← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 144

Sashe 65

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Laala suna Falo suna ta Fira da su Fati Asma"u kawai aka bari da Muhibba suna falo suna hiran su,gidan shuru saboda duk sun watse sai bayan sallar isha"i Su ya mujaheed suka dawo suka kawo musu Kaji da Madaran Holladian iyakar su Falo suka musu sallama sai da Safe Hotel suka kama suma inda zasu kwana kafin Gobe Saifuddeen kuma basu san ina ya shige ba suma basu nemesa ba.

Su dai sun cin sun sha, Muhibba madaran kadai ta sha ta kasa cin kazan Saboda Cikinta yana Tushe ne,Barci kuma Sai Asuba Muhibba tayi shi Kwana tayi salla da Nafila Saboda Ta kasa barci Tana gani su Asma'u nata barci ita da Aisha da Fati Su Laala da su siyama dayan Dakin suka kwana.

Basu da matsalan ruwan zafi kowanne Tiolet akwai na zafi har da na Sanyi dashi suka samu sukayi wanka Karfe goma Mudansir da Datti suka kawo musu abun karyawan su kayan Tea da ferfesun nama da suka yi oder Sa"adatu na gidan su Muhibba tare da Adda Sadiya Muhibba ta yi wanka ta saka Less dinta mai kyau na kayan da Ya Habiba ya dinka mata ne tun Safe ta rika kiran Inna tana Fadin su Anty Habiba shuru basu zo ba Inna na Mirmishin Farinciki Autar ta ta kwana gidan auranta tace suna Tafe an juma kadan..

Basu suka zo ba sai bayan azahar tare da Tawagar su Mama zuwaira da su Umma Babba Anty habiba da Anty Zeenatu suka kwaso ma Muhibba kayanta na gida duka wadanda ta ware sai kayan lefenta da abubuwan da zata Bukata sai kuma sauran kayan irin su Turare wuta da na jiki Gida ya kara cika kuma sun zo da abinci Aka ci aka sha karamar walima dai akayi aranar yan anguwa duk sun iso Anty Zeematu da yan gidan su Har da kawayen Muhibba na islamiya su Nusaiba da Jamila gida cike da Mutane,Sai bayan La"asar aka fara shirin Tafiya ana ta kuma gyara inda aka bata su Mama zuwaira da su Goggo Naja su suka fara yin gaba suka bar yara yaran na gyaran gida su kuma su Anty Habiba suna shirya Amarya Ta karayin wanka ta sauya kaya ta saka atamfa suka fesheta da Turare.

Basu suka bar gidan ba sai mangariba Suka bar mata Asma'u da Aisha Saboda kada a barta ita kadai su Mujaheed sai yamma suka samu wayar Saifudeen Masifa Mujaheed ya fara yimai sannan ya fadi inda yake suka je suka same shi,sun fadamai sai gobe zasu koma shi kaduna zai yi da matarsa su Mudansir Gaya shi da su Umma Baba Datti kuma Delta zasu wuce shi da matarsa Dakyar suka Samu Saifudeen yayi wanka ya saka Wata Farar shadda mai Babban Riga Dole ya saka Hula Saboda masifar mujaheed sai da sukayi sallar Isha"i suka tafi gidan su Muhibba suka gaida da Surukai Saifudeen dai duk yana jin sa a Takure ne kaza suka siyamai da yoghourt da Madaran Holladian suka Rankaya sai gidan Amarya sai Faman kunci yake yi kamar wanda akace yayi auran Dole.

Afalo suka yada Zango su Asma'un ne suka fito Muhibba dai bata fito ba kuma basu damu ba addu"a suka yi musu basu Dade ba suka mike su Asma"u basu koma cikin Dakin Muhibba ba suka bi bayan su Mujaheed suka bar Saifudeen zaune afalo da ledan kaza a gabansa.

Tare suke da su Bama suna Haraban gidan domin baza su je ko'ina ba Saboda suna kan aikin su ne mikewa yayi yana jin kasala ya nufi Dakinsa ya saka makulli ya bude Hatta wayoyinsa da Ledan kazan nan Falo ya barsu Babbar rigar jikinsa ya Cire Da Hula Domin sun Damesa ya samu gefen gado ya zauna yayi Tagumi ya kasa Motsi haka kurum yake jin wani irin Faduwar gaba ta ina zai fara..?

Yayin da Muhibba bata san me ya faru ba sai da taji shuru gidan sannan tasan su Asma"u sun mata wayau sun gudu tare da su Mujaheed sai kukanta ya Karu tana kan gado tun tana kuka har ta gaji ta Bingire da kayan Jikinta da Hijabin da komai sai barci daman ga gajiyar Biki ga rashin barci.

Shima Saifudden daga bangaransa yana zaunen nen bai san ya akayi ba Sai dai ya tsinci kansa kan gadon ya Bingire da barci Kofar Falo a Bude kofar Dakinsa ma haka sannan ita kanta Muhibba bada shiri Barcin ya Sureta ba.

Barcin daga kan shi zata fara Fuskarta kalubalen dake Tattare da auran SAIFUDEEN..!
_TAFIYAR KADDARAR MUHIBBA DA SAIFUDEEN ZATA FARA_
*Janafty*
*SFD0024*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Barci ne da ya kwasheta cikin yanayin da bata saba kwanciya ba,Ta saba in zata kwanta tana sauya kayan jikinta zuwa na barci sannan ta dauro alwala tazo tayi addu'o'in kwanciya Barci wanda Annabinmu Salallahu alaihi wasallam ya koyar damu kuma ba mugun barci gareta ba Muhibba kawwamuna ne ta biyo Inna wajen yawan Ibada da Sallar Dare.

Sai na yau yasha bambam da kowani Rana wani irin barci ne ya Dauketa wanda bata taba jin irin sa ba jikinta yayi mata nauyin kamar an Dora mata Dutsen kufaina ko yatsanta bata iya Dagawa,bazata iya sanin wani Lokaci bane ammh tasan cikin Dare ne sosai tana kwance gefen gadon da barcin ya tafi da ita abun kamar mafarki yazo mata sai dai kuma ba mafarki bane ya faru a zahiri
Iska ce mai bala'in karfi ta mamaye Dakin gabad'aya Labulan windows na kad'awa tare da Bugawar glass din Windows din suna Gif Gif kamar zasu cire sannan kofar bedroom din yana Budewa yana Rufewa Bam!bam!

Da kunnuwanta take jin komai ammh kuma Idanuwanta kamar an saka Super glue an danne su ta kasa Budewa,Ballatana jikinta da Hannayenta dataji kamar an saka Dutse mai nauyi an danneta bakinta kuma shima kamar an saka mai zare da Allura an dinke mata ta kasa Bude bakinta ballatana ta iya addu"a Sama sama taji ke abun sai ya zama na kamar mafarki take jinsa Daga chan nesa nesa ma.

Kamar wasa taji kamar wani abu ya fado saman kirjinta Ya daketa da Mugun karfi kafin kuma taji kamar kafafun mage ne a saman kanta tana Takata tun daga samanta har kasanta Lokaci daya kuma ta sake jin wannan gigitattaciyar Dariya acikin kunnuwanta lokaci daya ba"a daina Takata ba Akan kirjinta ba,koma wani irin Hallita ne yake daka Tsalle yana Fado mata Lokaci daya ana Sakin wata Dariya mara Dadin ji da Saurare tana ji, jikinta na Faman rawa Zufa na ketomata ammh kuma ko yatsanta ta kasa motsi dashi kamar almara taji an yi sama da gadon take yana lilo a sama Lokaci daya iska taji tana kadawa da karfi har tana jin karan Gadon ta da kuma karan Murafan wardrope din Dake dakin Lokaci daya da madubin dake shake da kayan kwalliya Haka take jin karan Haduwar kwalabe suna bada Sauti Gif! gif!

Da karan rufewar kofa da Murafan wardrope dinta mai shidda,Karan ya Kaure Dakin Tare da Dariyar da bata san daga in take Fitowa ba sai ya bada wani Sauti na Dabam mara Dadin ji da Saurare.
na cikin wannan yanayin taji gadon datake kai ya fara bugun bango Daga yammah zuwa arewa kuma ita ta na kai ammh ko motsi ta kasa tana dai jin yadda aka dinga wujijjigata kamar ana kwallo da ita in gadon yaje Bango Yammah sai taji kanta ko Kafafunta ko kugunta sun bugi bango sun amsa tana jin Lamarin na Faruwa da ita har na Tsawon Wani Lokaci mai Tsaho Sai kuma taji Dif ko'ina yayi Tsit kamar wani abu bai Faru ba kafin Daga Bisani Sauran jinta ya Dauke na Dogon Lokaci ba ita taji duniyar ta tadawo ba sai da karar sautin wayarta na Kidan Larabawa ya dinga shiga kunnuwanta sama sama har dai ta Fahimci a duniyar ta ne abun ke Faruwa kamar wacce aka tasheta daga barcin Mutuwa haka ta tashi a Firgice kamar mahaukaciya.

Idanuwanta ta fara Budewa Lokaci Daya taji nauyin jikinta ya saki gabadaya kuzarinta ya dawo Lokaci daya da Hasken Kwan lantarkin dake Dakin ta Fara cin karo cikin mamaki ta fara bin Dakin da kallo kursuwa kursuwa komai yana nan yadda yake babu abunda ya sauya kanta ta Dafe Lokaci daya ta Runtse ido al"amarin daya Faru yana dawo mata sai dai kuma Tana Tunanin mafarki ne mummuna tayi shi jiya da Daddare Saboda yanayin data kwanta.

Karar wayarta ne ya katse mata Tunanin data ke yi da Hanzari ta mike tsaye jikinta na amsa mata,kugunta taji ya rike da bala"in zafi da saur
i ta Dafe bango tana fadin"Wash..!

Bata kawo wani abu ba sai gajiyar Biki Tana Dafe da bangon ta Dau wayarta kiran ya katse ta duba 15,Missed call tagani gabanta ya yanke ya fadi innalillahi me ya faru..?

Tana dubawa taga Anty Habiba ta kirata haka ma Sani da Anty Zeenatu sai na karshen Adda Sadiya jikinta na rawa ta koma gefen gado ta zauna tana kokarin Laluban Adda Sadiya sai ga Kiranta da Hanzari ta Dauka domin ita Muhibba duk a Tunaninta a suba ne gari bai waye ba.
Chapter 65 · 0% Book details