← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 144

Sashe 54

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tace"Bata sani ba in ta dawo yau Ni da yayanku zamu sanar da ita ni nace kada a fadamata abaya kin san Halinta zata ki mganar ne kuma kinga Shekaru na Wucewa Habiba bazamu Biyema Auta ba."
Baba Surajo na jinjina kai yace"Kin yi Tunani Fatima ai Don ma kuna Birni ne in chan Gaya ne ai da Tuni tana Dakinta da ya"yanta."
Anty Habiba ta Hadiye mganarta kafin tace"to inna wanne daga cikin ya"yan kawun..?Kuma a ina yaga Muhibba din..?

Inna tace"To ni dai bai Fadamin sunan sa ba..ni dai ina Tunanin Mudansiru wanda ke bin babban Datti da yayi aure kwanaki."
Ya Habibu yace"Nima shi nake Tunani."
Baba Surajo dake sauraransu yace"Ku Dakata wai wani Mudansirun naji kuna mganar shi da Muhibba.?

Ya Habibu yace"Ba shi bane wanda zai auri Auta din ba..?

Baba Surajo yace"Wani Mudansiru..?Dan wajen Alhaji sunusin kuke mgana..?

Inna tace"Eh inace shine mai neman Auta din.?

Baba Surajo ya gyara zama yana Fadin"To ko dai baku ji da kyau bane..Bafa dan wajensa bane..D'an wajen Zaliha ne kaninta Babban yaronta da suka Haifa da mijinta na Farko Sojan nan mutumin lere..babba ne dai domin mun hadu dashi a Wajen gaisuwar diyar Alhaji Data rasu har muka gaisa dashi sunansa ne na manta ya shigemin."
Tsakanin Inna da Ya Habibiu da Anty Habiba suka fara kallon juna a ka rasa mai mgana sai Anty Habiba ce tace"SAIFUDEEN..!

Da sauri Baba Surajo yace"Kwarai an yi haka Saifudeen kamar kwamisina ne akace anan yankin ko..?

Sai alokacin Ya Habibu yace"Eh kwamishinar ilimi ne na jahar kaduna."
Baba Surajo yace"Ba shakka..Iyayensa masu karamci ne Su suka zo nema masa auran anyi komai cikin girma Gaskiya tayi dace duk da ban zauna da yaron ba na gansa yana da cikar kamala."
Inna dai hum kawai ta iya cewa ta kasa mgana ba basu Furta komai gaban baffa Surajo ba illah Ya Habiba daya muna basu ji sunan dakyau bane,Baba Surajo bai tafi ba sai da aka Raba Kayan alewa gida uku aka bashi kashi daya na Mutanen Gaya dangin Uba kenan sauran muma akabar su nan Dakin Inna sai bayan Azahar bayan yaci abinci yayi musu sallama Ya Habibu ya rakasa tasha ya Hau mota bai Dawo gida ba ya wuce wajen aikinsa kasuwa duk da abun nata basa mamaki sai dai bai Damu ba, Tunda Namiji ne shi.

Anty Habiba ke ta nanata mganar da Inna ta gaji ne tace"Habiba kiramin Alhajin sai nace na Fasa basu Auta tunda ba Dan wajensa bane."
Ta fada ranta bace Anty Habiba tace"Allah ya baki Hakuri Inna ni ba haka nake nufi ba..

Inna tace"In ba haka kike nufi ba sai ki gayamin nufinki.?

Anty Habiba ta zauna gefen Inna tana Fadin"Inna gani nayi Auran nan kamar ba irin auran da muke so Auta tayi bane..Inna Saifudeen din ko Taba mgana da auta basu yi ba sannan kin fa gansa bai da sakewa kwata kwata bana Tunanin shima yana son auran nan kada fa mu yi abunda zai zo yana Damunmu Inna kinsan Halin Auta fa."
Inna tayi shuru kafin ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Kema kin yi mgana Habiba sai dai ina mafita.?

Babu bakin Alkalmi ya riga yagama Bushewa..Daman inaga chan Abunda ya kaddara kenan shiyasa Haduwar ta haifar da Sabani Habiba namu addu"a ne kawai da Fatan Alheri in ba Alheri bane Allah sai ya musan ya mata yanzu dai ku lallasheta ku nuna mata Martabanta shine gidan auranta."
Anty Habiba tausayin Inna ya kamata sai ta gyada kai tana Fadin"Shikenan Insha Allahu zamu mata mgana."
Inna ta shiga sakama Anty Habiba albarka,Tare da Inna da Anty Zeenatu da Anty Habiba ta kirata Innata mata bayani itama tana ta Murna suka Kara Raba Mintin Daya suka bar shi wanda Inna zata kai ma Danginta na Bakori sauran suka Raba aka Dibarma Inna wanda zata bama makota,sai na Muhibba har Sani sai da Inna tace su ijiyemai nashi shima ya Habibu an Dibar mai shi da ya Zeenatu sauran kuma Anty Habiba ta Dauka ita da ya"yanta da mijinta.

Koda Auta ta dawo sai Buhunhunan Masara ta gani bata kawo komai ba Zaton ta Na yaya Habibu ne,agajiye ta Dawo Dayake sun gama Jarabawa Gobe ma Hutu zasu yi aikin Report card da Shigar da Record ya sakata gaba bata tsaya ma lura da yanayin su ba.

Ammh tayi mamaki har Dare Anty Habiba bata tafi ba su Siyama suna gidan kakaninsu sai da ya Habibu ya Dawo tana Dakinta tana aikin Report Card taji kiran Inna tatashi taje yanayin data ganau kadai ya isa taja Jinin jikinta sai dai tun Fara Jawabin Ya Habibu na nasiha da Tausaswa tasan wani abu ne ya faru jikinta sai da ya Saki Lokacin da Ya Habibu ke Fadamata an biya Sadakinta kuma an saka mata ranar aure nan da wata Biyi.

Gabanta ne yayi mummunar Faduwa sanda taji inna na fadin SAIFUDEEN ne wanda zata aura..Saifudeen dai Data san Labarinsa kwanakin nan.

Ashe shiyasa Sadiya take ta Kiranta bata gani ba in tazo kuma ta gani ta kirata baya tafya sama sama ta ji yadda komai ya faru bata isa tace wani abu ba Tunda aikin gama ya gama Kanta yayi mata nauyin da bata samn wani abu zata ce ba.

Kanta na kasa tace"Allah ya sanya alheri."
Kawai tace tatashi ta Fice Inna ta rakata da saka albarka tana komawa Daki Saboda kada ma abun ya dameta sai ta cigaba da aikinta ammh Rabin Hankalinta baya jikinta ganin kada tayi lissafi ba da kyau ba yasa ta tattara komai ta ijiye ta koma gefen Katifarta tayi Tagumi sai ga Anty Habiba ta shigo ganinta yasa ta tashi ta Nufeta tana kuka ta Fada jikinta ita ta Dinga Lallashinta da bata mganganu har taji hankalinta ya kwanta Sai Goma Abban walid yazo ya Dauketa bata bar gidan ba sai da Taga Muhubba ta saki ranta.

Muhibba ta Dawo Dakinta ta kwanta Idanuwanta na kallon Ledan Alewan da Anty Habiba ta kawo mata wai na Saka Ranar ta da Mutumin da bako ne a rayuwarta da Duniyarta gabadaya duk da yana da alaqa da kaddarata ammh ai gaskiyan sani ne wanna
n Sabani ne wanda ta sani ba Mutum bane bata jinsin alaqa dashi wannan kuma yafi karfinta ammh kuma ta ya ya yanzu kaddaran ta zata Hado su zama a waje d'aya a karkashin Sunar ma"aiki mai Suna AURE!?
*Janafty*
*SFD0020*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Washegari jumma"a ranar ne zasu yi Hutu ba domin haka ba kwanciyarta zata yi taki zuwa saboda yanayin datake ciki ammh bazai samu ba,Saboda Alhakin sallama yaran suna wuyanta ne.

Haka taje sukuku wadanda suka santa sosai irin su Uncle Hafiz sai da suka Tambayeta ko tana Lafiya tace Lafiyantaa lau,Ana gama bada Hutun sallama ma sama sama suka yi da su Anty Jidda duk yadda ta rika nacin tazo su je gidanta sai da Muhibba ta Zille Adaidaitan su siyama tabi zuwa Gidan su saboda Yau da safe Inna Haushi ta ba ta yarda ta ganta tana ta Kulla alewar saka rana sai faman Fara"a take yi tana gayamata zata aika ma makota da abokan arzuka ta gama Fahimtar Inna in tace zata ce wani abu kan wannan auran Inna zata iya Saba mata da Haushin Abun ta baro gidan sannan Inna tun Safe tayi Sadakan Kuli kuli Kuma tasan saboda haka din ne duk da sadaka ya zama jinin jikin Inna.

Anty Habiba sai dai ta ganta ita da yara Taji Dadin ganinta Daman da ita ta kwana aranta kwata kwata Muhibba ta kasa sakin jikinta Sai Siyama ne ma ke Debemata kewa da Surutunta Ita dai Anty Habiba nata Nasiha ne da bin baki Hatta Abban Walid daya dawo ya ganta Bayan ya natsa sai da ya Kirata ya kara mata Nasiha sosai mai ksshe jiki wanda yasa data koma Daki sai da tayi kuka Daga Karshe ta share hawayenta Tabi Shawaran Anty Habiba ta mike ta Dauri alwala ta fara sallar Nafila sai har sai da tayi sallar asuba tayi azkar sannan ta bingire tana barci ta yarda ta Amince zata bi Lamarin da addu"a.

Inna kuma Tunda taga bata Dawo ba tasan Tana gidan yar"uwarta ce ammh Saboda Tabbatarwa sai da ta Kira Anty Habiba ta tambayeta ta amsa mata da tana gidanta.

Cikin wani yanayi Inna tace"Habiba ki kara Lallasamin Auta kin ji ko..?

Ki nuna mata tabi Lamarin da addu"a kawai In alheri ne Allah ya tabbatar in babu kuma Allah ya zaba mata wanda ya fisa."
Anty Habiba ta amsa da "Ameen Insha Allahu Inna."
Da haka sukayi sallama kuma itama Daga bangaranta Autar take tayawa da addu"a kuma har ga Allah taji Zuciyarta ta kara kwanciyar da al'amari sakamakon jiya bata samu barci ba,Barcinta ta sha aranar sai gabda azahar tatashi tayi wanka tayi sallah sai kuma taji zuciyarta ta sauka Kasalar ya ragu har ta fito Falo suna Hira da Anty Habiba su siyama suna makaranta acikin Hirar ne Anty Habiba ta kalleta tana fadin"Kin rabama kawayen naki alewar..?
Chapter 54 · 0% Book details