Sashe 60
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saifudeen ya rasa wa zai kira yace ya turamai Layin Muhibba sam tunanin sa bai kawo masa Adda ba sai ya Kira Mujaheed wanda Tun da watan Bikin ya kama basu kara waya ba,ballatana su hadu yana chan shi da Mudansir suke gudanar da shirin su sai Datti da Suke Taba juna ta waya ko Tunanin jiransa ma basu yi ba.
Mamaki da Takaici sun kama Mujaheed sanda Saifuddeen ke Tambayansa Lambar Muhibba baki ya Tabe kafin yace"Kai ammh ka bala"in raina min wayau Man..Ni ne zaka kira kana tambayata Lambar wayar matarka nan da kwanaki kadan..?
Saifudden ya dakuna Fuska kamar yana ganinsa kafin yace"Zaka bani ko bazaka bani ba..?
Kai tsaye yace"Ba ni dashi..Kai ba"a samu a wurinka ba sai a wuri na..?
Ina ruwan kaza a acin danko..?
Bai jira cewar sa ba ya datse kiran,kansa ya Dafe aransa yana Tunanin da yasan haka auran nan zai zo masa da bai taba Furta ma kansa ba wannan ai wahala ce.
Kamar an mai wahayi ya Tuna da Sadiya ita ya kira yace ta turo Masa Lambar Muhibba tun da taji haka tasan kwanan zence saboda ai sun yi mgana da Ummi,kai tsaye ta Turamai Saboda bai da abunda zai ce mata in ya Kira yasa ya Rattaba mata address din ta Test massages a kasan Sakon ya Saka sunansa.
"*DR.SAIFUDEEN CONEL.SALAHUDEEN LERE.*
Muhibba bata ga sakon alokacin ba, sai Daga baya Lokacin Dare yayi ana ta kiran sallar mangariba abun sai ma ya bata Dariya to ba dole ba ta fara Tunanin Al'amarin na wasa ne ammh zuwa yanzu tasan komai dake Faruwa da gaske ne Anty Habiba ta Dankama wayar bata re da tayi mata karin bayani ba ita kuma tana gani ta gane sai ta gayama Inna GRA ne ya kamata su je su duba gidan su gani kafin gobe su tafi da masu kayan gadajen, Goggo Naja tace hakan za"ayi Muhibba ko Tafiyar su bata sani ba suna Daki tare da Fati suna Hira ita ta taimaka wajen rage mata Damuwa.
Dayake anguwan ta Gra ta samu dashi ne sannan Gidajen su nada Tsari ta Lambar dake Rubuce na gidajen mai adaidatam yabi kuma kamar dan gari ne ya saba shigowa anguwan sai gasu har kofar gidan Sai dai Lokacin da suka Buga get din Junaidu ya leko suka gaisa sun mai bayani ammh kuma akwai Hakki mai gidan a kansa na Amana kuma shi bai ji ko Labarin Yallabai zai yi aure ba shiyasa yace musu yana zuwa ya koma gefe ya Daga wayarsa Kirar Tecno ya Kira Saifudden sai da yayi mai kira uku bai Daga ba yana shirin karawa sai ga Kiransa Daman yana da Lambarsa tunda mai gadin gidansa ne.
Bayan gaisuwa Junaidu ya mai bayanin Abun da su Anty Habiba suka ce Kansa ya Dafe dake saramai Tun dazu yana zaune kan darduma Dakyar ya iya sallar mangariba sama sama.
Cikin Nauyim baki yace Junaidu ya basu izini su shiga yasan da zuwan baki Junaidu ya Bude cikin murna yana Fadin"Allahu Akbar Yallabai aure zaka yi..?
Ko tsayawa kula tambayan Junaidu bai yi ba ya katse wayarsa yana jin Ransa na baci haka kurum shi dayake bai san yadda ake yi ba,Ya zata zasu je su ga gidan ne kaawai bai san ana wani Jere ba tunda shi yasan gidansa akwai kayan Gado da kujeru.
Sun shiga ko"ina na gidan kuma sun yaba ba wani gyara tunda a satin mai mai share share yazo yayi gyaran Gidan mai Dauke da Falo Biyu da Bedroom guda uku sai kitchen da Store sai wani korido mai kofa ta baya da zaka fita wajen Tankin ruwa da pampo inda mutum zai iya wanki ya shanya da Sauran Bukatu.
Sannan bedroom biyu suka samu a bude Cafet ne kadai aciki ba komai Dayan yana Rufe na megidan ne sai Falo guda daya shima Empty sai Cafet kawai Falon farko kadai ke da Jeren kujeru da Tv sai kichen shima ban da gas Cooker mai shidda sai kettle da kofuna na Tea bakomai aciki gidan dai komai yayi masha Allah baya Bukatar karin komai Tunda bai yi shekara da siyansa ba sai dai yadda suka ga komai na Rayuwar Namiji ne ganin yadda abubuwan gidan suka zama Daya daya.
Sun dawo sun fadama Inna Lokaci daya da Tsara yadda Jeren zai kasance,Anty Zeenatu tace Falon na Biyu a jerama Muhibba kujerunta da Kayan kallonta kitchen ba matsala tunda Babba ne sai bedroom din guda Biyu a jera mata Gadajenta shikenan Tsarin yayi kuma suma su Anty Habiba sun yi Na"am da shi.
Washegari Ina makaranta suka tafi yin Jerensu Har kuma na Dawo suna chan sai gabda sallar mangriba suka Dawo da Hotuna da Vedio gidan kala kala a wayar Anty Habiba tana gwada ma Inna ita kuma sai saka albarka take yi tana fadin"Allah yasa gidan zamanta ne.."
Su goggo Naja na amsawa da Ameen Fuskokinsu cikin Farinciki Anty Habiba ta kawo min wayar wai na gani na kauda kaina bana son gani Anty Zeenatu na Dariya tace"Kar ma ki kallah Auta ke da zamu kai ki mu baro..?Fati na gefe tace"Kallo kuwa har sai gaji da kallon gidan."
Hararanta nayi ban yi mgana ba Goggo Naja ta kalleni kafin tace"Ni naga autar ma sai faman ramewa take yi ne..?
Inna ta kalleni da gasken na rame tace"kyaleta kin san Auta ce duk zullimin auran."
Inna Firdausu ta amshe da Fadin"Aure kenan yakin mata Muhibba sai Hakuri da haka kowa ya saba."
Mganganun su kamar zai sakani Rauni yasa na bar Dakin na koma nawa Fati ta Biyoni tana faman bani Labarin gidan ni kaina nasan yan"uwana sun min kokari hatta su Baba surajo ba"a barsu a baya ba kudi suka dunkule suka bama Inna ban dai san ko nawa bane an yimin kaya na alfarma ko yar attijiri albarka kayan ciki kamar na mace Biyu ga Fridge dina guda biyu har da Frizer da Tv babu abunda basu siyamin ba,bani da bakin gode musu tun fara wannan Hidimar Ya Habibu da Anty Habiba basu yi sukuni ba Haka Innata duk dai Burinsu su aurar dani su cika wannan bangaran aure irin na kowacce mace yar gata sai na samu kaina da kuka ina gode musu acikin raina Harta Sani dake makaranta ko da yaushe cikin yimin waya yake yi duk da Shakiyancinsa ammh nasan ya Damu dani Fiye da yadda ban yi zato ba.
Washegari Talata su Goggo suka koma Gaya sai kuma ana gobe Biki Anty Habiba ma ta koma gidanta bayan ta ta dauki kaya kala goma cikin akwatin lefe zata kaima telan ta dayake min Dinki Bayan ta gaji da min korafin ban zabi kayan da zan saka ba nayi mata banza ta gaji ta zaba da kanta kayan da ban kallesu Sosai ba ammh nasan kayan na alfarma ne.
Har Biki na ya rage saura kwana Tara ban taba Fadama wani ko wata zan yi aure ba ko a makaranta islamiyan mu a gari suka ji dayake Inna ta raba alewar gayyata Anty zeenatu ma ta raba nata ita da yan gidansu ni ba katin barayin ango ko daya a Hannuna sai wanda Ya Habiba ya Buga nasa ya bani guda Hamsin ko akwai da wanda zan gayyata na dai amsa ne kawai ba domin zan yi amfani dasu ba Tun daga wannan Test din da angon nawa kamar yadda suke Fadi ban kara ji daga garesa ba ballatana na saka kaina asahun Amare kamar yadda su Anty Habiba ke Fadi.
A makaranta ina ta Dari Dari ina Fargaba ko Labari yaje musu sai dai ban ga alama ba,hakan yasa na Saki jikina kadan duk da nasan ko ba jima Labarin sai ya fita.
Ballatana da Anty Habiba ta Fadamin Abban Walid yace yaji Sanarwan Daurin auran agidan Radion Nageria Kaduna Abokinsa ya bada sanarwa Mujaheed,Sai dai kila Saboda ba ZARIA bane kuma ba kowa ke juran kamo tashar Nageria Kaduna ba,kila ba lalle su ji ba..
Bikin ya rage saura kwana Takwas Ranar al'hamis dayake jumma'ane Daurin auran kamar yadda na gani a kati za"a daura auren ne a masallacin gidan Hakimi,dawowata makaranta kenan agajiye na iske Asma'u kanwar Abban Walid sai Aisha kanwar kawar Anty Habiba Maman Arfat na kongo Daman muna Mutumci dasu sosai sannan suna Tabani a waya suce ya Shurye shirye nace musu Oho ban sani ba.
Ba zuwan su bane ya bani mamaki ba A"a sai Tarin wasu Had'dad'un Katunan aurena da suka Zube a gaba na daga gani katin ba na kananan mutane bane kati ne na yan ubansu masu kyau da Burgewa da sai da nima suka Burgeni na Bude na karanta Daga bangaran Ango da sunana baro Baro MUHIBBA BELLO MAIRAGO.
ban iya cewa komai ba sai dai ina kallonsu cikin mamaki ganin Haka yasa Asma"u ta faramin bayani.
"Ina gida kwana biyu da suka wuce aka kirani da bakuwar Lamba bayan na Dauka mun gaisa yace min sunansa Mujaheed shi abokin Mijin da zaki aure ne ya fadamin Anty Habiba ta bashi Lambata kan Hidiman Biki da abunda zamu Bukata ban yi mgana dashi ba sai da na kira Anty Habiba tamin bayanin komai tace kada mu Saurareki itama Sadiya kanwar Mijin naki ta kirata tana Fadamata Mijinta ya kiraki kin ce ke baki da wani shiri.
Sai alokacin Muhibba ta Tuna ya Kirata kan wani tsari gareta tace bata da wani Tsari shine ya biyo ta bayan Anty Habiba tana jin Asma"u na Fadin bashi da Lokacin jiya ya saka mata Card din a mota aka kawo mata Zaria ta karba sannan yanzu yana Jiranta ne ta fadamai me dame dame zasu Bukata su fadi kudin ya Tura musu.
Muhibba ta mele baki kawai batayi mgana ba Aisha tace"Bama son wulakanci yana fa jiran mu ne."
Muhibba ta bude baki kamar bata so kafin tace"Ni fa bazan yi komai ba ku kyaleni."
Asma"u tace"Ko yar Walima..?