Sashe 142
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jikina ya fara samun karfi Saboda Saboda Sahihin jego Goggo Barira ke yi min ba Mugunta aciki,Labarin Haihuwata har Gumel Hajiya babba ta Kirani tamin barka da arziki na tambayi su Amina Hajiya tace sun fi wata Biyu da komawa Madina Su Hamida ma suna Gidajen su,Zasu kirani illai ko sai ga shi sun kirani sun yi min barka ana gobe taron sunan Sahla Amina ta kirani Daga Madina da lambarta tachan tamin barka har ta bani Iman muka gaisa,Naji dadin karamcin su sosai ballatana da Mukayi mgana da Hajiya tace mallam baya kasar sun je India a duba Lafiyarsa shi da Alhaji Sa'idu in sun dawo zata zo ta Dubani muka rabu cikin godiya.
Bani da matsalan komai Tunda ba abunda Saifudeen bai tanadar mana ba Ni da Sahla Ummi ta koma Abuja Saboda aikinta ammh ta bar Majeeda anan sai bayan suna zata koma.
Tun ana goben suna Mutane suka fara cika gidan,Daga Lere Goggo Atika ce tazo sai Inna Talatu Daga Gaya Mama Zuwaira sai Umma Babba,Sai Goggo Naja da Goggo Fa"iza Daga gidan su Babammu,Adda Sadiya tazo tun Safe ita da Wasila Anty Habiba ma su Siyama duk suna gidan Sai dai ita tana Gidanta chan zasu yi girke girken sunan.
Ranar da na cika kwana goma sha Hudu da Haihuwa ranar Litini muka tashi da sunan Suwaiba(Sahla) Raguna Hudu Saifudeen ya yanka mata Tun safe mahauta suka yanka suka gyarasu Su Goggo Naja suka fara aikin siyan su Daman kaji Tun jiyan suka gyarasu suka soya komai.
Tun Safe na fara shiga ina Fita da Ranstatun kaya masu kyau da yarari ni da Sahla Kafin sha Biyun Rana su Anty Habiba duk sun gama girken girken su dama ita da Adda Sadiya ne sai su Laala sai Asma"u kanwar Abban Walid da kanwar Maman arfata ta Kango Aisha da itama tayi aure tun lokacin ina Halin jinya ban samu zuwa ba.
Suna kawo wa nace su Dibar ma Inna da Saifudden shi da Mujaheed Adda Sadiya tace ta Dibarmu su yana gidan Anty Habiba har da Abban Walid da Sani da Isma'il da shi ya kawo su Mama zuwaira.
Ni dai Hankalina bai kwanta ba Sai da Naga an Dibar ma Inna da mutanen ta Dake chan,duk da itama sun yi girkin su achan.
Khalipa Anty Habiba ta bama kudin mashin yaje ya kai musu Tare da Naman kaza da lemuka da Ruwa sai kunin Aya da Zobo da akayi.
Ba wani taro ba ne sosai,Sai yan'uwa da abokan arzuka Su Anty Jidda duk sun zo min har da Anty Khadija da Usaina sai yammah suka tafi kuma basu zo Hannu Rabbana ba da abun alherin su ga Sahlan sai ranar dai kunya yasa suka nemi gafarata nayi Dariya nace ni ban taba Rike su araina ba,ko'ina na wuce sai kallo ake yi Jikina yayi Danye sannan na Sabe kadan sai haske na ya fito,Kafana da Hannayena sun sha kunshi ja da Baki kaina yaji kitso kanana da Wasila tayimin domin ta iya kitso sosai.
Har ta Nusaiba sun zo min barka,Nusaiba tayi aure a kano tazo ganin gidane sai kuma taji na Haihu tazomin suna nakuma ji dadi sosai,Duk wannan zirgan zirgan da nake yi ban manta da Angon karni ba Baban Sahla na kira wayarsa ina Tambayansa yaci abinci..?
Yace min gasu gidan Anty Habiba sun ci sun sha naji mganar Mutane a kusa da shi nace mai suwaye.?
Sai yace min Sani ne da Isma"il sai Mujaheed da Abban Walid sai Ya Habibu nace duka a gaishe su muna gama waya ya kalli Mujaheed yana Fadin"Ummi Sahla tace tana gaida ku"
Mujaheed din kadai yajisa sai ya karkace baki da kai yana Fadin"To muna godiya Abu Sahla"
Suka yi Dariya gabadaya sai Dare bayan kafa ta Dauke na gansu sun zo gidan Lokacin su Mama zuwaira sun koma gidan Inna su kwana Dagani sai Goggo Barira sai Fati,Sai Asma"u sai su Laala,Su Adda kuma da Anty Habiba da Anty Zeenatu suna Kitchen suna kaye kaye yau fa an ci an sha hatta su Bama yau sun shaida..
Falon farko suka yada Zango Saifudden ne da Mujaheed sai Sani da Isma"il basu Shiga ba saboda kunyar Goggo Barira,ni na biyo su Dauke da Sahla na kashe Dauri ina Fitowa Sani ya saita Camera yana Dauka na Hoto Fadi yake"A gaida Uwar Sahla..Irin wannan kashe kala haka..!
Na karkace ya Daukeni Hoto ina Fadin"Wani abu ma sai ma ranas.!
Matsowa yayi ya bani Hannu muka tafa Muna Dariya Isma"il yace"Ni dai bani yata kada ku kadamin ita"
Mujaheed yace"Ka taimaki Abu Sahla ai tun dazu yake kallon su ya kasa mgana ne"
Dariya nayi na mika ma Isma'il ita ya karbeta ni kuma muna gaisawa da Mujaheed yana tambayanta ya Hidima sai ga su Anty Habiba sun fito nan suka gaggaisa,Adda Sadiya ta karisa wajen Saifidden tana fadin"Hamma kaci abinci..?
Kafin ya yi mgana Mujaheed ya Rigasa da Fadin"Sannu da aiki Ga matarsa Agefe kin manta da mijinki kina Tambayan yayan ki ko yaci abinci..?
Adda na Dariya ta nufesa tana Fadin"sorry Sweet."
Hade rai yayi yana Fadin"ba wani Sweet naga gano kin fi son wannan akaina"
Yafada yana nuna Saifu da baki shi ko baki ya tabe bai ce komai ba Sani yake kallo sai Daukan Hotuna suke su da Sahla da Isma"il chan sai ga Majeeda ta fito ganin Sani da Isma"il yasa ta koma Dakin da suke da gudu tana Fadin"Kai laala ga su Bros sun zo.."
Daman haka suke kiran su adangi waye bai san Sani ba ai babu shi..
Da gudu suka fito suka gaida yayyin nasu Sani na ganin su yace"yan matan gidanmu ashe kuna ciki..?
Zeeha tace"Muna ciki Bro ya garin ne..?
Kace zamu sha Hotuna duk yau bamu ganku ba..?
Sani yace"Manta kawai ai gashi mun shigo yanzu"
Ya fada yana kallon Laala Dake leken Sahla a hannun Isma"il suna Hada ido ta hararesa shima ko ya rama Duk Zeeha na Lura da su aranta tace munafukai..
Saifudden na kallon su suna ta Hotuna Sahla Daga wannan hannun zuwa wannan hannun har da Wasila acikin su ta zama yar gida sai alokacin ya Tuna su Laala sun gama makaranta ba waya ahannunsu kuma shi yayi alkawarin in sun yi Candy zai siya musu ya zama Dole ya cika wannan alkwarin.
Sani ne ya juyo yana Fadin"Family Pic Who want to miss it..?
Da gudu muka taso muka shige Hoton Saifudden na zaune mujaheed ya taso sa yana Fadin"Hoton bazai taba cika ba in dai ba Abu Sahla aciki."
Dukkammu muka shige muka gyara a Iphone 13 din da Sani ya gama Tara kudi ya siya Asm"u ta Daukemu Sahla na makale Hannun Laala kamar zata maidata ciki mun sha Hotuna kala kala ni da Saif sai ya nuna ya gaji Sani Photograper sai yace"Plz just 1 pic.."
Ahaka dai duk ya daaukemu kuma sun yi kyau sosai akwai wani wanda yafi burgeni wanda muka hada kai ni da Saifudden muna kallon Sahla da muka Tallabeta tare shi yana Sanye da Shadda mai ruwan sararin Samaniya ni kuma ina sanye da Less shima mai Ruwan Sararin Samaniya nace ma Sani in ya gyara Hotunan ya Turamin yace an gama Auta na ballamai Harara sai ya kama Dariya yana Fadin"Sorry Ummu Sahla"
Sai nayi mai fari ya rike baki yana Fadin"Ya zama Dole nayi auran nan kafin ki kara Haihuwa kice kin girme ni"
Gwalo nayi mai ina Dariya Laala na Tayani yana Hararmu,Goggo Barira dai na ciki bata fito ba ta kyalemu mu sha Shagalin mu,ni barci ne yaci idona na shiga na kwanta Sahla kuma Goggo Barira ta karbeta ta sake mata wanka tana Fadin tasha Dauka duk jikinta yayi tsamib ni ban ma san Tafiyar su Sani ba,Domin gajiya yasa nayi barci sai da Safe na iya tashi Shima Goggo Barira ce ta tasheni Domin nayi wanka.
Aranar zuwa yammah baki duk sun fara tafiya gida Mutanen Gaya Tuni sun wuce bayan an dibar musi nasu naman sunan bangaran su kawu da kuma Bangarena,Adda Sadiya ma aranar suka koma Kaduna ita da Wasila da Majeeda da ta bisu Zata kwana washegari ta wuce Abuja suma su Laala sun kusa komawa an kusa Fara Biyan Jamb.
Anty Habiba da Anty Zeenatu a Daran suka koma gida aka barni da su Laala sai Goggo Barira aranar agida Saifudden ya kwana washegari da Safe kuma ya tafi kaduna.
An raba Naman sunan an Dibar min nawa,da ni da Saifudden na Mutanen Lere kuma su Inna Talatu suka tafin mu su dashi Su Inna kuma Sani da yazo na bashi nasu,Inna ta kirani tana ta saka albarka harta Ya Habibu,sai na aika mai da na shi Dabam shi da Abban walid,kowa sai son barka yake yi Na Ummi Majeeda na bamawa sanda zata tafi ta kaimata..
Cikin kwanciyar Hankali na Cigaba da Jegona Baba lami na zuwa Lokaci bayan Lokaci tana taimaka ma Goggo Barira,Cikin Sati Hudu da Haihuwata na yi garas dani kamar ba aiki akayi min ba Ni da Sahla mun samu jegon gata mun sauya kamar zara acikin wata.
Nayi arba"in da kwana Biyu su Laala suka koma Abuja tare da Saudart da tazo min barka lokacin da akayi suna tana makaranta,Sun tafi da Sha tara na arziki har da Tsaraban Sabbi wayoyi Daga Hamman su Murna kamar zasu yi hauka sun tafi da kewar Sahla da suka saba da ita,Goggo Barira kuwa Hanata Tafiya Saifu yayi yace ta bari mu da kanmu zamu maidata gida to hakan bai samu ba mun shirya tafiyar sai Rasuwar Babani ta Dakatar da komai Allah yasa Kasarta a garin zaria take anan gidan Inna akayi zaman gaisuwa har akayi bakwai sannan aka watse.
Allah ya jikan Babani da gafara Inna tayi rashi sai hakuri da Fatan muma Allah yasa mu cika da kyau da Imani.
Kwana goma da Rasuwar Babani muka tafi kai Goggo Barira har gida da kayan arziki tayi ta mana Godiya,kwanan mu Uku a gaya biyu a gidan su Babanmu nayi Daya kuma Gidan kawu Tare kuma da Saif muka yi wadanan kwanaki domin Baya zuwa Office sosai siyasa ce ta gabato.