Sashe 126
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A sanyaye majeeda ta Daga kanta Inna talatu ta Cigaba da fadin"Har yanzu baki kai shekarun da zaki Raba Dai dai da akasasin ba..Mganar Saifu ko Lokacin auran ki na Farko da shi ban taba Fadamiki ba sai yau har ga Allah ban so ba Majeeda Saboda nasan zai karbeki ne Saboda alfarma da kuma bazai iya yi ma su Iya Gardama ba ammh Yanayin Rayuwar ku ba Daya ba..Saifudeen ba Sa'an auran ki ba ne Majeeda akwai Tazara mai yawa a Tsakaninku na aminta dake dashi Tushen ku daya ammh kun tashi a mabambanta Wajewaje na Rayuwa shi Dan boko ne da zai shiga ko"ina a Dama dashi shi mai mikami ne a gwammati sannan Dan birni ne mai wayewa da Sanin Rayuwa Majeeda ke kuma anan aka Haife ki anan kika Tashi karatun nan ba kamar Birni ba,wayewar ba Daya bace duk da ina son kije inda zaki ji Dadi ammh bana son kije inda ba"a son ki na fiso ki yi aure inda aka san mutumcinki da Darajan ki"
Ta Dakata tana kara Nazarin yadda Majeeda take karban mganar nata sai ta Fahimci Majeeda ta natsu da alamu mganganun suna shigarta ganin haka yasa ta gyara zama ta saka Hannayenta ta riko Hannun majeeda ta Damke gam ta cigaba da fadin"A farko ko da saifu ya zauna dake majeeda to alfarman su iya kikaci ba Domin yana sonki ba..Sai kuma ya sake ki har ga Allah naji ba Dadin wannan Tozarcin ammh Daga karshe sai na Fahimci hakam yafi alheri Shiyasa da mganarsa tataso ana Biyu nima na ki aminta da mganar,Saboda ko bakomai ina so ki yi aure inda ake son ki da ganin kimarki da Darajan ki ba bazan so ki yi aure inda zaki zauna Saboda alfarma ba ke a Tunaninki ko ahakan Saifu zai so ki ne Majeeda..?
Ba zai so ki ba da zai soki da bai kawo miki tsarin ki bar mganar aure ba kiyi Hakuri ba..Yana Sonki ammh ba Soyayyar aure yake yi miki ba Sai dai yana miki Kauna ta jini da yan"uwantaka Sannan yana son yaga ki cigaba watarana ko bashi ba wani ma wanda ya Fisa zai iya ganinki yaji kin kwantamai arai saboda me..?Saboda Rayuwarki ta inganta,Inganta da Ko wani Namiji bazai ji shakkar auranki ya kai ki gidan sa ba..Saboda haka ki Tsaya Ki natsu ki Fahimci mganata Majeeda Shin da auran sa da kuma Inganta Rayuwarki wanne kika Zaba..?
Majeeda tayi shuru ta kasa mgana Inna talatu ta Cigaba da Fadin"Ba lalle in kin aure sa yaji da ke kamar yadda yake ji da matarsa ba..Saboda ita yana son ta ke kuma an Chusa mishi ke ne..Da ki aure sa baya sonki gwara ki Tsaya ki inganta Rayuwarki Majeeda a gaba in shi da kansa ya nuna yana ra'ayin ki har ni nan ina Maraba da haka Domin ba iya ke ba Kaf garin nan abun Alfaharin iyaye ne Saifudden ya zama surukin su zamu fi kowa Farimciki da haka ammh ayanzu don Allah ina Rokon ki Majeeda ki bar wannan mganar..Ki cire wannan Tunanin aranki ki Tsaya ki amshi Tallafin su zuwa ga Rayuwarki kada ki bari wata baraka ta saka Zaliha ta fara nadamar Daukan ki ta Hada ki cikin ya'yanta ta Damu sai kirana take yi tana Tambayana ko wani Laifi suka yi miki ita da su Zainabu Haba Majeeda kada idanuwanki su rufe ki Bude zuciyarki da kirjinki ki Hasaso Alherin Zaliha gareki damu iyayanki gabadaya..Ta Dauke ki ta Hadaki Cikin ya"yanta ba Tsamgwama ba Nuna bambamci D'anta ya saka ki a makaranta ya Dauki duka walhalhalin ki Majeeda ai ba ke kadai bace adangi suna da yawa ammh suka Zabo ki Saboda mene..?Saifu yana kaunarki yana so ki inganta Rayuwarki watarana ki samu wanda ya Fisa Zaliha kuma tana miki rikon Diya ce ba Dangin miji ba ina Rokon ki, ki kori wannan shedan din da ke miki wannan karatun yana kawata miki gaibu ki watsar da komai ki Rumgumi Sabuwar Rayuwar kibda kudurin bazaki bama wadanda suka Tallafeki kunya ba Majeeda"
Ta Karishe tana kallon majeedan da mganganun Inna talatu suka kashe mata jiki Sai Majeeda ta saka kuka Tana kallon Inna Talatu tace"Inna na shiga uku na yanzu da wani ido zan kalli Ummi da su Laala..?
Nasan kwanakin baya duk na zauna da su ba Dadi Innarmu ya zan yi..?
Da Sauri Inna talatu tace"Akwai yadda zaki yi mana Majeeda gobe ki shirya ki koma Habujan ki Sameta ki bata Hakuri suma su zainabun ki basu hakuri ai durkusa ma wada ba gajiyawa ba ne Majeeda balle ke da kika yi musu laifi nasan zasu yafe miki Daganan sai ki gyara mu'amalan ki da su na Tabbata daga Lokacin komai zai wuce"
Majeeda ta Sauke Numfashi kafin tace"ammh innarmu ki tayani ba ma Ummi Hakuri don Allah"
Inna Talatu tace"In sha Allah ammh nima ki yi min alkwarin daga yau anan wajen bazan kara jin mgana makamancin wannan ta kara tasowa ba kin barta har Abada Majeeda zaki tsaya ki inganta Rayuwarki Domin goben ki"
Da Sauri Majeeda ta kara Damke Hannun Inna Talatu tana fadin"In sha Allahu Inna nayi miki wannan alkwarin"
Inna talatu ta saki mirmishi jin Dadi kafim tace"Naji dadin jin haka..Allah yayi muku albarka Gabadaya"
Majeeda ta amsa da Ameen Inna Talatu da kanta ta share mata Hawaye suna Dariya a tare Ta mike tana Fadin"Muna nan muna mgana har an yi sallar mangariba"
Jin haka yasa Majeeda ta mike suka fice atare suka Dauro alwala suka zo suka yi sallah Daganan Inna Talatu ta saka Tuwon Iya Majeeda ta Dauka ta kai mata tana saman Darduman ta ta Sameta tana ganinta tace"Yar nema me ya kawo ki Dakina..?ai tunda kin ki To sai ki yi ta zama ba ke kadai ce a dangi ba nace ga yar wajen Atika Sailuba Zalihar tatafi da ita"
Da Sauri Majida ta Dungure mata kwanukan Tuwom ta agabanta tana Fadin"Ni gobe nan zan koma..Sai dai ki Tura Sailuban Kauru inda Yayarta Shema'u ke aure ba dai Abuja ba"
Tana gama mgana ta Fice Iya ta rakata da Fadin"ai yarinya kin ma kanki Tunda kikace bazaki koma ba Ta zauna"ita dai Majeeda bata ko kara bi ta kan iya ba ta koma shashensu.
Ummi kuma sai bayan isha"i sannan Inna talatu ta samu ta kira ta kafin Baffa Hashimu ya shigo suka yi mgana ta na ta bata Hakuri Ummi tace"Nifa Majeeda batamin komai ba..So nake ji Dalilinta na cewa bazata dawo ba!
Inna Talati ta kasa Fadamata Dalilin Saboda kunya da kuma rike ma yarta Daraja yasa tace"Shirme ne kawai Zaliha..Kinsan yarinta wai ita aure zatayi na yi mata fada ta dawo cikin Hayyacinta"
Ummi na jin haka bata ja da Nisa ba ta Dauki Saunan mganar Daman ai Tasan za"a rina sun yi sallama da cewa sai goben In majeedan ta Taho Sai wajem goma na Dare Baffa Hashimu ya shigo da labarin Ummi ta Turo ma Majeeda kudin mota ta shirya Tun safe ta bi Gaddafi,ko alama Inna Talatu bata nuna mai wani abu ba Duk da yayi mamakin ganin Majeedar ta sake sai dai ya zata Inna talatun ne tayo mata jan ido shiyasa ta daina Tsiyar data fara ya shiga Dakin Iya ya iske barci ya riga ya kwasheta shiyasa bata gumtsa mai mganar ba.
Washegari kuwa tun Karfe 7:00am na Safe su Majeeda suka Dauki Hanyar Abuja bayan Inna talatu ta bata tsaraban su kuka kubewa garin kunu Busashiyar Zogala da Shuwaka sai gyada mai gishiri da ta saka ayi ma su Laaala Mutanen gidan ma ba da kowa tayi sallama ba ciki kuwa har da iya sai dai da ta Laluba aka ce mata ai su majeeda sun kusa sauka a garin Habuja Iya ta cizi yatsa tayi ta Jaraba tana fadin ai da tasan Lokacin tafiyar da sai ta ga yadda Majeeda zatayi ta tafi ai Tunda tace bazata koma ba sai dai ta zaunubgarin abun Dariya har Iya ta saka an kira mata Goggo Atika ta gayamata sai gashi jiki na rawa ta Taso Sailuba da kulin kayanta suka zo suka iske Iya na Jarabar Majeeda ta tafi Goggo Atika ta kalli Iya tana Fadin"Meyasa kika barta tatafi Iya..?
Kin sa na saka ma Sailuba rai ni yanzu ya kike so nayi da ita..?
Tunda tace bazata koma wani uwar kuma ya maida ta..?
Iya tace"Yo ina zan sani..yamzu haka Talatu ce tace ta hada kayanta ta koma ni na sani"
Inna Talatu na shashenta tana ji ko Fitowa ba tayi ba Domin a Tsskar Gida Iya ta fito ta tona komai wadanda ma basu san anyi ba duk sai da Jarabar iya ta saka suka Fahimci komai.
Tana jinsu Daga karshe Jarabar iya ta koma kan goggo Atika da Sailuba da ta fara kuka tana ita sai an tafi da ita Habuja Iya ta fara Fadim"Ke tashi ja'ira ki bani waje..Kafin na miki Dukan Tsiya daman nima karambani na ne ina zan yarda akai ki habujan yadda kike da kazantar nan ai sai ki sa makotan Zaliha su fara kyamatar ta sannan Uwar ki da bakinta ta Fadamin kina da Halin yan Dauke Dauke salon kije kawai ki ja masu bala"i Habuja ai ba kamar Lere bace don Ubanki kika je kika yi sata achan Folice zasu kamaki"
Ta karishe Fada tana Neman Sandan da zata rafka ma Sailuban tana ganin haka ta mike tana fadin"Ni ba Barauniya bace kuma sai naje Habujan sai dai ki mutu"
Tana gama fadin haka ta kwashi kayanta ta ruga aguje ta fice Daga gidan.
Iya ta rike baki tana salallami Cikin Takaici tace"Lalle yarinyar nan bata da Tarbiya Atika kina kallo yarki na Zagina bazaki tsawarta mata ba..?
Goggo Atika da takaicin ga samu ga Rashi ta kyabe baki tana fadin"To iya ai ke kika ja..Gaban fa mutane kika ce mata kazama har kina fadin tana Dauke Dauke ni me zan ce..?