← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 144

Sashe 102

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuru zuru suka same su suma cikin wani yanayi Inna sai kallon Saifudden take yi shima duk ya Rame Tausayin su ya kamata sai sharan kwallah take yi da Adda Sadiya ta gaisheta ta amsa tana fadin"Sadiya ya muka ji da wannan al'amarin..?

Auta dai sai abunda Allah yayi tana neman ta fice Daga Tunaninta"
Jikin Sadiya yayi sanyi ta kura ma Muhibba ido dake kwance rabin jikinta na kan Inna kanta na kan Sani da shi ya gama shiga wani yanayi bayan ya samu Labarin Muhibba ta Dade cikin Lalurar nan bai taba sani ba.

Mujaheeed yace"Muma hankali tashe yaje ma da safanan..Shi ne muka taho muji ya ake ciki yanzu..?

Ya Habibu na falo suna mgana da Mallam Haruna Anty Habiba
ne tace"Mallam dai yace koma meke Firgirata bai rabu da ita ba sannan kaima yana Shafarka ta yarda zata rika ganin Sufaffinka na sauyawa kamar dai yadda ya faru wannan karon..an mata Rikiya shuru Ammh ya Shaka mata wani mgani Shi ne ka ganta ta bige tana barci"
Jinjina kai suka yi Saifudden kaansa na kasa ya kasa mgana Adda Sadiya ne tace"Inna kawai a kara maida Sister gida zamanta anan akwai matsala"
Sai alokacin Saifudden yayi mgana Cikin Sanyin sa yace"Daman Inna zata tafi da ita"
Daga bakin Kofar Dakin sukaji muryan mallam Haruna yana Fadin"Wannan karon bazata gujema koma menene ba..Zata zauna domin mu gano wani irin al'amari ne"
Gabadayan aka bisa da kallo shigowa Dakin yayi bayansa ya Habibu ne,bai damu da yanayin su ba yace"Zata zauna agidanta in sha Allahu Shi megidan nata tunda bata son ganinsa to yayi nesada ita..ya koma wajen aikinsa zamu yi Turaren wani gayen mganin junnu Acikin kowani kusurwa na gidan nan koma menene ya kusa ya bayyana kansa mugunta ake so ayi mata so ake yi kafin ta bar gidan sai ta HAUKACE"
A Razane suka kallesa kai ya jinjina yana Fadin"Haka ya sha Faruwa wasu in suka kwace suka fita har Abada baza a kara ganinsu ba itama tana da karfin jini sannan addu"a da kariyar Allah na Tare da ita shiyasa kanta bai gama Tabuwar da suke bukata ba har yanzu tsoro yake bata ina kyautata zaton koma menene ransa ya kusa bacin da zai bayyana kansa"
Inna ta saka kuka Tana fadin"tsakaninmu da wannan aljanin sai Allah yayi mana Hisabi"
Mallam Haruna yace"Kada ki Damu Inna zan koma an juma su Gaddabi zasu zo su yi Turare in ta Farka zata farka lafiya lau sai abunda ba"a rasa ba"
Da haka yayi musu sallama ya fice su Saifuddeen suka fita rakashi a mashin dinsa suka zo shi da almajiransa sun rabu kan sai anjuma za"a zo a Turara mganin
Kamar yadda ya fada na Farka da Dama Dama sai dai da kuka ammh na daina Zabura,saifudden bai yarda ya shigo na gansa ba ni kuma yana raina ammh na kasa tambayansa.

Da yammah Mallam Haruna ya Turo su Gaddafi suka Turara wani Turare mai kauri mara Dadin ji Sai tari nake yi Tunda na Shake shi Saifudden nata Fada ai cuta ne shakan wannan Turaran shi Waje ma ya fita ya shiga Mota kaurin Turaran har cikin kansa.

Bayan mangariba su Adda Sadiya suka koma Kaduna Tare da Saifudden da bai samun min sallama ba.

Aranar harta sani a gidana ya kwana,Anty Habiba ce kadai ta koma gidanta ta kwana Taki barin Inna ta koma gida sai da tamin kwana Uku Lokaci na warware sai dai ba Duka ba ammh har na fara kewar mijina kuma na Daga waya da kaina na kirasa da yacemin yana kaduna kuka na sakamai ya tafi bai Fadamin ba Dakyar ya Lallasheni na hakura.

Ganin na fara Dawowa Hayyacina Inna ta koma gida ta barni da Wasila ammh kullum Sani da ya Habibu sai sun zo Dubani da Anty Habiba Ummi kuma Adda Sadiya ta Fada mata ta kirani ta gaisheni gashi dai nasan wani abu ya Faru ammh sai na rika jin komai kamar mafarki ne.

Kwana bakwai tsakanin Faruwar wannan al'amarin Nayi gudun ceton rai gudun da shine Tsanin Silar bayyanar Sirrin dake Boye.
*Janafty*
*SFD0037*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
A Daran cika kwana bakwai da Faruwar lamarin muna zaune afalon Farko ni da wasila wainar Fulawa da manja nace ta soya mana shi kawai naji ina sha'awa bayan ta soya mana,Sai muka hada da Zobon da Anty Habiba da zo mana dashi jiya da tazo Dubani,zaune nake a saman Cafet Wasila na gefe na jan majina nake yi saboda Wasila ta cika Tarugu da yawa sannan ga Yajin Tafarnuwa da nake dangwala wainar Fulawan dashi.

Yanzu ne da yammh nan na sake dazu bani da walwala Saboda kewar Saif duk ta isheni tunda na dawo Hayyacina ban gansa ba sai dai ya kirani a waya dazun ma kuka na gama sakamai akam yazo ina son ganinsa in shima ya Gujeni ne sai ya Fadamin gaskiya Dakyar ya Lallashe ni da gobe zai taho da haka sai naji Sanyi araina naji zuciyata ta yi Sanyi har na sake muna Hirar mu da Wasila.

Shi kuma ba baya son zuwa ba ne,ya na Tsoron yazo abubuwa su sake rikicewa,Komawarsa kaduna ko wa ya gansa sai ya ce Lere wani abu na Damunsa duk ya susuce ya rame yana Fama da wannan Gulity din na ganin duk abunda ya faru Laifin sa ne ammh kuma ya kasa Fadama kowa Tabbas ya fara shinshinar shima akwai wani daya dangance da ke kokarin Shafan Muhibba duba da yanayinsa tun farko sai dai Tsoro ya hanasa ya iya fadin komai mganar da bayan Mahallacinsa bai taba Tattauna ta da kowa ba kuma bayajin zai iya Tattaunata da wani nan kusa.

Yajin da nake dankwalen da shi ne ya Sarke ni Wasila dake kusa dani tayi Saurin bani ruwa a kofi na sha Sannan na koma ina Sauke Numfashi Cikin muryanta tace"Anty yajin nan yayi yawa ko..?sai da nace kada na yanka attarugun nan duka zai yi yawa kikace na saka shi duka"
Dakyar na Bude idanuwana Domin tabbas sarkewan da nayi yajin ya shige ni har saman kaina Majina ta Hanci ta baki Cikin wani yanayi nace"Laifina ne kam wasila ban zata zai yi yawa ba"
Daganan naji komai ya fitar min acikin raina sawa nayi ta tattara komai ta kai kitchen ammh sai da na kara Shan zoben nan cikina sai ya cika ko tashi bana iya yi tun da naji Wasila shuru nasan wanke wanke take yi saboda na koya mata Tsafta bana son barin kwanuka su kwana da Datti sai dai in Dare yayi nisa ne.

Ina da kishigide jikin kujera duk da Tv nata yi ita Kadai Mb3 ce Wasila ke son kallo Saboda Cartoon hankalina rabi yana kansu rabi kuma barci ne ya Fara Dauka na kamar acikin kaina naji ana Knooking din kofar Falon nayi Firgit na Zabura na mike zaune ina zare ido,Na Dauka ban ji Dakyau ba ne jin kuma ban kara ji ba har na maida kaina jikin Cussion din kujera sai kuma naji an sake yin knooking wannan karon harda sallama Cikin muryan mace.

Har ga Allah Murya tayi min kama da ta Anty Zeenatu matar ya Habibu shi yasa na mike cikin rawan jiki ina fadin"Anty zeenatu da daddaran nan..?

Wasila na kwalama kira sai dai bata jiba ga karan Tv ga kuma karan Ruwan Famfon da ta kunna Daga Kitchen shiyasa kawai ina Nishin Cikina ya cika na nufi kofar Falo na Saka hannuna jikin key din na Bude ina Fadin"Anty zeenatu kec.....!

Sauran kalamaina sun samu mazauni ne saman Lebuna na Lokacin da naci karo da wacce na gani Tsaye bakin kofa matar nan ce da take firgitani yau ma Tana Sanye da Fararan kaya ba'a ko ganin kafafunta kanta ma ya Rufe cikin Dogon gashinta sai dai yau Ba'a kasa take ba kamar an Dagata sama,Baya naja da mugun karfin da sai da baya na ya amsa jikina ya fara rawa ina mazari kamar wacce aka Jona min wani abu baya nake ja ina Nuna ta ina so nayi Ihu ko na kira sunan Wasila ammh kuma na kasa saboda yadda bakina ya Kage a Bude kamar an Daskaran dashi.

Matsoni ta fara yi hannayenta a sama masu Dogayen akaifa jini na Diga Daga jikinsu kamar zata kamani sai kara ja da baya nake yi ita kuma bata Fasa bina ba Ina so nayi ihu ammh na kasa ko motsi da bakina sai dai rawan jiki da Bugawar zuciyata da ba daidai yake Tafiya ba.

Haka ta dinga bina har sai da muka Danganta da Tsakiyar Falon sannan na Zube saman cafet din falo kafafuna kawai nake iya Harbawa ammh na kasa yin wani yunkuri,Kamar al'amara sai wutar Falon ta fara Daukewa tana kawowa na tsorata tsoron da ban taba Sanin ina da shi ba na Firgita mummunan Firgitan da bawa yake yi in yaga wani abun tsoron da zai kashe sa a gabansa.

Kafin kiftawa da Bismillah Wutar gidan gabadaya ta Dauke Gidan yayi bakikirin da ko tafin Hannuna bana iya gani Daga Lokacin kuma sai naji kamar an Daki kaina yayi wani Dum!

Dam!

Dum!
Chapter 102 · 0% Book details