← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 144

Sashe 17

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan su Inna ke bashi Labarin mafarin Lalura shi kuma ya sanar dasu cewa Saifudeen bai tafi ba,ba wai don sun mike da neman mgani bane ya tafi a'a ya tafi ne Saboda na Girma sannan Bakina ya Bude,kuma basu suka rufemin Baki ba Shine saboda nayi girman da zan rika Fadin wasu abubuwan da zasu tadama su Inna Hankali sannan ya Sheda musu yana Tare dani sai dai ya Rufe Budewar idon da yayimin na Daina ganinsa kwatakwata ba Domin ya Rabu dani gabadaya ba.

Su Inna sun shiga damuwa sai ya kwantar musu da Hankali yace Insha Allahi zai rabu dani.Mallan Haruna ya Faramim Rubutu ayoyin Allah da kuma Wanka da Magarya koda yaushe Cikin ikon Allah komai yayi Sauki ban kara Fadi a ko"ina ba sannan Labarin Saifudden ya shude daga bakina,Saboda Inna ta Zaunar dani Ta Tsoratar dani da Fadamin SAIFUDEEN BA MUTUM bane.

Daga Lokacin sai na Tsorata ammh kuma akwai shakuwa da wata irin yarda a Tsakanimu dana kasa gasgaata Inna datace Saifudeeen zai iya Cutar dani.

Daga Lokacin sai wannan matsalan ta kau acikin gidanmu,na cigaba da karatuna Cikin Nasara kamarr yadda na Fara,Babanmu yaga auran Anty Habiba,Data auri wani Dalibin Bautar kasa,alokacin auranta da Wata Biyar Allah yayi ma Babanmu Rasuwa Dare zuwa Safe sakamakon ciwon Ciki wannan babban rashi ne da muka kasaa mantawa dashi har yau har gobe.

Mutanen Gaya sun zo sai da akayi bakwai suka koma su Kawu Surajo duk sun zama magidanta girma ya kamasu suma ya"yansu sun girma Dayake Gaya da Zaria ba Daya bane tuni sun aurar da yaransu har da Sa"annina aciki sannan ga Aminin baba Alhaji Sunusi shima da iyalansa har akayi bakwai Dayake ya kara aure anan Gaya din.
bayan Rasuwar Babanmu ne Kawu Surajo ya kira dilallai akayi ma Shashen Baba ma gaya kudi ya siya ya kawo Ma Inna kudin yace ko ba Bello wannan Shashen nasu ne halk malak duk sanda suka zo gaya nan ne masaukinsu.wannan karamincin na Kawu Surajo har yau Inna na nanatasa,Sannan gonar Babanmu Ta gaya har gobe ta na nan da Farko Kawu Surajo ke nomata Daga baya da Ya Habibu ya kawo karfi sai ya Karba yana nomata duk shekara..

Ko da Babanmu ya mutu ya bar mana kudade yau da gobe bata bar komai ba suka kare,Sai dai tallafin su kawu Surajo da Alhaji Sunusi suka Rikemu har Ya Habibu ya gama karatunsa,yayi Service dinsa Sannan Inna ta saida Dobbobinta data ke kiwo a bakori,ta bama Ya Habibu ya Fara kasuwanci a kasuwar Sabongari Farko daga karamin shago ne Allah yasa abun albarka daya yi karfi ne sai ya Fara Hadawa da Noma nan da nan Arzikinsa ya habaka cikin Lokacin..

Sannan ga Anty Habiba Mijinta ya fara Lacaring a Fce dake zaria sannan itama Anty Habibar ya sakata a Abu ta fara karatunta cikin Nasara shima ba"a barsa abaya ba yana Tallafa mana da Taimakomsa ne ma na samu Gurbin karatu a Fce dake Zaria.

Lokacin ya Sani na gida bai samu Tafiya Mkaranta ba,bai samu Jamb ba sannan ya Dake shi Law zai karanta shi ya kawomai tsaikon da har sai da na gama Nce dina bai tafi ko"ina ba yana Zaman jiran Bayero sannan kuma da Jiran Jamb domin duk shekara sai ya zana makinsa bai kai ba..tare dashi muka daga ni ina gamawa Result dina Dayayi kyau na Tacike D.E shi kuma ya Sani ya samu Gurbin karatu a Bayero kano Kuma ya samu Burin nasa wato Low da Taimakon Ya Habibu da Anty Habiba da su baba Surajo har da Alhaji Sunusi da shima yaron wajensa Isma"il a shekarar shima ya samu gurbin karatu a bayero.

Sai gabda zan kamallah B.Ed dina Mijin Anty Habiba ya samu karin girma ya samu matsugguni zama acikin gidajen staff na makaranta abaya a Tudun wada suke zaune ya"yansu Uku khalipa sai Walid sai Siyama,akuma Lokacin ne Ya Habibu yayi aure bayan ya gina shashen nan da Baba ya rufesa sannan ya kara gyara gidanmu ya kawatashi Ya fitar ma da Sani Dakinsa Dake Zaure nima kuma an Fitarmin da Dakina gefen na Inna..sunan matarsa Zeenatu Diyar kanwar Inna ce Hajiya Karima dake makotansu,dayake gabadaya kowa Da Innar Habibu yasan Inna dashi.

Yanzu haka ya"yan su Biyu Fatima Amal da Bello mai sunan Baba.

Zuwa Lokacin da girma da yantamaci ya kamani ban daina karban mgani wajem Mallam Haruna ba saboda ina yawan mafarkin Saifudden kuma ina Fadama Inna,Sai dai ba kamar surutu na Farko ba tun lokacin da bakina ya Rufe shikenan na zama shuru shuru..

Sai dai abu daya ne bai iya gushemin ba SAIFUDDEEN duk da nima na yarda na Amimce ma kaina Saifudeen ba Mutum bane saboda Dalilai masu Dama in mutum ne meyasa ban kara ganinsa ba?an kwarari shekaru goma sha biyar Rabona da ganinsa ammh kammaninsa bai taba bacemin ba a ko"ina na gansa zan iya shaidasa sai dai nasan bazan gansa ba Tunda muna da bambamcin Halitta ni dashi.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke*
*Janafty*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
Maganar su Inna kan Saifuddeen ba Mutum ba ne zan iya cewa na Aminta dasu bisa tarin Hujjojin da ni kaina nasan haka din ne sai dai zuciya ta bata Aminta da mganar ya aureni bazan taba aure ba, abu daya na sani nayi zaman Aminci da Saifudeen bani da masaniyar Mutum ne ko aljani ne duk da alokacin ina da karancin shekaru kuma wannan Aminci na rikesa a zuciyata yayi min Tasiri da nike Tunanin ko da muna da bambamci wajen Halita Saifudeen bazai taba cutar dani ba.

Na dogara ga Allah sannan na san shi ke yi alokacin da ya so da kuma sanda yaga dama,ammh ina shan magani ko da yaushe saboda Inna yadda take damuwa da al"amarin mganani na sai kaji Tsausayinta bata da wargi tana da Fada in nace ma bazan sha ba sai an ji mu ni da ita shiyasa bakina alekum nake karba nasha wani Lokacin ma daya kare da kanta take zuwa gidan mallam Haruna ta karbo min wani Tunda gidansa bashi da nisa da namu.

Inna ta fara gasgasta mganar wannan Bafulllatanin na Bakori Daga Sanda Girma ya kamani na zama Cikakkiyar Budurwa duk da dai ni Muhibba bani da wani kyau na azo agani ammh ni kaina nasan ina da Farinjini duk inda na shiga sai na samu masu sona ba ga matan ba ba ga mazan ba,Sannan ina samun makiya Saboda Sanyin Halina da Hakurina yakan siyamin soyayyar Mutanen da nike zaune dasu haka nayi Rayuwata a makaranta bani takamammiyar kawa sai abokan arziki da ake gaisawa dasu kuma har na kamallah nayi Service ban tantance wata Aminiyata ba sai dai ana mutumci sannan akan gaisa ta waya Lokaci bayan Lokaci..

Ko fita nayi Inna ta aikeni bana Dawowa sai wani ya tareni yace yana sona ammh duk wannan Rubibin da ake yi akaina wani namiji bai taba Dadani da kasa ba,ban taba jin wadanda ke sona suna Burgeni ba,Babani ta na nan araye a garin Bakori agidansu Inna ita ke kara Fadama Inna tunda taga bana son kula masu sona Ta tabbata Aljanin ya aure ni kenan ita kuma Inna sai ta yarda da mganarta Sau tari Ya Habiba bai cika yarda ba In inna ta zaunar dashi tana Fadamai sai an mike Tsaye abubuwana suna ta karayin gaba shi dai Sai dai yace koma da wata matsala Inna mu cigaba da gayama Allah Lokaci ne Watarana sai Labari..In yace Haka Inna haushi take ji sai ta kallesa tace"Lokaci ne ammh ai kasan Akwai aure tsakanin mutum da Aljan..Sannan kana da ilimi kasan Akwai junnul Ashiq ko..?

Bai kara mata mgana sai dai ya bata Hakuri Sani ne yafi biye mata in tana irin wad'andan mganganu shima Saboda ya Tsokane ni Sani har suna ya Taba samin wai matar Aljani Tun ina Tankasa muyi ta Hayaniya watarana Inna ta tankamu watarana kuma Tayi banza damu ta cigaba da aikin gabanta,Danagaji ne na kai karar sa wajen Ya Habibu shine ya taka mai Burki ya daina Kirana da wannan sunan..

Sau tari na fi kaunar zuwa Gaya babban gidansu Babanmu akan Bakori Saboda Babani har tafi Inna Zafi gata da Mitar Tsiya in naje garin nan ta rika yawo dani gidajen masu mganguna har fa gidan wani Boka tataba kaini to boka Mana tun da Yana kallona yana Zare ido nan take yace ai Saifudeen ya Dade da aurena ya"yan mu goma ma dashi kaji karya goma kamar wata akuya har tambaya yayi wai bana mafarkin ina shayar da Jarirai na tura baki nace ni banayi Babani ta Dunguremai kai tace ai ko" ki nayi bazata Fadi gaskiya ba abunda yasa nace Boka ne cewa yayi Babani zata bada kudin yanka ni kuma ina da Ilimi na daidai gwargwardo duk da ban yi sauka ba Ammh ai ba inda bazan karanta ba acikin Alqur"ani ba sannan Sauran Littafai ina da sani a kansu har yau har Gobe ban daina Neman ilimi ba Domin shine ado da kyalkyalin ya mace bayan Hallaya mai kyau.
Chapter 17 · 0% Book details