← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 144

Sashe 37

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kun yarda MUTUM ne ba Aljani bane ko..?Wlh shine Saifudeen dina ne shi ne wlh..!"
Nake fada da karfi lokaci daya ina kuka Kafin kawai na karisa gaban Saifudeen Fuskarsa na fara shafawa iba Tattaba jikinsa kamar wata zararriya Fadi take na ke yi "Shine wlh..Saifudden ne..Ni daman nasani Watarana zan sake haduwa dakai..Na kuma san cewa kai mutum ne Cikakkake kamar yadda nake Mutum Bil'adama su inna suna ta cemin nayi gamo gamo ban yarda ba ni nasan cewa zaka dawo gareni ina ka shiga..?ina ka tafi ka dauki Lokaci baka zo gareni ba..?Nayi kukan kewarka ban san iyaka ba"
Kawai sai na fada jikinsa na Rumgumesa ina sakin wani irin kuka mai cin rai ai sai gabadaya Hall din aka mike ba ga malamai ba baga Dalibai ba har da Iyayan yara cikin mamaki da al"ajabi masu wayoyi kuwa sun dauko suna ta Daukan Hoto tare da yan jaridun dake wajen Anty Habiba ta rude jiki ta har rawa yake yi ita da Sani suka juya suka kalli juna sun kasa mgana Abban Walid ya kalli Matarsa yana Fadin"Maman Siyama kije ki kama Muhibba wani abu na faruwa fa.!"
Kamar an dasata ta kasa motsi sunan da Muhibba take kira ai ba bako bane a wajensu Saifudden take ambato kuma su dai sun san Saifudeen din da Muhibba take gani ba Mutum bane Sani ne ya fara Tafiya yasa itama ta Samu karfin gwiwan bin bayansa.

Sadiya ta rike Mujaheed tana Fadin"Hamma..Hamma..meke faruwa ne..?

Shima Mujaheed alokacin baya iya gane komai yasa ya kasa mgana bai ce komai ba sai dai yana tsaye shima yabi Sahun masu kallon abunda ke Faruwa Cikin Al"ajabi da mamaki mai girma.

Saifudeen da mamaki da tsoro suka sandarar dashi sannan uwa uba kalaman wannan yarinyar dake nuna ta sanshi a ina ta sanshi..?

Shi da bai taba ganinta ba sai yau..?Tana wasu mganganu da bai gane musu ba,Komai nasa ya tsaya cak ne Lokacin data Rumgumesa gabadaya Jikinsa sai ya Dauki rawa,Wani irin yanayi ne ke ratsasa Tundaga Tafin kafarsa har zuwa Tsakiyar kansa,Yanayi ne da bai taba tsintar kansa aciki ido biyu ba,sai dai acikin mafarki bayan Janet ba macen da tataba Hada jiki dashi a wanchan Lokaci bai ji komai game da yunkurin janet ba sai dai wannan karon Haduwar tasha bambam domin wani yam yam kawai yake ji yana neman ma ya fadi ne saboda jiri ne ke dibansa Sai dai kamar wanchan lokacin wannan karon ma ya sake Faruwa,Domin Cikin wannan yanayin yaji wani irin azaban zafi ya gauraye ilahirin jikinsa kamar ana huramai wuta ajikin fatarsa,yanayin da yake jinsa in ya Rab'u da wata mace Zafin dayasa ya rasa control dinsa alokacin,Da baisan Sadda ya Tattara duka karfinsa ba ya rike Muhibba ya bambareta Daga jikinsa ya wani tureta da karfi sai da tayi baya ta fadi a kasa kugunta ya Daki kasa sai da ta saki wani irin ihun da su Anty Habiba suka jisa har cikin kansu da gudu suka karisa gareka Sani yayi azaman Rikota Cikin wani yanayi Anty Habiba sai da ta Durkushe gaban Muhibba ta fashe da kuka ganin haka yasa Abban Walid da Asma"u suma suka baro wajen zamansu suka karisa ga Muhibba su siyama dake cikin Dalibai ganin Antynsu da Mommynsu na kuka yasa suka nufesu Siyama sarkin kuka sai Hawaye Walid ne da Khalipa sukayi jigum jikinsu yayi sanyi,Sadiya ta Dafe yarta Nihad dake hannunta jikinta na Rawa tace"Sweety Ka dakatar da Hamma kada ya illata yar mutane..!"
Yana jinta ammh shima alokacin bai da wata mafita yasa ya kasa motsi Sai dai yana kallon yanayin Saifudden da ya tsaya yana Huci cikin Wata irin murya yaace"Who are u..?.

Who send u..? waya turo ki ki batamin suna ni ban taba sanin ki ba."
Mganar tana ansa kuwwa saboda yana gaban Microphone ne Hall din ya amsu da mganarsa balle wajen yayi shuru kowa na kallon abunda ke Faruwa Cikin mamaki.

Muhibba duk da azaban dake Damunta a kafarta bai sa ta kula da wannan ba Rinanun idanuwanta ta Dago ta na kallon Saifudden wanda yake kallonta cikin yanayin da bata gane ko na Menene ba.

Cikin Raunin murya na nuna kaina ina fadin"Baka taba sani ba fa kace Saifudden..?

Kai Tsaye yace"Yes..Do i know u..?

Ya fada cikin wani irin Zati da Haiba Sai kwarjininsa ya fito Muhibba ta Rude Tunanin ta yadda abokinta Saifudeen zai ce wai bai santa ba kanta ta kara nunawa tana Fadin"Ni ce fa..Muhibba..MUHI..!

MUHI dinka ce fa SAIFF"
Kallonta yayi na wani Lokaci kafin kawai ya kada kai Lokaci daya yana Fadin"Stay away from me..I dont know u..!

Daga haka ya taso daga wajen Tim da Bama suka Rufamai baya Sani da Ransa ya gama baci yasha gabansa Cikin bacin rai yace"Ashe kai baka san Darajan dan adam ba..?

Ko ma me tayi maka kayi mata wannan Tozarcin acikin mutane..?

Saifudden sai ya kasa mgana kawai ya Tsaya yana kallon Sani Bama da Tim suka sha gaban sani suka saka Hannu suna Turasa baya ammh bakinsa bai yi Shuru fadi yake"Nasan ko baka Haihu ba ai kana da kanne mata. insha Allahu yadda kaci Zarafin tawa kanwar kaima sai wani ya Tozarka taka kanwar.."
Sai waje yayi shuru,Tim ya daga hannu Zai naushi Sani Mujaheed ya kariso wajen ya hanasa Saifudeen kuma duk da kalaman Sani sun Dakesa bai tsaya ba tafiya ya farayi Cikin Sassarafa ya fice daga Hall din Tim da Bama suka Rufamai baya yana Fita Waje ya kaure da Hayaniya kowa na Fadin albarkacin bakinsa D.Musa ne yabi bayan Saifudden da Sauri shi da Uncle James Mujaheed wajen su Muhibba ya tsaya shi da Sadiya dake kuka tun Mganar sani jikinta ya fara rawa,Meyasa Hamma yayi haka..?

In bata sanshi ba ai bazatace ta san shi ba..?

Gaban Muhibba Dake kuka ta Durkusa fadi take"Kiyi hakuri baiwar Allah..Sai kuma ta koma tana kallon Sani dake fadin"Muhibba tashi muje gida kin ga kin zama abun kallo anan wajem."
Sadiya ta hada hannayenta tana Fadin"Don Allah kuyi hakuri ku yafema Hamma na..!

Sai alokacin suka Dago suka kalleta sai da tayi mgana suka ga kamarsu sannan ai dazu ma an gabatar da ita a matsayin kanwar mai makarantan Anty Habiba ce kawai tace bakomai banda Sani da ya wani Hade rai Mujaheed kuma da Abban walid sukayi musabaha yana bashi Hakuri kan abun da ya faru Abban Walid yace bakomai komai ya wuce.

Dakyar Sani ya Daga Muhibba tana Dingishi sai kuka take Uncle Hafiz da Anty Jidda suna wajen ammh sun kasa mgana domin abun ne ya basu mamaki kafin kace me taro ya tashi Tuni mutane sun fara fita waje ya Hautsine Muhibba Fadi take"Sani da gaske nake yi saifudden nagani..Wlh ba Aljani bane mutum ne..Na rasa meyasa yace bai sanni ba.

Sani ya daka mata tsawa yana Fadin"Bashi bane..An ce miki bashi bane..Kada ki kara mgana anan wajen..."
Sai muhibba ta kara Sakin kuka Hawayenta haka suke faman zuba su Anty Khadija harsuna leke saboda suga komai dake faruwa ransu fari fes suna ta Dariya suna fadin Taga mai kyau mai kudi zata ce ta sanshi ai mganinta kenan sannan sun Dauki duk abunda ya faru a waya sun yi kuma alkwarin baza shi a duniya.

Har Haraban makarantar Sadiya da Mujaheed suka rabo muhibba da Sani ke riketa da ita Anty Jidda ta bama Anty Habiba Jakar Muhibba da Aword dinta yan Jarida da basu samu ngana da Saifudden ba sai suka dawo jin ta bakin Muhibba nan ma ba Dama Domin Sani ya rika yi musu ihu Dole suka ja baya Sadiya ta rike hannun Muhibba tana Fadin"Don Allah ki yafe ma Hamma na.."
Muhibba ta kalleta ammh ta kasa mgana Anty Habiba ce tace bakomai Muhajeed ya karbi Lambar Abban Walid kafin Asaka muhibba amotarsa su fice daga Haraban makarantar suma basu tsaya ba suka nufi tasu Motar ransu ba Dadi suma suka Fice Hanyar kaduna suka Dauka zukatansu na Amsa kuwwa da abubuwan da suka faru yau a wajen wannan taron...

Sadiya ta ja hanci kafin tace"Na rasa gane komai kainaa ya kulle..Yarinyar nan a ina ta san Hamma...?

Kana ji fa ta kira har sunansa Sannan Mganarta nada alamun sani ammh kuma shi ya nuna bai santa ba.

Muhajeed na Driving yace"Uhm ni kaina ammh abu daya na sani zan kuma yi shaidar Saif akan haka bai san wannan yarinyar ba.."
Bai santa ba ina da tabbaci kan hakan sai dai in da wani abu kuma da yayi Sabani acikin Lamarin nan."
Sadiya ta kallesa ya jinjina mata kai yana Fadin"Saifudden bashi da wulakanci..Bazai taba wulakantata in har ya santa ba."
Sadiya ta jinjina kai tana Fadin"Kuma Fa hakane..To ammh ita meyasa take nunawa kamar tun chan da Dadewa suka san juna..?

Muhajeed yace"Shi ne abunda ya bani mamaki nake kuma son na sani..Sannan baki ji wata mgana Datake gayama yan'uwanta ba..?

Cewa take yi kungani Saifudden Mutum ne ba ALJANI BA..!

To me hakan yake nufi..?

Na shiga rudi sosai Sadiya kan wannan Lamarin."
Sadiya ta yi kasake tana Tunani kafin tace"Ni kaina na rasa gane komai Sweety..!

Mujaheed yace"Shiyasa na karbi Lambar magidanci dake tare dasu Saboda naga Namijin saurayin nan ko yayanta ne ya Harzuka bazai bari mu samu wani bayani ba..Ammh Tabbas zan Bibiyi lamarin nan Ina son naji a ina aka haihu a ragaya.

Sadiya tace"Yauwa gwara da kayi hakan nima ina son na sake basu hakuri a madadin Hamma.

Daganan suka cigaba da Tattauna duk abunda ya faru har suka shiga garin kaduna sai dai a zuciyoyinsu abun ba"a cewa komai damuwa ne fal acikinta.

Bangaran su Muhibba kuwa gida suka Zarce Direct sai dai Inna ta gansu sun Shigo rike da Muhibba tana Faman dingishi a zuciyar Inna ta kawo cewa Auta Hatsari tayi ganin sai kuka take itama Inna ta fara kuka tana Fadin"Na shiga uku ni Fatima Fadi suka yi kan abun hawan ne sani..?

Ba wanda ya mata mgana sai da aka kai Muhibba kan gadon Inna Anty Habiba ta kalli Inna tana Fadin"Inna ba Hatsari bane..ta bugu ne a kugunta.."
Inna ta kara sakin Salati bata Di reba Anty Habiba tace"Inna ya Habibu na gida..?.
Chapter 37 · 0% Book details