Sashe 20
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iya tace"To ai shikenan zamu je dakai Hayatu yau ko gobe duk abunda kenan zakaji Saifu Allah dai ya Dubeka ya warware maka ita kuma wannan Aljanar data aureka sai an yi mana Hisabi da ita Ranar gobe kiyama Tunda ta zama azzaaluma banda zalunci ina ta taba jin Aure Tsakanin Mutum da jinsu aljanu."
Ba wanda dai yace ma Iya komai sai Fada take Saifuddeen ya karkace ya Zaro Sabbin kudi yan Dubu Bandir Biyu a aljihun sa ya sauke ma iya a gabanta sannan ya kara zaro Wasu Biyu ya sauke mata sannan ya karo Daya duka ya Sauke agabanta yana Fadin"Gashi nan iya naku ne..Wannan kuma in kunje wajen mai mganin sai ku basa.."
Iya tana ta saka albarka har da Goggo Atka da addu"an albarka ta bisa domin Saifuddeen ba daga nan ba baya zuwa ya barsu haka ita kuwa Iya Fadi take"Allah sarki shi kanshi Laluran ta Dameshi Zaliha ce ba wayau ita da ya kamata ma ta fara sani."
Sai jin dadi take ganin ya bada kudi har da na wajen mallam nan kuwa bata san bagarda tunaninsu yayi na kada a kara acusamai auran yarinyar nan.
Bai jima ba yayi musu sallama ya Fito Daga Dakin gabda zai bar gidan Daga shashen Baffa Hashimu ya hango yarinya tana lekensa tana kuka yana ji wata mata tana fadin"Ke dai majeeda anyi mara zuciya..Yaron da yayi miki sakin wulakanci kike leke kina kuka..?
Sai ya kara kallonta domin shi ko kashe shi za"ayi ai bazai taba nuna Majeeda ba, yana gani uwar ta janye ta tana Fada Dariya ta kamasa sai dai ya kanne bai bar gidan ba sai da yabi yaran gidam da kudi har matan su Baffa ma sun samu rabonsu.
Chan waje ma mutane suna ta Jiransa nan dai ya bata Lokaci sai wajen 12 ya bar garin na lere,Sau da Dama Iya tasha Fadamai Mahaifinsa ya gado shima in yazo Lere mutane basa yankewa a kofar gidansu mutum ne mai kyauta da kyawawan zuciya shiyasa shima yake kokarin kwatatanwa
Bai sauke numfashi ba sai da suka bar garin Lere suka Dauki hanyar Abuja Tim ke tuka Motar Bama na zaune gefen Direba shi kuma yana gidan baya yana Sauke Numfashi sai alokacin ya murmusa.
Afili ya furta"Nagama da wannan yaki ..Saura guda daya dake jira na a Abuja.
Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke
*Janafty*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*ABUJA*.
_Area:APO._
Ya shigo anguwar tasu ta Apo dake garin Abuja Har an riga anyi sallar azahar domin daya duba agogon Fatan Dake hannunsa 1:54pm na rana sai bai karisa gida ba sai da ya tsaya nan wani babban masallaci dake cikin anguwan yayi sallah sannan suka karisa.
Megadin dake gadin gidan Ummi na Abuja Musulmi ne ammh bayarbene,Mai suna Ibrahim,yana jin Hon din mota bai kawo ma ransa ma Yallabai bane ya zata Hajiya ce da tafita Dazu bada jumawa ba,sai dai yana Bude karamar kofar ya leka sai yaga bakar prado din Saifudden da Tim agidan gaba yana Tuki jikinsa na rawa bakinsa kamar zai tsage ya koma Ciki da Sauri ya wangale get din Tim ya sulala da motar a kyakyawan dan karamin Tsakar gidan na Ummi.
Tunda yaga bai ga motar ta ba Jikinsa ya basa bata gida,kuma yasan ba inda Zataje wanda ya wuce wajen aiki meyasa ma bai yi tunanin Ummi bata gida ba..?Koda yake bai yi Tunanin zata shiga wajen aiki ba yau ganin yau Lahadi ne sai dai ya manta da yanayin aikin na Ummi a koda yaushe bata da Ranar Hutawa.
Kafin ma Bama ya fito ya Bude mai murfin Mota Ibrahim ya rugo ya Bude mai Cikin Cukurkudaddiyar Hausan sa ya duka har kasa yana Gaisheshi Saifudeen daya fito Daga Mota yana gyara Rigarsa ya kalli Ibarhim cikin wani yanayi kafin yasa Hannu ya Dagosa bai ce mai komai ba illah Buga kafadarsa da yayi sau biyu Lokaci daya yana mai sakarmai kayattacen Mirmishi,kafin ya wuce zuwa Kofar glass din da zata sadashi da Falon Ummi.
Bama yana Biye dashi da wayayoyinsa sai Tab dinsa yayin da Tim suka sarke hannu da Ibrahim suna mgana,Dayake shima Bayarbe ne.
Zaune suke su ukun a cikin Tsararan Falon,Gidan gabadaya bashi da wani Girma shiyasa har Falon ba wani mai Girma bane samun gida mai girma agarin Abuja ai sai wani kusa a gwannati duk da shima Saifudden din wani ne a gwamnatin kaduna ammh kuma sanda ya siya ma Ummi wannan gidan bai gaji komai ba sannan shi din ba wani bane alokacin kuma yadda Ummi ta saba da inda take baya Tunanin zata yarda da Tsarin sauya mata wajen zama.
Kwata kwata basu ji shigowarsa Falon ba ballatana sallaman da yayi Laala ce Zaune saman kujera mai zaman mutun biyu Ipad ce a Hannunta tana Buga game Saudat na kan mai zaman mutum Uku ta yi matashi da Cussions din kujeran yayin da Zeeha ke kwance kan Cafet tayi matashi da kanta jikin kujeran da Saudat ke kwance Talabijn ne a kunne Cikin tashar Mbc2 sun kuma dan kure kara kadan shiyasa basu ji sallamar Hamman nasu ba.
Laala da Hankalinta ke kan abunda take yi ta tsinkayi muryan Saudat na Fadin"Zeeha wai Hamma ko ya kira Ummi Tunda muka dawo..?
Zeeha da Romot ke hannunta tana ta Sauye sauyen tasha,Tace"Anya..? bai kira ba..Kusan fa Hamma ba yanzu ba sai Ummi ta gama hucewa sannan zaku gansa.
Tafada tana gyara kwanciyarta,Dayake sun gama Jsce suna jiran Wani term ne su shiga SS1 itama haka Saudat dayake tare suke Tafiya shiyasa ma bata koma kano ba ta biyo Ummi Abuja saboda su Zeeha.
Laala dake game dinta tayi karaf tace"Ai Hamma bazai taba zama da mata ba..Na sha fada muku Aljannah Zanka"dadiya ta auresa shiyasa yake sakin su Majeeda a washegarin auran su ya maidasu Kananun zawarawa.
Saudat na dariya tace"Ke dillah Sakin Wawa ake cewa..!"
Gabadayansu suka kwashe da Dariya har Saudat na Dagowa suka tafa da Zeeha Laala ta Dago da niyar mgana suka Hada kyakyawan kallo da Saifudeen dake Tsaye hannayensa Harde a kirjinsa ga Bama a bayansa Dauke da Wayoyinsa.
Ai sai Laala taji bakinta ya kafe ta kasa mgana Saudat da Zeeha basu gansa ba shiyasa har Saudat tana Fadin"A islamiyarmu fa Ya sayyadimmu ya fadamana Aljanu mata in sukaga Namiji yayi musu suna shiga jikinsa su auresa kamar yadda Mazan su suke auran mata jinsin mutane.
Zeeha tace"To daman mana su Ummi ne sukaki yarda..ammh ai mganar Laala akwai kamshin gaskiya..kuma kinsan Hamma akwai kyau taga mai kyau ta auresa ta cucesa.
Saudat na Dariya tace"Ta kusa maidashi Tazuru..Ammh ta wani bangaran su Amira sun huta da sun aura ma kansu kila dukansu za"a dinga yi Cikin Dare kafin safe sun suma yafi sau goma.
Saudat ta karishe fada suna Dariya,Zeeha ma na cikin Dariya sai ta Sarke Laala kuma sai uban zare ido take yi tana gyaram Murya ammh banzayen basu gane ba sai da Zeeha ta mike zata isa ga kitchen sannan Allah ya bata ikon Ganin Hamman nasu.
Ai tsoro taji ta saki ihu ta kwashi gudu zuwa bayan kujeran da Laala ke zaune jikinta na rawa itama Saudat sai alokacin ta gansa Cikinta sai da ya yi wani kara kolulu,Ido ta Zare bayan tatashi zaune tana wani Raba ido,Shi Bai damu da mganarsa da sukeyi ba duk da bai zauna da kannensa nasa ba yasan sucwajen gulma sannan ai duk su suke kitsama Ummi wasu maganganun bacin ransa Daya kayan Dake jikinsu daga mai riga da wando sun kamata sai mai riga gajera iya Cinya Laala ma karamin wando ne da ko Kauri bai rufe mata ba,Sanin Bama na bayansa yasa ya juya ya karbi Wayoyinsa shi kuma ya saramai kafin ya juya ya fita waje shi kuma ya fara Taku zuwa Cikin Falon ai da gudu suka isa ga juna suka Dungule waje Daya ganin ko kallonsu bai yi ba zai Wuce inda Dakinsa yake yasa Laala tayi kukan kura
cemai"Sannu da zuwa Hamma..!
Jin ta samu bakin mgana yasa suma Sauran sukabi bayanta wajen Rawan jiki yimai barka da zuwa bai amsa musu ba illah tsayawa da yayi wani yamutsa fuska yana bin falon da kallo duk sun bata Cafet din da maikon Chaculate da Ladojin Biscuit da suka gama ci Saifudden mutum ne mai Tsafta sosai yake da kyamkyami Saboda kyakyaminsa yasa ba"a ko"ina yake iya ko shan ruwa ba Tun kafin yakai haka ana Tunanin Tsaftarsa tayi yawa daga baya ne fa ya rage abaya ko Hannu bai cika Hadawa da mutane ba in kuma ya hada ranar wuni zai yi yama Faman goge hanunsa.
Fuskarsa ko kadan bata sauya ba Daya bayan Daya ya kallesu yadda suka wani sunkuyar dakai kamar mutanen kwarai aciki yayi tsakinsa kafin ya Daga Sautinsa yana Fadin"Ina Ummi..?
Wannan karon Zeeha ce ta amsa da Sauri tana fadin"Tana na wajen aiki..!
Kai tsaye"Yau Sunday..!"
Zeeha tace"kiranta akayi shiyasa.
Sai da ya juya kamar zai tafi sai kuma ya juyo yana kallonsu Lokaci Daya da Harara yana Fadin"Saboda Ummi bata nan sai ku maida gida kamar bola ko.?kuna kwance kuna ta sharholiyarku ko.?