← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 144

Sashe 64

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed yace"Yayan matarka ce ita ke Binsa wanda ke karatun Lauya a kano."
Sanin ya kara kalla wanda ke ta Hoto da su Ya Habibu kai tsaye ya samu kansa da cewa"Duk sun fita kyau."
Mujaheed me zai yi in ba Dariya ba,Saifudeen ya ji Haushi sai kawai yayi banza dashi sai da ya gama Dariyan sannan yace"Dama ka san yadda Matar taka take kake mana iskanci..?
bai tanka sa ba,ya wani sha kuni ammh ai yasan Muhibba,koda sau uku ya ganta ammh ya Gama Haddace kamaninta Mujaheed ya jasa wajen su Baffa Hashimu da mutanen Lere suka gaishesu daganan sai wajen su kawu suma suka gaisa sai su baba Surajo suna ta saka albarka Har da ya'yan Babani maza Daga bakori sun zo suma su Ya Habibu ma sun yi musabaha dasu suna Taya juna Murna anan gidan Hakimi akayi kayattacen Walima aka ci aka sha sannan Aka fara watsewa Tawagan Ango ta yada Zango gidan kawu suna shiga Sadiya ta fito Daga Daki Sanye da atamfa Super ta Rangada guda a kunnen Saifudeen kafin ya farga mata sun rufu kansa suna Sakin gud'a akai akai neman guduwa yake yi Mama zuwaira ta rikosa ,Mujaheed da Mudansir suna ta Dariya ganin yadda Saifudeen ya Rude Dakyar ya samu shiga Dakin da Ummi take ya duka suka gaisa Ummi na sharan kwalla ta Dafa kansa Tana Fadin"ALLAH yayi maka albarka..Allah ya zaunar daku Lafiya..!"
Acikin ransa ya amsa mata Ameen bai Dade ba ya fito ta fadamai Sadiya dasu Laala zasu bi su zaria su ijiyesu gidan su Muhibba gobe kuma da Safe su Mama zuwaira da su Umma zasu iske su chan,bai iya cewa komai ba sai Toh Ummi tayi mai Nasihan yanzu girma ya hau kansa Amana ce mai girma ta hau kansa don Allah ya rike auran nan da Mutumci da kima Daga karshe ta rokesa da in yana son ganin Farincikinta kada ya Saki Muhibba in kuma yana son ganin Bakinta ya ce zai Saketa kamar yadda ya saba shi dai kansa na kasa abu Daya ya sani wannan auran ya bambamta da wanda yayi abaya yanaji ajikinsa zai iya zama da Muhibba ko da ba har Abada bane.

Basu yi shirin barin Gaya ba sai da akayi sallar Jumma"a su Ya Habibu sun Riga su mika Hanya su sai daga baya suka Taho da Sadiya da su Laala Bakin su har kunne har da Farko suna Fargaban kada Hamma ya hana su zuwa shi bai ma Damu dasu ba ta kansa kawai yake yi sun isa Zaria Shida saura na yammah shi Saifudeen da shi da Excort dinsa Hotel yaje suka kama anan cikin Sabon gari ya kama Daki yayi wanka ya Huta Saboda bai Taba gajiya irin na yau ba Tunda yau gidansa ba nasa bane yayi tsaki yafi Dubu shi kadai ga yunwa yanaji banda Ruwa yau komai bai shiga Cikinsa ba Odar abinci yayi aka kawomai Sakwara da miyar Ogun itama kadan yaci cikinsa duk ya tushe Sallar La"asar ma da mangriba ya Hada Daganan ya kwanta yana ta barci kamar ya mutu bayan ya kashe Duka Wayoyinsa.

Yasan su Mujaheed na nan basai an nemesa ba su kuwa ya bari da Hidima Datti har da Matarsa Sa"adatu ta Biyo su Adda Sadiya Tunda da ita mijinta yazo ganin zai taho Zaria tace zataje,Sun samu Tarba sosai agidan su Muhibba Anty Habiba ta Dinga ina ta zata saka su ita dai Adda sai faman Tambayan Muhibba take yi Anty Habiba tace yanzu su Goggo Naja zasu je su taho da ita ba jimawa sai gata cikin Lafaya ta sanya wani leshi tayi kyau har ta gaji da kyau Muhibba suka Rumgume da Adda Sadiya ta gabatar mata dasu Laala suma suka Rumgumeta suna murna nan take ta shiga ransu Gabadaya kawayen Muhibba sun dawo gidan Inna Tunda an ce za"a tafi da Muhibba din ne bada jimawa ba yan makarantar sun mata kara duk da wasu gulma ya kawo su irin su Anty Usaina da Khadija suna gidan sai sun ga komai ammh sun sha mamakin ganin kayan alfarman da Muhibba take cirewa tana Sakawa kuma sannan sun ji ana Kiran kwamishina zata aura to basu gama mamaki ba sai da suka ga su Mujaheed da Sadiya suka sakankance da Al"amarin domin ai sun gansu wajem Taron makarantarsu in Tunanin su daidai ne mai makarantar da suke aiki tare ne Muhibba ta aura wanda ta nuna ta sani yace bai santa ba bakin ciki Tuni ya Rufe su suka kasa mgana aransu Tsanar Muhibba ta kama su ita kan Anty Jidda sai Daga baya ta Fahimta ita kam murna ta taya Muhibba acikin ranta.

Sai da aka sa ta sauya kaya ta saka Dogon Hijabi sannan aka kaita gaban Inna da Ya Habibu da su Babani da su Goggo Fa'iza Nasiha dai ba wanda Muhibba bata jisa ba sai kuka take yi Sani baya Dakin yana waje wajen abokansa,Babani Fadi take yi"Ban da yada sirrin auran ki Auta..Yi nayi bari na bari..Ki rike sa da Amana ki kuma zama mai hakuri da juriya..Ki yi mai Biyayya domin shugaban ki ne.."
Ya Habibu kuma Hannunta ya rike ya Damkamata azkar da 40Rabbana da Qur"ani Cikin Dauriya yace"Duk inda kika samu kanki Auta kada ki manta da Allah..Allah ya baku zaman lafiya.."
Yana fadin haka ya mike ya fita yana sharan kwallah Anty Habiba ma sai ta kasa Tsayawa Saboda Kada tayi kuka Muhibba bata san haka abun yake ba Sai da Inna ta rike Hannunta Cikin Kaunar datake mata tace"Auta duk abunda zan fada miki yan"uwana sun Sanar dake..Abu daya zan Fada miki ki zama mai Rufe sirrin mijinki..Ki zama mai tattala Dukiyarsa kada ki zama mara Lura da Tattalin kayan mijinki..Ki yi hakuri ki kuma kara Hakuri ki kuma zama mai Hakuri..Banda kawo kara ban da Tunanin yin yaji ko wata masatala ta Faru Tsakanin ku ku zauna ku warwareta..Sannan ki yi masa Biyayya ya zama Dole tunda kin tashi Daga Hannun mu kin koma nasa gabadaya Daga Karshe ina Umartan ki da kibi Danginsa ki kula da Mahaifiyarsa da kannensa ban amince ki yi musu rikon Sakainar kashi ba ki rike su kamar yadda kika Rikemu Tashi kuje Allah yana Tare dake nima kuma addu'ata bazata gu she miki ba Har sai Ranar da na daina Numfashi."
Muhibba taji Hankalinta ya tashi ta Rumgume Inna tana wani irin kuka Duk dauriyan Inna sai da tayi kuka Saboda kewar Muhibba ta shaku da auta,ko kwama tayi bata agida sai taji ba Dadi balle tafiyar har Abada,Dakyar su goggo Naja suka Raba ta da jikin Inna,Haka take mika Hannu Tana kiran sunan Inna cikin kuka Inna sai ta fice ta zari Buta ta shige Toilet yara ma sai kuka suke kada su Siyama su ji Labari harda Walid,Anty Habiba a tsakar gida suka Hadu da Muhibba ta riketa tana kuka itama sai kuka sai da Babani ta Fara Fadan sannan aka kwace muhibba haka ta kara rike ya zeenatu itama sai sharan kwallah tana Fadin"Auta bamu rabu ba zamu rika zuwa kullum ni da yayanki da ya"yanki."
Kallonsu kawai ake yi cikin Tsausayin su da kauna Sadiya dasu Laala suna ta kallonsu cikin sha"awa,Haka aka Fita da Muhibba tana kuka kamar ranta zai Fita Motoci uku ne har da Wacce isma'il yazo da ita Hudu kenan Sauran mutane kuma adaidaita zasu shiga Tunda ba motocin sosai.

Ai Muhibba na kyala ido taga Sani ta kwace jikinta ta nufi Sani ta Rumgumesa Sani duk Jarumtarsa sai da yayi kwallah Da kansa ya saka Muhibba a mota ya kuma Tabbatar mata da cewa da shi za'a kaita kamar yadda yayi mata alkwari
A motar Mujaheed aka Dauki Muhibba ita da Babani da Goggo barira da Goggo Fa'iza sai Sadiya agidan gaba sauran motocin kuma kawaye suka shiga Anty Habiba da Anty zeenatu sai gobe zasu zo masu zuwa har da Su Anty Usaina sun ce sai sun ga kwal uwar Daka kamar yadda suka yi alkawari Anty Jidda ma ta samu zuwa Sani ma Motar isma'il ya shiga sai GRa gidan Muhibba Junaidu baki har kunne ya wangale get Motoci suka Sulala kowa yaga gidan Muhibba sai ya tafi ya na santi har su kansu su Anty Usaina sun san na gaba yayi gaba na baya sai Tsintar Hula.

Muhibba na Lullube cikin Hijabi Hannunta cikin na Goggo Barira da Babani Har kofar Falon shiga gidan Babani Fadi take"Shiga da kafar baya Auta..Sannan bakin ki Dauke da Bismillah."
Kamar yadda suka Umarceta haka tayi Tare da addu"ar data sani na shiga Sabon wajen sai dai Lokacin data Daga kafa na shiga Falon gidan da Tuni sauran mata suna ciki Taji kamar wata iska mai karfi ta jata ta maidata baya tayi haka kamar sau uku ana Hudu ne bakinta Dauke da Hailala ta samu ta shiga cikin Falon sai taji wani sanyi na shigarta kamar an watsa mata kankara bata Daina Hailala ba har aka Direta kan Bedroom dinta daya fi girma akan gadonta aka sauketa Asma'u da su Aisha suna chan suna ganin Dakuna suna son barka sun hade da su Laala Adda ce ta zauna kusa da muhibba tana Lallashinta,Matan kuma suna ta shiga suna fita suna son barka su Usaina sai yake ammh har suna fadin cewa kila shi yayi kayan Dakin ba iyayen Muhibba ba,balle Kitchen din daya Hadu sai wanda ya gani.

Sani ya shigo har Bedroom dim Muhibba sannan ba inda bai shiga ba acikin gida yana ta son barka yana Fadin"Kai ni dai kwamishina ya bani Daki naga gida.!"
Ana ta Dariya ko kafin ayi mangariba su Babani an maida su gida Anty Jidda daganan ta wuce gida sai gobe,su Usaina ko sallama baau mata ba Sadiya ma gidan su Muhibba ta koma su Laala ta bari anan zasu kwana Tare da Muhibba har da Siyama take makale da Amarya sai su Aisha da Asma'u Muhibba najinsu suna ta Santin gidan Fadi suke"Muhibba kin ga gidan ki kuwa Aljanar Duniya Falon ki Biyu Bedroom ma haka sai guda Daya kila na megidan ne.."
Tana jin su bata kansu take yi ba sai kuka take yi kewar gida da Inna ya gama Cikata.
Chapter 64 · 0% Book details