← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 144

Sashe 127

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kema kin san baki kyauta ba.."
Sai iya ta fashe da kuka tana Fadin"Zo ki fice min daga gida Atika
Daga ke har mara tarbiyan ya"yanki kar na kara ganin kafar wani acikin gidan nan kuma Sailuba in dai ina Raye bazata ko kara rabar arzikin Zaliha ba Shegiyar yarinya mai kama da tsofaffi"
Goggo Atika bata bi ta kan Iya ba ta Fice akabar Iya nata jaraba ta na kuka Inna talatu dai bata fito ba Gaje ce Matar Baffa Hayatu ta fito ta na bata baki ita dai Hankalinta bai kwanta ba sai da Rana da Ummi ta kirata tana Godiyam sako Majeeda ta iso Lafiya har gida Gaddafi ya kawota sai da yaci abinci ya huta Ummi ta basa kudin mota ya karisa Sulaja.

Hankalim Inna talatu ya kwanta jin Majeeda ta isa lafiya da Daddare da Baffa Hashimu ya shigo ta fadamai Majeeda ta isa lafiya yayi hamdala Da bakinsa yake fada masa Iya ta fadamai irin dibar albarkar da Atika tayi mata ita da yarta Ita dai Inna Talatu Allah ya kyauta kawai tace bakinta kanin kafarta.

Majeeda kuma da ta dawo ta Fahimci su Laala suna baya baya da ita duk da sun yi murna da Dawowarta Ummi kuma ko a fuska bata nuna mata ba ta Shiga rawan jiki da su ita da Gaddafi sai bayan ya tafi ne ta shiga Daki tayi wanka ta sauya kaya Zeeha na Zaune saman Cafet ta Dukufa Tana Zane a Littafinta na Biology ita kuma Laala na Gugan Uniforman dinta.

Majeeda ta rasa ta ina zata fara sai ta kalli Laala tana Fadin"Laala ga na wa ki goge min..?

Zeeha tayi saurin cewa"Naki fa goggu ne ne kin manta wannan week din baki je School ba"?

Sai majeeda tace"Au hakane fa na manta"
Laala na jinsu batace kala ba tana Cigaba da guganta Sai majeeda ta kara Fadin"Laala na zo mana da gyadan shan gari fa"
Dayake suna son garin kwaki da Suga Musmman Ummi ke siyo musu in ta shiga kasuwa.

Laala ba sakewa a lamarin tace"Angode"
Ba Majeeda kadai taji wani iri ba Harda Zeeha sai da ta Dago Tana Fadin"Haba Laala why..?

Da Sauri Majeeda tace"kyaleta Zeeha ba Laifin ta ba ne nawa ne..Don Allah Laala ki yafemin kan abun da ya Faru ba Laifina ba ne sharrin Shedan ne"
Laala ta dago tana Hararanta kafin tace"Kin Dauki Lokacin kafin ki bni Hakuri maji"
Zeeha ta kwashe da Dariya tana Fadin"Finally..!

Laala ta Kashe Soket din da ta ke guga ta mike tana Fadin"finally Finally yau dai maji ta Fahimci Shedan ne ya Gurbata Tunaninta"
Dariya suka saka gabadayan su Kafin Laala tace"Ni ban rike ki a raina ba Maji..Ko zeeha..?

Zeeha tace"Wlh mun yi kewarki Maji plz karki kara tafiya ki barmu"
Sai hawaye ya ciko idon Majeeda ta mike ta Rumgume Laala tana Fadin"am sorry Sisy.'
Laala ta riketa tana fadin"Let it be mana Maji"
Zeeha ta mike tana Fadin"Dis is Cheating"
Da Sauri Majeeda ta jawo ta da Hannu daya suka Taru suka Rumgume juna suna Dariya Ummi na tsaye a bakin kofa Tana kallon su taji dadi aranta Sai da ta Murmusa kafin tace"To in kun gama Rumgume Rumgumen kuzo mu ci abinci"
Sai Lokacin suka ga Ummi da laala da zeeha gudu suka Nufeta suka Fada jikinta suna Fadin"Ummin mu"
Ummi na Dariya ta rike su ta Dago tana kallon majeeda da kunya ya Hanata karisowa ta kira ta da Hannunta tana fadin"Come here my Dota..'
Da gudu majeeda ta karisa itama ta Fada jikinta ta Rugume su aranta tana mai Hamdala acikin ranta.

Daganan suka fita falo suka ci abinci nan da nan Falon ya kwace da Hira Laala sai bama Majeeda Labarin abunda ya faru bata nan ta ke yi Zeeha na Fadin laala kin cika Gulma Majeeda na tare mata,Ummi na gefe tana kallon su Annuri ya cika mata ciki Hamdala tayi afili domin Haduwar kan ya"yan ta yafi komai yi mata Dadi.

Sai zuwa Dare Majeeda ta Samu Ummi adaki tana waya sai da ta jira ta gama sannan ta Duka agabanta kamar tayi kuka tana bata Hakuri Ummi ta saka Hannu ta Dagota ta zaunar da ita agefenta ta saka Hannu ta goge mata Hawayen da suka gangaro mata Lokaci daya tana Fadin"kamar yadda nake fatan Laala ko Zeeha tayi aure gidan da ake son ta ake Daraja ta haka nake miki wannan Fatan Majeeda..Yau in Yaro ya nuna yana Ra"ayin ki da kan shi sai nafi kowa Murna ammh a yanzu bazan yarda ki Cusa kanki ko mj cusa mai ke ba Majeeda ki bari akwai Lokacin da bama yaro ba..Har wanda ya fisa ma sai kin ja mai aji ke ko Takaicin Sakin Wulakacin da yayi miki a farko baki ji ba..?

Ai bazai same ki a arha ba sai ya wahala in kuma muka samu wanda ya Fisa wlh basa zamu yi"
Sai ga Majeeda tana Dariya kamta na kass Ummi ma ta Dara tana fadin"Yauwa to daga yau bana so ki Sauya ma Yaro matsayi Daga Hamman ki kin ji ko Majeeda..?

Da Sauri majeeda tace"im sha Allah Ummi"
Ummi taji Dadi har sai da ta Nuna a saman Fuskarta kafin tace"Allah yayi muku albarka gabadayan ku"
Tun daga ranar Majeeda ta Dawo kamar baya daman Shedan ne da kuruciya tun da Inna Talatu ta ganar da ita shikenan komai ya fita kanta abu Daya ke gabanta yadda zata inganta Rayuwarta.

Wannan Hutun sun ce Gaya zasu je su yi Saboda Saudat ma chan zataje Ummi tace su yi fatan Allah ya kai su Lokacin in suna da rai da lafiya sai su je din.
******
*ZARIA*
Bayan sati biyu.

ASIBITIN CHIKA.

Sati biyun da Dr.Anandi ya Dibar mana har ya cika gashi mun dawo gabansa ni da Saifudden wannan karon a Duhu ya sani bayan ya gama yimin Tambayoyin da ya saba ni bansan yadda akayi ba muna tare da Saifudden da Dr.Anandi kawai sai gani nayi Duhu ko Tafin Hannuna bana iya gani sai tsoro ya kamani jikina ya fara kyarma na fara ja da baya ina kamkame jikina kiran sunan Saif nake yi da karfi Cikin Fitan Hayyaci jim bai amsa ba sai na rasa Hankalina na Duke a kasa na Fashe da kuka ina Fadin"Na shiga uku..Saif..Saif"
Kamar an tabani naji sai na kwalla kara ina fadin"Kiyi hakuri kada ki kasheni..Kada ki kasheni"
Idanuwana suna Runtse ne ina kuka jikina na rawa na Takure kaina waje daya sai naga Haske a idona Lokaci daya kuma naji an tabani ana kiran sunana Cikin tsoro na kara jan baya da Sauri naji Muryan Saif na fadin"Muhi."
"Muhi am here"
Jin muryan sa yasa na Bude ido ina ganinsa na mike na Fadamai ina kara Fashewa da kuka cikin kuka ina Fadin"Meyasa ka tafi ka barni.?

Meyasa ka saba alkwari bayan kace min kana tare dani bazaka taba barina ba..ka barni..Zata kasheni"
Yanayin yadda nake dukan kirjinsa ina kuka zaka tabbarar cewa bana cikin Hayyacina.

Kamkame ni yayi yana Shafa Kaina zuwa baya cikin sigar Lallashi yake fadin"Shii..Am herre babu abunda zai Faru dake muhi dita"
Dr.Anandi kuwa na zaune a mazauninsa yana kallon mu Lokaci Daya yana ta Rubuce Rubucen sa.

Sai da ya gama ne ya Dago yana kallon mu kafin yace"Plz Mr and Mrs Lere can u hv a sit..?

Ban yarda ya sakeni ba ina Rike da shi muka zauna,Dr.Anandi ya kalleni yadda duk na Firgice sai yayi mirmishi kafin yace"Mrs lere me kika gani da ya firgitata ki..?

Cikin Firgici nace"Na ganta..Wlh na ganta"
Sai Hawaye sharr Dr.Anandi yace"ba ita kika gani ba Mrs Lere"
Na fada miki wachan zuwan naki babu abunda kike gani a zahiri
ki Dauke sa mafarki ne..Shi kuma mafarki ai kin tabbatar min ba Gaskiya ba ne ko..?

Sai na gyada mai kafinn nace"Ammh sai naga kamar na ganta..Naji ta tabani"
Dr.Anandi ya gyara zama glasa dinsa yana fadin""Yauwa gwara da kikace kama..To ki dauka kamar haka kika gani..Yanzu zam maida ki cikin wannan Duhun ki sani ko kin ga kamar kin ganta kada kiji tsoro ki Sarrafa kanki Tunaninki da kwakwalwarki ta gayamiki ba Zahiri ba ne mafarki ne shi kuma mafarki ba Gaskiya ba ne karya ne..In kika ji ta tabaki ki Dake..Mganata ta Dawo miki Kwakwalwarki ta hasko miki ba gaskiya ba ne karya ne"
Jinjina ma kai nake yi ammh Cikin Tsoro Dakyar na yarda Saifudden ya Sakeni ina kallonsa ina hawaye ya Shafa kaina yana Fadin"Ina tare dake..Karki damu"
Sai da ya sake ni Duhu ya mamaye Office din Tsoron da bana so ya kamani Shi ya shige ni ko Tafin Hannuna fa bana gani Sai na fara kuka ina Juye juye wlh ina ganinta acikin Duhun nan na fara da ja da baya ina kuka ina ihun kiran sunan Saif ammh ban gansa ba kuma ban ji mganar sa ba kamar Daga sama naji Muryan Dr.Anandi Lokaci daya yana Fadin"Mrs Lere zaki iya Sarrafa Tsoron ki.Ki sani ba gaskiya ba ne
Ba zahiri ba ne"
Sai kuma naji shuru na Dafe kaina nayi kasa ina jijjiga jikina ina Fadin"Hakane ba gaskiya ba ne..Karya ne ba Zahiri ba ne"
Sai naji kamar an tabani na zabura sai naji na kume da Bango na saki kara ina fadin"Ita..ita ce gata nan"
Sai kuma naji kamar kaina na amsa mganar Dr.Anandi cewa ba gaskiya ba ne Ba zahiri ba ne sai na Tsaya kaina dafe na Runtse ido na ina makyarkyata jikina na rawa ina sauke Numfashi A hankali na fara Bude ido na ina Bin Duhun Dakin da kallo Duk da ina kamar ina ganinta haka na Daure ban kara ihu ba kuma ban yi wani motsi ba sai dai jikina nata uban rawa kamar walkiya sai kuma Haske ya kawo na hango Saifudden da Dr.Anandi a gefe chan suna kallo na.
Chapter 127 · 0% Book details