Sashe 50
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun bai yi mgana ba Saifudeen ya Fahimci inda ya dosa Hannu kawai ya Dagamai bai kara mgana ba Datti da Salamatu suka yi gum sun kasa mgana,Sanyin yayi yawa har yana Ratsasu Salamatu ta fara rufe jikinta da mayafi ta fara takura shi kanshi Datti sanyin yayi mai yawa Cikin wani yanayi yace"Saif don Allah a rage karfin A.C din nan sanyi yayi yawa sannan ka ga salaamatu ma tana rawan sanyi.."
Saifudden na jinsa bai ce komai ba Saboda shi kwata kwata bayajin Sanyin sai zafin,Datti da yaga yayi banza dashi sai ya kama kansa bai kara mgana ba sun dauki Hanya sun fara Nisa Saifudden yasa Bama ya Tsayar da Mota da sauri ya fita ya koma gaban mota bayan yace ma Tim ya koma baya,Haka ko akayi sannan suka cigaba da Tafiya sai a Lokacin Saifudeen yaji sa ya dawo daidai Sai kuma yaji ya fara jin Sanyi Sai ya saka Bama ya Rage A.c din ya kaita Lambar karshe sai alokacin Salamatu ta dawo Daidai da Farko Ta tsorata sannan ga Uban sanyi sai gayen da aka kira da Saifudeen ya fara bata tsoro kamar wani mai aljanu.
Sun tsaya a hanya sun yi sallar azahar sannan aka sissiya lemuka da Nama banda Saifudeen da ko Ruwa da Datti ya basa yace baya sha Salamatu dai Malatina tsha kawai naman kuma ta saka ajaka saboda ta kasa sakewa da Farko tana ta iyayi sai daga baya Ta Fahimci iyayinta bazai taba Tasiri anan ba Domin yayi mata Nisan da kafin ta kamosa ta sha wahala.
Kafin La"asar suka isa gaya Lokacin da Moticin suka ci Taya kofar gidan Kawu Yara suka kwashi gudu cikin gida suna ga Amarya nan ta iso daman sun san sun taso tun dazu sai ga Mata suna ta fitowa tarban Amarya Cikin su Harda Sadiya,Saifudeen dai su Datti na sauka yace ma su Bama su wuce akwai Wani Hotel a garin na Gaya yakan sauka anan in kwana ta kamasa agarin nan yaje ya kama Daki yayi wanka yayi sallar ya koma ya kwanta bayansa duk ya kage ga yunwa yana ji ammh bai Damu ba Saboda bashi da inda ya aminta dashi a garin nan da zai ci abinci sai gidan kawu kuma ana Biki mata sun yi yawa Sosai shiyasa ya Hakura.
Baisan duk Bidirin da akayi ba Mujaheed nata kiran wayarsa bai Sani ba yana barcin Asaran daya zame mai jiki bai tashi ba sai bayan mangariba ya sake yin wanka yayi salla,lokacin ana ta sallar Isha"i yasa ya mike ya kawo ta sama sama kamar yadda ya saba kananun kaya ya saka Bakin wando da riga fara mai Gajeren Hannu Cikinsa har ya Murde Saboda yunwa har jiri yake gani sai da ya Dauki Wayarsa Sannan yaga Kiran Mujaheed bai bi ta kansa ba ya Dauki karamar Wayarsa sauran kuma ya barsu nan ya fita su Bama na ganinsa suka taso ya shiga mota suka fice Daga Haraban Hotel din.
Gidan kawu ya koma kofar gidan cike da yara suna ta wasa saboda Zirga Zirgan Jama"a get din yana wangale ne sannan ba wuta akwai Duhu dayake Wata batayi nisa ba.
Wayarsa ya Dauki ya dinga kiran Sadiya bata Daga ba Har Ummi ya Kirats itama bai sameta ba Dole kanwar naki ya Fito daga Motar zuwa Cikin Haraban gidan sai faman Dubawa yake yi ko zai ga Cikin yaran nan su laala sai dai bai gansu ba.
Shahada yayi ya nufi kofar da zata Sadashi da Cikin Falon gidan ko zai samu wanda zai kiramai Sadiya.
Ya kawo kansa wajen kofar kenan bai kunna Fitila ba da Hasken wayarsa yake ganin inda yake takawa Ita kuma Muhibba ita da Fati da Sadiya ta rakosu Tun bayan mangariba suka zo Dayake gobe Bakori zasu tafi tun Safe kuma agoben zasu koma zaria Inna dai tana nan ba gobe zata koma ba.
Kwata kwata basu gansa ba Muhibba ta Duka tana saka Takalminta mai igiya ne Ta Dago kenan taji ta Bangaji Mutum har Hannunta da nashi suna Gogan Juna Da sai da dukkansu sukaji wani irin Zir ya ratsasu da Sauri Saifudeen yaja baya gabansa na Fadi ko bai san ko wacece ba zai iya tuna wannan yanayin da a wajen mace D'aya ya Taba jinsa
Muhibba itama baya taja tana Fadin"Subhanallah..!
Sadiya dake bayansu tace"Sannu badai Tuntube kikayi ba.?
Nepa basu kyauta ba sun Dauke wuta sannan kuma gen ance yaki tashi kwata kwata."
Fati ce tace"Karo sukayi da wani inaga."
Sadiya tace"Wani..?Lokaci daya Tana Fadin"Muhibba Haska wayarki na bar tawa a dakin Mama zuwaira."
Fati ce waya ke hannunta ta Muhibba tana jaka ita ta kunna wayar tata Karaf kuma sai ta hasken Saifudeen daya juya zai bar wajen keyarsa Sadiya ta Hanga ta daga murya da Sauri Tana Fadin"Hamma.!
Cak ya tsaya kafin ya Juyo Daidai Lokacin da Nepa suka maido wuta Haske ya gauraye wajen yara suka Dauki Shewa suna Fadin Nepa..!
Ido Hudu suka Hada da Muhibba data Dago suna kallon juna atare gabansu ya fadi Ras!Saurin kauda kanta tayi Fati ta fito tana Fadin"Muje Muhibba Dare yayi..!"
Sai ta kasa ma fitowa Sadiya kuma wajensa ta Nufa tana Fadin"Hamma ina ka shiga da kuka dawo..?
Kai tsaye yace"Ina nan..ina kika bar wayarki..?
Tace"Dakin mama zuwaira."
Kafin yayi mgana Muhibba ta fito Tana gyara mayafin kanta sanye take da less Riga da sikat Sai mayafinta Sadiya ta kalleta tana Fadin"Har zaku Tafi Muhibba..?
Aransa ya maimaita MUHIBBA..!
daman yasan itace..Itace kadai in ya ganta gabansa ke fadi sannan in Jikinsa ya hadu da nata yake tsintar kansa Cikin wani yanayin da baitaba Samun kansa aciki ba.
Saboda Nauyi baki Fati ce ta amsa mata mganar Sadiya ta juya tana Fadin"Hamma baka gane Muhibba ba ko..?
Cikin mamakinta kai Tsaye yace"Na ganeta.."
Saboda ai bazai taba mantawa da ita ba Sadiya tayi dariya tana Fadin"Muhibba ku gaisa da Hamma.
Muhibba ta kallesa shima ya kalleta Cikin wani yanayi tace"Ina yini.
Kauda kai yayi kafin yace"Lafiya..!
Bata tsaya ba tayi gaba tana fadin"Adda mun tafi.
Sadiya ta bisu tana fadin"Bari na taka musu nan kofar gida Hamma.
Bai ce mata komai ba ya bisu da kallo yana kallo sukayi sallama da zasu fita ta Juyo ta kara kallonsa shima sai ya kalleta abun mamaki sai yaga ta mai Mirmishi shima bai san sanda ya maida mata martanin mirmishin nata ba sai da yaji mganar Sadiya
tana Fadin"Hamma kai da wa ye kake mirmishi..?
Sai alokacin yasan abunda ya aikata sai yayi saurin gimtse fuska,ya kalleta kafin yace"Addata yunwa nake ji ki samamin abun zan ci."
Sadiya tace"Hamma ina ta nemanka Ni nayi muku girkin Tarba fa..Nasa ka Sweeety ya kiraka baka daga ba sun kwashi abinci sun tafi gidan Hakimi suci."
Saifudeen yace"Ni dai ki samanin abun da zan ci."
Sadiya tace"To ina zaka ci..?
FALON kawu ma na cike da mata"
Tafiya ya farayi yana fadin"Mota."
Daga haka ya wuce ta rakasa da kallo kafin ta girgiza kai kawai ta koma Cikin Gida Makullin Store ta amsa wajen Umma babba ta bude Ta dauko Daya ta Fere ta wanke ta Dora mai Sai ta yi blanding din kayan Miya ta yi mai miyar souces kadan tayi Dadi,Ta kwashe mishi cikin Kananun Filet ta Hada mai ruwa mai sanyi ta yi Lullube ta Fita har mota ta kai mai ya amsa yana saka mata albarka kamar yadda ya saba bata koma cikin Gida ba motar ta shiga yana ci suna Hira sai da ya gama ta koma Cikin gida da kwanukan daya bata shi kuma ya koma Hotel din daya kama ya kwanta Saboda washegari yana so ya koma Kaduna akan Lokaci Tunda komai ya kare.
Basu hadu dasu Mujaheed,sai Washegari da safe da yayi shirin tafiya yazo sallama dasu kawu,suka hadu shi sai anjuma zasu mika Hanya Ummi ma aranar zasu koma Abuja, saboda aikinta da makarantar su Laala wasu bakin ma duk ranar zasu koma acikin Dakin Umma babba yaga Inna tazo har suka gaisa anan ma yake jin tana fadama Ummi su Muhibba tun safe suka Dauki Hanyar Bakori Ummi na fadin Zuwaira ta Fadamata Habibu yazo har gidan nan Jiya Lokacin suna Hanya basu kariso ba.
Bai jima ba ya fito kawu ne karshen sallamansu Inda ya rakasa da Nasihun daya saba yana bakin motarsa ne yaga fitowar kawayen Amarya Salamatu da wata kallo basu ishesa ba daman Datti suke nema kuma suna sallama ne Saifudden yana ganin sun Tunkarosu ya bashi Hannu sukayi musabaha Tim ya Bude mai Mota ya shiga kafin su kariso sun Wuce sai dai tashin kurarshi suka gani Salamatu tabi Motar da kallo Jikinta na karayin sanyi..
Saifudeen bai samu natsuwa ba sai da ya gansa a gidansa na kaduna Wanka kawai yayi ya kwanta yayi ta barci Sai Yamma ya tashi Ya hada tea yasha ya rama Salolin dake kansa Sannan ya Kira Ummi tace yanzu suka Sauka tare da su Sadiya suka zo kaduna Daganan suka hau Motar Abuja.
Saifudeen yace da sun kirasa da su Bama sun kai su Ummi tace ba Damuwa Tunda sun sauka Lafiya Ummi nata godiya kawu yace Ya bashi 50k Dattin ma ya saka mai 50k gudummuwa.
Washegari Mondaya Tun 8 ya shiga Office sha daya na rana suna da ganawa da gwamna shiyasa bai bata Lokaci ba Duk da har Lokacin gajiyar bawai ta sake sa bane a yayin da ita kuma Muhibba tana makaranta tana Fama da Dalibai aranar Inna na Gaya suka barta jiya sai dare suka iso Zaria Gidan Anty Habiba ta wuce Anty Zeenatu daman tun jiya tabi yo mijinta suka koma gida.
*******
Bayan sati daya da gama sha"anin gidan kawu Amarya d
a ango tun Ranar talata suka wuce chan Delta ita da yan"uwanta kawayenta daganan suka kama kansu Salamatu kaduna tayi gidan yayarta suma Dangin nata kwana daya sukayi bayan sun gama siyan abunda zasu siya mata.
Washegari suka kama Hanyar Bauchi sai fatan Allah ya bada zaman lafiya.
Iya sai daga baya ma tasan da Bikin Abakin Ummi da sukayi waya ta Dinga Fadan bata maidata bakin komai ba shiyasa bata Fada mata ba.