"
Nan ta fara bamu Labarin irin fafatawar da Mallam Surajo ya sha yi da kafuran aljanu.

Mun kasa kunne muna jin Labari sai ga Kawu ya kira Ummi Dole muka mike har Falon waje matan mallam Surajo suka rakomu.

Ummi da Inna suna ta yi ma mallam Surajo godiya Kawu yace"Muma muna ta godiya yaki amsa mana wai da yasan godiya muka zo da bai amince mun zo ba ya Dauka ziyarar ta zumunci ce"
Inna tace"ta zumunci ne mana ai an zama daya da yardan Allah..Ammh godiya ta na dadi ko Allah in ya bamu muka gode masa sai ya kara mana"
Gabadaya aka amsa da Hakane Mallam Surajo ya murmusa yana nan yadda yake ya sha rawani da Farin gemunsa yace"Na karbi Godiya ammh bazan karbi kudin ku ba..Ni don Allah nayi domin Darajan Mallam"
Inna tace"ko sa aranka muma Saboda Zumunci mukayi..Kayi hakuri don Allah ka karba ba Saboda abun da kayi mana bs,sai saboda zumunci"
Inna duk ta daure mallam Surajo da kalamanta ya karbi kudin da Saifudeen ya basa 100k yana ta godiya da saka albarka ina chan gefe ku sa da su Laala ya Daga ido yana Fadin"ina Muhibban take..?

Naga dai Saifudden ammh ban gan Muhibba ba. ?

Ummi ta juyo tana fadin"Gata nan mallam"
Tafada tana yafito ni da Hannu na kariso gabansa ya kalleni kafin yace"Muhibba ina YARIMA SAIFUDEEN..?

Na kallesa cikin mamaki kafin na Dago na kalli mijina ina fadin"Ai gashi nan maallam"
Mirmishi yayi kafin yace"Ba wannan ba..wannan ai SARKI ne..Shi Yariman naki nake mgana"
Sai kowa ya kasa mgana ana kallon kallon cikin mamaki,Mallam Surajo yayi Dariya kafin yace"Yarima Saifudden bazai taba barin ahalin ku ba..Ba ku ba har duka sauran zuru"arku gabadaya..Ina Fatan baki kara Fuskatar wata matsala ba ko.?

Shi mijin naki na tambayesa ya tabbatar min da komai lafiya"
Kaina na kasa na gyada mai kai cikin jinjinawa yace"Dakyau daman har Abada in dai wannan matsalar ne ta tafi kenan..Allah ya zaunar daku lafiya"
Aka amsa da Ameen Babar karime tace"Mallam ba ka yi addu"an Allah ya Raba lafiya..?

Ya kalleta cikin mamaki kafin yace"To to..Har an samu karuwa..?

To Allah ya Sauke Lafiya Allah yasa albarka gabadaya Allah yasa ki haifi Namiji ki yi ma YARIMA SAIFUDEEN takwara domin ke kin Hada Yarima da Saraki ne alokaci guda"
Ya karishe fada cikin Sigar zolaya aka saka Dariya gabadaya ni dai kai na kasa na kasa Dagowa Saboda kunya maallam Surajo ya dago yana kallon Saifudden yace"In kuma macece..Ka saka mata Suna MUHIBBA domin ta gado jajircewa da Jarumta irin ta matarka"
Saifuddeen ya jinjina kai kafin yace"In sha Allahu"
Daganan ya cigaba da Tunasar damu muhimanci addu"a da azkar domin neman taari ni kaina ya kara Jadaddamin Daga Karshe yace"Ki rika karanta Suratul yasin da Khafi duk Safiya sannan ki rika karanta Suratul Rahman kina tofawa a ruwa mai tsafta kina sha
in sha Allahu zaki haifi cikin jikin ki Lafiya kalau".

Na amsa mai cikin gamsuwa wasa wasa sai biyu na rana muka bar Bazanga da tsaraban su magarya kuka Goriba da Taura tsaraban dai mutanen kauye har da Nono Saboda Mallam Surajo shima yana da garken Shanu da fararan akuyoyi.

Muna tafe a hanyar mu ta zuwa Gumel sai hirar karamcin Mallam Surajo suke yi Saifudden da Baffa Hashimu da muke tare a motarmu.

Mun tsaya a kano mun yi sallar La'asar bamu ci abinci ba Saboda bama tare da yunwa sannan ma Hajiya babba da Alhaji Sa"idu sai kira suke yi suna faman tambaya muna ina..?

Bazasu ji dadi ba in muka isa a koshe yadda suke da karamci da girmama bako.

Ko da Biyar tayi muna cikin garin gumel biyar na yammah da wasu mintina motocin mu suka ci taya kofar Babban get din gidan Baba mallam cikin ikon Allah Alhaji Sa"idu sauran yaran gida magidanta suk suna Kofar gidan jiran isowarmu Alhaji Sa"idu da kansa ya Bude ma kawu mota ni kaina sai da na Saki baki ina kallon Tsaruwan wad'anan gidaje ni da nazo ina barci ai ban ga komai ba.

Sani kuwa sai da bakin sa yayi mgana ya kalleni yana Fadin"Auta kinga Duniya fa har nan daman aka kawo ki neman mgani..?

Turesa nayi ya koma gefe yana Dariya Wasu magidanta guda Biyu Dayan yana yanayi da Alhaji Sa'idu d'ayan kuma Kamar Baba mallam suka bama mazan hannu suka gaiggaisa.

Mu kuma muka Dumguma zuwa Cikin gida da Jagoranci wani Saurayi matashi fari da Alhaji Sa"idu yace"Kai Jawaad mika su Falon Hajiya Babba"
Yana gaba muna bin bayansa har ina Tuntube wajen kallon Tsarin gidan,Mama zuwaira sai fadi take yi"Kunga gida anguwa guda Jama"a?

Ummi na Dariya tace"Kallo ma ai sun min shiga ciki.."
Mama zuwaira tace"Ko dai ya"yan nasa daga gwamna sai yan majalisu ne hala..?

Harta wanda aka Kira da Jawaad dake gaba Sai da ya Juyo yana Dariya Ummi tace"Ko daya..Sai dai dukan su ma"aikata ne matan kuma kowacce na gidam mijinta"
Muna barin wajen suma mazan Alhaji Sa"idu ya kwashe su zuwa Falon Mallam da bakinsa yaki Rufuwa fadi yake "Maraba da bakin zazzagawa'
Kawu na Dariya ya karisa gabansa yana Fadin"Har bakin kanawa Baba maallam"
Sai aka saka Dariya gabadaya Saboda Falon cike yake da baki akwai ya'yan mallam Irin su Akilu shamsu,Nazim,Uzairu,Manya kuma su Ya Danmallam da Nazir Nazim sune ke chan gaban mallam sai Manyan jikokin sa Yunus na wajen Nazir sai kuma yan Biyun masu kama Daya mgajin Mallam da Aban yara.

Sai sauran yaran ga sunan gwanin ban sha"awa.

Haka suka duka suna gaishe da su kawu cikin girmamawa Dukkansu sai da suka yi musabaha da kowa Sani ya karkace baki yana yi ma Isma"il Rada"Kai baba ko dai gidan Larabawa muka zo..?

Isma"il ya turesa yana fadin"Da alamu kaga yara sai tashin Larabci ke bakin su,kamar ya"yan larabawa..?

Suma chan su Mujaheed tsegumin da suke yi a ransu kenan.

Baba mallam ne yayi gyaran murya yana kallon su kawu kafin yace"Ina su sauran ya"yan nawa..?

Kawu yace"Sun shiga cikin Baba"
Baba maallam yace"Dakyau Sannun ku da zuwa mun gode Sosai Allah ya bar zumunci"
Gabadaya aka amsa da Ameen Baba mallam ya gyara zaman alkyabbarsa kamar wani Saraki kafin yace"Kun zo a daidai kun iske gida ya cika da ya"ya da Jikoki..Duka yaranmu da iyalan su gida suka yi sallah"
Kawu ya jinjina kai kafin yace"Mun ji Dadin haka sosai"
Baba mallam yace"Sannun ku da zuwa ya kuka baro wajen su Surajon..?

Kawu ya amsa da Lafiya tare da Godiya Baba mallam ya gyara zaman gilashin idon sa kafin yace"Ina UMARU ya ke ne..?

Dagachan bangaran DANMALLAN ya dago kansa yana zaune kusa da Dan"uwansa Nazir cikin kamalarsa yace"Gani nan Baba"
Baba mallam yace"Matso ku sa kai da Sauran yan"uwan ka baki su gan ku su gane ku ko domin nan gaba"
Ba musu suke mike shine kan gaba yana Sanye da Riga da wando na Shadda Fara tana maiko kansa Dauke da Hula irin ta larabawa Kafafunsa suna waje ne Saboda wandon sa ya Dage Farare cike da gargasa su suna faman Nitsewa saman Cafet din dake falon Baba mallam.

Gaban kawu da Baba mallan ya zauna ya tankwashe kafa haka suma Sauran suka yi,Su kawu kallon wanda aka kira da Umar kawai suke yi suna Jinjina kai Wani irin kwarjini suke gani da Haiba Fuskar ma'abociyar kamala ya Dago ya sauke kan kawu Danmallan fa ya fara manyanta Domin farin gashi sun kai goma a gemunsa haka ma kansa gasu nan to jiya ba yau ba,ya haura Hamsin a Duniya fa ko Jidalin Aminene ai ya isa yasa kansa ya rufe da Furfura.
Chapter 133 · 0% Book details