Sashe 143
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daganan Lere muka yada zango a Dakin Iya na sauka wannan karon itama tana ta fama da kafa da jikin Girma mun kwana Biyu agarin Sahla ta sha Dauka ni in ba Nono zan bata ba Sahla bata zama ahannuna.
Abuja kuma bamu je ba muka bari sai mun koma Kaduna gabadaya ban yarda mun koma sai da na gyara kaina da Taimakon Anty Habiba,Saifudden wani irin mutun ne mai Hakuri da kawaici sannan yana da Tattalin Lafiyata fiye da komai a Rayuwarsa bawan Allah yafi wata uku bamu hadu ba sai da muka Dawo Daga Lere sannan muka kara Haduwa da juna Dagani har shi sai da mukayi Hawaye yana godemin ina Gode masa shi dai Fatansa kawai na kula da kaina Domin in wani abu ya sameni to shi fa bazai yi amfani ba.
Sai da na hada wata Hudu cif a zaria sannan muka koma Kaduna,Ba wanda ya Rakamu dagani sai Mijina sai Sahla nasan da Sani na nan zai Rakani sai dai Yana Abuja sun shiga Barr tun wanchan Satin.
Ranar da muka Dawo Wasila ta Dawo ta tayani muka gyara gidan da Sauran ayyukan Sahla na goye ram a bayanta Allah yasa bata da Rigima sosai.
Sai da muka Huta,Ranar jumma"a da muke da Sati Daya da Dawowa Kaduna muka sauka abuja Wannan karon Harda Adda Sadiya da Mujaheed,Ummi ta ga baki kamar Daga sama su Laala kamar zasu Tsaga gidan Saboda murna ga su Sahla da su Nihad Ummi ta kasa zama baiwar Allah ta Dauki Sahla ta Dauki na wajen Adda Sadiya duk murna ta cikata Ni da Adda Dakin Ummi muka sauka mazan kuma Dakin Saifudden.
Garin Abuja ya yi min Dadi matuka Sati Daya muka yi mun sha Yawo park park ba in da bamu je albarkacin Mu har da su Laala muke zuwa Ummi dai tana gida sai fada da take yi mana kada mu kwaso ma yara Sanyi.
Dukkamu arana Daya muka Dawo,Tunda Wannan tafiyar nace zan huta agida domin nagaji ban je bakori ba Saboda Baa babani ban kuma san wajen wa zani ba Shiyasa itama Inna bata matsamin ba.
Na kwantar da Hankalina ina Cigaba da Renon Salha ni da Saifudeen,jikima da zuciyata gabadaya sun samu Hutu,Saifudden kuma suna Tsakar Siyasa an yi zabe Lafiya Shugaban kasa mai ci ya koma sannan dayawan gwamnoni ma sun koma Kujerar su ciki har da Gwamna Abdulhadi Shutu abun farinciki ma bai Sauya ma Saifudden mikami ba Duk da duk ya sauya wasu kwamishinonin,ammh shi kam dan Amanan gwamna ne sunan sa ya kara zanawa a karo na Biyu a matsayin kwamishinan ilimi na Jahar Kaduna.
Saboda murna har Walima na hada agidanmu na Kaduna na tara yan"uwa suka zo suka tayamu murna,Sani zasu yi Calling of bar a garin Abuja,Sani yaci burin wannan karatun nasa Allah Sarki Burinsa ya Cika Ni da Saifudden mun je tare da Sahla,Ummi da Tawagan ya"yanta sun zo Adda Sadiya da Mujaheed Ya Habibu gidan gabadaya yazo da su Har da Inna Domin Sani yace yana bukatar ganin Inna a wajen,Daga Gaya Mama zuwaira da Isma"il da Mudansir sai Baba Jibirl,Anty Habiba da duka iyalanta Mota guda ita da Abban Walid..
Lokacin da na Hango Sani cikin lauyoyi yan"uwansa sun saka kayan su na Lauyoyi da Hulanansu sai da nayi hawayen Farinciki Saifudden ya Rumgumo ni gefen kafadarsa yana Fadin"Finally He is now a Barrister Muhammad Sani bello mai Rago"
Ina Dariya na share Hawaye na ce"Yes Saura Burinsa Daya na zama lauyan gwamnati"
Saifudden ya kalleni kafin a Hankali yace"shima in sha Allahu ya kusa cika"
Kara lafeewa nayi jikin mijina ina Mirmishi Sahla bata hannun mu tana Hannun iyayenta su laala..bayan an gama tarom muka samu ganin Sani ana ta mai Fatan alheri ya Rumgume Inna ya saka mata Hular kansa yana Fadin"Alhandulillah Inna ta zama maman lauya"
Gabadayan mu muka saka Dariya na mikamai Hannu muka sarke ina Fadin"Congratulation ya Ahki..Ummu Sahla da Sahla suna maka Fatan alheri"
Kawai sai ya Rumgumeni yana Fadin"Nagode kanwata..Thank you for ur support"
Na jinjina kai ina Dariya haka ya Rumgume Saifudden yana Fadin"Ina kara godiya Abu Sahla"
Saifudden ya shafa Kumatun Sani yana Fadin"Har na Hango mana Sabon Lauyan mu na gidan gwamnati Barrister Muhammad Sani"
Gabadaya muka yi Dariya ganin yadda Sani ke wani Blushing,Haka ya rumgume ya Habibu da Anty Habiba yana ta zuba musu godiya Ummi da Mama zuwaira suka yi mai Fatan alheri ya amsa haka su Majeeda suna ta fadin"Congratulation Bro"
Yana amsawa da"Tanque yan matan gidanmu"
Laala ce ta coge taki mgana Sani ya kalleta yana Fadin"Ke ko yar congratulaton din bazaki iya ce min ba..?
Zeeha tace"Itama tana so a tayata Murna ne Domin cigaban ka nata ne ko Laala.?.
Kallo sai ya koma kansu ganin haka yasa Laala ta Boye bayan Ummi Mama zuwaira tace"Ah to Allah ya tabbatar da alherinsa muna murna"
Inna da Ummi dai suna ta Mirmishi basu ce komai ba Sani suka Rumgume da isma'il yana Buga bayansa yana fadin"Ina murna My Barrister"
Sani ya amsa cikin jin Dadi Daganan mukayi Hotuna Sai muka ci abinci Ummi tazo mana dashi sai yammah muka koma gidan Ummi Sani kuma chan muka barsa sai yace sai nan da kwana Biyu zai dawo..
Kwana Daya muka yi muka juyo kaduna yan zaria kuma suka yi zaria su Mama zuwaira kuma suka sauka agaya.
********
*MURFI*
*SHEKARU BIYAR DA SUKA GABATA*
Alhmdulillah zan ce ga Dukkan Ni'imominsa gareni Tabbas bayan wuya sai Dadi sannan ko wani kaddara akwai karshenta bayan Kaddarorin da suka Zagaye rayuwata ni da Saifudden yanzu sai dai mu yi Hamdala mu godema Allah
Cigaban Rayuwa ta ko'ina ya rufe Rayuwarmu a yanzu haka watanni Takwas da suka gabata mun bar Kaduna mun Dawo Abuja da zama Sakamakom Ministan ilimi na kasa baki daya da akayi ma Dr.Saifudden,Tunda Shekaru hudu Gwamna Abdulhadi ya gama wa'adinsa ya sauka sai aka bashi mataimakin Shugaban kasa a jami'yarsu cikin ikon Allah kuma suka Haye bai manta da Mutanen kwarai irin su Saifudden da suka taimakamai wajen tafiyar da Mulki a kaduna,Ya ko zana sunan su ga Shugaban kasa shi kuma ya kai gaban yan majilinsu kasa suka Duba Chanchanta rana tsaka mukaji wannan abun alkairin gashi Lokacin an bashi Co'dinator na Department din B.A english na Abu samaru sannan yaje U.S america a shekaran baya ya yi Course kan abunda ya Shafi Siyasar cikin gida.
Yan"uwa duka sun tayamu murna sai da muka shiga gidanmu na Abuja sannan muka yi walima,an samu Cigaba sosai ta fannin Rayuwa sannan an samu rashi Iya dai Lokaci yayi sai Fatan Allah ya jikanta Sannan an samu aure aure Sani yayi aure tare da Laala sannan burinsa ya cika yana Daga cikin Lauyan gwamnatin jahar k kaduna da taimakon Ministan ilimi Dr.Saifudeen Salahudeen lere.
Isma"il ma yayi auransa da Saudat suka Daidaita a kano suke zaune inda yake aiki,Majeeda ma tayi aure ta na nqn Abuja likita ta aura kanin Barrister Mu'az ne,Zeeha kuma gombe ta Lula wani abokin ya Mujaheed ta aura dukkansu sun Haihu,Ummi ta yi Ritaya ta ijiye aiki tana Gida tana Hutawa Wasila ce kadai batayi aure ba tana Hanunmu har Lokacin ni da ita mun fara karatu a University of Abuja ni ina Master ita kuma Tana Degree dinta Na cikama Inna Burinta na kai ta Hajji nima naje Sannan Sani ya kara kaita ita da Ya Habibu da ya kara zama uba yanzu Sannan Khalipan Anty Habiba yana Lagos wajen su Adda Sadiya da aiki ya maida Mujaheed chan,yana karatu ne a Lagos University.
Sani ya sa an rushe gidanmu an sake gina na zamani ya Habibu ya gina Gidansa a Hanwa chan suka koma Sai Baba Lami ta Dawo gidan suna zaune Tare da Inna,Sai barayin Sani da Ya Habibu in sun zo ganin gida.
Rayuwa duka ta cika da komai na Ni"imar Ubangiji sannan Gaya ma Babban gidammu duk an sauya musu Fasali,Kawu dai yace har Abada bazai bar Gaya ba shiyasa Saifudden ya kyalesa ammh ya kara gyaramai gidansa da Sabuwar mota.
Chan lere ma ko da ba ran Iya ba abunda ya Rage su da shi ni kaina ba"a barni a baya ba,Nihad Da Sahla duk suna Hannun Ummi wajen suka fara karatu bayan Sahla na kara Haihuwan Mai sunan Inna Fatima muna kiranta Batula sannan na kara yin mai sunan Anty Habiba,Muna kiranta Hibbana sai kuma karaminnsu YARIMA SAIFUDDEEN acikin shekaru Biyar nayi ya"ya Uku atare,Ina son ya"ya Haka Zalika shima Saifudden yana son yara shiyasa ko da wasa ban fara Tsarin iyali ba ko da na Fara karatu.
Saifuddeen ya kara Bunkasa SAIFUDDEEN ACADAMY,ya yi Reshenta a garin Kaduna sannan yana nan yana kara bude wata makarantar anan Abuja mganar Sani da Mujaheed ta Tabbata gidan mu gidan ilmine gaba da baya,sannan kuma Saifudeen
Ilimi ne da Kafafunta ba Sako ba."
Har zuwa wannan lokacin zumunci b
ai yanke ba tsakanin mu da Ahalin Gidan Baba mallam ba,Hajiya tazo lokacin muna kaduna lokacin da na Haifi mai sunan Inna batula,Ita da Hanne suka zo min barka da kayan arziki Amina kuwa muna waya ko da wani Lokaci mun zama kawayen juna sosai nake kaunar Aminene ita din ta Musamman ce.
Bayan shudewar wasu shekaru biyun.
Mun aurar da Wasila ni da Saif Shekara daya da ya gabata,Tana auran wani Navy anan Abuja,sannan na samu nasaran kamallah karatun na,Na fito da shedar takardan Mastas Degree d'i na akan abunda ya shafi Biology Education wattani da suka gabata.
Ban taba sanin makarantar da yake ginawa ni ya ginmawa ba,Har zuwa Lokacin da aikin makarantar ya kamallah,bai taba fadamin ba,Nasan dai yana gina Sabuwar makaranta anan garin Abuja ammh na Dauka Reshen ta zaria ce zai samar da ita anan Abuja.
Sai Ranar da za"ayi walimar Bude makarantar sai ya Hadamin da Walimar Gama karatuna a Jami"ar Abuja.
******
*Abuja..*
Sanye nake da wani Less mai kyau da Tsari mai ruwan dark Blue da Kwalliyar pink sai na saka Lafaya na Nade jikina da shi Kibana ya sauka sai dai ban koma rammiya ba,Shekaruna yanzu Talatin da Biyar na tashi Daga matashiya na shiga jerin manyan mata domin da matam Ministoci nake gogawa.
Bani da masaniyar gayyar da Dr.
Saifudeen yayi min ni dai kawai yace na Shirya zamu fita.