← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 144

Sashe 43

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya tace"Tana ciki taki fitowa.."
Ummi tace"Je ki kirata su gaisa da YARO"
Ba musu sadiya ta mike ta fita zuwa Dakin muhibba ta isketa ta kasa zama sai kai da kawo take yi acikin D'akin Tana ganin Sadiya jikinta ya Dauki rawa ta koma ta zauna Dabas gefen katifarta Jikinta ba inda baya rawa.
*Janafty*
*15/02/2023*
*SFD0015*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
Adda Sadiya ta kalleta cikin mamaki kafin ta karisa kusa da ita a gabanta ta duka lokaci daya da riko hannayen Muhibba tana fadin"Ki saki ranki Muhibba babu abunda zai faru kin ji ko..?

Dakyar Muhibba ta sauke Numfashi cikin wani yanayi Adda Sadiya ta kara kallonta tana fadin"Ummi tace na kiraki ku gaisa da Hamma."
Sai Muhibba ta bita da kallon karin bayani Sadiya tace"Hamma Saifudeen."
Muhibba sai taji kamar Numfashinta zai dauke cikin wani yanayi ta fara kokuwa da Numfashin ta ganin haka yasa Sadiya tace"Ki natsu..Shaki Numfashi Sama da kasa zaki dawo daidai."
Sadiya ta rika kwantata mata da Kanta har Muhibba ta rika jan Numfashi tana saukewa har sai da ta Samu natsuwa,Sannan Sadiya ta mikar da ita tsaye Hijabinta dake saman akwatinta ta Dauko mata ta taimaka mata ta saka sannan ta kama Hannunta suka fice tana jin yadda Hannun Muhibba ke rawa sannan hannun ya jike da zufa a hannun Sadiya duk irin Turjiyan da Muhibba keyi ,bata sake taba sai da suka shiga Cikin Dakin suka wuce su Saifudden har gaban Ummi sannan ta saketa Muhibba kafafunta sun kasa Daukanta saboda wani iri take ji acikin Jikinta gaban Ummi ta zube kanta na kasa Ummi ta Dago kan Muhibba tana Fadin"D'iyata dago kanki."
Muhibba ta dago ta kalleta cikin wani yanayi Ummi ta nuna mata Saifudeen da kansa ke kasa tun shigowar Muhibba yaji wani Dumi na shiga jikinsa,Kasa kasa Muhibba ta kalleesa Daidai Lokacin da Ummi ta kalli Saifudeen tana Fadin"yaro ga Muhibba wacce rashin Fahimta ya shiga Tsakaninku jiya ashe kuma ku din yan"uwan juna ne."
Inna na dariya tace"Kuma su suka Farfado da zumunci ba,domin in ba haka ba Yaushe Rabon da na ganku Zaliha ai an juma wlh."
Umma babba tace"Ai Daga yanzu komai Damu za"a rika yi."
Inna tace Allah yasa,Saifudden kuwa Dakyar ya Dago kansa sai da yayi Nadama Saboda yana Dagowa karaf sai ana Muhibba yarinyar da in ya kalleta ma wani iri yake ji acikin Ransa gabansa sai da ya fadi ras da Sauri ya kauda kai Muhibba kuwa ta kasa Dauke idanuwanta so take ta kallesa dakyau ta ga abun da ya rabasa da wanchan Saifudeen din sai dai bata gani ba komai iri daya ne Wata zuciyar tace Har da Kamshin Turaren iri d'aya ne..?

Meyasa haka in kamaanni yayi daidai sai ya zama har da Kamshin iri daya ne..?Domin tun da ta shigo kofofin Hancinta suka shako mata wannan kamshin sannan da zasu gifta ta gefensa Sai kamshin yafi yawa Daga barayinsa,Uwa uba kamshin Nasa Turaran ya rika ya Dishashe na kowa a dakin gabadaya Hira suke yi abunsu ba wanda ya lura da Muhibba datake ta kare ma Saifudeen kallo har acikin Ranta so take taga ko akwai wani bambamci sai dai bata ga bambamci ba komai iri daya ne to in ba shi bane ta ina suka hada Komai da wannan..?

Al"amarin da yasa ta fara rasa Tunaninta da inda zata kama sai dai Tana Bukatar wani ya fitar da ita acikin Duhu.

Ganin yadda taki sakewa ne yasa Sadiya ta kama hannunta suka koma Dakin Muhibba din sai alokacin ta Sauke Numfashi mai karfi Ta zauna kan katifarta tayi Tagumi Sadiya ta zauna gefenta ta cire mata Tagumin tana Fadin"Bana ce banda damuwa ba?Muhibba ta sauke Tagumin tana Fadin"Komai fa iri daya Anty Sadiya..Har ta kamshin su shine kai na ya Daure na rasa wani Tunani zan yi shin saifudden din da na sani Shekaru da dama shine wannan ko kuwa akwai wani sabani..?

Sadiya tace"Zan fi jin dadi in kika kirani da Adda domin dashi kowa ke Kirana."
Muhibba ta jinjina kai alamun gamsuwa,Sadiya tayi mirmishi kafin tace"Nagode..Kinsan wani abu..?

Ba ta bata zarafin mgana ba ta cigaba da Fadin"a lokacin da naji labarinki Naji wani iri saboda ban taba jin Labari irinsa ba..Ban zan iya cewa komai ba saboda bansa Labarin Aljanu da mu"amalansu ba ammh Bisa bayanan da su Inna sukayi na Fahimci cewa Wanchan Saifudden din da Hamma mutane dabam Dabam ne,Kamannin da komai da kikace ne bansan me zan ce miki ba abu daya na Sani Hamma na bashi bane wanchan da kika sani nafi bada karfi yana Fito miki ta suffar Hamma din ne."
Muhibba tayi shuru tana jinta kafin tace"Har da kamshin Turaren..?

Sadiya tayi yar dariya kafin tace"Duk zai iya yuyuwa su da suke ganinmu bama ganinsu kin ga kuwa Allah ya basu ikon iya sarrafa ko wani irin abu ne alokacin da suka ga dama."
Daganan Muhibba bata kara mgana tayi shuru Saboda bayanan Sadiya ba komai take iya ganewa ba Sadiya ganin haka yasa itama ta kyaleta ta Samu natsuwa ta fice ta barta ita kadai.

Muhibba tana ta tunane tunane har barci ya Dauketa bata sani ba,Sai wajen Biyu na rana ta tashi shima Hayaniyar su Anty Habiba ne ya tadata ita su da su siyama da suka Dawo Daga Hadda suna cin abinci Tana tashi Sadiya da suke cin abimci da Anty Habiba da Anty Zeenatu suka Hada bakin Wajen fadin"Sannu Muhibba kin tashi..?

Da kai ta yi musu mgana Siyama ce ta kalleta tana Fadin"'Anty ya jikin ki..?

Muhibba tayi mirmishi kafin tace"Da Sauki siyamata..!"
Walid ma ya gaisheta khalipa dai jiya da Babansa yazo ya bisa suka koma Gida mikewa tayi a kasalance ta fita Tsakar gida ta Dauki Buta ta zuba ruwa ta shiga bayi ta gyara Jikinta,Tana Fitowa daidai Lokacin da Saifudden ya fito daga Shashen Ya Habibu suka kara Hada ido Muhibba sai jikinta ya fara rawa shi kuma Saifudden kallo daya yayi mata ya kauda kai kamar ana jansa haka ya Fice Daga gidan da Sauri sai da ya shiga Mota ya zauna ya iya Sauke Numfashi A.C din Motar ya kunna domin Zafin dake cikin jikinsa ne yaji yana Damunsa kan sa ya jingina jikin Kujeran motar ya Dafe kansa wai meke Faruwa dashi ne..?

Meyasa in ga yarinyar nan sai ya rika jin yanayin da bai taba ji ba wajen ko wata mace yanayin da sai a mafarki yakan tsinci kansa,Abun ya Daure mai kai Tun haduwar su daga jiya zuwa yau bai huta da Tunaninta ba da kuma Tunanin yanayin dayake ji in ya ganta wani irin al"amari ne Tare da yarinyar nan..?

Ya rasa me basa wannan amsar sannan akwai wasu maganganun da yake neman karin bayani,ya rasa wanda zai ta
mbaya Mujaheed shi kuma yaga alaman yaga wajen zama shi baisan duk yana Takure bane Daga Dakin da su Ummi ke ciki Masallaci suka je sukayi sallah ya Dauka suna Dawowa zasu tafi Ummi tace sai sun ci abinci,Shashen Ya Habibu aka shirya musu abincin,Har Ummi tana ce ma Inna ga D'anta nan zai rika zuwa cin abinci indai yana Zaria Saifudeen yake kawai yayi Ummi kamar bata san halinsa ba baya cin abinci a duk inda yaga Dama duk da yaga gidan suna da Tsafta sai dai wannan Tsarinsa ne,Ruwa kadai ya sha anyi anyi yaci abinci yace ya koshi Alhalin Rabonsa da wani abu tun Ruwan Zafin dake cikinsa jiya da Daddare da yunwa ta tashesa cikin Dare ya hada yasha Mujaheed ya san karya yake yi yana jin yunwa bazai ci bane shiyasa bai bi ta kansa ba ya saki jiki suna Diban gara shi da ya Habibu jefi Jefi suna Taba Hira Isma"il da Sani kuma suna cikin Dakinsa suna cin nasu Mujaheed da gayya yaki Fitowa da wuri sai da ya gama shanya shi Sannan suka yi sallama da Ya Habibu ya rakosa yayi ma su Ummi sallama kan zai je gidan Saif sai gobe zai dawo in zasu tafi da Ummi ta tambayi Saifudeen sai yace mata yana Kofar gida an kirasa a waya ne.

Har bakin Mota ya Habibu ya rakosa sukayi sallama Dole Saifudeen ya fito sukayi musabaha kafin su yi sallama ya koma Cikin gida su kuma Motar su ta bar kofar gidan har suka fita anguwan ba wanda ya kara mgana Saifudden da Haushi ya kumesa ya kalli Mujaheed yana Fadin"meyasa ka zauna alhalin kasan ina waje ina jiranka..?.mujaheed Hankalinsa na wajen Tuki yace"Kawai kuma saboda kai ban gama cin abinci ba sai na taho..?

Saifudden yayi tsaki bai ce komai ba Mujaheed yace'Gwara na cika cikina gidan ka ba"a samun komai sai ruwa da kayan Tea ni kuma matata ta batani da girke girke bazan biye taka ba na kashe kaina ba."
Karamin Tsaki Saifudden yayi bai kara mgana ba har suka isa Gra,Suna yin Hon Junaidu yazo ya wangale musu get suka shiga ciki,Tim da Bama suna jin dawowarsu suka fito daga Dakin da suke sauka in sun zo garin suka zo suka Bude musu kofofin mota suka Fito Saifudden kamar kububuwa haka ya shige ya bar Mujaheed na Binsa da kallon Tausayi to in ba abun Tausayi ga abinci kaki ci kana Fama da yunwa ai ya zama Dole a Tausayamai.
Chapter 43 · 0% Book details