Sashe 63
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kamar yadda gidan kawu ya kachame a Gaya chan ma a lere haka ne Domin Hajiya Iya haka ta shirya nata Bikin Su Goggo Atika ba mafita Dole ta shiga Cikin Hidima su iya an sha Leshi Har da Goggoro sai Faman bada Umarni take yi tana masifa inda taga an yi ba Daidai ba,Ba tun yau ba kowa yasan Saifudeen Dabam yake cikin jikokinta.
Ango da nashi Tawagan sun shigo garin Gaya sha d'aya Rabi ta yi ma Sai ga wasu manya manyan Jifaa jifai suna ta shigowa garin Gaya sai wanda ya gani Saboda sun Tsaya su taho da Sauran mutane ne yasa suja bata lokaci Kwamishinoninsu na kaduna Doguwar Motar gwamnati wasu suka Shigo wasu kuma a tasu motocin Dauke da masu Tsaran Lafiyarsu Gwamna bai samu zuwa ba ammh mataimakinsa yazo bakajin komai sai karan Jiniya da kuma Diran motar Dss da yan Sanda basu ci burki ko'ina ba sai kofar gidan su Baba Surajo daman Mujaheed sun yi mgana da kawu yace su kariso nan kawai daganan ba Nisa da kafa zasu karisa masallacin da za'a Daura auran.
Motoci haka suke ta fakawa cikin burgewa Sani sai da ya fiddo waya yayi ta Daukan Video saboda yadda abun ya Burgesa bakajin komai sai karan Jiniya da Karan kafafun Masu tsaran Lafiyarsu saboda kwama kwaman Takalman dake Kafafunsu.
Yau shigar da su Bama sukayi na Dabam sun fararan suit ne yau sabanin bakake da suka saba sskawa,ammh sun toshe Fuskarsu da Bakaken Gilasai Fuskar nan a Turbune ba Fara'a ko kadan kamar yadda ta Ogan nasu ta bayyana bayan sun bude musu kofofin Motarsa baka prado suka bayyana waje.
Dashi da Mujaheed da Mudansir da suke Kaduna tare dashi su kawu wajen mai girma mataimakin gwamna suka nufa ana gaisawa Aransu suna fadin Haihuwa mai Rana yau sune gasu ga Mataimakin Gwamna baki yaki Rufuwa waje ya cika da Mutane bakajin komai sai karan Jiniya sai kuma Kai da kawon Sojoji da Dss yara sai dai Hange Daga nesa..
Saifudden sanye cikin Shadda mai Ruwan Sararin samaniya wagambari ce tana maiko wacce Daga ganinta ta bama Dubu dari biyu baya sai Hulan kansa zanna kalan shaddarsa ne zaren aikinta mussaman mujaheed ya bada Sakarta a garin maiduguri Kafarsa Wani Uban su bakin Takalmi ne dan Italiyan sai hannunsa Dauke da Bakin Agago na Fata mai kyau da yarari A Fuskar ba ya Fara'a ko kadan sai dai ba wanda ya Damu sanin Halinsa Mujaheed da Mudansir Fararan Shadda suka saka Harda Datti da Isma"il da Tun jiya suna Gaya suka zo suka Tarbi Angon suna zubamai kirari ammh bayajin su ji yake kansa yayi masa wani Dum kunnensa bayaji sosai kamar an Buga mai karar wani karfe mai Kara wani Dim kawai yake ji kamar dodon kunnensa ya samu matsala.
Tuni su kawu sun yi gaba da Sauran Mutane Tafiyar Minti shidda suka isa masallacin gidan Hakimin Gaya,Har da Sarkin garin Gaya acikin Tawagan madaura auran Muhibba Tunda wanda ya haifi mahaifin Muhibba suna yi da Maimartaba duk Jumma'a dashi ake zaman Fada shiyasa Hakimi na Fadamai Daurin auran yace dashi Za"ayi sai a ka Hade da mataimakin Gwamna dashi ma yake shirin bayan Daurin aure ya Isa gidan Sarki yakai gaisuwa sune suka samu shiga masallacin manyan gwamnatin sai su kawu da su Baffa Hashimu da su Baba Surajo tunda su Waliyai ne.
Ko su Saifudden suna Daga waje sai dai suna jin abunda ke Faruwa ta Lasifar masallacin.
Baba Surajo yayi ma Hakimi kara shi suka Nada a matsayin Waliyin Amarya Ya Habibu na wajen shi da Sani da ya mike sai Video yake yi bakinsa har kunne Abbati na Zaune jikinsa yayi sanyi Tun da yaga Saifudeen yasan Muhibba ta Hadu da Babban goro daman tun agida yake ta jin Rade raden Kwamishina ne bai amince ba sai da ya ganin ma idon san.
Jin dadin wannan karamcin yasa Hakimi ya bama maimartaba Sarkin Gaya Walicin shi kuma Sarki yaji Dadin wannan karamcin yana ta saka albarka nan da nan aka fara sigar Neman aure Baffa Hashimu bashi ya neman ma Saifudden aure ba abokin mahaifinsu ne yanem masa auren Sarki kuma ya basu Cikin abunda bai gaza Mintina Goma Ba tabbataccen aure ya kulli Tsakanin MUHIBBA BELLO MAIRAGO DA angonta SAIFUDEEN CONEL.SALAHUDEEN LERE.
alokacin da aka Daura auran Sha daya da Mintina arba"in ne,ana Shafa Fatiha Saifudeen ya kara jin kansa yayi Dum!
Dum!!!"
Kamar wani abu na Dukan kansa haka yaji sai da ya Dafe kansa saboda yadda yaji kansa kamar zai fado ya Rabu da gangar jikinsa.
Kamar yadda ya Faru da Muhibba a Gidan su ya zeenatu tana Tsakiyar Asma'u da Aisha dakin har da su Anty Jidda da su Fati duk suna Falon Zahrajj ce tazo ta kara yi mata kwalliya ta shirya cikin Shaddar da Ya Habibu ya Dinka mata tayi kyau har tagaji da kyau sai daukan ta Hotuna suke yi Tun sha Daya da rabi suke Zolayanta da An Daura aure suna Guda su Asma"u suna kiran Amarya dayake har sun dawo sun gama Girkin sun taho dashi,Tun alokacin gabanta ke fadi sai dai bata kara jin mummunar Faduwar gaba wanda bata taba ji ba sai da aka shafa Fatihar Daurin auran ta Daga chan masallacin gidan hakimi na garin Gaya taji gabanta ya wani yanke ya Fadi irin wanda bata taba ji ba Hannunta guda daya ta saka ta Dafe kan nata Tana fadin'"Wash..!
Daidai Lokacin da Guda ya cika Gidan saboda shigowar Anty Habiba tana Fadin yanzu Abban walid ya Kirata yace yanzu aka Daura auren.
Tana shirin Dago kanta kamar walkiya taga wani abu ya gifta ta gabanta bata gama dawowa Hayyacinta ba taji acikin kunnuwanta an saki wata gigitacciyar Dariyar data Razanata ta gigita ta wacce take jin ta kamar za"a cire mata Dodon kunni Sama Sama take jin gud'an Mutane a samanta kanta,Hannunta duka Biyu ta saka ta toshe kunnuwanta tana girgirza kanta jikinta ba inda baya Rawa Hawaye wasu na bin wasu tana so ta yi addu'a ammh ta kasa bakinta yayi mata wani irin Nauyi Anty Jidda ce ta matso kusa da ita ta Dafa kanta tana Fadin"Yau ba Ranar kuka bace Anty Rana ce mafi Muhimmanci a Rayuwarki.Allah zaki ambata ki yi mai godiya ba kuka ba..Ki yi ta Fadin La"ila ha'illalahu Muhammandan Rasulallah..Sannan ki cike da Hasbunallahu wani"imal wakeel."
Kamar a wata duniya haka taji muryan Anty Jidda Cikin Sauri Bakinta ya karbe da Fadin"Hasbunallahi wani"imal wakeel maimaitawa take yi da karfi har Hankalin su Asma'u ya koma kanta kamar kuma an yi ruwa an Dauke taji kanta ya Daina Sara mata sannan Dariyan ta Dauke Dif ta Dago kanta Ido jage jage da Hawaye tana Binsu da kallo kawai sai suka saka mata Ihu suna fadin"Ta zamo Amarya ba Domin Daukaka bq..ta zamo Amarya..Ta zamo Amarya..!"
Kawai sai ta tashi ta shige Uwar Dakin Innar su Anty Zeenatu ta Fada kan gado tana kuka Anty Jidda ce ta Bita ciki Tana Lallashi ga Fargaban aure ga kuma Tunanin abunda ya faru da ita yanzu me hakan ke nufi..?
Hayaniyar mutame yasa bata tsaya Tuna komai ba sai ta bar shi a Kila haka kowacce mace ke jin in aka Daura mata aure..
In da Muhibba ta san auran Saifudden Shimfidaddiyar kaddara ce ke jiranta da bata aminta ba..Sai dai bata da Tsumi ballata Dubara bakin Alklami ya riga ya Bushe Allah ya Had'a kaddaran su waje daya Yanzu ne abunda ke Boye zai bayyana An Dade ana zaton wuta a makera Kafin daga baya kuma a Sameta tayi Kane kane a masaka.
Achan Gaya abunda ya Biyo bayan Daurin auran duk Fatan alheri ne ga ango,Mataimakin Gwamna da Sauran Commissioners basu tsaya ba ana Gama Daurin auran suka zo suka gaisa da Saifudden suka bar garin Gaya sai tawangan su Mujaheed ne a wajen da Sauram mutane Fatan alheri da Musabaha har sai da Saifudeen yaji ya Fara gajiya har da Sani sun gaisa ya kuma ce don Allah yana so su yi Hoto Dole ya tsaya Abbati ya Dauke su Hoto Harda Mujaheed sai da ya bar wajen ne Saifudeen ya kallesa yana Fadin"Who is he..?