← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 144

Sashe 46

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar rai yayi kafin yace"Go to ur Class..Ki yi ma Uncle Hafiz mgana ya gayamiki inda ya tsaya ma Student din sai kiyi Covering daganan."
Muhibba ta dago tana kallonsa Cikin Salama kafin tace"Tanque sir..Thank you very much.."
Yana kallon gefe yace"U are wlcm.

Har ta fice yana kallonta Abunda ya faru tsakaninsa da Saifudeen yake Tunawa yadda ya ce ba wata alaqa tsakaninsa da muhibba sabani ne to shin da gaske sabanin ne kamar yadda ya fada ko kuma akwai wani abu ne na Dabam..?

Ganin
bai da wanda zai mishi wani bayani yasa ya watsar da komai ya kama aikin gabansa daman ya tambayesa ne kada yazo ta cigaba da aiki Laifi ya shafe shi duk da bai san konai game da personal life dinsa ba Sai dai suna da kyakyawan mu"amala na Uban gida da yaronsa sannan akwai kyautatawa mai girma a Tsakaninsu dashi sosai yake ganin girmansa Daman kuma shi kanshi ba zai so rasa Malama irin muhibba ba she is very Brilliant duk Primary section daga uncle hafiz sai ita sosai suke bama yara gudummu wa wajen karatunsu shi kanshi yaji Dadi da Sabanin daya faru bai taba aikinta ba.

Muhibba kuwa hatta Studeent dinta sun yi murna da ganinta itama haka Daman koyarwa ai zabinta ne sannan yaran ta saba dasu tana jansu ajiki matuka shiyasa suke matukar kaunarta iyayan yaran kuwa musamman suke zuwa wajen D.Musa suna fadin yadda yaran ajin Muhibba ke labarin kirkinta tana mu"amala da Student dinta kamar ya"yanta ko kannenta Kaf makarantar sun yi murna da ganin Muhibba da farko har wasu sun fara tsoron kada Dalilin haka ya shafi aikinta Anty Jidda sai da ta Rumgumeta sannan bata matsa mata da wata tambaya kan abunda ya faru Ranar ba.

Ranar Anty Khadija bata zo ba,bata jin dadi Anty Usaina ta kirata ta Fadamata Muhibba ta dawo bata aminta ba sai washegari da tazo makarantar ta leka ajin Muhibba din ta ganta tana Rubuta bisa Allo bakimciki kamar ya kashe su suna Tunanin wata alaqa ne tsakaninta da mai makarantar nan da har tayi wannan aikin sannan kuma ta cigaba da aikinta..?amsar da suka kasa samu kenan sai dai bakinciki da Hassada daya cigaba da cin ransu sun kasa ganewa..

Yadda Rayuwar tazo haka bawa daman zai karbeta kamar yadda Sani ya bama Muhibba shawara ta karbeta sosai kuma ta dawo da yanayin Rayuwarta ta saka aranta wanchan Saifudden ba Mutum bane shi kuma wannan kama ce da Suffa ammh bata da wani Hadi dashi ko alaqa,shiyasa sai ta zauna Lafiya ammh ko da yaushe suna waya da Ummi har su Laala ta taba bata sun gaisa yaran suna da mgana da Hira duk da bata taba ganinsu ba Sadiya ma suna mgana Lokaci bayan Lokaci,Sani Tuni ya koma makaranta Tunda Hutunsu ya kare Muhibba ce kadai da Inna wacce ke ta shirin Bikin Autar Inna Firdausi da za"ayi watan gobe zata tafi chan gaya da wuri,Dagachan zata wuce bakori Babani nata fama da Jikin girma Dayake Tana gidan Babban d'anta ne Isuhu,Kamar yadda Hajiya Tafisu ke ta fama da kafa har Lokacin..

Muhibba dai tace bazataje ba saboda Makaranta Inna tace sai taje ai ta dade bataje gaya da Bakori ba,Ta biyo Habibu Ranar daurin auran suzo tare Muhibba ta tura baki batayi mgana ba ta Tsani zuwa bakori wajen Babani ta Cika Fada da shegen yadda da mganar malaman karya shi kuma Gaya bata da wani Sakewa har gwarama bangaran Goggo Naja sauran kuma bata da sakewa dasu kwata kwata.

Wannan karon har Anty Habiba Inna tace ta shirya sai taje bata musa ba tace zata je ta raka Inna har Bakori suyi zumunci ta gayama Abban walid kuma ya barta sai Muhibba tasan zuwa ya gama kamata tunda Har da Anty Zeenatu ma ya Habibu yace da ita za"a tafi to ina zata je..?

Sai dai tana fatan Allah yasa Lokacin an basu hutun Mird team break da taji ana mgana sai ta hada dashi ta samu ta dan kwana Biyu achan tare dasu Inna.
******
*LERE*
_Friday_11:30AM_
A wannan karon Ranar jumma"a ya taho daga zaria yake yau din ma yayi karatu da Dalibai 8 to 10,Sai daganan ya taso zuwa Lere saboda Iya ta ishesa da Kira ba kakkautawa Sannan kuma zai wuce Abuja Daganan duk da wanchan watan yaje ya kwana Daya ya koma kaduna,shima makarantar su Laala ne ya kai shi sun fara SS1 Capital Science School Acadamy Abunda ya kaisa kenan yayi musu Rigistration Saudat ta koma gaya dagachan ta wuce kano inda ake rukonta itama har ta shiga makaranta ta fara karatunta kamar su Laala..

Zaune yake a falon Iya kamar wanchan karon,Sai dai yau daga Iya sai Baffa Hashimu Baffa Hayatu baya nan yana cikin gari Goggo Atika kuma taje cin kasuwa bata kusa,Iya ce ke ta sakamai albarka saboda ya zo musu da kayan abinci buhun doya da Buhun Dankali kuma yace araba acikin gida Iya tana ta saka albarka Cikin Sharan Hawaye da Haban Zaninta tace"Allah ya jikan mahaifinka yaron nan..Kaf Halayen naka na Salahudden ne ka Dauko haka yake zuwa mana da wannan Hidiman ba gamu mu kadai ba har yan"uwansa da Dangi gabadaya da makota sai sun shaida marasa karfin garin nan kuwa har ya koma ga Allah yana mai kyautata musu shiyasa yanzu in naga kana wani abun sai na rika ganin ka kamar shine agabana..Allah ya jikansa da Rahma da Sauran musulman mu da suka Rugamu gidan gaskiya."
Baffa Hashimu da Saifudeen suka amsa da Ameen yau a dan Bokonsa ya fito Domin Suit ne ajikinsa Farare,Daga coat din har Farar Ciki sai da yayi amfani da Tie baki ya matse wuyansa Sai ya koma kamar matashi dan shekara ashirin da wani abu Tsabar yadda kyau gashi Zatinsa ya bayyana.

Iya ta gyara zama bayan ta gama koke koken tace"Kana shan mganin ka wanda arnen dakake aikowa yana karban maka kuwa.?

Kansa na kasa yace"Eh iya ai nama shanye na karshen "
Aransa kuma gafaran Allah yake nema da karyan da ya sharara mata,Ita kuma Iya jin haka yasa ta washe baki Tana Fadin"Masha Allah ai Daman yace da insha Allahu indai ka sha sau uku an gama yanzu tunda kazo sai ka tashi muje tare domin shi ya matsa yana son ganinka."
Saifudeen yaji gabansa ya fadi shi fa baya zuwa gaban irin wadanan malaman kamar bokaye mganin da bai Taba sha ba wari ma suka fara Cikin wani bakin galan yasha Datti da su Bama da suka fadamai yace su kwasa su kai su zubar in ba mutuwa yaga zai yi ba har Abada bazai iya shan wannan kazantar ba yana cikin Saka yadda zai yi ne yaji Baffa Hashimu yace"Iya basai mu fara jin ta bakinsa fa ko ya fara ganin chanji..?

Iya tace"Ai in mun je chan duk sai yamai bayani Hanzarta Hashimu muje kasan an fi samunsa da Safe in Rana tayi akwai layi."
Iya na shirin mikewa Kamar an kwato Mganar daga bakinsa yace"Ai..ai na warke iya..!"
Iya sai ta koma ta zauna Dabas ta kalli Baffa Hashimu shima ya kalleta,Kafin dukkansu su maida hankalinsu kan Saifudden suna mamakinsa Iya ta karkace kai tana Fadin"Eh kace me..?

Saifudden yana kallon Daud'and'an Cafet din dake falon Iya kafin ya muskuta ya kara fadin"Nace na warke Iya."
Iya ta washe baki tana fadin"Alhandulillah..Da gaske kake yi D'an nan..?

Kai ya gyada mata aransa yana Fatan Allah ya Kubutar dashi sai dai kamar an Wurgota haka ta Fado Dakin Tana Fadin"Iya ina mazan kwai..!"
Sai mganarta ta makale Lokacin da Idanuwanta ya Hango mata mutum zaune gaban su Iya ya sadda kansa ko bai Dago ba tasan ko waye Ya Saif ne ai kaf Gidansu ba gaye kamarsa sannan yadda take matukar kaunarsa yasa ta Haddace kamshin Turaransa sannan ita daga Gidan goggo Atika take ta baya ta shigo kai Tsaye zuwa Shashen iya bata ma tsaya Lura da Hadadden bakin Takalmin dake waje kofar Dakin iyan ba"
Gabadayansu suka Dago suna kallonta banda Saifudden da bai gama ma tantanceta ba sai da yaji Iya tace"Ke Majeeda meyasa baki da natsuwa ne..?Daga ina haka kamar an koroki..?

Sunan data ambatane ya fara zagaye kwakwalwarsa Shiyasa ya Dago yana Bin a wacce aka kira da majeeda da kallo wata bakar yarinya ya gani Gajera Duku duku kayan jikinta shi wlh in aka barsa sai yace kilama mahaukaciya ce Ita kuma ganin yana kallonta sai taji kunya ta rufe Fuska da Tafukan hannayenta sannan ta kwashi gudu ta fice Daga Dakin Iya tayi Dariya tana Fadin"Ina ruwan Majeeda..!"
Saifudden aransa Barka yake ma kansa da yayi ma kansa gata ya Sahale
auran yarinyar nan ai da ko Dattinta zai sa ya kamu da wata cutar,Sai dai bai gama Sauke ajiyar ran Salama ba Yaji Iya na fadin"Hashimu ai faduwa tazo Daidai da zama ma.."
Baffa Hashimu yayi yar Dariya kafin yace"Ai nima abunda zan ce kenan Iya..Tunda an samu waraka sai a maida auran su da majeeda domin kinsan tana son shi Kafin ma ta Dawo ta Fara walwala ai an kwana Biyu,don ma uwar nata na Faman tausanta.."
Saifudden sai yaji kansa yayi wani Dum gashi zaune ana neman kara kaisa ga wani bala"in bai kara jin ya Shiga tsaka mai wuya ba sai da yaji Iya na Fadin"Shikenan kuwa..Ranar jumma"a rana ita yau kenan sai a maida auran nasu tunda ko Jeranta da akayi mata agidan sa da Talatu zata saka a kwaso nace abarsu tunda zata koma Dakinta,Ba wani sha"ani za"ayi ba Tunda anyi na Farko arufe Amarya akaita Dakinta in ya tashi tafiya ya tafi da Matarsa chan inda yake aikin.

Baffa Hashimu cikin jin dadi yace"Hakan ma yayi Iya."
Iya ta kalli Saifudden tana fadin"Kana jin mu bakace komai ba.

Saifudden ya hadiye wani miyau mai karfi a makogwaronsa,Kafin ya kara risinar da kansa yace"Duk yadda kuka Tsara Iya .!"
Iya tayi dariya kafin tace"Dan albarka..Daman nasan bazakayi Gaddama ba Allah yayi maka albarka.

Bai amsa mata yana ta faman kokuwa da yanayin dayake ciki yaji Baffa Hashimu yace"Iya ni kin kaisa da Nisa ko yau din ma basai ya Tsaya a Dauran ba..?.iya ta yi shuru kafin tace"Ko..?

Yace"To Iya mai zamu jira?
Chapter 46 · 0% Book details