← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 144

Sashe 16

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Al"amarin kamar almara kamar kuma acikin shirin Film sai dai kuma ba Fin bane kuma ba almara bane Da gasken ne na Fara ina girma sunan Saifuddeen na kara zama abakina Sannan ina haduwa dashi aduka inda yaso hakan,Sannan a hankali Shakuwa ta shiga Tsakanina da Mutanin da ban sanshi ba..?.bansan Daga ina yake ba..?

Bansan komai akansa ba sai sunansa sannan mafarin Haduwata dashi kangon gidanmu sannan yasha Fadamin nan ne gidansu shima..

Awannan yanayin su Inna basu Taba farga da hakan wata mtsala bace agareni sai da na fara girma na shiga matakin primary 5 alokacin ko makaranta na dawo da na ijiye jaka zan zauna na fara bama Inna Labarin Saifudeen sai inna ta kwabeni da cewa nayi mata shuru sannan nake iya kama bakina,Babanmu ne Allah ya jikansa da Gafara ya fara Lura da yawan labarin Saifudeen abakina yayi yawan da ya kamata sun san waye shi akwai wata rana da Inna ta bani Labarin mafarim da suka fara Dora Ayar Tambaya akan Waye wannan Saifuddeen din da Muhibba ke yawan ambata..?ta fadamin Ranar da Daddare duka muna Tsakar gida muna cin abinci Daman haka muke yi in Babanmu na gari,Ina kusa dashi muna cin Tuwon da Inna tayi Sani kuma na gefen Inna ya gama Fushin Babanmu ya fi sona shi kuma yace mai eh yaje wajen Innarsa.

Bayan mun gama cin abinci naji Baba na Fadin kwananan zai tada ginin nan ya Rufesa Inna tace ya kamata Ya Habibu na gefe yana Duba Littafansa na makaranta domin Lokacin yana SS2,yayinda Anty Habiba ke JSS3 Sani kuma Daman da aji Daya ya Tsereni Prinary 6 yake ni kuma Ina aji Biyar sannan duk gidammu kokarina irin na Ya Habibu ne duk da karaancin shekaruna ina da kwanyan Daukan abubuwa nan take basai an sha wahala ba.

Naji Babanmu na fadin Wajen Sani ne da Habibu ko bayan ransa suna da Inda Zasu zauna kamar yadda Mahaifinsu shima ya bar musu Fili mai girma achan Gaya,In naji am anbaci gaya Dadi nake ji Saboda ina son garin nataba zuwa sau biyu,Bakori na ma haka na ukun kuma muka kwana takwas achan Saboda Rasuwar Marikin Inna kawu.

Ammh duk rawan jiki na jin am ambaci gaya sai da na tsaya da Dariya jin Babamu zai gina gidansu Saifudeen batare da Lura da komai ba cikin yarintata na kallesa ina Fadin"La..Baba gidan su Saifuddeen ne fa chan..

Na fada ina nuna musu gabadayansu suka bi inda na nuna da kallo Cikin mamaki Baba yace"Auta ai nan ba gida bane kango ne ko baki gani ba..?

Sai idona ya ciko da hawaye Nace"A"a ba Kongo bane..nan ne gidansu Saifudeen ai anan na fara ganinsa sannan ya fadamin nan ne gidansu..

Don Allah Baba kada ka gina musu gida in ka gina ina zasu samu su zauna..?

Sai kuka kamar wacce aka Dake ta alokacin Inna ta fadamin gabadaya jikinsu sai da yayi sanyi Babammu ya kamani yana Lallashina Sani na gefe yayi Dariya yana kallona yace"BABA MUHIBBA ta hadu da Aljani..!

Sai Inna ta kwabe mai baki tana Fadin"Kai bama son shirmen banza Ina Aljanin..?

Sani ya bata rai kafin yace"To inna in ba Aljanu ba wake zama a kongo..?.

Ko malam Haruna na islamiyan mu ya Fadama na aljanu suna zama a kongo bola da ginin Daya Dade ba"a gina sa ba."
Wannan bayanin na Sani sai ya kara Haska musu wani abu a Daran dai Inna sai ta kara kwabar sani Baba kuma bai ce komai ba sai da mukayi barci wajen kwanciya,Sannan Baba yayi ma Inna mganar cewa Lamarin Muhibba abun dubawa ce,alokacin sai Inna bata wani Dauki mganar da wata manufa ba tace ma Babanmu yarintace in na girma zan Daina da wannan mganar sai Babanmu ya bar mganar Sai dai abun na ransa har alokacinn.

Sai dai maimakon abun ya yi Sauki sai yaci gaba Domin na fara wayan sanin wasu abubuwan Har abin ci ina zuwa dashi daga islamiya ko Boko nace Saifudeen ya siyamin zuwa Lokacin sai Inna ta fara tsorata da al"amarina,sannan kuma ranar da mukayi Common interest nazo gida Ina Murna,da tarin Sweet da Chaculate na nuna ma Inna Saifudeen ne ya bani kuma yace yana gaisheta Inna ta tsaya tana kallona ta kwace abun hannuna ta watsar sai na Fashe da kuka na zura da gudu na fita sai mukaci karo da Baba ya rikoni shi ya Dawo dani gida yana Lallashina ya kuma kwashe kayan kwalamana ya maido mini da kaya aranar Inna tayi fushi dani ko mgana nayi sai ta kwabani ta kuma gargade ni da in karajin sunan Saifudeen ko Labarin sa sai ta mun dukan kawo wuka,Tundaga Lokacin sai na Rage mganarsa ammh bawai domin na Daina ganinsa ba Saifuddeen shine Mutum na Farko bayan iyayena dana Fara Shakuwa dashi.

Ganin yadda Inna take Fushi Dani yasa Ranar na sameta na Fadamata tayi hakuri Sannan Saifudeen ma yace ta yafemai bashi da nufin Cutar dani,Sannan zai zo ya bata hakuri Inna ta kasa mgana ammh Saboda ta kara Tabbatar da Zarginta yasa tace yazo tana son ganinsa.

Sai dai me..?

Ina nuna ma Inna Saifudeen Inna tana fadin ita bata ga kowa ba,Tun daga Lokacin Inna ta tabbatar da cewa wannan Saifudeen din ba Mutum bane Aljani ne Inna ta Rude ta kamani ta Rumgume tana kuka Tana Fadin"Bawan Allah ka yi wa girman Allah in kai musulmi ne ka kyalemin yarinya kada ka Cutar da ita.

Ina ganin Sanda Saifuddeen ya tashi Daga gaban Inna yana sharan hawaye ya fita na bisa Ina kiran sunansa Inna ta kamani ta shigar dani daki ta kulle ina kuka,tana kuka agabana ta Kira Baba waya tana kuka tace yazo gida ba Lafiya Dayake yana gari yana Dawowa ta sanar dashi komai ta Dora da Cewa"Baban Habibu na yarda wlh Muhibba gamo da aljani tayi..!

Anema mata mgani kafin ya Cutar da ita.

Da wannan Shawaran Baba ya yarda Inna ta Kira Babani ta fadamata ita tace azo dani Bakori akwai wani mai bada mganin gane gane,washegari kuma tun da Safe muka Dauki Hanyar Bakori,kwanammu Hudu muka Dawo an kaini wajen wani malamin adddinin musulunci Bafullatani ne shi yace Aljani ne ke tare dani Sannan ya Budemin ido ina ganinsa ta Sufar Mutanen dayake zuwarmin sannan ya Sanar dasu Inna tun ina karama yake Tare dani sannan so na yake aurena yake da shirin yi ba domin sun zo da wuri ba da mgana ta kare Inna nata kuka Ni kuma duk raina ya baci za"a Rabani da abokina Saifudeen
Ya bada mangunguna har da na Turare tun achan Babani da Inna suka Faramin ko da zan yi kukan jini sai sunyimin Inna har da Duka take hadamim da muka Dawo gida Inna ta Sanar dasu Baba yadda sukayi da malamin Hankalin Baba da yan"uwana ya tashi harta Sani da bama Shiri Faruwar haka yasa Baba ya Tada gini aka Rufe Dakunan da Kwano Ranar na Dinga kuka ina Fadin an tashi gidansu Saifudeen.

Daga karshe duka naci hannun Innarmu,Daga Lokacin da Inna take min amfani da mangunguna sai na koma Shuru shuru sabanin abaya da nike da yawan mgana da Surutu labarin Saifudden kuma kamar anyi Ruwa an Dauke sai hankalimsu su Inna ya kwanta suna Tunanin komai ya kare ashe wasa farin girki.

Tafiyar mu Gaya alokacin sakamakon Faduwar da Hajiya Tafisu tayi a Bandaki ne kafarta ta gulle shikenan mafarin ciwon kafarta mukaje gaisheta ni da Inna da Baba Lokacin ban fara zuwa makaranta ba su Ya Habibu kuma suna gida Saboda makaranta alokacin Alhaji Sunusi abokin Baba ya Dawo nan gaya da Zama tun bayan fadan da ya gudana agarin Bungudu da Fulanin mazauna garin da Hausawa,kan Shanaye na Cinye amfanin gona to anyi Fada sosai sannan ga matsalan yan boko Haram da masu garkuwa da Mutane.
a wanchan Lokacin dayawn yan garin sun sauya sheka.

Shima nan ya dawo ya siya gida da Taimakon Babanmu suka Dawo shi da Iyalansa Kannensa sun yi Aure Daya tana Kano Daya tana kaduna.

To bayan mun kwana Daya mun Dawo ne washegari bakina kamar an Budesa na Fadama Inna naga Saifudden a gidan su Baba da mukaje Gaya sai inna ta Rude suna Murna ya rabu dani ashe lambo yayi Inna tayi ta tambaya na ko yayimin mgana nace mata mun sha Hira har abun Da'di ya kawomin Inna ta zabura tace naci nace mata sosai ma.

Sai inna ta fara salati Baba na Dawowa ta Fadamai kuma yace ta Kira Babani,tako kirata itama tace Inna ta sake Dawo dani haka kuwa akayi muka koma bakori wajen Mallam Dan Fulani ya sake Dubani yace ai Sona yake yi kuma Sai anyi Da Gaske zai rabu dani,sannan ya Bude min ido da kwakwalwata in su inna basu Mike tsaye ba har Abada bazan taba aure ba Hankali tashe muka Dawo Zaria da Sabbin mangungunar daya sake bamu Inna ta cigaba da min amfani dashi,Wannan Dalilin shi yayimin Tsaikon bata Shekara Daya kafin na shiga makaranta.

Awannan shekarar komai ya Lafa na daina Zencen Saifudeeen sannan na Daina ganinsa saboda Damuwa har Ciwo na kwanta,Daga baya naji Sauki Baba yamin Rigistration na koma makaranta Jss1 na cigaba da karatu Cikin Nasara Lokacin Sani har yakai Jss3 Ya Habibu kuma yana Abu zaria yana karantar Kasuwanci,Anty Habiba kuma sume wadanda zasu gama wannan shekarar.

Muna jarabawar Zango karatu na karshe da zamu shiga Jss2 Ranar na Fadi a makaranta nima bansan me ya Faru ba sai gani nayi an dawo Dani Daga gida,kuma ban yi alamun na Aljanu ba to bayan wannan na sake wani a Islamiya wanda Malamin mu mallam Haruna da kanshi yazo gida ya samu Baba da Inna yayi musu bayani akaina..

Mallam Haruna malami ne sosai sannan yana bada mganin junnu In dai kina da Shafarsu daya gani zai gane,Shi yake fada ma su Inna akwai aljanin Dake Bibiyata kuma Aljanin Basarake ne,sannan kuma musulmi me sai dai bai sani ba ko mai cutarwa ne ko akasasin haka..?
Chapter 16 · 0% Book details