Sashe 110
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka ya fito jikinsa a sanyaye su kawu ya fara ma fadan yanayin da nake ciki bai kamata arika shiga inda nake ba suna taimako na ba ne suna kara Rikita Tunanina ne a yanzu a yanayin da nake ciki kowa Mugu ne zai kasheni nake Daukan su saboda haka su yi nesa Dani har zuwa Lokacin da zan bari kwakwalwata ta fara karban Treatment din su.
Nan ya bar su Anty Habiba nata kuka,Abun gwanin ban Tsausayi,Allah Sarki Iya tana sharan hawaye tana Fadin"Shiyasa nace muku ciwon nan na yarinyar nan ba nan ba ne kun ki yarda dani"
Adda Sadiya na jikin Ummi tana sharan kwallah tana fadin"Nima dai na fara zargin haka Ummi ku yi ma Hamma mgana Abun sai kara gaba yake yi kullum ba Sauki"
Ummi ta kasa mgana Kawu ne ya waiga yana Fadin"ina shi Saifu din.?
Mujaheed yace"Yayi nan hanyar Kawu.."in da mujaheed ya nuna mai yabi chan ya gansa ya Rakube a wani Baranda yana ta rawan sanyi sai ji yayi an Dafa kafadarsa ya juyo a Firgice yana ganin kawu kawai sai ya Fada jikinsa ya fashe da kuka mara Hawaye yana Fadin"kawu laifina na ne..Kawu duk ni naja wannan abu..Wlh Laifina ne..'
Kawu ya rikesa cikin Tausayawa duk ya Dauka cikin Firgici yasa Saifu fadin haka bai san abunda yake mgana akai Dabam ba.
Bayansa Kawu ya shiga bubbugawa alamun Lallashi kafin ya Dagosa yana Fadin"Ka da kayi fushi da Jarabawan Ubangiji da ikon Allah mun kusa cinye wannan jarabawar.
Saifudeen ya kalli kawu cikin wani yanayi kafin yace"Kowa haka yake Fadi kawu..Kalli Halin da Muhi take ciki..Sai yaushe ne zata koma kamar kowa..?Zuwa yaushe ne komai zai Daidata din..?
Kawu ya girgizamai kai yana Fadin"Kada Firgici ya saka kayi Sabo mana Saifu..Kada ka manta muna da tauhidi mun kuma yarda da Allah ke yi alokacin da ya so.
Ka aminta da hakan..?
Kai ya gyada mai Kawu ya Dafasa yana Fadin"Naji dadin haka to mu kaima sa kukan mu shi ne mganin kowace matsala..Sannan Ina so ka aminta a maida yarinyar nan gida Saifuddeen"
Da Sauri ya kalli kawu cikin wani yanayi kafin yace"Gida kuma kawu..?
Meyasa zaka biye ma Iya..?
Kawu yace"Ba iya na Biye mawa ba abunda ya kamata na Duba..Yanzu zuwa zamu yi ka samu likita ya bamu sallamarta..Akwai in da zamu kai Matarka ina yakini da ikon Allah za"a samu waraka."
Saifudden sai yaji ya aminta da kawu sannan ya kasa mai gaddama ba wanda ya san me suka Tattauna ko me suka aikata an ga dai suna ta Shige da fice sannan kawu duk ya Tarkata mutane gida yace su koma su Jira su Mujaheed kadai a kabari da su Datti Har Sani ance ya koma gida ganin yanayinsa Matan kuma Daman sun Rikice da kuka.
Sai dare suka samu sallama shima ba yadda Likitocin zasu yi ne suna ta kokarin kada su Dauke muhibba Kawu yace zasu dauketa in da yuyuwar Dawowa zasu Dawo har Dr.Anandi sai da Dr.Isa ya kira ya fadamai ya Kira Saif ya na bashi baki da cewa cikin Satin nan zai bar Duk abunda yake yi ya Dawo Saboda Muhibba kada su kaita inda zata kara Rikicewa Saifudden ya aminta da mganarsa kawu ne ya Dage sai da aka basu sallama..
Ina barci aka Dawo dani gida,Sai dai kawai suka gansu sun shigo Dani a Shimfide su Iya sun Rude sun zata ma ko na mutu ne Domin halin da nake ciki ba wanda yayi Tunanin Tafiya sai da kawu yayi musu bayanin ina da Rai sannan kuma sun Dawo dani gidane akwai inda yake so a kaini.
Dakina a kai kaini aka shimfide kamar Mattaciya,Salla ma domin ya zama Dole ne kowa yaje ya Gabatar abinci kuma Anty Zeenatu ta Dafa da Taimakon kannenta kowa yaci ne mganin yunwa ba domin dadi ko kwanciyar Hankali ba.
Sai bayan an natsa ne Kawu yayi musu bayanin Dalilin dayasa aka Dawo dani gida Baba Surajo yace"Ni ina Tunanin a kaita gidan Hajiya yalwa mai mgani na nan gaya mana Alhaji"
Kawu yace"A"a ba nan zamu kaita ba Hajiya yalwa ai yar
bori ce."
Da Sauri Saifudden dake zaune gefe kusa da Mujaheed yace"Ba za"a kai min mata Wajen yar Bori ba kawu.."
Mama zuwaira ta aika mai da Dakuwa tana Fadin"Sannu mara kunya an ji matarkace..Nan kuma iyayenta ne da yan"uwanta."
Sai yayi shuru kansa na kasa Kawu yace"Kyalesa yana da gaskiya..Kinsan matsala kadan za"a samu ta kara rikicewa suma Likitocin abunda suke Gudu kenan..."
Iya tayi Tsaki tana Fadin"Yo likitoci ko makyaryata wazai biye mganar su."
Baba Jibril yace"Sufa kudi suke ci kawai anan wajen ammh ciwon Muhibba yafi karfin su wlh..Abu na jinnu ai sai malamai.."
Iya tace"Yo daman Allah na Tuba ina zasu iya yin wani abun sai dai kara Rikita yarinyar mutane"
Sai kowa ya fara Tofa albarkacin bakinsa,Kawu ne yace a Dakata ya gyara zama yana Fadin"In da nake so mu kai Muhibba wajen wani babban malamin addinin sunna ne..In na Fada sunanshi duk da ba anan garin yake ba wasu zasu san shi anan wajen."
Har hada baki akayi wajen Tambayan kawu waye shi kuma bai yi kauran baki ba yace"SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA dake garin Gumel"
Sai Dakin Inna ya Dauki Shuru Ummi tace" ban taba ganinsa ba ammh ina jin Labarinsa.
Mama zuwaira kuma tace"ni na taba ganinsa sau daya wani taron Saukar Qur'ani da Daliban wata makarantar islamiyan dakr kusa damu a kano da Dadewa ammh Dattakonsa bai bace min ba."
Kawu yace"Alhamdulillah naji Dadin jin haka Babban malami ne..Sannan malamin sunna ne ban sani ba ko yana taimakon irin haka ni dai kawai nafi natsuwa dashi din ne."
Sai Lokacin Inna ta sako baki
cikin Sanyin tace"Tunda haka ne sai ayi abunda ya kamata ta wacce hanya za'a samu Muhibba ta isa wajensa..?
Kawu ya gyara zama yana Fadin"Ta Hannun babban D'ansa Alhaji Sa"idu Gusai da muke cinikayar Dabbobi dashi Dayake suna da kargen Dabobbi muna Harkan kasuwanci dashi..Dazu da kuka ga ina waya dashi muke mgana Daman mun taba mganar dashi kwanaki na nuna mai muna neman Taimako sannan na Gayamasa Halin da yarinyar nan take ciki sai ya nuna min mallam baya bada mganin Aljanu ammh dai bazai ki taimaka mana ba in dai mukaje muka same sa da wasu sharwari ko kuma wata mafitar damu bamu hanga ba"
Kowa sai jinjina kai yake yi alamun gamsuwa Kawu ya cigaba da fadin"To Dazun mun yi mgana dashi yace yau da Daddare zai gayama mallam din yadda sukayi zuwa gobe da safe zai kirani in ya amince sai muje mu gansa da Muhibba din."
Gabadaya kowa ya amsa da Allah yasa adace
da alheri da waraka.
Sai aka fara Lissafin wadanda zasu tafi Kawu ya saka Iya aciki Saboda Kara ita kuma sai tace"A"a Sunusi ina ni ina doguwar Tafiya wannan ma bakaji Kafafuna ba sai dai cikin su Hashinmu gasu nan"
Baffa Hashimu yace ba sai sun je su kawun ma sun wadatar iya tace"Shikenan kuwa Fata dai adace da abunda ake nema"
Aka amsa da Ameen an Tsaida mganar In Tafiya ta yuyu Za'a tafi da Saifudden Sai Muhibba sai Ummi da Inna,Sai kawu sai Baba Surajo da ya Habibu,da Mujaheed Anty Habiba harda kuka tace sai taje da Sani akace sai yace shi ya Hakura ita taje jin haka yasa Adda Sadiya tace kafarta kafar mijinta Kawu da yace bazata je ba,Iya ta saka baki sannan aka amince da ita za"a tafi Gumel neman ma Muhibba mgani sai Fatan Allah yasa adace.
Adakin Muhibba mata matan suka kwana manya kuma suna Dakin Inna mazan kuma Hotel Saifudden da Mujaheed suka kama musu suka kwana.
Inda Allah ya taimaka ban farka ba Sai da Safe ina kuma Farkawa aka sake maidani Domin Dr.Isa ya Rubuta mgauguna aka siyamin kafin mu baro asibitin har har da na barci,suna Doramin na koma barci kamar mattaciya.
Sai wajen Tara na Safe su kawu suka Shigo gidan da albishrin din ceqa Mallam Yusus yace a kai masa Muhibba ya ganta.
Karyawa ma sama sama kowa yayi.Aka fara shirin Tafiya sai alokacin Inna tace bazata je ba Ya Habibu ya tafi ba wanda ya matsa mata sai aka kyaleta,Amotar Saifudden prado aka saka Muhibba da Ummi da Anty Habiba sai Kawu Saifuddeen yana Motar Mujaheed shi da Adda Sadiya da ya Habibu da Baba Surajo,Abban Walid da su khalifa sun zo da Safe suna gidan ma har muka Dauki Hanya su Iya ma suna ta shirin komawa Lere da mutanen Gaya Mama zuwaira dai zata zauna da Inna har mu Dawo ita da Goggo Naja Sauran kuma ba Dadewa suma suka kama Hanyar garuruwan su da Fatan Allah yasa adace makota sai shigowa suke yi suna yima Inna Fatan Allah yasa adace da mgani na Alheri.da Fatan Allah ya warware lamuran ciki harda Lami mahaifiyar Wasila da wasilan kanta da bata da aiki sai kuka Tana fadin"Innar mu Anty zata warke ko..?
Allah sarki Sabo turken wawa.
Allah ya riga ya karbi addu"arsu sun tafi inda za"a warware musu lamuran su inda Sirrin Boye zai bayyana Kaddaran Saifudden zai fito fili Sannan Muhibba zata fahimci komar data fada.
*Janafty*
*SFD0040*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
*DUTSE*
Gumel.