← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 144

Sashe 74

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibba har ta gama Hada kayanta cikin karamar akwatinta bata Daina mamaki ba kwanaki kenan zasu yi achan..?

Bata da mai bata amsa cikin karamar akwatinta ta gida ta hada abun bukatar ta har da Brush sai da ta Dauka da Littafin azkar dinta kada su je chsn tamai mgana ya watsata Tunda Daman ya fadamata kafin ta fito sai ga kiransa tana Dauka yace"Na tsani jira..Kina batamin Lokaci."
Baki ta Tura bayan ya kashe wayar tace"To ba shiryawa nake yi ba.

Tana fitowa da akwatin nan da ledojin da bai san me ta zuba aciki ba Bama ya karba ya saka a Booth din Farar 4Matic dinsa wannan karon bada prado dinsa yazo ba.

Ciki ta koma ta kashe gabadaya wutar gidan ta kulle dakunanta tazo ta kulle kofar babban falon yana cikin mota yana kallonta aransa yaga iyayinta me ye na kulle Kofar falo shi bai Taba Rufesa ba Tunda yana da megadi shi alokacin ma tunanin yadda zai yi zamam mota Daya da ita yake yi yasan yanayinsa Zama da wacce ba Muharramansa ba akwai Damuwa kamar Tuni yaji zuciyarsa tace"muharraman ka ce Mana Tunda matarka ce..!"
Shi dai bai ma sani ba yana chan yana Tunani yaji shigowarta motar kamar wanda aka Tsikara haka ya koma jikin window ya lafe kamar zai fita a motar itama haka tana ganin yadda yayi itama ta kama kanta ta yi gefe suka bar Tazara mai yawa a Tsakaninsu.

Sun Fice Daga gidan Junaidu na binsu da Fatan Dawowa lafiya,Tunda suka Dau hanya bai ko kalleta ba itama wayarta ta Dauko ta Bude karatun Qur"ani na karatu tana karantawa acikin ranta ammh yana ganin bakinta na motsi shima Tap dinsa ne a Hannunsa yana Daukan lacture ammh Duk yana rude ne baya son wannan zafin dayake ji acikin jikinsa in ya Hada zama da macen da bata da alaqa daahi.

Sai dai kuma Tun yana tsoro har kuma ya saki jiki Sai dai sanyi ne yaga yayi mata yawa tana ta kara rufe jikinta da mayafinta shima sanyin ya fara shigarsa sanin Halinsa ne yasa Su Bama suke kure Tempretute din A.C.ammh yau cikin mamaki yace su yi Low din Tempreture din zuwa kasa nan da nan suka Rage sai sanyin ya Dauke sai kadan kadan da bazai cutar da mutum ba yana gani ta sauke Numfashi ta gyara zama tana kokarin kallon barayinsa yayi saurin maida hankalinsa kan wayarsa gabansa na Faduwa ya rasa meke damunsa baya iya kame kansa indai a gabam Muhibba ne.

Sai gabda zasu isa ya rufe Tap dinsa ita kuma ta maida wayarta jaka ta koma tana kallon Hanya karfe daya Saura suka yi parking a kogar gidan su Saifudden na Lere Muhibba ta Dago tanaa kallon gidan mai kama da ginin zamani duk da samfarin ginin kauye ammh ya samu kwaskwarinma Ma"aikatan zamani.
*Janafty*
*SFD0027*
GIDAN Babban gida ne mai dauke da shashuna guda uku d'aya na Hajiya iya ne,wad'anda ke hade suna kallon juna kuma na Baffa Hayatu ne da Baffa Hashimu su da iyalansu gidan shimfide yake da siminti ba Datti ko kasa sai dai rashim kimtsi na mutanen kauye ko'ina a baza kaya kamar an samu daki.

Tun kafin su shigo cikin gidan Labarin zuwansu ya isa bayan yaran da suka shiga suna Ihun ga Ya Saifu nan,su bama sun riga su shiga gidan Dauke da Buhun doya da na Dankalin turawa sai,sai jarkan manja da mangyada sai kayan fruit jigge a lodoji ita kanta Muhibba bata san dasu ba,kila chan a hayarsa ya tsaya ya siya.

Yana kan gaba tana bin sa a baya har Falon Hajiya Iya wacce ke musu maraba cikin Tsananin Farinciki da ya kasa Boyuwa saman Fuskarta.

Sai faman gyara musu inda zasu zauna take yi Saifudeen ya samu gefe ya zauna muhibba tabi bayansa ta zauna gefensa wajen zama cikin Rashin Sani kafadarta ta gogi nasa kamar ta doramai cuta haka yayi saurin matsawa itama sai ta kara nesa dashi.

Shi ya fara gaida Iya ta amsa tana Washe bakinta cikin Muryanta tace"Yaron nan tafiya haka ba Sanarwa..?ai da sai ka kira ko Baffan naka kace kuna tafe kai da bakuwa ayi muku saukan baki a shiga kuma gidan ku a kintsa muku sai kuyi saukar ku achan..!"
Kansa na kasa bai ce komai ba ganin haka yasa Muhibba ta kara sadda kanta tana gaishe da iya,iya ta kalleta Dakyau kafin ta amsa mata cikin Sakewa tana Fadin"Sannu yar nan..Sannun kinji ko..?

Allah yayi albarka Allah ya zaunar daku lafiya sannun ku da Hanya."
Muhibba ta amsa da Ameem acikin Ranta Iya ta mike ta fice tana kwalama Talatu kira sai gata daga cikin Dakin suke jinta tana Fadin"Ke da gaje baku ji zuwan su Saifu da matarsa bane..?

Inna Talatuwa tace"Yara sun shigo suna Fada iya daman yanzu nake so na shigo mu gaisa."
Iya tace"To ku sama musu wani abun kinji ko..?

Talatuwa mahaifiyar Majeeda ta amsa ma iya cikin Ladabi kafin ta koma Shashenta ta sanyo mayafi ko da tazo Dakin Iya ta iske gaje ta shigo suna Gaisaawa itama tabi bayanta Matuka sun yaba da Muhibba sai kallonta suke cikin sha"awata ita ce ma take amsa gaisiwar tasu cikin Fara"a Gogan kansa na kasa kamar ma bashi a wajem duk basu damu ba Sanin Halinsa
Sai da zasu fice ne Iya tace"Ku sama musu wani abu mana kun gama girkin Ranar dai ko..?

Talatuwa tace"ya kusa sauka Hajiya iya."
Sai alokacin yayi mgana cikin Sanyin sa yace"Iya ba yanzu ba mun ci ba munci abinci kafin mu fito sai dai zuwa an juma."
Iya bata damu ba daman tasan ko Ruwa baya sha in yazo garin ba Domin Raini ba sai haka Halinsa yake Hararansa tayi kafin tace"To kai in baka ci ita fa..?

Yarinyar ai zataci ita ba irinka bace."
Bai iya mgana ba Yaji muhibba na cema Iya a kawo zata ci ya waigo suka Hada ido kowa ya Dauke kansa kamar yaga kashi,Shi dai daga karshe ma Ficewa yayi Lokacin salla ya gabato Itama Sallar tace ma iya zata yi yaran gidan duk basa nan suna makarantar Allo na rana.

Iya ta bata ruwa a buta ta shiga Bayin Iya tsabtacecce ta kama ruwa ta fito ta Daura alwala ta zo tayi salla saman Darduman da iya ta Shimfida mata ko kafin ta idar an cika gabanta da kwanuka Iya ta saka aka siyo mata Fura aka Da ma mata yadda Tsohuwar ke ta Hidima da ita yasa Muhibba ta saki jikinta,Har da Dankali Dafaffe da kuli cikin abincin da aka kawo mata shi ta zauna taci Sosai da dora Fira har kuma Lokacin bai dawowwa ba sai suka cigaba da Hira da Iya tana kara Tambayanta garin su da asalinsu Muhibba na gayamata Iya ta gyara zama tana Fadin"Allah Sarki ai mutanen Garin Gaya mutamem kirki ne kin fito daga Babban gida..naji Dadim auran ku matuka har acikin raina Burina da Fata ne shi ne naga Tsatson Salahudeen tana Hayayafa hakan nasani naji Dadi acikin raina."
Ko kafin Muhibba ta kara mgana Saifudeen yayi sallama ya shigo Dakin bayansa kuma Baffa Hashimu ne nan suka gaisa da Muhibba ta amsa kanta na kasa Iya ta kallesa tana Fadin"Ina dan'uwam naka..?

Baffa Hashimu yace"Baya kusa iya kamar ya shiga kaduna ne."
Iya tace"Allah ya dawo dashi Lafiya ga Diyar taku nan muna ta Hira da ita tun dazu..'"
Baffa Hashimu yace"Naji iya sannun su da zuwa ina fatan nan zasu kwana..?
saifudden naji bai yi mgana ba Sai Muhibba ne ta amsa musu Iya ta Washe baki tana Fadin"masha Allahu ai da kun yi mgana Tun dazu da anje gidan naku an gyara muku sai kuyi kwanciyarku achan."
Yana jin haka gabansa ya fadi da Sauri yace"Iya nan wajen ki zata kwana ita"
Iya bata ko Tsaya bi ta kan manufarsa ba ta shiga washe baki tana Fadin"Lale..Kace zuwan nawa ne to Allah yasa albarka sai mu kwana Hira ni da d'iyata domin bana jika da ita".

Baffa Hashimu ya murmusa bai ce komai ba sai Iya ce ta nuna mai Tsaraban Saifudeen shima yabi ayarinta wajen godiya sai Lokacin Muhibba ta tuna da Tsarabarta ta kallesa taga ya Hade rai kawai sai ta karkata kanta ganin su iya suna mgana cikin Sanyin murya tace"Tsaraba ta fa..?

Yaji ta sai yayi kamar bai ji ba Sai da ta kara maimaita mai sannan ya Daga waya ya kira Bama yace su bude Booth su dauko kayan ta nata kadai ban da nashi ba jimawa sai ga shi Dauke da akwatinta da Tsarabarta sai dai wajen Daukowa Roban Dambun kaza ya shige kasan booth basu gansa ba tamai mgana akwai Sauran ya Dauke kansa sai ta kyalesa Ta mika ma Iya tace a raba ma Yara Da turmin atamfar tace Iya ta dinka ai Iya har da taka rawa tana ta godiya ta kwalama ma su Talatuwa kira sai ga sun shigo Ta nuna musu abun arziki suka taya Iya Godiya duk da bai san da Tsarabar nata ba sai yaji dadin yadda ta karrama Kakarsa da Danginsa ammh a Fuskarsa bai nuna komai ba.

Gabadaya Talatuwa tabama su Cake din tace su dibar mata nata sauran su Raba su dasu da yara nan suka fice suna Rabo Cike da jin Dadim domin yaran sun Dawo Daga Allo.

Majeeda na shigowa taji zuwan Hamma Saif ta Rumtomu Dakin har kasa ta Duka ta gaishesu Saifudden ya amsa kai Tsaye yana kallonta Itama Muhibba ta amsa mata cikin Sakewa tana kallonta Iya ce tace"Majeeda kenan duk murnan tafiya Habujan ne..?To ai zalihar bata ce ga ranar tafiyar taki ba ta dai ce zata aiko a Dauke ki."
Majeeda ta tura baki tana Fadin"Ni fa iya ba murnan Habuja nake yi ba."
Iya ta tabe baki tana fadin"Ke dai kika sani tashi ki baama mutane waje kin tasasu gaba kina faman kallon su."
Ta mike ta fice tana gunguni Iya tace"Kin ma uwarki Talatu gunguni ko Uban ki Hashimu."
Muhibba sai da tayi Dariya Iya ta kalleta tana Fadin"Basu da kunya ne yaran nan..Kin ganta ne zaliha ce ta ce abata rikonta zata tafi da ita Habuja Tun Lokacin ta kasa sukuni Data ganku Tana murna ne ko Daukan ta kuka zo yi."
Muhibba tace"Allah Sarki..!
Chapter 74 · 0% Book details