← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 144

Sashe 77

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kuma suna Falo suna Tattaunawa Saifudden ya riga ya yanke Shawaran Lesson teacher za"a daukan ma Majeeda da Safe ya rika koyar da ita kullum weekend kuma ya koyar da su Laala daman Tun tuni yaso yin haka kuma ta hama Saboda Gidan Barrister da ya riga yace su Laala su rika zuwan gidansa ammh zuwan Majeeda sai itama ta aminta da mganarsa da Niyar nan da wata shekara sai a saka Majeedan a makaranta in ta fara sanin wasu abubuwan.
*Janafty*
*SFD0028*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Suna zaune suna tattaunawa har aka kira sallar La'asar Umm
i ta mike tana Fadin"Ka tashi kaje masallaci kada ka rasa Jam"i."
Da toh ya amsa mata kafin shima ya mike zuwa Dakinsa matuka ransa ya baci a nan tsakar Dakin ta bar mai karamar akwatinta,Kila shi ne bawanta da zai Dauke mata shima haka ya tsallake sa ya shiga Tiolet ya Dauro alwala yazo ya sauya kaya zuwa wata bakar Jallabiya sannan ya fita zuwa masallaci daman a Abuja baya rasa salla cikin jam"i saboda Ummi tana tsaye a kansa ammh da Zarar ya koma Kaduna Sai abunda Allah yayi kawai.

Muhibba ma da Ummi ta leka ta musu mgana kafin ta wuce Dakinta nan wajen su Laala tayi sallar ta bata koma Dakin nasa ba sun idar tana gefe tana Hailala su kuma sun kacame da Hira da Majeeda Laala Sarkin Zence Gwara ma Zeeha ma bata da mgana Sosai.

Majeeda ce tace"Ya Saifu yace zai sakani a makaranta."
Laala tace"Zai saka ki mana Kin ji Dadin ki ma ba"anan yake zaune ba da wannan rawar kan ki daya gyara miki shi."
Ta karishe fada tana Dariya Majeeda bata ma gane mganarta ba tace"Nima zam fara jin Turanci."
Zeeha na Dariya tace"Sosai zaki kara zama yan mata."
Laala na Dariya tace"Toshiyar baki ne Hamma yayi mata Na radadin sakin Aurenta Waahegarin Bikin su."
Zeeha ce ta Dungureta a kafa tana nuna mata Muhibba da tayi kamar bata jisu ba,laala ta Sausssauta murya tana Fadin"Nayi shuru..!"
Majeeda ta tura baki tana Fadin"Ni na daina son sa karatu zan yi.

Me zasu yi in ba Dariya ba Laala Harda rike ciki kafin tace"Duk Birgima da Ihun da kika sha a kansa..Wayyo Ya Saifudeeen ya Sakeni na shiga uku.."
Ta karishe Fada tana kwaikwayon muryan
Majeedan Zeehan ta Daka ma Laala duka itama Dariyan na cinta Majeeda tayi kwalkwal kamar zatayi kuka kasa kasa suke mganganunsu sun zata bata jinsu ne nan kuwa gabadaya hankalinta na wajen su itama tana Dariyan Majeeda acikin Ranta daman ai hadin bai yi ba ita kanta ya ta kare ballatana Majeeda.

Shigowar Ummi dakin ne ya katse Dariyan su Laala daga Bakin kofar Dakin ta Tsaya tana Fadin"Dariyan me nake ji ne tun daga Falo..?

Majeeda zatayi mgana da Sauri Laala ta Tareta da Fadin"Muna hira ne kawai Ummi."
Ummi tace"shi ne kuke damun Muhibba da Hayaniya ko..?

Da Sauri Muhibba tace"Basu Dame ni ba Ummi.

Zeeha ta marairaice ta amsa da cewa"Eh wlh Ummi kasa kasa muke mganarmu."
Ummi ta juya tana Fadin"Ku tashi ku gyara gidan nan bari na shiga kitchen yayanku na gida bazai ci girkin ku ba.

Daga haka ta fice Laala na Fadin"Hamma nan fa ya raina mana Iyawarmu ne"
Zeeha tace"Hamma akwai kyamkyami Girkin Ummi dai Girkin Ummi dai ko ya yake cin na matarsa?

Ta fada kasa kasa tana kallon Muhibba wacce ta mike Tsaye Laala ta karkata bakinta a kunnen Zeeha tana Fadin"Matarsa kika ce..Kuma kinga ita yar gayu ce bazai Raina ta ba...tana jinsu sai da ta Murmusa cikin Ranta tace nima duk irin ku yake kallona a fili kuma sai ta kallesu tana Fadin"Bari naje na taya Ummi aiki.

Ta fada tana kallon Majeeda ta hankalinta ya koma kan wani littafi English tana ta Kallon Hotunan mutanen dake ciki amsa ma Muhibba sukayi da Toh Anty ta fice ta barsu suna Hada ido Aranta tace kannen Saifudeen kamar ba kannensa ba suna da Dadin zama Fiye dashi.

Ummi na tsaka da gyaran Kitchen din sai ga Muhibba ta shigo Ummi na ganinta tace"Me ya shigo dake..?

Oya koma Daki ki kwanta ki huta akwai gajiyar tafiya."
Muhibba ta kariso Kitchen din Tana Fadin"Ummi bafa wani gajiya..Tafiyar ai bata da yawa..Nazo na tayaki aikin ne dame zam kama miki..?

Ummi taji Dadi har afuska sai da ta nuna ta kalli Muhibba tana Fadin"Tuwon Shinkafa zan yi miyar agusi da Naman rago."
Muhibba ta Cire Hijabinta ta Rataye sa a kofar Kitchen tana fadin"Ummi bari mu fara dora tuwon sai mu hada Miyar mu daga baya."
Ummi ta amsa mata da Toh cikin jin Dadi da kara yi ma Allah godiya da ya bata Suruka irin Muhibba.

Ita ta dora Tuwon Ummi kuma sai Tayi Blanding dim kayan miya ita kuma Muhibba sai ta fara Tafasa naman Rago mai Hade da kashi suna aikin su suna Hira Ummi sai tambayan su Inna take yi Muhibba ta tabbatar mata da suna Lafiya Innar ma na gaisheta duk sai da Safen da suka yi mgana ta gayamata yau Abuja zasu zo ta kuma bata gaisuwa ga Ummin.

Daman Muhibba bata da bakunta ga wanda ta aminta da shi nan da nan ta saki jiki da Ummi suna ta Hira su Laala kuma suna ta gyaran Dakunan sun gyara Har Falo sun goge sun kunna Burner kamshi ya cika gidan.

Suna cikin Mulmula Tuwom a Leda Ummi na zaune samam karamar kujera dake kitchen din ita kuma Muhibba tana tsaye ita ke zuba ma Ummi tana kulle Tuwon a leda kamar Daga sama taji Ummi na Fadin"D'iyata ina fatan kuna zaune Lafiya ke da yaro ba wata matsala ko..?

Kanta na kasa tace"Eh Ummi ba matsala."
Ummi tace"In da shi don Allah ki Fadamin..Kada ki Dauke ni a mahaifiyar Yaro ni mahaifiyarki ce Tamkar Yata haka na Dauke ki ki yi ma girman Allah ki Samar dani in akwai wata matsala"
Ta karishe Fada cikin wani yanayi Muhibba tayi saurin amsarta da Fadin"Babu wata matsala Ummi."
Ummi ta kalleta na wani Lokaci kafin tace"Kin Tabbata..!?

Muhibba ta daga mata kai tana Fadin"In sha Allahu.

Ummi ta Rausayar dakai kafin tace"Shikenan in da wata matsala don Allah Muhibba kada ki kira Su Innarki ki kirani ne kin ji ko..?

Muhibba ta daga kai bata ce komai ba ammh Jikinta yayi sanyi Saboda kada Ummi ta Fahimci wani abu yasa sai tayi Saurin gyara yanayinta sun gama Tuwon sun zuba cikin wata Cooler mai girma miyar ne bata karisa ba Ba zato kawai Muhibba taga Ummi ta mike Lokaci daya ta riko Hannayenta cikin nata Kafin tace"Muhibba wata alfarma nake so na roke ki."
Muhibba tace"Haba Ummi ai ni yarki ce ba alfarma zam miki ba Umarni zaki bani kawai nabi.

Ummi ta yi mirmishi kafin tace"Muhibba Amanar yaro zan damka a hannunki bai da kowa sai ke..Kece kike kusa dashi a halin yanzu."
Muhibba ta kalli Ummi cikin mamaki ammh batayi mgana ba Ummi ta gyada mata kai tana fadin"Eh hakane bashi da kowa sai ke Muhibba..Ni na Haifi SAIFUDEEEN ammh kuma ban zauna dashi na shaku dashi a matsayina ta uwa a wajensa ba..Yana da Shekara goma aduniya Conel ya rasu daga Lokacin kuma Rikon sa ya koma Hannun dangin mahaifinsa Sadiya ce kadai ta zauna Dani har na aurar da ita ammh Yaro bai zauna Dani ba ban zauna dashi bai san Dadin Uwa ba Sai da ya girma ban ginasa kan Tarbiyata ba in na Tuna wannan abun har kuka nake yi Muhibba Yaro ya tashi a Lere yawancin Rayuwarsa a makaranta yayi ta bai da wanda zai kula dashi in takaice miki shi ya kula da kansa har girmansa hutu kadai yake zuwa min shima ba ko da yaushe ba Sannan Daga baya ya tafi kasar waje ya Dade bai Dawo ba Hatta su Laala bai san Haihuwarsu ba yana Dawowa ya fara Aiki a zaria ba dadewa aka bashi kwamishina ya koma Kaduna da zama chan yake Rayuwarsa shi kadai bai da kowa sai ni da yan"uwansa Rayuwarsa tafi yawa cikin Kadaici Muhibba ni na Haifi yaro nasan Halinsa Tunda ya amince zai zauna Dake to kina da matsayi a wajensa Ki yi Hakuri dashi ki kara Hakuri dashi Sannan ki kula dashi Ki kula dashi kwatankwacin kular da bai Samu awajena ba Yaro yana da kyamkyami baya cin abinci in dai ba nawa ba ammh nasan ke zai ci naki ina da wannan yakinin,Ki kula cikinsa Don Allah ki gusar mai da yunwar da Dade tana Damunsa Ki kula da mu"amalarsa da mutane sannan ki kula da Ibadarsa..Domin yana da Rauni wajen Ibada ni uwace abun na Damuna bani da yadda zan yi ne bazai yi kusanci dani a wannan shekarun nasa ba ammh ke matarsa ce kina da kusanci dashi ta bangarori da Dama don Allah ki Kula dashi ki kuma kula da Ibadar sa ina baki tabbacin zaki ji Dadin zama da yaro Fiye da yadda kike Tsammani."
Ta karishe cikin karyewar murya Muhibba itama duk jikinta yayi sanyi cikin wani yanayi tace"Ummi meyasa shi bai zauna a wajen ki kamar yadda Adda Sadiya ta zauna ba..?

Ummi ta dago ta kalleta kafin ta kauda kai ta koma ta zauna cikin Sanyin murya tace"Muhibba samu wuri ki zauna.
Chapter 77 · 0% Book details